Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/09/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/09/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

DagaHaruna Kakangi da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Masu bin shafin namu nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. Kotun Kenya ta tsare wani da ake zargi da safarar ƴanƙasar don yi wa Rasha yaƙi a Ukraine

    Wata kotu a Kenya ta bai wa ƴansanda izinin tsare wani mutum da ake zargi da safarar ƴanƙasar don yi wa Rasha yaƙi a Ukraine.

    An kama Edward Gituku ne ranar Laraba yayin wani samame da ƴansanda suka kai a wani gida da ke kudancin Birnin Nairobi.

    Hukumomin ƙasar sun ce an ceto wasu maza su 21 da ke shirin tafiya zuwa birnin Moscow yayin samamen.

    Ƴansanda sun yi zargin cewa Gituku ya yaudari matasan ne da alƙawuran ayyukan yi, amma sai suka tsinci kansu a fagen daga a Ukraine.

  3. MDD za ta kaɗa ƙuri'ar zaɓin ɗage wa Iran takunkumi kan shirin nukiliyarta

    Ayatollah Ali Khomenei

    Asalin hoton, Getty Images

    Nan gaba a yau ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai kaɗa ƙuri'ar ɗage sake ƙaƙaba wa Iran takunkumai masu tsauri kan shirinta na nukiliya.

    Jami'an diflomasiyya sun ce da wuya a zartar da ƙudurin - wanda China da Rasha suka gabatar .

    Ana sa ran za a fara aiwatar da matakan ne daga gobe Asabar bayan da ƙasashen Birtaniya da Faransa da Jamus suka zargi Tehran da karya yarjejeniyar da aka ƙulla a shekarar 2015 da nufin hana ta ƙera makamin nukiliya

  4. MSF ta dakatar da aiki a birnin Gaza saboda hare-haren Isra'ila

    Kungiyar agaji ta Medicine sans frontiers (MSF)ta ce ta dakatar da duk wani aiki a birnin Gaza saboda hare-haren da Isra'ila ke kai wa.

    Kungiyar ta ce sojojin Isra'ila sun kewaye duka cibiyoyin kiwon lafiya da ke birnin.

    Isra'ila ta umarci Falasɗinawa su fice daga birnin Gaza, wanda ta bayyana a matsayin tungar ƙarshe ta Hamas.Amma MSF ta ce dubban -- ciki har da masu matukar rauni, kamar jarirai marasa lafiya ba sa iya guduwa.

  5. Shettima ya gana da shugaban MDD kan sama wa Najeriya kujerar dindindin

    Shettima da Gutteres

    Asalin hoton, Stanley Nkwocha

    Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya gana da babban sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres a shalkwatar majalisar da ke Amurka.

    Cikin wata sanarwa da ofishin Shettiman ta fitar ta ce shugabannin biyu sun tattauna batutuwa da dama masu muhimmai ciki har da ƙudirin Najeriya na samun kujerar dindindin a Majalisar Dinkin Duniya.

    A lokacin ganawar, Shettima ya ƙarfafa buƙatar Najeriya na neman goyon bayan Majalisar Dinkin Duniyar don cimma ƙudirin nata na samun kujerar dindindin a kwamitin tsaro na majalisar.

    Shugabannin sun kuma tattauna batutuwan ƙarfafa cimma muradun ƙarni, da sauyin yanayi da ƙararra dimokradiyya a Najeriya da ma yankin Afirka.

  6. Ƴansanda sun kama kawalin da ke kai ƴanmata karuwanci a Dubai bayan binciken BBC

    mutumin rike da lasisin tuƙinsa

    Ƴansandan ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun kama gawurtaccen kawalin nan da ke kai ƴanmata Dubai tare da tilasta musu karuwanci bayan binciken BBC ya bankado shi.

    Charles "Abbey" Mwesigwa, wanda a baya-bayan nan binciken ƙwaƙwaf na BBC ya gano yadda yake gudanar d amummunarr sana'ar safarar ƴanmata domin tilasta musu yin karuwanci a Dubai.

    Ya faɗa wa wakiliyar BBC yana bayar da ƴanmata ga masu buƙatarsu a kan kuɗi daga dala 1,000 zuwa sama.

    Ya ce ƴanmatan kan yi duk abin da masu kwana da su ke buƙata su yi.

  7. Gomman wakilai sun fice daga taron MDD yayin da Netanyahu zai fara jawabi

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

    Gomman jami'an Diplomasiyya ne suka yi ta tururuwar ficewa daga babban zauren majalisar Dinkin Duniya yayin da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai fara gabatar da jawabinsa.

    Babban ɓangare na zauren ya kasance fayau yayin da Netanyahu ke gabatar da jawabin nasa, a daidai lokacin kuma masu zanga-zangar adawa da yaƙin Gaza suka taru a dandalin Times, kusa da wurin da ake taron.

    Yayin jawabin nasa Netanyahu ya soki wakilan ƙasashen musamman na Yamma da suka amince da kafuwar ƙasar Falasɗinu.

    Netanyahu ya bayyana matakin amincewar a matsayin ''alamar abin kunya'', da ya ce yana aika saƙon cewa ''kisan Yahudawa na da riba''.

    Isra'ila ta fuskanci matsalin lamba daga ƙasashen duniya kan matakin soji da ta ɗauka kan Gaza, lamarin da ya sa Birtaniya da Faransa da Kanada da Australiya da wasu ƙasashen suka amince da kafuwar ƙasar Falasɗinu a wannan mako.

  8. Ma’aikatan lantarki sun janye yajin aiki bayan gwamnati ta shiga tsakani

    ...

    Asalin hoton, BBC Hausa

    Ma'aikatan lantarki ƙarƙashin kamfanin rarraba wutar lantarki ta TCN sun dakatar da yajin aikin da suka fara, bayan shiga tsakani na gwamnatin Tarayya kamar yadda gidan talbijin na gwamnatin Najeriya NTA ya ruwaito.

    An cimma wannan sulhu ne a wani taron gaggawa da ministan wutar lantarki ya haɗa da haɗin gwiwar ma’aikatar ƙwadago da shugabannin TCN da na NISO da sauran ƙungiyoyin ma’aikata.

    Bayan dogon tattaunawa, ɓangarorin sun amince da muhimman matakai da za su ba da damar dakatar da yajin aikin

    Ƙungiyoyin sun amince da sake duba rahoton taron kwamitin da za a yi tsakanin 6 da 7 ga Oktoba 2025, domin aiwatar da shawarwarin daga baya a cikin watan.

    Wannan zai taimaka wajen ganin cewa duk wasu matsaloli an warware su kafin fara aiwatar da shawarwarin.

    An tsara wani taro na gaba tsakanin shugabannin ƙungiyoyi da kamfanoni domin tattauna sauran matsaloli da suka rage.

    Wannan zai taimaka wajen hana sake barkewar yajin aiki nan gaba.

  9. Rasidi Ladoja ya zama sabon Olubadan na 44

    ...

    Asalin hoton, @OloyeSomorin

    An naɗa tsohon gwamnan jihar Oyo Rasidi Adewolu Ladoja a matsayin sabon sarkin masarautar Ibadan Na 44.

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na daga cikin manyan bakin da suka halraci bikin naɗin, da aka gudanar da fadar sarkin.

    An gudanar da taron naɗin sabon sarkin ne a filin wasan Mapo inda jama'ar garin da baƙi da manyan baƙi tuni suka isa wurin domin halartar bikin naɗin.

    Ladoja, mai shekara 81 ya zama Olubadan na 44, bayan shekaru masu yawa da fara zama Magaji.

    Bayan ya zama Magaji a shekarar 1980, ya riƙa hawa matakai har ya kai matsayin Jagun Olubadan a shekarar 1993.

    ...

    Asalin hoton, Bayo Onanuga

  10. Kotu ta daƙile buƙatar Nnamdi Kanu ta neman a kai shi asibiti

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban Kotun Tarayya ta daƙile buƙatar Nnamdi Kanu na neman a kai shi asibiti, inda ta umarci shugaban ƙungiyar likitocin Najeriya (NMA) ya kafa kwamitin likitoci tsakanin takwas zuwa goma domin tantance lafiyar shugaban ƙungiyar IPOB da ya ke ikirarin fama da rashin lafiya mai tsanani.

    Mai shari’a James Omotosho ne ya bayar da wannan umarni yayin da ya ke yanke hukunci kan buƙatar da Kanu ya shigar, inda ya nemi a mayar da shi ɗakin kulawa na musamman a asibitin ƙasa saboda yana fama da rashin lafiya mai tsanani.

    Alƙalin ya ce kwamitin da NMA za ta kafa zai binciki ainihin matsalar lafiyar Kanu domin gano ko hakan na iya hana shi ci gaba da fuskantar shari’a.

    Haka kuma, kwamitin zai duba ingancin cibiyar kiwon lafiya ta Hukumar Tsaro ta DSS, domin tabbatar da ko za su iya kula da lafiyar wanda ake tuhuma yadda ya kamata.

    Omotosho ya kuma ƙara da cewa kwamitin zai tantance ko akwai buƙatar kai Kanu asibitin ƙasa kamar yadda ya nema, da kuma ko matsalolin lafiyar sa za su iya hana shi tsayawa gaban kotu.

    Haka zalika, kotun ta umurci babban daraktan asibitin ƙasa ko wakilinsa ya kasance cikin wannan kwamitin.

    Ya kuma uarci shugaba da sakataren kwamitin su saka hannu kan rahoton binciken sannan a mika shi ga kotu cikin kwanaki takwas daga yau (26 ga Satumba, 2025).

  11. An kama mutum 260 da zargin damfarar intanet a ƙasashen Afirka 14

    ...

    Asalin hoton, interpol

    An kama mutane kusan 260 da ake zargi da gudanar da damafar ta intanet a ƙasashe 14 na Afirka.

    Wannan aiki na musamman, wanda Interpol ta tsara tare da tallafin Birtaniya, ya mayar da hankali kan ƙungiyoyin da ke amfani da shafukan sada zumunta da intanet wajen lalube wa mutane kudi ta hanyar zamba da soyayyar ƙarya da kuma batsa ta intanet.

    Interpol ta bayyana cewa an gano fiye da mutum 1,400 a Ghana da Kenya da Angola da wasu wurare.

    Neal Jetton, daraktan sashen intanet na Interpol, ya ce waɗannan zamban sun fi shafar manya, kodayake mutane na kowane zamani na iya fadawa tarkonsu.

  12. RSF ta ƙara ƙarfi a El-Fasher, yayin da yaƙi ke ci gaba

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Dakarun RSF ta Sudan ta ƙara ƙarfi a yunƙurinta na ƙwace cikakken iko da garin El Fasher a Darfur, bayan ta mamaye wani muhimmin ginin soja a garin da ake kewaye da shi.

    Bidiyon da RSF ta saki wanda BBC ta tabbatar da ingancinsa ya nuna cewa suna wurin hedkwatar makaman artilleri, wuri da sojojin ƙasa suka riƙe a baya, wanda ke kusa da filin jirgin sama na El Fasher.

    Ana ci gaba da fafatawa a cikin birnin a yau.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana garin jiya a matsayin “cibiya ta wahala”, inda ake hasashen cewa akwai mutane kusan 260,000, ciki har da yara 130,000, da ke maƙale a cikin garin da aka kewaye fiye da kwanaki 500.

    Halin da ake ciki ya janyo damuwa a matakin ƙasa da ƙasa, yayin da al’ummomin gari ke fuskantar karancin abinci, ruwa, da kayan kiwon lafiya saboda mamayar da aka yi wa birnin.

  13. Za mu dakatar da ayyukan masu sa ido kan nukiliya idan aka sa mana takunkumi - Iran

    Jagoran addini na Iran Ali Khamenei

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Jagoran addini na Iran Ali Khamenei

    Ministan harkokin waje na Iran Abbas Agarachi ya yi gargaɗin cewa Iran za ta yi watsi da yarjejeniyar da ta ƙulla ta barin jami'an Majalisar Dinkin Duniya masu sanya ido kan nukiliya su duba cibiyoyinta, matuƙar ƙasashen Yamma suka sake ƙaƙaba mata takunkumi.

    A ranar Asabar ne ake sa ran mayar da wasu takunkumai kan Iran bayan da Birtaniya da Faransa da Jamus suka zargi Tehran ɗin da saɓa wa yarjejeniyar nukiliyar ƙasar na shekarar 2015, wadda aƙa ƙulla domin hana ƙasar mallakar makamin nukiliya.

    Hukumar kula da makamashin Atam ta Duniya na ta ƙoƙarin ganin ta gyara alaƙarta da Iran domin komawa kan aikin sanya ido kan shirin nukiliya na ƙasar, tun bayan harin da Isra'ila da Amurka suka kai kan cibiyoyin sarrafa makamashin nukiliyarta a watan Juli.

    A yau Juma'a ne ake sa ran kaɗa ƙuri'a a kwamitin tsaro na MDD game da wani ƙuduri da Rasha da China suka gabatar na ganin an jinkirta matakin ƙaƙaba wa Iran ɗin takunkumi, to amma masana diflomasiyya na ganin cewa da wuya ƙudirin ya samu amincewa.

  14. Ƴansandan Kenya sun gano gungun masu safarar mutane zuwa Rasha

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    ‘Yan sanda a Kenya sun ce sun gano wata ƙungiya da ke safarar ‘yan ƙasar zuwa Rasha bisa ƙarya da musu alƙawarin samun aikin yi.

    Jami’an sun ce waɗanda aka yaudare sun amince da shiga wannan tsarin ne da tunanin za su samu aiki na yau da kullum kafin su tafi Rasha, inda daga bisani ake tilasta musu shiga rundunar sojin ƙasar.

    A yayin gudanar da aikin, ‘yan sanda sun kama mutum ɗaya da ake zargi, sannan suka ceto mutum 21 a wani gida dake gabashin Nairobi.

    Wannan bincike ya biyo bayan bidiyon da aka ga ɗan wasan Kenya, Evans Kibet a makon da ya gabata a Ukraine, inda ya bayyana cewa an yaudare shi shiga rundunar sojin Rasha.

  15. Ba mu nemi shiga wata jam'iyya ba - Kwankwaso

    ...

    Asalin hoton, @KwankwasoRM

    Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta rahotannin da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke cewa ya tura takardar neman shiga wata jam’iyyar siyasa a ƙasar.

    Ya bayyana cewa labarin ba gaskiya ba ne, yana mai jaddada cewa ba su nemi shiga wata jam'iyya ba.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake yaɗa jita-jita cewa Kwankwaso da tawagarsa na shirin komawa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Kwankwaso ya ce: “Mun samu labarin wasu jita-jita a shafukan sada zumunta cewa mun gabatar da takardar niyyar shiga wata jam’iyyar siyasa a ƙasar. Muna so mu fayyace cewa ba mu gabatar da irin wannan bukata ga kowace jam’iyya ba.”

    Sanarwar ta kara da cewa irin waɗannan rahotanni na bogi ba su da wata manufa face rikita jama’a da kuma yaɗa ƙarya..

    “Jama’a su yi hattara da irin waɗannan labarai na bogi da ake yadawa don daukar hankalin mutane kawai,” in ji Kwankwaso.

    Kwankwaso ya kuma shawarci jama’a da su ci gaba da bibiyar sahihan bayanai daga ofishinsa da hanyoyin sadarwa na hukuma.

  16. Jam'iyyar su Bulama Bukarti Access Party ta caccaki INEC kan hana su rajista

    Tambarin ƙungiyar Access Party

    Asalin hoton, Bulama Bukarti

    Ƙungiyar Access Party (AP) da ke neman rajistar zama jam'iyyar siyasa a Najeriya ta nuna rashin jin daɗi kan matakin hukumar zaɓe ta kasa INEC da ta ƙi amincewa da bukatarsu ta samun rajistar.

    A cikin wasiƙar da INEC ta aika wa ƙungiyar ranar 12 ga Satumba 2025 - wadda suka karɓa a 19 ga Satumba - hukumar ta ce tambarin jam’iyyar bai dace ba kuma yana kama da na wata ƙungiya mai suna Democratic Leadership Party (DLP).

    A cewar jagoran kungiyar, Barrister Bulama Bukarti, "wannan dalili na INEC ba shi da tushe domin DLP ba jam’iyya ce da aka yi wa rajista ba".

    "Doka ta bayyana cewa ana iya hana tambari ne kawai idan yana kama da na wata jam’iyya mai rajista a hukumance, ba wata ƙungiya da har yanzu take kan matakin neman rajista ba," in ji sanarwar.

    "Tambarin AP da na DLP ba su kamanceceniya ba domin na AP yana dauke da kan shaho [eagle] mai launin kore da fari tare da rubutun “Access Party”, yayin da na DLP kuwa yake dauke da shuɗin tsuntsu."

    Ƙungiyar ta ce babu dalilin da zai sa ‘yan Najeriya su rikice da tambarin ko sunayen jam’iyyun biyu.

    Kungiyar ta kuma yi zargin cewa INEC ta kauce hanya wajen katse musu samun rajistar gaba ɗaya, maimakon ta buƙaci su sake sauya tambari idan ta ga bai dace ba.

  17. An kama tsohon daraktan FBI James Comey da laifuka biyu a Amurka

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahukunta a Amurka sun tabbatar zargin da ake yi wa tsohon daraktan hukumar tsaro FBI James Comey da yin karya ga majalisar dokokin kasar da kuma kawo cikas ga shari'a.

    Shugaba Trump ya kori Comey ne a shekarar 2017, jim kadan bayan da aka tabbatar da cewa yana gudanar da bincike kan alakar kwamitin yakin neman zabensa da Rasha.

    Ana tunanin tuhumar da ake wa Comey na da alaka da shaidar da ya bai wa kwamitin shari'a na majalisar dattawan kasar a shekarar 2020.

    A lokacin ne ake zargin ya musanta sakin wasu bayanan sirri ga kafafen watsa labarai game da katsalandan din da ake zargin Rasha ta yi a zaben kasar na 2016.

    Comey dai ya mayar da martani kan tuhumar da ake yi masa, inda yace yana maraba ya fuskanci shari'a a halin yanzu.

  18. ADC ta buƙaci mambobinta su daina raba ƙafa

    ...

    Asalin hoton, Atiku Abubakar/X

    Jam’iyyar ADC ta buƙaci mambobinta su daina raba ƙafa, su yi murabus daga sauran jam’iyyu sannan su mai da kai da ccikakken alƙawari ga ADC.

    Wannan na daga cikin manyan matakai uku da aka cimma a taron sirri da mambobin jam'iyyar suka gudanar a Abuja ranar Alhamis, wanda tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya halarta tare da manyan shugabannin jam’iyyar.

    A cikin taron, wanda shugaban jam’iyyar na ƙasa, David Mark, ya jagoranta, an tattauna hanyoyin haɗin kai da dabarun da za a yi amfani da su domin tunkarar zaɓen 2027.

    Haka kuma, dukkan masu sha’awar tsayawa takarar shugaban ƙasa sun amince cewa za su goyi bayan wanda ya fito daga cikin su bayan an kammala zaɓen fidda gwani.

    Atiku Abubakar ya tabbatar da halartar taron ta shafin sa na X, inda ya bayyana shi a matsayin wani yunkuri na haɗin kan ’yan adawa.

    Daga cikin mahalarta akwai tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai; tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi; tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal da dai sauransu..

    Sai dai ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, bai halarci taron ba, amma ya aike da sakon cewa yana tare da su.

  19. Trump ya ƙaƙaba sabon haraji kashi 100 kan kayayyaki daga ƙasashen waje

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Amurka ta sanar da sabbin haraji kan kayayyakin da ake shiga da su ƙasar daga ƙasashen waje.

    Shugaba Trump ya ce daga ranar Laraba, kamfanonin samar da magunguna da ke shigar da su kasar za su fuskanci harajin kashi 100 cikin 100 matsawar basu fara samar da masana'antunsu ba Amurka.

    Manazarta sun yi imanin cewa harajin zai cutar da ƙasashe irin su Ireland, wacce ta fi kowace kasa fitar da magunguna zuwa Amurka.

    Trump ya kuma ba da sanarwar ƙarin haraji kan kayayyaki daban-daban tun daga manyan manyan motoci zuwa kayan kicin da na daki da sauransu.

  20. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Juma'atu babba rana.

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.