Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/04/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/04/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Isiyaku Muhammed

  1. Iran da Amurka sun ce 'akwai haske' bayan tattaunawarsu kan nukiliya

    Iran da Amurka sun kammala zagaye na farko na tattaunawarsu kan shirin Iran na makamin nukiliya, wanda aka yi a ƙasar Oman.

    Ƙasashen biyu sun bayyana cewa 'akwai alamar haske' bayan tattaunawar, wadda aka yi domin samar da yarjejeniya kan dakatar da shirin Iran na samar da nukiliya.

    Donald Trump ne ya fice daga yarjejeniyar Iran da ƙasashen duniya a 2018, inda ya ce zai jagoranci tsara wata yarjejeniyar daban da "za ta fi dacewa."

    Tattaunar ta farko, wadda aka yi awa biyu da rabi ana yi, rahotanni sun ce an gudanar da ita cikin girmamawa, sannan ta buɗe ƙofar shiga zagaye na biyu.

    Wakilin Iran a taron, ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi ya ce, "ina tunani tattaunawar ta yi kyau domin an yi ta ne cikin girmamawa ba tare da cin mutunci ba," in ji shi a tattaunawarsa da talabijin na Iran.

  2. Iran da Amurka sun ce 'akwai haske' bayan tattaunawarsu kan nukiliya

    Iran da Amurka sun kammala zagaye na farko na tattaunawarsu kan shirin Iran na makamin nukiliya, wanda aka yi a ƙasar Oman.

    Ƙasashen biyu sun bayyana cewa 'akwai alamar haske' bayan tattaunawar, wadda aka yi domin samar da yarjejeniya kan dakatar da shirin Iran na samar da nukiliya.

    Donald Trump ne ya fice daga yarjejeniyar Iran da ƙasashen duniya a 2018, inda ya ce zai jagoranci tsara wata yarjejeniyar daban da "za ta fi dacewa."

    Tattaunar ta farko, wadda aka yi awa biyu da rabi ana yi, rahotanni sun ce an gudanar da ita cikin girmamawa, sannan ta buɗe ƙofar shiga zagaye na biyu.

    Wakilin Iran a taron, ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi ya ce, "ina tunani tattaunawar ta yi kyau domin an yi ta ne cikin girmamawa ba tare da cin mutunci ba," in ji shi a tattaunawarsa da talabijin na Iran.

  3. 'Dakarun RSF sun kashe ma'aikatan agaji tara'

    Wata ƙungiyar agaji da ke aiki a Sudan ta ce an kashe ma'aikatanta tara a wani hari da mayaƙan ƙungiyar RSF suka kai kan wani sansanin ƴan-gudun hijira.

    Ƙungiyar - Relief International ta ce mayaƙan RSF sun far ma sansanin Zamzam da ke yankin Darfur ta Arewa a jiya Juma'a da yamma.

    Akwai rahotannin da ke cewa an kashe gomman farar-hula a sansanin da kuma wani sansanin na El Fasher da ke kusa.

    Ƙungiyar agajin ta ce an lalata daruruwan gidaje na wucin-gadi. Sansanin na Zamzam na zaman wani matsuguni ga dubban ƴan gudun hijira. Tsawon shekara biyu ƙungiyar RSF na yaƙi da rundunar sojin Sudan - wadda a da suke tare.

  4. An haramta wa babbar jam'iyyar adawar Tanzania shiga zaɓen ƙasar

    An haramta wa babbar jam'iyyar hammaya ta Tanzania shiga babban zaɓen ƙasar da za a yi a wannan shekarar, saboda ta ki yarda ta sa hannu na amincewa da wata sabuwar dokar zaɓen ƙasar.

    A wata wasiƙa da ta aike, jam'iyyar ta Chadema, ta ce ba za ta amince da sababbin dokokin ba, muddin ba a yi wasu sauye-sauye ba.

    Wakilin BBC ya ce, masu raji na cewa, Shugaba Samia Suluhu Hassan na ƙara zama mai danniya kafin zaɓen da za a yi a watan Oktoba.

    A farkon makon nan aka tuhumi jagoran jam'iyyar hamayyar, Tundu Lissu, da laifin cin amanar ƙasa.

    An kama shi ne kuwa bayan ya halarci wani gangami inda ya yi kira da a samar da sauye-sauye a tsarin zaɓen ƙasar ta Tanzania.

    Kafin wannan ma an sha tsare Mista Lissu, kuma ya tsira daga wani yunƙuri na hallaka shi a 2017. Haramcin shiga takarar na nufin jam'iyyar ta hamayya ba za ta shiga zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokoki ba, ko wani zaɓen cike gurbi, tsawon shekara biyar.

  5. Isra'ila ta ce za ta faɗaɗa hare-harenta a Gaza

    Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz ya ce nan ba da jimawa ba sojojin ƙasar "za su faɗaɗa" hare-harensu a mafi yawan yankunan Gaza.

    Katz ya kuma ce rundunar tsaron ƙasar, IDF ta kammala ƙwace wasu yankin tudun-mun-tsira da ke tsakanin biranen Rafah da Khan Younis a kudancin Gaza.

    Haka kuma sojojin na Isra'ila sun umarci mazauna Khan Younis da masu maƙwabtaka da su da su fice daga yankin, inda suka ce za su fara luguden wuta a matsayin martani kan harba wani makami mai linzami da aka yi Gaza, wanda kuma Hamas ta ɗauki alhaki.

    Isra'ila dai ta koma luguden wuta a kan Hamas ne a ranar 18 ga watan Maris bayan yarjejeniyar tsagaita tsakaninsu ya samu tsaiko.

    Daga lokacin zuwa yanzu, Isra'ila ta ƙwace yankuna da dama, sannan ta yi sanadiyar raba dubban ƴan Gaza da muhallinsu.

    Haka kuma ta ƙwace yankunan tudun-mun-tsira da yankin Falasɗinu, inda ta ce ta yi haka ne domin hana kai mata hare-hare.

    Hukumomi a Isra'ila sun ce ƙasar kai hare-hare ne domin tursasa Hamas ta saki sauran waɗanda ke hannunta su 59 - ciki har da mutum 24 da ake tunanin suna raye.

  6. Jagoran juyin mulkin soji na son zama sabon zaɓaɓɓen shugaban Gabon

    Jama'a na tururuwa domin su je su kaɗa ƙuri'a domin zaɓen shugaban ƙasar Gabon, inda a karon farko a gomman shekaru babu wani daga gidan iyalan Bongo da ke takarar.

    An hamɓare tsohon shugaban ƙasar Ali Bongo daga mulki wata 19 baya a juyin mulkin da Janar Brice Oligui Nguema, wanda ya sauya kundin tsarin mulkin ƙasar don ya tsaya takara a zaɓen na ranar Asabar, ya jagoranta

    Akwai jimullar ƴantakara takwas da suka tsaya zaɓen - ciki har mace ɗaya Gninga Chaning Zenaba.

  7. Iran ta ce tana fatan samun 'yarjejeniya ta adalci' kan shirinta na nukiliya

    Iran da Amurka sun fara tattaunawa a Oman kan shirin Tehran na nukiliya - wanda shi ne tattaunawa babba ta farko a tsakanin ƙasashen biyu tun a shekarar 2018.

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bayyana wa gidan talabijin na Iran cewa ƙasarsa na fatan samun "yarjejeniya ta adalci", sannan kakakinsa ya ce ba ya tunanin tattaunawar za ta ɗauki lokaci mai tsawo.

    Donald Trump ne ya fice daga yarjejeniyar Iran da ƙasashen duniya a 2018, inda ya ce zai jagoranci tsara wata yarjejeniyar daban da "za ta fi dacewa."

    Har yanzu babu tabbacin ko za su zauna a ɗaki ɗaya ne domin tattaunawar, kasancewar wakilin Amurka Steve Witkoff ya ce yana so a tattauna ga da ga, shi kuma Araghchi ba ya son haka.

    Sai dai abin da ya fi muhimmanci shi ne tattaunawar, da kuma irin yarjejeniyar da za su shiga.

    A watan jiya ne Trump ya aika wa shugaban addini na Iran wasiƙa ta hannun Haɗaɗdiyar Daular Larabawa, inda a ciki ya ce yana so Iran ta dakata da shirinta makamin nukiliya, domin guje wa amfani da ƙarfin soji daga Amurka da Isra'ila a kan Iran ɗin.

    Sai dai a nata ɓangare, ita Iran tana so ne a yi yarjejeniyar da za ta taƙaita shirin, amma ba ta watsar da shi ba baki ɗaya.

  8. Tsohon kocin Super Eagles Christian Chukwu ya rasu

    Tsohon ɗanwasa, kuma tsohon mai horas da ƴan ƙwallon tawagar Super Eagles ta Najeriya, Christian Chukwu wanda aka fi sani da Chairman ya rasu.

    Christian Chukwu ne kyaftin ɗin tawagar Super Eagles lokacin da Najeriya ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 1980.

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, NFF ce ta tabbatar da rasuwar tsohon kocin, wanda ya rasu ranar Asabar yana da shekara 74 a duniya a jihar Enugu da ke kudancin ƙasar.

    A sanarwar da NFF ta fitar, ta ce, "mun yi rashin mutumin kirki, jagora a filin wasa da wajen fili, shi ya sa ba a banza ake kiransa da chairman ba.

    "Muna fata Allah ya sa ya huta, sannan muna fata Allah ya ba iyalansa haƙurin rashinsa."

    An haife shi ne a ranar 4 ga Janairun 1951, sannan bayan taka leda, ya horar da ƴanwasan ƙungiyar Enugu Rangers da Kenya da tawagar Super Eagles, wadda ya jagorance ta zuwa matakin na uku a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 2004 da aka yi a ƙasar Tunisia.

  9. Trump ya cire haraji kan manyan wayoyin hannu da kwamfutoci

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce gwamnatinsa ta cire wayoyin hannu da kwamfotoci daga cikin kayayyakin da ya ƙaƙaba wa haraji, ciki har da harajin kashi 125 da ya lafta wa kayayyakin China.

    Hukumar kwastam da kula da iyakokin Amurka ce ta sanar da haka a ranar Juma'a, inda ta ce za a cire kayayyakin daga cikin waɗanda za a riƙa karɓar harajin kashi 10, da ma kashi 125 na China.

    Wannan matakin na zuwa ne bayan kamfanonin fasahar zamani na Amurka sun koka kan cewa na'urori za su yi tashin gwauron zabi, saboda yawancinsu daga China suke sayensu.

    An yi hasashen cewa farashin Iphone zai iya ninkuwa da kusan ninki uku da ba a cire haraji kan wayoyin ba.

    Amurka ce ƙasar da aka fi amfani da wayar IPhone, kuma kashi 80 na wayoyin IPhone da ake amfani da su a Amurkar daga China ake sayenssu.

  10. Ndume ya buƙaci Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangaren tsaro da tattalin arziki

    Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume ya yi kira ga shugaban Najeriya, Bola Tinubu da ya ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangaren tsaro da tattalin arzikin ƙasar.

    Ndume ya bayyana haka a ranar Juma'a a shirin Politics Daily na tashar Channels, inda a ciki ya kuma soki matakin da Tinubu ya ɗauka na ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers mai arzikin man fetur.

    "Kawai shugaban ya ajiye komai ya fuskanci abubuwa guda uku - tsaro da jin daɗin ƴan ƙasarsa da tattalin arziki," in ji shi.

    "Waɗannan abubuwan ne ya fi kamata ya mayar da hankali, ya ba su fifiko, sannan su ne ɓangarorin da suka kamata ya ayyana musu dokar ta-ɓaci."

    Ndume ya ce ya yi mamaki da Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓacin a jihar Rivers, lamarin da ya ce kuskure ne matuƙa ɗaukar wannan matakin.

  11. Tun yana ƙarami burinsa shi ne ya yi fice - Mahaifin Elon Musk

    Elon Musk shi ne mutumin da ya fi kowa arziki a faɗin duniya, mutumin da ya zuba jari a fannin fasahar zamani, wanda kuma ke da dama ta musamman a ofishin shugaban Amurka.

    BBC ta tattauna da mahaifinsa, Errol Musk domin jin yadda yaruntar hamshaƙin attajirin ta kasance, da yadda ta tallafa wa rayuwar mutumin da ake yi wa laƙabi da ''ɗan ƙaramin shugaban Amurka''.

    "Ya aika min da wasu kuɗi domin sayen tawagen injin jirgin sama da nake son saya,'' in ji Errol, yayain da yake bayyana hulɗa ta baya-bayan nan tsakaninsa da ɗan nasa mai matuƙar tasiri.

  12. Sabbin haraje-haren Amurka na haifar wa duniya ruɗani - China

    Ministan kasuwanci na China, Wang Wentao ya faɗa wa Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya, WTO cewa haraje-harajen Amurka na haifar wa duniya ruɗani.

    Wata sanarwa da Beijing ta ce Mista Wentao ya yi magana da shugabar ƙungiyar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala a ranar Juma'a.

    A yanzu haka China ta ƙaƙa haraji kashi 125 kan kayyakin Amurka da ke shiga ƙasarta, a wani mataki na mayar da martani kan ƙarin harajin kashi 145 da Donald Trump ya yi wa kayayyakin China da ke shiga Amurka.

    Abokiyar hamayyar China - Taiwan mai cin gashin kai - ta ce tana tattaunawa da Amurka domin duba yiwuwar ɗage mata ƙarin harajin.

    Matakin da masana ke zargin Amurka da fifita tattaunawar kasuwanci da makwabciyar Chinan.

  13. Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti don nazarin tasirin sabon harajin Amurka

    Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin da zai yi nazarin tasirin ƙarin harain baya-bayan nan da Amurka ta yi wa kayayyakin ƙasar da ake shigarwa Amurka.

    Gidan Talbijin na Channels ya ambato kakakin ma'aikatar harkokin yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Manga na bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.

    Manga ya ce an ɗauki matakin ne bayan taron tawagar lura da tattalin arzikin ƙasar, ƙarƙashin jagorancin ministan kudin ƙasar, Wale Edun.

    Yayin da sabon harajin Amurkan bai shafi man fetur - babban abin da Najeriya ta dogara da shi wajen fitarwa ƙetare - ba, matakin ya zo ne a daidai lokacin da farashin man fetur ke sauka a kasuwar duniya.

    Masana dai na nuna damuwa kan yiwuwar samun cikas ko giɓi a kuɗin shiga da ma kasafin kudin ƙasar.

  14. Babbar jam'iyyar adawa a Tanzaniya ta ƙi saka hannu kan sabuwar dokar zaɓen ƙasar

    Babbar jam'iyar adawa a Tanzaniya ta ƙi sanya hannu kan sabuwar dokar zaɓen ƙasar - da ake tunanin za ta haramta wa jam'iyar shiga takara a zaɓen ƙasar da ke tafe cikin wannan shekara.

    Cikin wata wasiƙa da jam'iyyar Chadema ta aike wa hukumar zaɓen, ta ce ba za ta amince da sabbin dokokin matsawar ba a yi sauye-sauye a ciki ba.

    A farkon makon nan ne aka tuhumi shugaban jam'iyyar, Tundu Lissu ta zargin cin amanar ƙasar.

    An kama shi bayan ya bayyana a wani gangamin jam'iyyar, inda ya yi kiran samar da sauye-sauye a tsarin zaɓukan ƙasar.

    An dai tsare Mista Lissu a lokuta daban-daban kafin ya tsallake rijiya da baya a wani yunƙurin kashe shi a 2017.

  15. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ƙasurgumin ɗanbindiga Gwaska da wasu guda 100

    Hukumomi a Najeriya sun ce jami'an tsaron ƙasar sun halaka ƴanbindiga 100 ciki har da gawurtaccen ɗanbindiga, Gwaska a jihar Katsina da ke Arewa Maso Yammacin Ƙasar.

    Hadin gwiwar jami'an tsaron kasar ne suka ƙaddamar da harin a ranar Juma'a wanda ya yi sanadin kisan Gwaska - wanda ya kasance mataimakin shahararren ɗanbindiga Malan, shugaban ISWAP a yankin Arewa Maso Yamma.

    Bayanai sun nuna cewa Gwaska Dankarami ya jima yana ɓuya a dajin Munumu da ke jihar Katsina.

    Rahotonni sun ce sojojin sun lalata maɓoyar ƴanbindigar da dama a sassan jihar a lokacin harin, tare da ƙwato da kuma lalata wasu manyan bindigogi masu jigida da waɗanda aka ƙera a cikin gida.

    Harin na zuwa ne bayan da a farkon mako ƴanbindigar suka yi garkuwa da mutum 43 mazauna ƙauyukan Maigora da ke yankin ƙaramar hukumar Dandume

    Kwamishinan al'amuran cikin gida na jihar Katsina, Nasir Mu'azu ya bayyana matakin da wata gagarumar nasara a yaƙi da ƴanbindiga ake yi a jihar.

    “Abin farin ciki ne ga jihar, domin wannan nasara ta taimaka wajen wargaza hadakar ƴanbindigar da ke addamar garuruwa da ƙauyukan yankunan ƙananan hukumomin Faskari da Kankara da Bakori da Malumfashi da kuma Kafur,'' in ji Kwamishinan.

  16. Sojojin Isra'ila sun ce sun yanke birnin Rafah daga Khan Yonis

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta yanke birnin Rafah daga Khan Younis a kudancin Gaza.

    IDF ta ce ta karɓe da abin da ta bayyana da cibiyar tsaronta da ta yi wa laƙabi da ''Lungun Morag'', sunan wani ginin da Isra'ila ta taɓa yi tsakanin biranen biyu.

    A yanzu haka sojojin Isra'ila na gina titi a wurin, da nufin samar da wani wuri da Isra'ila ke iko da shi da ya raba Zirin Gaza.

    Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Hamas ke cewa ta aika wakilanta zuwa Masar domin tattaunawa da masu shiga tsakani kan yiwuwar dawo da yarjejeniyar zaman lafiya.

  17. Duk wata haɗaka da nufin kawar da APC ba za ta yi tasiri ba - Ganduje

    Shugaban Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya ce duk wata haɗaka da jam'iyyun hamayyar ƙasar ke shirin yi da nufin kawar da APC a zaɓen 2027 ba za ta yi tasiri ba.

    Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga manema labarai a jihar Kaduna lokacin ziyarar - da ya jagoranci shugabannin jam'iyyar wajen kai wa tsohon shugaban ƙasar - Muhammadu Buhari.

    Gabanin ziyarar su Gandujen, tawagar jagoran adawar ƙasar, Atiku Abubakar tare da tsoffin gwamnonin jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da Sanata Ahmed Makarfi da kuma Sanata Aminu Waziri Tambuwal ta fara kai wa Buhari ziyara a gidan nasa.

    Ganduje ya ce ziyarar su Atikun ba ta ɗaga musu hankali ba, saboda a cewarsa ''suna son ƙulla wata haɗaka da ba za ta yi tasiri ba''.

    ''Daga abin da muka gani mutane ne da ba za su iya haɗuwa ƙarƙashin inuwa guda ba'', in ji shi.

    Shugaban jam'iyyar ta APC ya ce a shirye suke kuma sun san yadda za su ɓullo wa lamarin kodayake ya ce ba zai faɗi dabarar da za su bi ba.

    Ganduje ya ce duk da cewa a yanzu haka APC na da iko da jihohin ƙasar 21, har yanzu jam'iyyarsu na hangen ƙarin wasu jihohin.

    ''Ko dai wasu gwamnonin da kansu su dawo jam'iyyarmu, ko kuma jihohin su dawo hannunmu ta hanyar zaɓe.''

  18. Kotun Kolin Indiya da bai wa shugaban ƙasar wa'adin sanya hannu kan dokokin jihohin ƙasar

    Kotun ƙolin Indiya ta bai wa shugaban ƙasar wa'adin wata uku da ya amince da sabbin dokoki da jihohin ƙasar suka amince da su.

    Akwai tarin ɗaruruwan dokoki da waɗanda jihohin ƙasar da dama suka amince da su - da suka ɗauki shekaru a ofishin shugaban ƙasar - suna jiran sanyawar hannun shugaban.

    Akwai rahotonnin da ke cewa an riƙe dokokin ne saboda bambancin siyasa tsakanin gwamnatocin jihohin da kuma gwamnatin tarayya.

    Masana fannin shari'a na cewa hukuncin kotun ƙolin tabbatar da damar jihohin ne na yin dokoki.

    Jihar Tamil Nadu ce dai ta shigar da ƙara gaban kotun ƙolin, inda bayanai ke nuna cewa tana da muhimman dokoki 10 da ke jihar sanyawar hannun shugaban ƙasar.

  19. Ƴansanda sun kama wani magidanci kan zargin yi wa ƴarsa ciki a Bauchi

    Rundunar ƴansandan jihar Bauchi ta kama wani mutum mai shekara 50, bisa zargin yi wa ƴarsa ciki a ƙauyen Kurmi Ado da ke ƙaramar hukumar Ganjuwa a jihar.

    Kakakin rundunar ƴansandan jihar, CSP Ahmed Wakil ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce rundunarsu na shirin gurfanar da shi a gaban kotu.

    Rundunar ƴansanda ta ce tana zargin mutumin mai shekara 50 da cewa ya riƙa yi wa ƴar tasa mai shekara 17 fyaɗe, lamarin da ya sa har ta kai ga ɗaukar ciki.

    CSP Wakil ya ce bayan samun rahoton zargin ne rundunar a fara gudanar da bincike tare da kama mutumin.

    Kakakin ƴansandan ya ce a lokacin da ake yi wa magidancin tambayoyi ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, inda kuma binciken likitoci ya tabbatar da cewa ya jima yana lalata da yarinyar, inda har take ɗauke da ciki.

    CSP Wakil ya ƙara da cewa a lokacin da ƴansanda ke yi wa yarinyar tambayoyi ta tabbatar da tuhumar mahaifin nata, tana mai cewa lamarin ya faru ne a lokacin da mahaifiyarta ta yi bulaguro zuwa wajen danginta.

    A lokacin da mahaifiyar ta dawo ne ta fahimci ƴar tata na da ciki, inda bayan ta tuhumeta ta ce mahaifnta ne ya yi mata, kamar yadda ƴandandan suka bayyana.

  20. Wakilan Iran sun isa Oman domin tattauna shirin nukiliyarta da Amurka

    Ministan harkokin wajen Iran ya isa ƙasar Oman domin tattaunawa - da aka gaggauta shiryawa - da Amurka kan taƙaita shirin nukiliyar ƙasarsa

    Jakadan Amurka a yankin Gabas Tsakiya, Steve Witkoff ne zai jagoranci tawagar Amurka domin halartar tattaunawar.

    Kawo yanzu dai ba a sani ba ko ɓangarorin biyu za su zauna a zaure guda domin tattaunawar ƙeƙe-da-ƙeƙe.

    Tattaunawar ita ce muhimmiya tun bayan da gwamnatin Trump ta janye daga yarjejeniyar da ƙasashen duniya suka cimma da Iran kan shirin nukiliyarta - shekara bakwai da suka gabata a lokacin wa'adin mulkinsa na farko.

    Shugaba Trump ya kuma yi gargaɗin amfani da matakin soji idan tattaunawar ba ta cimma matsaya ba.

    Ita dai Iran ta sha fadin cewa ba za ta cimma yarjejeniyar cikin matsin lamba ba.