Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/04/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/04/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Isiyaku Muhammed

  1. Al'ummar Gabon na zaɓen sabon shugaban ƙasa

    An buɗe rumfunan zaɓe a Gabon, yayin da al'ummar ƙasar za su zaɓi sabon shugaban ƙasar, kusan shekara biyu bayan juyin mulkin da ya hamɓarar da tsohon shugaban ƙasar Ali Bongo.

    Shugaban gwamnatin mulkin sojin ƙasar, Brice Oligui Nguema - wanda ya alƙawarta miƙa mulki ga farar hula - na daga cikin mutanen da ke takarar, kuma alamu na nuna cewa shi ne zai yi nasara a zaɓen.

    Yana fafatawa da wasu ƴantakara bakwai, ciki har da tsohon firaministan ƙasar, Alain Claude Bilir-By-Nze.

    Juyin mulkin da ka gudanar a ƙasar - da ke tsakiyar Afirka - a 2023, ya kawo ƙarshen mulkin iyalan Bongo na kusan shekara 60 a ƙasar.

  2. Dala ta yi mummunar faɗuwa saboda harajin Amurka

    Darajar dalar Amurka ta yi faɗuwar da ba a taɓa gani ba cikin shekara uku a kan kuɗin euro a ranar Juma'a, sakamakon ƙarin harajin da ƙasar ta sanya kan kayayyakin wasu ƙasashe a makon jiya.

    To sai dai Shugaban Ƙasar, Donald Trump ya ce a kowane lokaci dalar za ta ci gaba da zama kuɗi mai farin jini a duniya.

    Haka kuma masana sun nuna damuwa kan yadda ake sayar da kuɗin lamuni na Amurka.

    Tun da farko, Fadar White House ta dage cewa harajin da Amurka ke ƙaƙaba kan kayayyakin da ake shigar da su ƙasarta zai azurta ta.

    Wata babbar jami'a a babban bankin Amurka, Susan Collins ta ce bankin a shirye yake ya samar da daidaito a kasuwanni idan buƙatar hakan ta taso.

  3. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wanna rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtan ƙasashe.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.