Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya, 16/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Badamasi Abdulkadir Mukhtar, Aisha Aliyu Ja'afar, Rabiatu Runka

  1. Ana ci gaba da aikin ceto a tsibirin Mayotte

    An gaggauta tura dakarun Faransa da ma'aikatan ceto da na agaji zuwa Mayotte ta jirgin sama da na ruwa domin taimaka wa mutane da mahaukaciyar gugguwa ta afkawa, irinta mafi muni a cikin karni, a yankin da ke tekun Indiya.

    Guguwar da aka yi wa lakabi da Chido ta yi kaca-kaca da tsibirin a ranar Asabar, sannan ana fargabar daruruwan mutane sun mutu.

    Wakilin BBC ya ce Layukan lantarki da na sadarwa sun katse, sannan tittuna da filin jirgin sama da asibitoci da gine-gine da dama sun lalace.

    Mazauna yankin na ta kuka da yanayin da suka tsinci kansu na rashin abinci da ruwan sha da sauran muhimman abubuwan bukatun yau dakullum

  2. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa barkanmu da safiyar Litinin.

    Sannun mu da sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku rahotannin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Ku biyo mu a shafukan sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.