Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 23/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 23/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Umar Mikail

  1. Gwamnatin Neja ta rufe duka makarantun jihar

    Gwamnatin jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya ta sanar da rufe duka makarantun da ke faɗin jihar sakamakon sace wasu ɗaliban makarantar St. Mary mai zaman kanta a garin Papiri na karamar hukumar Agwara.

    Gwamnan jihar Umaru Bago ne ya sanar da haka yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Minna, fadar gwamnatin jihar.

    Matakin na zuwa ne bayan rufe makarantun a jihohin Filato da Katsina.

    Umaru Bago ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da ceto ɗaliban tare da maido su cikin kwanciyar hankali.

    Gwamnan ya kuma bayyana lamarin da ''abin takaici da bakin ciki, da ya girgiza al'ummar jihar''.

  2. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki, musamman Najeriya da maƙwabtan ƙasashe.

    Ku buiyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawa kan labaran da muke wallafawa.