Mutum 25 sun mutu bayan kifewar kwale-kwalen ƴan ci-rani a tekun Gambia
Gwamnatin Gambia ta tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 25 bayan wani kwale-kwale da ke ɗauke da ’yan ci-rani ya kife a gaɓar tekun ƙasar, yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara.
Jami’an tsaro sun ce kwale-kwalen na ɗauke da fiye da mutum 200, kuma har yanzu ba a gano dayawa daga cikinsu ba.
Rahotanni sun nuna cewa yawancin waɗanda ke cikin kwale-kwalen matasa ne daga ƙasashen Yammacin Afirka, masu kasadar ketare teku domin neman shiga Turai, galibi ta hanyar tsibiran Canary na ƙasar Sifaniya.
Ana yawan yin irin wannan tafiya ne da kwale-kwale marasa inganci da ke cike da mutane fiye da ƙima, lamarin da ke haddasa haɗurra masu muni.
Shugaban Gambia, Adama Barrow, ya bayyana cewa ƙasar na cikin jimami sakamakon wannan mummunan haɗari.