Daga Muhammad Annur Muhammad da Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Amma kafin nan, a madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza muke cewa kwana lafiya
An kama fiye da mutum 160 cikin wata biyu a Zimbabwe
Asalin hoton, Reuters
Sama da mutane dari da sittin ne aka kama a ƙasar Zimbabwe cikin watanni biyu da suka gabata, a yayin da kasar ke shirin karɓar baƙuncin taron ci gaban yankin a babban birnin ta Harare.
Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam ta Human Rights Watch da Amnesty International sun yi iƙirarin cewa sun bankaɗo yadda ake azabtar da wasu waɗanda aka kama, da suka haɗa da ƴan siyasa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago da kuma dailibai.
Akasarin kamen dai an dangata shi ne da zanga-zangar adawa da gwamnati ko kuma mara wa Jam'iyyun adawa baya.
Ecowas za ta buɗe wa Nijar, Mali da Burkina ƙofar komawa cikinta - Tinubu
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Shugaban ƙungiyar Ecowas, Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu - wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas - ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da janyo hankalin shugabannin mulkin sojin ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso domin koma cinkinta.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a Abuja lokacin da manyan hafsoshin tsaron ƙasashen yankin suka kai masa ziyara a fadarsa.
''Burin ƙungiyar Ecowas shi ne tabbatar da tsaro da inganta zaɓaɓɓun gwamnatocin da kuma kare su domin ciyar da yankinmu gaba'', in ji shugaban na Ecowas.
Shugaba Tinubu ya ce zamanin mulkinsa na jagorancin ƙungiyar ya gamu da gagarumin cikas, kasancewar mambobin ƙungiyar uku ne suka ɗauki matakin ficewa daga ƙungiyar.
''Don haka za mu yi duk mai yiwuwa domin janyo hankalinsu don su koma cikin wannan ƙungiya'', in ji shugaba Tinubu.
A baya-bayan nan ne dai ƙasashen uku suka ɗauki matakin ficewa daga ƙungiyar bayan da suka yi zargin cewa ƙungiyar ta kauce wa manufar da aka kafa ta a kai.
Sojojin Isra'ila sun ce sun kashe jami'in Hamas a wani hari da suka kai Lebanon
Sojojin Isra'ila sun tabbatar da kai wani hari ta sama kan wata mota da ke kusa da birnin Sidon na ƙasar Labanon inda suka kashe wani babban jami'in Hamas.
Rundunar ta IDF ta ce Samer al-Hajj ne ke da alhakin kai hare-hare kan Isra'ila daga Lebanon.
An san Al-Hajj a matsayin babban jami'in tsaron Hamas a El Helweh, sansanin Falasɗinawa mafi girma a Lebanon, wanda ke garin Sidon.
Harin Isra'ilar na baya-bayan nan na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin yankin ke ƙara ƙamari bayan da ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta yi barazanar kai wani babban harin ramuwar gayya bayan kashe babban kwamandan sojojinta a Beirut a makon jiya.
Mutum 62 sun mutu a hatsarin jirgin sama a Brazil
Asalin hoton, Alamy
Bayanan hoto, Jirgin Voepass ATR-72, iri ɗaya da wanda ya faɗin
Wani jirgi mai ɗauke da fasinjoji 62 ya faɗi a jihar Sau Paolo ta ƙasar Brazil.
Kawo yanzu dai ba a tabbatar da musabbabin hatsarin jirgin ba, da kuma ko akwai wanda ya tsira da ransa.
Jirgin dai ya taso ne daga yankin Cascaval na jihar Parana a kan hanyarsa ta zuwa filin saukar jiragen sama na Sao Paolo.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna lokacin da jirgin ke sulmuyowa ƙasa.
Tuni dai Shugaba Lula ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a hatsarin.
Kalli yadda ake aiko da labarin gasar Hikayata a aikace
A ranar 24 ga watan nan na Agusta za a rufe karɓar labarai a Hikayata, gasar ƙagaggun labarai ta mata zalla ta 2024.
A wannan bidiyon, za ku ga yadda za ku karanta ƙa'idoji da kuma turo labaranku a aikace, kamar yadda Nabila Mukhtar Uba ta nuna.
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Ambaliyar ruwa ta datse babban titin Kano zuwa Maiduguri
Asalin hoton, Bauchi State Gov
Ambaliyar da aka samu sakamakon mamakon ruwan sama ya yanke babban titin Kano zuwa Maiduguri a dai dai tsakanin ƙauyukan Malori da Guskuri a yankin ƙaramar hukumar Katagum da ke jihar Bauchi.
Ambaliyar ta datse tare da raba titin, da kuma haifar da ƙaton rami a tsakani, lamarin da ta tilasta wa matafiya sauya hanya.
Hotunan da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya mamaye kan titin, tare da kiran mafiya su sauya hanya.
Yayin da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, gwamnan Bauchi Sanata Bala Muhammad ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kawo wa titin ɗauki.
Gwamnan ya kuma bayyana muhimmancin titin wanda ke ɗaya daga cikin muhimman titunan da suka haɗa arewa maso gabashin ƙasar da sauran yankunan arewacin ƙasar.
Jihar Bauchi na ɗaya daga cikin jihohin arewacin ƙasar da ke fuskantar ambaliya a wannan shekara, lamarin da ya haifar da ɓarna mai yawa a wasu ƙananan hukumomin jihar.
Mali ta buƙaci jakadan Sweden ya fice daga ƙasar
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin ƙasar Mali sun umarci jakadan Sweden ya fice daga ƙasar nan da kwanaki uku.
Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta tabbatar wa BBC matakin.
Matakin na zuwa ne bayan ga gwamnatin Sweden ta ɗauki matakin kawo ƙarshen tallafin da take bai wa ƙasar.
A farkon wannan shekarar ne Sweden ta rufe ofishin jakadancinta a Bamako saboda taɓarɓarewar tsaro a Mali.
Mamallakin kantin sayar da kaya ta intanet ya fi kowa arziki a China
Mutumin da ya mallaki kantin Temu mai sayar da kayayyaki ta internet ya zama wanda ya fi kowa arziki a ƙasar China.
Colin Huang a yanzu ya mallaki fiye da dala biliyan 48.6, kamar yadda ƙididdigar mujallar Bloomberg mai tattara bayanai kan attajiran duniya ta bayyana.
Manhajar sayara da kayayyaki ta Temu ta kasance ɗaya daga cikin hanyoyin saye da sayarwa a duniya wanda ke da kayayyaki masu rahusa da kuma inganci.
A yanzu Mista Huang ya shiga gaban Zhong Shangshan, mai shagon sayar da abubuwan sha, wanda ya mamaye kasuwar kayan sanyi dandin lemuka a ƙasar ta China.
A shekarar 2022, Mista Huang - wanda tsohon ma'aikacin kamfanin Google ne - ya ƙaddamar da manhajar Temu.
Ukraine na faɗaɗa samame ta ƙasa a cikin Rasha
Asalin hoton, Reuters
Rahotanni daga yammacin Rasha na cewa Ukraine na ci gaba da faɗaɗa samame a yankin bayan kwashe kwana uku suna musayar wuta ta ƙasa a kan iyakar yankin Kursk.
Gwamnan yankin ya bayar da umarnin kwashe al'ummar kauyuka huɗu bayan abin da ya kira da gagarumin harin jirage marasa matuƙa na Ukraine.
Gwamnan ya shirya kwashe mutanen ne a bas-bas da kuma jiragen ƙasa.
Ya ce: "Mun cimma yarjejeniya da hukumar jiragen ƙasa ta Rasha. Yanzu haka jirage uku sun iso waɗanda za su kwashi mutum 2,400."
Rasha ta ce ta tura da dubban dakarunta da motoci masu sulke zuwa yankin.
Gwamnatin Najeriya ta dakatar da shirinta na sayar wa ma'aikata shinkafa mai rahusa
Asalin hoton, OTHERS
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dakatar da shirinta na sayar wa da ma'aikatan gwamnati buhun shinkafa mai nauyin kilogram 50 ko mai kwano 17, da ta sanar a baya a kan farashi mai rahusa - naira dubu 40.
Ma'aikatar ayyuka na musamman ce ta sanar da haka a wata takarda da ta fitar, ɗauke da sa hannun darektar kula da harkokin jama'a, Aderonke Jaiyesimi, mai kwanan wata, 2 ga watan Agustan 2024, kamar yadda jaridar Daily Trust ta labarto.
Sai dai takardar ba ta yi bayani kan dalilin da ya sa aka dakatar da shirin ba, ko ma an soke shi ne gabaɗaya ko kuma zuwa wani lokaci aka ɗage shi.
A shirin da aka sanar tun farko, a ranar 1 ga watan Agusta, 2024 ta wata takarda dama'aikatar da fitar, an buƙaci ma'aikatan gwamnati da ke son sayen shinkafar da su je shafin intanet na ofishin shugaban ma'aikata na tarayya su cike wata takarda.
Gwamanan jihar Oyo ya musanta maganar Shugaba Tinubu kan tallafin kuɗi ga jihohi
Asalin hoton, Seyi Makinde Facebook
Gwamanan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya musanta maganar da Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya yi cewa gwamnatin tarayyar ƙasar ta bai wa jihohi, sama da naira biliyan 570, domin tallafa wa jama'a
A jawabinsa na neman kwantar da hankalin al'ummar ƙasar da ke zanga-zangar tsadar rayuwa da rashin shugabanci na gari, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta raba kuɗin ga gwamnonin jihohin ƙasar 36 na ƙasar, domin sauƙaƙa wa jama'a matsin rayuwa.
Ƙari a kan waɗannan kuɗaden Shugaba Tinubu ya ce, gwamnatin tasa, ta kuma bai wa ƙananan harkokin kasuwanci 600,000 tallafi, sannan kuma akwai wasu ƙarin ƙananan sana'o'in 400,000 da za su amfana da tallafin su ma.
To amma Gwamnan na jihar Oyo, Seyi Makinde a wani saƙo da ya sanya a shafinsa na X,a jiya Alhamis, ya ce shi dai jiharsa ba ta san da wannan kuɗi da Tinubun ya ce gwamnatinsa ta raba wa jihohi ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnan ya ce yana mayar da martani ne kan maganar da wani ɗan jihar tasa ya yi kan iƙirarin gwamnatin tarayyar cewa ta bai wa jihohi sama da naira biliyan 570 domin tallafa wa jama'a kan ƙuncin rayuwa.
Mista Makinde ya ce, maganar na daga irin babtutuwan da gwamnatin tarayyar ke yi ne na faɗin abin da ba haka yake ba, yana mai ƙarin bayani da cewa : '' Kuɗaden da ake magana na daga cikin rancen bankin duniya na shirin NG-CARES, wanda kuɗi ne da ake tallafa wa jihohi wajen farfaɗowa daga annobar Korona, inda jiha za ta yi amfani da kuɗinta ta aiwatar da shirin, daga baya kuma bankin duniya ya mayar mata da kuɗin ta hanyar gwamnatin tarayya bayan bankin ya tantance abubuwan da jihar ta yi da nasarorin da ta samu.
Ya ce, '' Ya kamata ma fa a sani cewa kuɗin na bankin duniya bashi ne ga jihohi ba tallafi ba, saboda haka jihohi za su biya kuɗin.
Gwamnan ya ce jiharsa, Oyo, ta samu kuɗin ne, kashi biyu, inda a kashin farko aka ba ta naira biliyan 5.98, sannan a kashi na biyu ta samu naira biliyan 822.
''Saboda haka a taƙaice gwamnatin tarayya ba ta ba jihar Oyo wani kuɗi ba.
Makinde shi ne gwamnan jam'iyyar PDP, na biyu da ya soki Tinubu a kan jawabin a kwanakin nan.
Na farko shi ne Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da ya ce jawabin shugaban soki-burutsu ne kawai - ko holoƙo ne - hadarin kaka.
Tsadar rayuwa ta ƙaru da kashi 19 cikin ɗari a wata ɗaya a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta ce tsadar rayuwa a ƙasar ta ƙaru da kashi 19.2 cikin ɗari a watan Yuni na wannan shekara 2024, kaɗai, wanda hakan ya zarta ƙarin da aka samu a watan Mayu da ya gabata na naira 1,041.
Wannan yana ƙunshe ne a cikin sabon rahoton da hukumar ta fitar, na yawan kuɗin da yawancin mutane aƙalla za su kashe wajen sayen abinci mai gina jiki a rana, inda ƙaruwar ta kasance da naira 1,241 a watan na Yuni.
A watan na Yuni hauhawar farashin kaya da ayyuka ta ƙaru zuwa kashi 34.19 cikin ɗari, inda ta ƙaru da kashi 0.24 cikin ɗari idan aka kwatanta da hauhawar a watan Mayun 2024, kamar yadda hukumar ta nuna.
Wannan mizani da ake amfani da shi wajen kiyasin matsayin rayuwar jama'a a duniya, bai ƙunshi kuɗin sufuri da kuɗin haɗa abincin ba.
A cikin watan na Yuni tsadar rayuwar ta fi girma a yankin kudu maso yamma, inda take naira 1,545 a kan duk magidanci ɗaya a rana, yayin da a yankin arewa maso yamma take naira 956.
A matakin jihohi, Ekiti, ita ce ta fi ganin karuwar tsadar da naira 1,640, sai Ogun mai naira 1,599, sai kuma Osun mai naira 1,557.
Jihar da tsadar take kafi kankanta ita ce Katsina mai naira 878, sai Kano mai naira 926 sai kuma Jigawa mai naira 937
Idan kuwa ana maganar sashe ne to sashen kudu maso yamma ya fi ganin tashin tsadar rayuwar inda aka samu 1,545 a rana sai kuma yankin kudu maso kudu mai naira1,376.
Za a kammala aikin titin Abuja zuwa Kano a naira biliyan 280 cikin wata 14 - Minista
Asalin hoton, PR NIGERIA
Ministan ayyuka na Najeriya Sanata David Umahi ya ce, gwamnatin ƙasar za ta rinƙa biyan kamfanin Julius Berger naira biliyan 20 a duk wata domin kammala aikin sashen kilomita 82 na titin Abuja zuwa Kano, tsawon wata 14 nan gaba.
Ministan wanda ya bayyana haka a yayin ganawa da kamfanin domin sake duba dukkanin kwangilolin tituna da kamfanin ke yi, ya nuna damuwarsa kan ƙarancin kuɗi don kammala ayyukan da gwamnatinsu ta gada.
A game da titin na Abuja zuwa Kano, ministan ya buƙaci kamfanin da ya tsaya a kan aikin ɓangare ɗaya na titin, bayan ya kammala sai ya koma ɗaya ɓangaren.
Ministan ya kuma umarci kamfanin na Berger da cewa nan da mako uku ya cike dukkanin ramukan da ke titin da duwatsu domin magance matsalar rashin kyawun hanyar da masu motoci ke fama da ita.
Kamfanin ya kasa ragowar aikin gida huɗu kuma ya yi alƙawarin kammalawa duka cikin wata 14.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a wata sanarwa da, jami'in yaɗa labarai na ministan, Orji Uchenna Orji, ya fitar, ya ce ayyukan titunan sun haɗa da na Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano, da kashi na biyu na titun Legas zuwa Ibadan da Gadar Anacha ta biyu, sai kuma gadojin da ke jihar Legas - Gadar Third Mainland, da Gadar Iddo da kuma Gadar Carter.
Rasha na fama kan yadda za ta kare kanta daga hare-haren Ukraine
Asalin hoton, OTHERS
Rahotanni daga yammacin Rasha na cewa Ukraine na ci gaba da faɗaɗa hare-hare a yankin bayan kwashe kwanaki uku na musayar wuta ta ƙasa a kan iyakar Kursk.
Gwamnan yankin ya bayar da umarnin kwashe al'ummomin ƙauyuka huɗu bayan abin da ya kira da gagarumin harin jirage marassa matuƙa na Ukraine.
Gwamnan ya shirya kwashe mutanen ne a motocin bas da kuma jiragen ƙasa.
Ya ce sun cimma yarjejeniya da hukumar jiragen ƙasa ta Rasha.
Yanzu haka jirage uku sun isa can, inda za su kwashi mutum 2400.
Rasha ta ce ta tura da dubban dakarunta da motoci masu sulke zuwa yankin.
Donald Trump da Kamala Harris za su yi muhawara
Asalin hoton, Getty Images
Donald Trump da Kamala Harris sun amince da ranar da za su yi muhawara ta farko a gidan talabijin din ABC,inda suka ce za a gabatar da muhawarar a ranar 10 ga watan Satumba.
Hakan na zuwa ne bayan da Mista Trump ya ce a shirye yake ya yi muhawara da abokiyar karawar tasa ko sau nawa ne kafin zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a watan Nuwamba.
Trump ce dole ne sai ɗaya ɓangaren ya amince da sharuɗɗan muhawarar, ''ban sani ba ko za su amince, ba ta iya tattaunawa da ƴan jarida saboda haka da ƙyar ta iya.
Ms Harris, mataimakiyar shugaban Amurka Joe Biden ta samu takarar ta jam'iyyarta ta Democrat a zaɓen da za a yi a watan Nuwamba bayan da Mista Biden ya haƙura da takarar saboda matsin lambar jiga-jigan 'yam'iyyar tasa, ta tabbatar da cewa za ta halarci muhawarar.
Kotu a Amurka ta samu tsohon ministan kuɗi na Mozambique da laifin zamba
Asalin hoton, AFP
Wata kotu a Amurka ta samu wani tsohon ministan kuɗin Mozambique da laifin haɗa baki shekaru goma da suka gabata da ya janyo matsalar tattalin arziƙi a ƙasarsa.
An samu Manuel Chang da laifin karɓar wasu kuɗaɗe ta bankunan Amurka da sunan bashi cikin sirri waɗanda aka nuna cewa za a biya wasu tarin jiragen kamun kifi da wasu sauran ayyuka.
Sai dai an yi sama da faɗi da rancen da aka karɓa tare da barin Mozambique da bashin sama da dala biliyan biyu.
An kama Chang ne a Afrika ta Kudu, inda aka wuce da shi Amurka domin fuskantar shari'ar zamba cikin aminci da cin hanci da rashawa.
Za a yanke masa hukunci nan gaba da zai iya kaiwa zaman gidan yari na shekara ashirin.
Jami'an tsaro na ƙara zama cikin shiri kan tarzomar Birtaniya
Asalin hoton, PA Media
Gwamnatin Birtaniya ta shirya sosai domin fuskantar yuwuwar ƙarin tarzoma a ƙarshen wannan makon, kamar yadda wani minista ya sheda wa BBC.
Nick Thomas-Symonds ya ce a shirye suke su fuskanci duk wani abu da ka iya tasowa, bayan da Firaminista Keir Starmer ya umarci 'yansanda su kasance cikin cikakken shiri.
A halin da ake ciki kuma a yau Juma'a ne za a sake yanke wa karin mutanen da aka kama da laifin tayar da hankali a lokacin tarzomar ta tsawon mako daya hukunci a kotu.
Shi kuwa Magajin garin birnin Landan Sadiq Khan ya buƙaci gwamnati da ta sake nazari a kan dokokin amfani da shafukan sada zumunta da muhawara, yana mai cewa sababbin dokokin da aka yi ba su dace ba.
Mutum aƙalla 140 aka tuhuma da laifin tayar da husumar, inda tuni aka yanke wa sama da 12 hukunci, kuma daga ckin mutum 116 da aka tuhuma 110 mata ne.
Tarzomar ta ɓarke ne bayan wasu 'yan mata uku da aka daɓa wa wuƙa a, tarzomar da ta kasance mafi muni a sama da shekara goma a Birtaniya.
Labaran karya da ake yadawa a intanet su ne suka ƙara rura wutar tarzomar da masu kyamar baƙi da tsattsauran ra'ayin riƙau na kishin fararen fata suke yi.
Kusan mutum 500 aka kama, inda aka tuhumi kusan 150 daga cikinsu a garuruwa da birane a faɗin Ingila da Irealnd ta Arewa
Amurka da Masar da Qatar sun nemi Hamas da Isra'ila su koma tattaunawar zaman lafiya
Asalin hoton, Getty Images
Ƙasashen Amurka da Masar da Qatar sun fitar da sanarwar haɗin guiwa, inda suka yi kira ga Isra'ila da Hamas da su koma teburin tattaunawa domin tsagaita wuta tare da sakin waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza.
Sanarwar ta ce an tanadi abin da yarjejeniyar ta ƙunsa abin da kawai ya rage shi ne matakan da za a bi wajen aiwatarwa.
Isra'ila ta amince za ta halarci zaman a Doha ko a Alƙahira, sai dai Hamas ba ta ce komai kan hakan ba.
Batun cimma sabuwar yarjejeniyar diflomaisyyar na zuwa ne bayan da zaman ɗar-ɗar ya ƙaru a yankin na Gabas ta Tsakiya sakamakon kashe shugaban Hamas Isma'il Haniyeh a Tehran.
Hamɓararriyar firaministar Bangladesh ta ce za ta koma ƙasar
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan tsohuwar firaministar Banglaesh, Sheikh Hasina, ya shaida wa kafar watsa labaran Indiya cewa mahaifiyarshi na shirin komawa ƙasar bayan sabuwar gwamnatin riƙon-ƙwarya ta tsayar da lokacin da za ta gudanar da zaɓe.
Sheikh Hasina, ta sauka daga muƙaminta tare da tserewa maƙwabciyar ƙasar Indiya a ranar Litinin bayan kwashe makonni ana zanga-zangar ƙin mulkinta.
An rantsar da gwamnatin riƙon ƙwaryar da Muhammad Yunus wanda ya taɓa samun kyautar Nobel ta zaman lafiya zai jagoranta a jiya Alhamis.
An kashe mutum sama da 400 a tarzomar da aka yi fama da ita a kasar, kafin hasina ta tsere, kuma yawancin wadanda suka mutu farar hula ne da jami'an tsaro suka harbe, to amma kum har da 'yansanda a cikin wadanda suka rasu.
Tarzomar ta kasance rikici mafi muni da aka zubar da jini wanda ba a taba yi ba, tun bayan yakin da ya ki kasar ga samun 'yancin kai a 1971.