Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gasar kofin duniya 2026: Mbappe ya yaga ɓarakar Senegal

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Matakin rukuni
France 3 , Senegal 1 at Full time
Faransa
Senegal
Full time
Hutun rabin lokaci Faransa 0 , Senegal 0

Key Events

Faransa

  • K. Mbappé Goal 66 minutes, Goal 90 minutes plus 6
  • B. Barcola Goal 82 minutes

Senegal

  • I. Mbaye Goal 90 minutes plus 5
Ba da ƙwallo a ci
Faransa,M. Olise (66 minutes), A. Rabiot (82 minutes)
Senegal,I. Ndiaye (90 minutes plus 5)

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon AI

  1. , Faransa 0-0 Senegal

    Yanzu dai Faransa suna takurawa Senegal, sun danno sosai, amma ba wata matsala daga Senegal.

  2. , Faransa 0-0 Senegal

    Kalidou Koulibaly ya yi kuskuren bai wa Kylian Mbappe kwallo, wanda nan da nan ya bai wa Ousmane Dembele, sai dai ta yi masa yawa.

    Nan da nan Edouard Mendy ya fito ya kama.

  3. , Faransa 0-0 Senegal

    An yi wa Doue keta, amma nan da nan ya tashi ya ci gaba da wasan da har yanzu ba a kai wani mummunan hari ba.

  4. , Faransa 0-0 Senegal

    Wani mummunan kuskure da Aurelien Tchouameni ya kusan barin Senegal ta ci kwallo, amma Mike Maignan ya fito da kwarin gwiwa ya bata ta.

  5. , Faransa 0-0 Senegal

    Ismaila Sarr ya ja kwallon da ya samu daga wajen Nicolas Jackson, sai dai Dayot Upamecano ya tarar da shi ya kuma yi cikas.

  6. , Faransa 0-0 Senegal

    An yi wa Sadio Mane keta, amma ba a bayar da katin gargadi ba, ketar ba ta da muni.

  7. , Faransa 0-0 Senegal

    Senegal ta samu bugun kusurwa, ta kuma buga babu wata matsala, alkalin wasa ya busa, saboda mai tsaron ragar Faransa yana kasa da gwiwa biyu.

  8. An fara wasan, yanzu sai mai rabo, Faransa 0-0 Senegal

    Filin wasa ya dinke da yan kallo, saboda karawar tana da mahimmaci tsakanin tawaga daga Turai da ta Afirka.

  9. , France v Senegal

    Tawagar Faransa ta saka riga mai ruwan bula da farin wanda da jar safa.

    Ita kuwa Senegal ta sanya farar riga da wando kore da kuma farar safa.

  10. , France v Senegal

    Yan wasa sun fito cikin fili daga nan za a rera taken kasashen sai a take leda zuwa minti 45 daga cikin za a yi hutn shan ruwa.

  11. , France v Senegal

    Ko Kylian Mbappe zai taka rawar gani a wasan yau kuwa?

  12. Tun bayan da Senegal ta fice daga gasar Kofin Duniya ta 2022 a Qatar a zagayen ƴan 16, tawagar ta Teranga ba ta sha kashi ba a wasa 30 a jere tun daga lokacin.

    Abin lura shi ne, wannan ƙididdigar ba ta haɗa da wasan ƙarshe na AFCON mai cike da cece-kuce ba.

    Wannan tarihi na nuna irin ƙarfi da zama a kan ganiya da Senegal ke ciki, lamarin da zai sa Faransa ta shiga wasan cikin taka-tsantsan.

    Senegal za ta shiga wannan wasa da kwarin gwiwa, tana fatan ci gaba da wannan gagarumin tarihin rashin shan kashi, yayin da take neman sake gdoke Faransa a babbar gasar cin kofin duniya.

  13. Allah ya jikan maza

    Senegal ta yi nasara a kan Faransa a gasar cin kofin duniya a 2002.

    Papa Bouba Diop ne ya ci kwallon a birnin Seoul shekara 24 da ta wuce.

    Tsohon dan wasan Fulham da Portsmouth da West Ham da kuma, ya mutu a cikin shekarar 2020 yana da shekara 42.

  14. , France v Senegal

    Manhattan ta zama dan karamin birnin Faris

  15. Faransa ta kai hari, France v Senegal

  16. Ko za a iya kiran Senegal zakarun kofin nahiyar Afirka?

    Senegal ce ta lashe kofin zakarun Afirka da Morocco ta shirya wasannin.

    Sai dai an buga wasan karshe mai cike da rudani, inda Senegal ta yi nasarar doke Morocco ta lashe kofin.

    Daga baya Morocco ta shigar da kara hukumar kwallon kafar Afirka, wadda ta yanke hukuncin karbe kofin daga Senegal ta bai wa Morocco.

    Yanzu haka Morocco ce mai rike da kofin Afirka Afcon.

  17. Komai ya yi farko yana da karshe, France v Senegal

    Bayan kusan shekara 14 yana jagorantar tawagar Faransa, gasar Kofin Duniya ta 2026, za ta kasance ta ƙarshe a wajen kocin Faransa, Didier Deschamps.

    Deschamps na ɗaya daga cikin mutane uku kacal da suka lashe Kofin Duniya a matsayin ɗan wasa da kuma koci. Shi ne kyaftin ɗin Faransa lokacin da suka lashe gasar a shekarar 1998, sannan ya sake jagorantar ƙasar zuwa daukar kofin a shekarar 2018 a Rasha.

    A wannan bazarar, Deschamps na ƙoƙarin kafa wani tarihi na musamman, inda yake neman zama mutum na biyu, bayan kocin Italiya, Vittorio Pozzo, wanda ya lashe Kofin Duniya sau biyu a matsayin koci.

    Shin Deschamps zai iya yin bankwana da tawagar Faransa cikin ɗaukaka ta hanyar sake ɗaga kofin duniya karo na biyu?