Sai da safe
Mun kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafin na ranar Lahadi.
Za mu zo da wasu sababbi a gobe Litinin da safe.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 31/08/2025
Isiyaku Muhammed da Umar Mikail
Mun kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafin na ranar Lahadi.
Za mu zo da wasu sababbi a gobe Litinin da safe.
Mayaƙan ƙungiyar Houthi a Yemen sun kutsa ofishin hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Sanaa babban birnin ƙasar tare da tsare ɗaya daga cikin ma'aikatan wurin.
Wasu rahotanni sun ce ƙungiyar ta tsare mutane a wasu wuraren hukumar ta WFP.
WFP ta ce tana neman ƙarin bayani daga hukumomin yankin yayin da take ƙara ƙidaya duka ma'aikatanta da ke yankin, wanda ke ƙarƙashin ikon ƴan Houthi.
Gwamnatin Houthi ta ɗauki matakin tsare wasu jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya da dama bayan hare-haren da Isra'ila ta kai ranar Alhamis da suka yi ajalin firaiministan Houthi da wasu manyan mambobin ƙungiyar.

Asalin hoton, Reuters
Wasu jerin jiragen ruwa ɗauke da ɗaruruwan masu goyon bayan Falasɗinawa, ciki har da Greta Thunberg mai fafutika kan yanayi, ya kama hanyar zuwa Gaza daga birnin Barcelona na Sifaniya.
Waɗanda suka tsara tafiyar sun ce ayarin jirgin 20 shi ne mafi girma da ya taɓa zuwa yankin Gaza.
Ɗaya daga cikin masu fafutikar ya ce "yunwar da muke gani a Gaza an ƙirƙire ta ne da gangan".
A watan Yunin da ya gabata sojojin Isra'ila suka tare wani jirgin masu zanga-zanga da ke ɗauke da Ms Thunberg, sannan suka sake ƙwace wani a watan Yuli.
Ba za a bar ayarin su ƙarasa Gaza ba saboda takunkumin da Isra'ila ta ƙaƙaba na shiga ko fita.

Asalin hoton, Nafdac
Hukumar kula da lafiyar magunguna da abinci a Najeriya ta ce ta rufe wani wurin haɗa magungunan gargajiya ba bisa ƙa'ida ba a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar.
Sanarwar da hukumar Nafdac ta fitar a yammacin yau ta ce ta ƙwace kayayyakin haɗa maganin da suka kai darajar naira miliyan biyar a Mararaba Jos da ke ƙaramar hukumar Igabi.
"Bayan samun bayanan sirri, dakarnmu sun gano kayayyakin haɗa maganin marasa tsafta kuma ska tabbatar cewa abubuwan da ake haɗawar na iya haifar da matsala ga lafiyar al'umma," in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa ta ƙwace ƙunshin maganin mai suna Shifa'unnur da ya kai darajar N5,000,000 tare da rufe shi har zuwa lokacin da za ta kammala bincike.

Asalin hoton, Nigerian Army
Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram 12 a wani samame da suka kai a yankuna da dama na jihar Borno, a cewar rundunar sojin ƙasar.
Gidan talabijin na gwamnatin ƙasar NTA ya ruwaito cewa dakarun rundunar Operation Hadin Kai ne suka halaka 'yanbindigar a ƙaramar hukumar Mafa mai nisan kilomita 59 daga Maiduguri babban birnin jihar.
Sun kai harin ne bayan samun bayanan sirri inda suka auka wa sansanonin mayaƙan a Tamsu Ngamdu, da Dalakaleri, da Gaza.
Cikin makamai da kayayyakin da suka ƙwace daga hannun 'yanbindigar har da bindigogi ƙirar AK-47 guda takwas, da ƙunshin harsasai takwas, da kuma ƙwayoyi.

Asalin hoton, Reuters
Isra'ila ta yi iƙirarin kashe mai magana da yawun ƙungiyar Hamas Abu Ubaida a Birnin Gaza.
Ministan tsaro Israel Katz ya wallafa saƙo a shafinsa na X yana yaba wa rundunar sojin sama ta ƙasar IDF, da hukumar tsaron cikin gida Shin Bet, saboda "gudanar da aiki cikin nasara".
Bai yi ƙarin bayani ba game da lokaci ko wurin da aka gudanar da aikin, amma IDF ta ce wani jirginta ya kai hari kan "wani babban ɗanta'adda" a unguwar al-Rimal ranar Asabar.
Hamas ba ta tabbatar da mutuwarsa ba tukunna, amma a baya ta ce harin Isra'ila ya kashe gomman fararen hula a unguwar.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce suna da aniyar kai hare-hare tsakiyar Rasha yayin da aka ga Ukraine ɗin ta ƙara ƙaimi a hare-hare kan tashoshin makamashi.
Mista Zelensky ya ce dakarunsa sun shirya tsaf domin kai ƙarin hare-hare domin dakatar da mamayar dakarun Rasha.
Ya zargi Rasha da gazawa wajen cimma muradanta a yankin Donetsk mai muhimmanci.
Tun da farko Rashar ta ce kakkaɓo jiragen Ukraine marasa matuƙa sama da 100 cikin awa 24 da suka wuce, da kuma kai wa tashoshin jiragen ruwa hari a cikin Ukraine ɗin.

Asalin hoton, Nigeria Police website
Tsohon shugaban ƴansandan Najeriya Solomon Arase wanda ya jagoranci rundunar a tsakanin 2015 zuwa 2016 ya rasu yana da shekara 69 a duniya.
Arase ya rasu ne a asibitin Cedar Crest da ke Abuja da safiyar yau Lahadi, kamar yadda jaridar Daily Trust mai zaman kanta ta ruwaito.
Mamacin ya fara aikin ɗansanda ne a shekarar 1981, bayan ya kammala digirinsa na farko daga Jami'ar ABU a shekarar 1980, inda ya karanci kimiyyar siyasa.

Asalin hoton, Rivers
Jam'iyyar APC ta lashe ƙananan hukumomi 20 cikin 23 a zaɓen ƙananan hukumomi jihar Rivers da aka gudanar a jiya Asabar.
A ɗaya ɓangaren kuma, jam'iyyar PDP mai mulki a jihar, ta samu nasarar lashe ƙananan hukumomi uku, kamar yadda hukumar zaɓen jihar ta sanar.
Dakataccen gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya sha kaye a ƙaramar hukumarsa ta Opobo-Nkoro, inda ɗan takarar jam'iyyar APC ya lashe zaɓen.
Shugaban hukumar zaɓen, Dr Michael Odey ne ya sanar da sakamakon zaɓen a hedkwatar hukumar da ke titin Aba a Fatakwal kamar yadda jaridar Punch mai zaman kanta ta ruwaito.
A bara dai an yi wani zaɓen, inda Fubara ya tsayar da na hannun damarsa a jam'iyyar APP, inda suka doke ƴan takarar Wike a zaɓen, amma mutanen tsohon gwamnan suka je kotu, inda aka yi ta tafka shari'a har kotun ƙoli ta soke zaɓen daga baya.
Bayan sulhu tsakanin Fubara da Wike wanda Tinubu ya jagoranta aka shirya wannan zaɓen, inda tun farko aka ce an tsara yadda ake so ta kasance.

Asalin hoton, Getty Images
Mutanen garin Kasuwar-Garba da ke ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja sun ƙone wata mata da ranta a yammacin jiya Asabar bisa zarginta da ɓatanci ga Annabi Muhammad.
Matar, wadda ake kira da Amaye, tana sayar da abinci ne a yankin, inda jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani kwastomanta ya yi mata magana cikin raha cewa yana so zai aure, sai ya ambato maganar Annabin, ita kuma a nan ta faɗa wata magana ta zama ɓatancin.
An ce an fara miƙa ta ofishin ƴansanda ne domin a gudanar da bincike, amma sai mutane suka ci ƙarfin jami'an tsaron, suka ƙwace ta, sannan suka cinna mata wuta.
Shugaban ƙaramar hukumar Mariga, Abbas Adamu Kasuwar-Garba ya tabbatar aukuwar lamarin, inda ya ce komai ya lafa zuwa yanzu.
A nasa ɓangaren, kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya ce da misalin ƙarfe 2 na rana ne suka samu labarin cewa, "wata mata mai suna Amaye ta yi wasu kalaman ɓatanci ga Annabi."
Sai dai ya ce kafin su tura ƙarin jami'an tsaro, "mutane su kutsa inda suka fi ƙarfin jami'anmu, har suka ƙwace ta suka ƙone ta." in ji shi, inda ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike kuma da zarar sun kammala za su tabbatar da hukunci. a kan waɗanda aka samu da laifi.

Asalin hoton, Sokoto state govenment house
Gwamnatin jihar Sokota ta ce za ta fara ware wa masallatan Juma'a na jihar wasu kuɗaɗe duk wata domin gudanar da ayyukansu, sannan ta ce tana ware wa limaman masallatan da na'ibansu da ladanai alawus duk wata.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin jihar, Abubakar Bawa ya fitar, inda ya ce gwmnatin ta ɗauki wannan matakin ne domin haɓaka karatun Alƙu'ani da ilimin addini a tsakanin yaran jihar masu tasowa.
Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana haka a ranar Asabar a wajen yayen ɗalibai 111 da suka haddace Ƙur'ani a makarantar gidauniyar Sheikh Ɗahiru Bauchi da ke Sokoto, inda ya ƙara da cewa alawus ɗin zai taimaka wajen ba malaman addinin damar nazari da ci gaba da karantar da addini.
"Mun bayar da kwangilar sabunta masallatai 65 na Juma'a, kuma tuni an kammala guda 25, waɗanda a ciki mun buɗe guda 15 zuwa yanzu.
"Haka kuma mun kasafta ware wa masallatan na Juma'a kuɗi tsakanin naira 300,000 zuwa 500,000, ya gandanta. Sannan ga biyan limamai da na'ibai da ladanai na masallatan alawus suma domin samun sauƙin gudanar da ayyukansu," in ji shi.
Gwamnan ya ce kula da harkokin addinin musulunci na cikin manufofi 9 na gwamatinsa, "kuma shi ne mai matsayi na biyu bayan tsaro."

Asalin hoton, Tribune News Service via Getty Images
Magajin garin Chicago, Brandon Johnson, ya sanya hannu kan wata takardar umarnin shugaban kasa a kokarin da gwamnatin Trump ke yi na maganace kwararar bakin haure cikin birnin na uku mafi girma a Amurka.
"Ba za mu amince a mamaye birninmu da jami'an tsaro ba," in ji Johnson wanda ɗan jam'iyyar Democrat ne.
Ya nuna damuwa ne a game da barazanar da shugaban kasar ya yi na tura dakarun tsaro na kasa zuwa Chicago, domin hana kwararar bakin haure.
Umarnin magajin garin ya haramta wa hukumar 'yan sanda taimakawa mahukuntan gwamnati wajen aiwatar da duk wani abu da ya shafi bakin haure.
Magajin garin ya bukaci shugaba Trump da ya fasa tura dakarun tsaro na kasar zuwa birnin.

Asalin hoton, Getty Images
Birtaniya ta sanar da kara ba wa matan Gaza tallafi sannan kuma ta yi alkawarin bayar da fiye da dala miliyan dari hudu domin taimakawa mata masu juna biyu da kuma masu shayarwa dama samar da audugar mata mai dumbin yawa ga matan zirin.
Sakataren harkokin wajen kasar David Lammy, ya ce halin jin kan da ake ciki a Gaza har yanzu abin damuwa ne sannan kuma mata da 'yammata ne suka fi a jikinsu.
Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa akwai mata masu juna biyu fiye da dubu 55 da yanzu haka suke a Gaza kuma ba sa samun kulawar da ta dace.
Ana kara samun barin ciki da haihuwar jarirai a mace sakamakon halin da ake ciki a Gazan.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Rasha Vladimir Putin da firaiministan Indiya Narendra Modi, na daga cikin shugabannin duniya fiye da 20 da ke halartar taron tsaro na kungiyar kasashen yankin Asiya da ake yi a China.
Wakiliyar BBC ta ce an samar da kungiyar ne a 2001, kuma kungiyar na mayar da hankali ne kan duk wasu abubuwa da suka shafi kasashen tsakiyar Asiya, kuma tun bayan samar da kungiyar ta ke kara samun mambobi da suka hada da India da Pakistan da Iran da kuma Belarus.
Gabanin taron da ake duk shekara na shugabannin yankin a birnin Tianjin, Mr Modi ya tattauna da shugaban China Xi Jinping.
Wannan itace ziyararsa ta farko zuwa China a cikin shekaru bakwai sannan kuma ziyarar ta Mr Modi ta zo ne a yayin da gwamnatin Trump ta sanya wa kayayyakin Indiya da ake shiga da su Amurka haraji a matsayin martani ga sayen man Rasha da Indiya ke yi.
Tuni gwamnatocin China da India suka amince su gyara alaƙar da ke tsananinu domin ciyar da ƙasashensu gaba.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Trump ta dauki matakin korar sauran ma'aikatan kafar yada labarai ta gwamnatin kasar wato VOA da ake kira VOA.
An aika wa ma'aikata fiye da 500 takardar sallama daga aiki da kafar kamar yadda shugabar rikon kafar, Kari Lake, ta sanar da matakin, wanda ta ce na rage ma'aikata ne, kamar yadda ta rubuta a shafinta na kafar sadarwa.
Ta ce matakin zai taimaka wadanda aka bari damar tafiyar da gwamnati da rage kudin da ake kashewa, duk da akwai yiwuwar za a kalubalanci wannan mataki a kotu.
A lokacin yakin duniya na biyu ne aka samar da kafar yada labaran ta VOA domin dakile farfagandar da ake yadawa a kan 'yan Nazi.

Asalin hoton, Reuters
Dubban mutane ne ke gudanar da zanga-zanga a sassan Mexico domin tunawa da ranar da aka tursasa wa wasu mutane yin batar dabo a kasar.
'Yan'uwa da abokan arzikin wadanda suka yi batar dabon da ma kungiyoyin kare hakkin dan'adam da dama sun yi taru a wasu titunan biranen kasar inda suke kira da a yi wa mutanen adalci sannan kuma gwamnati ta dauki mataki a kai.
Rahotanni sun ce mutane fiye da dubu 130 ne suka yi batar dabo a Mexico a lokacin, kuma yawancin batar-dabon mutanen na da alaka da ayyukan kungiyar masu safarar kwayoyi wadda ke kai wa matasa da marassa karfi hari.

Asalin hoton, Getty Images
Fusatattun masu zanga-zanga a Indonesia sun afka wa gidajen 'yan siyasa da dama ciki har da gidan ministan kudin kasar inda aka saci kayayyakin more rayuwa da dama.
Ana gudanar da zanga-zangar gama gari a sassan kasar bayan da 'yan majalisar dokokin kasar suka kara wa kansu albashi duk da halin matsi da tsadar rayuwar da ake ciki a kasar.
Wakiliyar BBC ta ce yayin da zanga-zangar ta shiga kusan mako guda, yawancin mutane na bayyana halin da ake ciki a Jakarta da wasu birane a matsayin marar dadi ga kuma zaman dar-dar.
Kazalika ana kara samun zaman dar dar bayan mutuwar wani direban tasi da motar 'yan sanda ta kade.
Aƙalla mutum hudu sun mutu bayan karawar da aka yi tsakanin masu zanga-zanga da kuma 'yansanda, sannan kuma an kona gine-ginen gwamnati da dama.

Asalin hoton, OTHER
A Najeriya, ana ci gaba da ƙoƙarin nemo gawarwakin mutanen ƙauyen Dan-Maga da haɗarin kwale-kwale ya rutsa da su a wani kogi, yayin da suke ƙoƙarin tsere wa harin ƴanbindiga a yankin ƙaramar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.
Ya zuwa yanzu dai an gano gawar mutum goma sha shida, kuma har an yi jana'izarsu.
Waɗanda kuma suka tsira da rayukansu suna can suna zaman gudun hijira a garin Nasarawar Kifi.
Haɗarin ya auku ne a kogin da ke tsakanin Dan-Maga da Nasarawar Kifi a cewar Bashiru Goga Ƴankifi, mazaunin Nasarawar Kifi wanda a tattaunawarsa da BBC ya ce, "Muna cikin jimami da kaɗuwa sosai bisa wannan iftila'i. A ranar Juma'a da daddare aka gano mutum 14, sai kuma a ranar Asabar aka sake gano mutum 2," in ji shi, inda ya ce jimilla yanzu sun gano gawarwkin mutum 16 ke nan.
Sai dai ya ce har yanzu mutanen da suka tsira suna ci gaba da gudun hijitra ne saboda suna tsoron komawa yankinsu kasancewar ƴanbindigar na nan a cikin daji.
Shi ma Mustapha Ahmad Gumi ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce "ɓarayi ne suka watsa mutane sai suka zo tsallake kogi, amma sai suka yi yawa a jirgin ruwan kuma yawanci mata ne da ƙananan yara, wanda hakan ya sa jirgin ya kife."
Jama'a barkanmu da wanan safiyar ta Lahadi daga nan sashen Hausa na BBC, ina za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Ku kasance tare da mu.