Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 23/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 23/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi.

    Za mu kawo wasu sababbi gobe da sasfe.

  2. Tinubu ya ba da umarnin janye 'yansanda daga gadin manyan mutane

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin janye dakarun 'yansanda daga gadin manyan mutane domin mayar da su aikin tsaro.

    Tinubu ya bayar da umarnin ne yayin ganawar da ya yi da shugabannin tsaron ƙasar a yammacin yau Lahadi, ciki har da Sufeto Janar na "Yansanda s Kayode Egbetokun.

    "Umarnin fadar shugaban ƙasa ya ce daga yanzu duk mutumin da ke son jami'an tsaro su yi gadinsa sai dai ya nemi jami'an tsaron Nigeria Security and Civil Defence Corps," a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar.

    "Sassan Najeriya da dama, musamman a karkara, ba su da isassun 'yansanda, abin da ke ƙara ta'azzara aikin tsaron al'umma."

  3. Isra'ila ta ce ta kashe jami'in Hezbollah Haytham Tabatabai a Lebanon

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kashe babban jami'in ƙungiyar Hezbollah Haytham Ali Tabatabai a wani hari da ta kai Beirut babban birnin Lebanon.

    Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce aƙalla mutum biyar aka kashe a harin tare da raunata wasu 28.

    Wannan ne karon farko da Isra'ila ta kai hari Beirut cikin wata ɗaya.

    Kawo yanzu babu wata sanarwa mai tabbatar da iƙirarin na dakarun Isra'ila, ko daga Hezbollah ko kuma daga gwamnatin Lebanon.

  4. Tinubu na ganawa da shugabannin tsaron Najeriya

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu na ganawa da shugabannin tsaron ƙasar a fadarsa da ke Abuja, yayin da 'yanfashi ke riƙe da ɗalibai fiye da 300 da suka yi garkuwa da su a sassan ƙasar.

    Cikin mutanen da Tinubun ke ganawa da su akwai babban hafsan tsaron ƙasa, da hafsan sojan ƙasa, shugaban tattara bayanan sirri, da babban sufeton 'yansanda, da shugaban hukumar DSS.

    "Muna samun bayanan abubuwan da ke faruwa da kuma ɗaukar matakan dawo da zaman lafiya a wuraren da lamarin ya shafa, da kare 'yan ƙasa," a cewarsa cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ɗauke da hotunansa tare da shugabannin tsaron.

    Tun da farko, Tinubu ya sanar da ceto masu ibada 38 da 'yanbindiga suka sace a wata cocin jihar Kwara, da kuma gano ɗalibai 51 cikin 315 da aka sace daga wata makaranta a jihar Neja.

    Sai dai zuwa yanzu babu wani bayani game da ɗalibai mata 23 da ke hannun 'yanbindiga bayan sace su daga sakandaren gwamnati a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin ƙasar ranar Litinin.

  5. 'Yanbindiga sun kashe 'yansanda biyar a jihar Bauchi

    Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Bauchi da ke arewacin ƙasar ta sanar da kashe jami'anta biyar yayin wani kwanton ɓauna da 'yanbindiga suka yi musu.

    Wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Ahmad Wakil, ya fitar ta ce dakarun na kan aikin tabbatar da zaman lafiya a rikicin manoma da makiyaya a ƙauyen Sabon Sara na ƙaramar hukumar Darazo lokacin da lamarin ya faru.

    Ya ƙara da cewa wasu jami'an biyu sun ji raunuka, yayin da dakarun suka yi nasarar kashe 'yanbindigar da dama.

    "Abin baƙin ciki, kwanton ɓaunar ya yi sanadiyyar mutuwar jami'ai kamar haka: DSP Ahmad Muhammad (SID), ASP Mustapha Muhammad (10 PMF), Sufeto Amarhel Yunusa (10 PMF), Sufeto Idris Ahmed (10 PMF), Kofur Isah Muazu (AKU).”

  6. Labarai da dumi-dumi, Tinubu ya sanar da ceto mutum 38 da aka sace a cocin jihar Kwara

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da ceto masu ibada 38 da 'yanbindiga suka yi garkuwa da su a cocin Eruku da ke jihar Kwara.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya kuma tabbatar da kuɓutar ɗalibai 51 cikin 315 da aka sace a jihar Neja.

    "Godiya ga jami'an tsaronmu a 'yan kwanakin nan, an ceto dukkan masu ibada 38 da aka yi garkuwa da su a Eruku na jihar Kwara," in ji shi. Sai dai ba yi ƙarin bayani ba kan yadda aka ceto su.

    "Ina ci gaba da bin halin da ake ciki kan yanayin tsaro a ƙasa baki ɗaya kuma ana ba ni bayanai akai-akai daga inda abubuwan ke faruwa," in ji shi.

    "Haka nan, ina mai farin ciki cewa an gano 51 daga cikin ɗaliban makarantar Catholic School ta jihar Neja."

    Tun da farko, ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya ta ce ɗaliban sun gudu ne daga hannun masu garkuwar tsakanin Juma'a da Asabar bayan sace su ranar Alhamis da dare.

  7. Trump ya zargi jagororin Ukraine da 'rashin godiya'

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya zargi Ukraine da ''rashin godiya'' dangane da ƙoƙarin da Amurka ke yi na kawo ƙarshen yaƙin da take yi da Rasha.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Mista Trump ya ce "Shugabannin Ukraine ba sa nuna godiya kan ƙoƙarinmu da kuma ci gaba da sayen mai da Turai ke yi daga Rasha''.

    "Na gaji yaƙin da bai kamata ma a ce ya faru ba, yaƙi ne da ya wahalar da kowa, musamman miliyoyin mutanen da suka mutu.''

  8. An kammala taron G20 a Afirka ta Kudu

    An kammala taron ƙungiyar G20 ta ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki da aka gudanar a Birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.

    Shugaban Afirka ta Kudu, mai masaukin baƙi, Cyril Ramaphosa ya ce shugabannin ƙungiyar sun sake nanata jaddada ƙudirin ''aiki tare''.

    An amince da ƙudirin magance sauyin yanayi, duk kuwa da adawa da hakan da Amurka ta nuna ta hanyar ƙaurace wa taron.

    Fadar White House ta zargi gwamnatin Afirka ta Kudu da mayar da shugabancin G20 makamin yaƙi, tana mai cewa za ta gyara hakan a shekara mai zuwa lokacin da Amurka za ta karɓi shugabancin ƙungiyar, wanda na karɓa-karɓa ne.

    Amurka ta ƙaurace wa taron ne bayan da Shugaba Trump ya yi iƙirari ''maras hujja'' cewa Afirka ta Kudu na muzguna wa tsiraru fararen fata a ƙasar.

  9. Labarai da dumi-dumi, Ɗaliban Neja 50 sun kuɓuta daga hannun ƴanbindiga - CAN

    Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya, (CAN) ta ce ɗalibai 50 cikin fiye da 300 da ƴanbindiga suka sace a makarantar kwana ta St. Mary da ke jihar Neja sun kuɓuta.

    Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Lahadi, ta ce ta samu labarin kuɓutar ɗaliban, waɗanda ta ce tuni aka sada su da iyayensu.

    CAN ta ce ɗaliban sun kuɓuta takanin ranakun Juma'a da Asabar.

    A ranar Lahadi da daddare ne wasu ƴanbindiga suka far wa makarantar da ke garin Papiri, lokacin da ɗaliban ke barci tare da sace fiye da 300 kamar yadda CAN ɗin ta bayyana.

  10. Ana zargin ƴar tsohon shugaban Afirka ta Kudu da tura ƴanƙasar su yi wa Rasha yaƙi a Ukraine

    Babbar ƴargidan tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jocob Zuma - ta shigarta da ƴar'uwarta ƙara kan zarge-zargen aikata manyan laifuka, saboda zarginta da hannu wajen ɗaukar wasu matasa ƴan Botswana da Afirka ta Kudu don yi wa Rasha yaƙi a Ukraine.

    Mai shigar da ƙorafin, Nkosazana Dlamini-Mncube ta yi iƙirarin cewa ƴar'uwarta, Duduzile Zuma-Sambudla, wadda a baya ƴar majalisa ce tare da wasu mutum biyu sun kitsa yadda wasu mutum 20 suka tafi Rasha a watan Yuli ƙarƙashin wani shirin basaja na horas da jami'an da ke tsaron jam'iyyar mahaifinsu.

    Ms Dlamini-Mncube ta ce mutanen sun bi ta Dubai kafin su isa Rasha, inda suka sanya hannu kan kwantiragin aikin soja da aka rubuta da harshen Rasha, aka kuma ba su kayan sojoji tare da aikata su filin daga ba tare da saninsu ba.

    Kakakin rundunar ƴansandan Afirka ta Kudu, Brigadier Athlenda Mathe ya ce rundunar ta ƙaddamar da gagarumin bincike game da lamarin.

  11. Fafaroma ya buƙaci ƴanbindiga su saki ɗaliban Najeriya

    Fafaroma Leo XIV ya buƙaci ƴanbindigar da suka sace ɗalibai fiye da 300 na makarantar St. Mary da ke Naja, su gaggauta sakinsu.

    Yayin da yake jawabi bayan kammala taron ibada a dandalin Peter da ke birnin Roma, jagoran ɗariƙar katolikan na duniya ya ce satar ɗaliban ''abin takaici ne ga waɗanda aka sacen da kuma iyalansu''.

    “Ina kira cikin kaɗuwa da babbar murya a gaggauta sakin waɗannan yara,'' in ji Fafaroman.

    Ya kuma yi kira ga hukumomin Najeriya su ɗauki matakan tabbatar da sakin su.

    A ranar Alhamis da daddare ne dai wasu mahara ɗauke da makamai suka far wa makarantar kwana da St. Mary da ke garin Papiri a jihar Neja tare da sace ɗalibai fiye da 300 da wasu malamai.

  12. Gwamnatin Kebbi ta rufe duka makarantu da ke jihar

    Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da rufe duka makarantun jihar na gwamnati da masu zaman kansu.

    Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da Kwamishinan ilimi mai zurfi jihar, Alhaji Issa Abubakar-Tunga, da takwararsa ta ilimi a matakin farko, Dokta Halima Bande suka fitar, sun ce matakin ya kunshi makarantun sakandire da na gaba da sakandire da ke faɗin jihar.

    Sanarwar ta ce matakin ya zama wajibi sakamakon samun matsalar hare-hare cikin wasu sassan jihar a baya-bayan nan.

    Matakin ya shafi duka manyan makarantun jihar, in ban da kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma da ke binrin Kebbi, babban birnin jihar, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

    Gwamnatin ta ce za ta sanar da ranar sake buɗe makarantun nan gaba idan al'amura suka daidaita.

  13. 'Wakilan Hamas na Masar domin ganawa da masu shiga tsakani'

    Rahotonni a cewa wakilan Hamas na birnin Alqahira na ƙaar Masar domin ganawa da masu shiga tsakani kan yaƙin Gaza.

    Wata majiyar ƙungiyar ta ce wakilan za su tattauna kan abin da suke gani a matsayin ci gaba da saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta daga ɓangaren Isra'ila.

    Jami'an lafiya a Gaza sun ce fiye da mutum 20 aka kashe ta hanyar hare-haren Isra'ila ta sama a ranar Asabar.

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce an kai harin ne bayan da wani ɗan Hamas ya far wa sojojin Isra'ila a yankin da sojojin ƙasar ke iko da su a Gaza.

    Mista Netanyahu ya ce an kashe wasu manyan kwamandojin Hamas biyar a harin.

    Haka ma Isra'ila ta zargi Hamas saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wutar.

  14. An gudanar da zanga-zangar adawa da muzguna wa mata a Faransa

    Dubban mutane ne suka shiga zanga-zanga a Paris da sauran biranen Faransa domin nuna adawa da muzguna wa mata a ƙasar.

    Aƙalla ƙungiyoyi 60 ne suka goyi bayan zanga-zangar, wadda ke buƙatar samar da muhimman dokokin yaƙi da cin zarafi da muzguna wa mata tare da samar da wani asusun tallafa wa ƙungiyoyin da ke taimaka wa waɗanda aka zalunta.

    Masu zanga-zangar sun riƙe alluna da ke ɗauke da saƙonnin kiraye-kiraye daban-daban, ciki har da waɗanda ke cewa ''A cikin kowane kwana biyar da wuni guda, namiji na kashe mace ɗaya''.

    Haka kuma akwai wanda ke ɗauke da saƙon ''Tara cikin mata 10 da aka yi wa fyaɗe, sun san waɗanda suka yi musu''.

  15. Ana ci gaba da neman ɗaliban da aka sace a makarantun Najeriya

    Jami'an tsaron Najeriya na ci gaba da neman ɗaliban da ƴanbindiga suka sace a makarantunsu cikin makon da ya gabata.

    A ranar Alhamis da daddare ne wasu mahara suka sace ɗalibai fiye da 300 a makarantar kwana ta garin Papiri na jihar Neja kwana biyar da sace ɗaliban jihar Kebbi.

    Wannan al'amari ya janyo firgici da razani a ƙasar, lamarin da ya sa wasu jihohi masu maƙwabtaka suka ɗauki matakin rufe makarantunsu.

  16. Rubio ya isa Geveva don tattauna kawo ƙarshen yakin Ukraine

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya isa birnin Geneva na ƙasar Switzerland domin tattauna batun kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.

    Shi ma babban mashawarcin tsaro na Birtaniya, Jonathan Powell ya kama hanyar Geneva daga taron G20 da yake halarta a Afirka ta Kudu.

    Ana sa ran wakilai daga Turai da Ukraine za su halarci taron na yau.

    An jima kaɗan ne ake sa ran tattaunawa tsakanin Shugaba Trump da Firaministan Birtaniya, Kier Starmer ta waya.

  17. Amurka da Ukraine da ƙasashen Turai za su gana a Geneva don kawo ƙarshen yaƙin Ukraine

    Wakilai daga ƙasashen Amurka da Ukraine da ƙawayenta na Turai za su halarci tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Ukraine a Geneva.

    Taron na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da wani daftari mai ƙunshe da ƙudurori 28 na kawo ƙarshen yaƙin, waɗanda Shugaba Putin na Rasha ya ce suna iya zama mafarin tattaunawar.

    Ƙudurorin sun haɗa da janyewar dakarun Ukraine daga wasu yankunan gabashin ƙasar, da haƙura da wasu yankunan ƙasar da ake yaƙi a kansu.

    Shugaba Zelensky na Ukraine ya yi gargaɗin cewa ƙasarsa ka iya shiga ''ɗaya daga mawuyacin hali a tarihi'', yayin da Trump ke matsa masa lambar amincewa da yarjejeniyar.

    Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar ranar Asabar a wurin taron G20, ƙawayen Ukraine sun ce ba su amince da daftarin na Trump ba.

  18. Al'ummar Guinea-Bissau na zaɓen sabon shugaban ƙasa

    A yau Lahadi ne al'ummar Guinea-Bissau ke kaɗa ƙuri'a domin zaɓen sabon shugaban ƙasar.

    Mutum 12 ne ke fafatawa a zaɓen, ciki har da shugaban ƙasar, Umaro Sissoco Embalo da ke neman wa'adin mulki na biyu.

    Sai dai an haramta wa tsohon firaministan ƙasar, Domingos Simoes Pereira takara - da ake ganin shi ne zai iya zama babban ɗan takarar hamayya.

    To amma ya umarci magoya bayansa su mara wa Fernando Dias na jam'iyyar Socila Renewal, baya a zaɓen.

    Ƴan ƙasar da dama na son mutumin da zai yi nasara a zaɓen ya magance musu matsalolin talauci da tattalin arziki tare da samar da ayyuka ga ɗimbin matasan ƙasar.

    Guinea-Bissau - da ke yankin Yammacin Afirka, mai yawan jama'a, fiye da miliyan biyu ta jima tana fama da rikicin siyasa, inda aka riƙa samun yunƙurin juyin mulki.

  19. Gwamnatin Yobe ta rufe duka makarantun kwana a jihar

    Gwamnatin jihar Yobe ya bayar da umarnin rufe duka makarantun sakandiren kwana da ke faɗin jihar saboda barazanar tsaro.

    Cikin wata sanarwa da babban darakta yaɗa labaran gwamnan jihar, Mamman Mohammed ya fitar ya ce gwamnatin ta ɗauki matakin ne domin kare ɗaliban da ke makarantun kwana.

    Matakin na zuwa ne bayan da a makon da ya gabata wasu ƴanbindiga suka sace ɗalibai a makarantun kwana jihohohin Naje da Kebbi.

    Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bayan taron ƙoli na tsaron jihar da Gwamnan Mai Mala Buni ya jagoranta, domin nazarin tsaron makarantu a wasu sassan ƙasar.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa matakin rufe makarantun ya fara aiki ne nan take, har zuwa lokacin da yanayi zai inganta.

    Hare-hare kan ɗalibai a makarantu a Najeriya cikin makon da ya gabata, ya haifar da rufe makarantun a wasu jihohin ƙasar da suka haɗa da Neja da Filato da Katsina.

  20. An kammala taron sauyin yanayi na duniya COP30 a Brazil

    An kammala tarom sauyin yanayi na duniya wato COP30 da aka gudanar a birnin Belém na ƙasar Brazil.

    Taron ya amince da ninka kuɗaɗen da ake bai wa ƙasashe masu tasowa da kusan ninki uku.

    To amma taron ya kasa cimma matsaya daina amfani da makamashin da ke gurɓata muhalli.

    Saɓanin da aka samu daga wajen ƙasashe masu albarkatun mai - da Saudiyya ke jagoranta - ya janyo rashin cimma matsayar ba, wani abu da ya danne ƙoƙarin ƙasashe fiye da 80.

    Ƙasar Kolombiya ce dai ta jagoranci ƙoƙarin dakatar da taron dangane da rashin cimma matsayar kan makashin da ke gurɓata muhallin.