Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/05/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/05/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza da Zubairu Ahmad

  1. 'Yan bindiga sun yi garkuwa da babban basarake a jihar Kogi

    Wasu ƴanbidga sun kai hari garin Okoloke da ke ƙaramar hukumar Yagba ta yamma a jihar ta Kogi, inda suka kashe aƙalla mutum uku are da jikkata wasu da dama.

    Maharan sun kuma yi garkuwa da babban basaraken al'ummar ta Okoloke, Pa Dada James Ogunyanda, a lokacin da ake tsaka da zaman fadanci, wanda bayanai suka tabbatar da cewa ba shi da cikakkiyar lafiya kuma yana daf da tafiya neman magani, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.

    'Yan bindigar sun kuma kashe ƴanbanga biyu da wani ma'aikacin kamfanin sadarwa da ke aikin gyaran ƙarfen samar da sabis a yankin.

    Rahotanni sun ce 'yan bangar na samar wa ma'aikacin sadarwar tsaro ne lokacin da maharan suka yi musu kwanton ɓauna inda suka buɗe musu wuta nan take.

    Hare-haren 'yan bindiga dai na ci aba da ƙaruwa a baya-bayan nan musamman a jahohin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya da ma shiyar arewa maso gabashin Najeriya. Waɗanda ke kashe mutane da garkuwa da wasu domin neman kuɗin fansa.

  2. Talauci ne tushen matsalar tsaron arewacin Najeriya - Gwamnan Kaduna

    Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya ce tsansar talauci da koma bayan tattalin arziki su ne manyan abubuwan da ke haifar da masaloli tsaro a yankin arewacin Najeriya, inda ya yi gargaɗin cewa muddin ba a magance su gaba ɗaya ba to yankin zai ci gaba da fuskantar matsalolin tashe-tashen hankaln.

    Gwamnan ya bayyana hakan a cikin shirin siyasa na Sunday Politics na gidan talibijin na Channels, inda ya ce gwamnatinsa ta soma ne da fito da hanyoyin yaƙi da talauci da rashin aikin yi tsakanin matasa, inda ya alaƙanta hakan ga irin ƙwarewar da ya ya samu lokacin da ya ke shugaban kwamitin da ke lura da bankuna na majalisar dattawan a lokacin yana ɗan majalsar dattawan.

    "Lokacin da aka zaɓe ni a matsayin gwamnan Kaduna, abinda na soma yi shi ne duba girman matsalar talaucin da ake fama da ita, ba wai a jihata kaɗai ba a'a duka yankin arewa. Na taɓa riƙe muƙamin shugaban kwamitin da ke lura da harkokin bankuna na majalisar dattawa. Ina da bayanai da dukan alƙalumman da aka tattara daga Sashen Bunƙasa Babban Bankin Najeriya (CBN). Ina mai tabbatar maka cewa girman talaucin da ake da shi a shekarar 2023, lokacin da muka zo ya kai wani matsayi mai muni" in ji gwamnan.

    A cewar sa fiye da kashi 60 zuwa 65 cikin ɗari na mutanen arewacin Najeriya - musamman a shiyar arewa maso yamma - na fama da tsananin talauci a lokacin da ya zama gwamman jihar Kaduna.

    Uba Sani ya ce hakan na iya sa matasa da dama su shiga aikin ta'addanci kasancewar ƴanbindiga za su iya ɗaukar su haya domin kai hare-hare.

  3. Gwamnatin Kano ta dakatar da nuna wasu manyan fina-finai 22

    Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da nuna wasu manyan fina-finai masu dogon zango 22 sakamakon zarginsu da saɓa ƙa'idar hukumar.

    Cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar, ya ce shugaban hukumar Abba Al-Mustapha ne ya bayar da umarin saboda a cewarsa masu shirya fina-finan sun saɓa ƙa'idojin hukumar waɗanda suka tanadi cewa dole ne hukumar ta tace su kafin a fitar da su.

    Wasu daga cikin fina-finan da dakatarwa ta shafa sun haɗa da:

    • Daɗin Kowa
    • Labarina
    • Gidan Sarauta
    • Manyan Mata
    • Ɗakin Amarya
    • Kishiyata
    • Garwashi
    • Jamilun Jiddan
    • Mashahuri
    • Wasiyya
    • Tawakkaltu
    • Mijina
    • Wani Zamani
    • Mallaka
    • Kuɗin Ruwa
    • Boka Ko Malam
    • Wayasan Gobe
    • Rana Dubu
    • Fatake
    • Shahadar Nabila
    • Tabarma
    • Rigar Aro
  4. Tinubu ya amince da bayar da lasisin ci gaba da aikin haƙar mai na Kolmani

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da ci gaba da aikin haƙar man fetur na Kolmani da ke tsakanin jahohin Bauchi da Gombe.

    Ministan albarkatun mai na Najeriya, Heineken Lokpobiri ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Nneamaka Okafo ya fitar ranar Lahadi .

    Ministan ya ce, "Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da tabbatar an bayar da duka lasisin da suka rage domin samun damar ci gaba da aikin na Kolmani".

    Ya ce tunin gwamnatin Najeriyar ta samar da wata cibiyar nazarin albarkaun man fetur da iskar gas a ƙaramar hukumar Alƙaleri da ke jihar Bachi domin tabbaar da an samu nasarar ɗorewar ci gaba da aikin.

    A watan Nuwamban 2022 ne aka fara aikin shirin haƙar mai na Kolmani, wanda ya bayar da damar soma neman ɗanyen man a shiyar arewacin Najeriya, wanda yanki ne na kogin Kolmani mai tarin arzikin man da ke tsakanin jahohin na Bauchi da Gombe.

    A makon da ya gabata shugaban kamfanin haƙar man fetur na ƙasa, Bayo Ojulari ya shaida wa BBC cewa kamfanin NNPCL ɗin zai ci gaba da aikin tono man a rijiyar ta Kolmani.

  5. Boko Haram na barazanar ƙwace ƙaramar hukumar Marte - Zulum

    Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya roƙi gwamnatin Najeriya ta fito da sabbin tsare-tsaren da za su taimaka wajen kare ƙaramar hukumar Marte daga faɗawa hannun mayaƙan Boko Haram da ISWAP.

    Zulum ya bayyana haka ne lokacin ziyara da ya kai garin a aranar Lahadi da maraice.

    Kafin ziyarar gwamnan, kusan duka mazauna garin sun gudu sakamakon harin da mayaƙan na Boko Haram da suka kai a ranar Juma'ar da ta gabata, inda dubban mutane suka soma gudun hijira a garin Dikwa da ke jihar.

    Gwamnan ya shaida wa manema labarai cewa ya yi ziyarar ne domin samar da haɗin kan jama'a da ƙarfafa gwiwar al'ummar da kuma ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro.

    A cewar sa, "an sake dawo da mutanen garin na Marte kusan shekaru huɗu da suka gabata, amma abin takaici cikin kwanaki uku an kai musu farmaki inda aka sake tarwatsa mazaunansa.”

    Ya ce, "akwai kimanin mutum 20,000 da suka bar garin zuwa Dikwa, kuma wannan adadi na da yawa wanda hakan zai ya barazana muddin aka tsugunnar da su a sansanonin 'yan gudun hijira domin hakan zai iya jefa ƙananan yara cikin haɗarin shiga ayyukkan ta'addanci''.

    "Alhamdulillahi, mun sake zuwa Marte kuma mun kwana a garin tare da taimakon jami'an tsaro da 'yan-sa-kai. Yanzu dai an sake maido da jama'a a karo na biyu. Kuma muna roƙon gwamnatin tarayya da jami'an sojoji su yi duk mai yiyuwa domin tsare wannan gari".

    Zulum ya ce a yanzu haka ƙaramar hukumar Marte na cikin hatsarin faɗa wa hannaun mayaƙan Boko Haram.

    “A baya ƙaramar hukumar Marte na da garuruwa da ƙauyuka fiye da 300, amma a yanzu gari ɗaya ne kawai ke hannun gwamnati, idan ba mu iya riƙe shi ba, za mu iya rasa duka ƙaramar hukumar...'', in ji gwamnan.

  6. Isra'ila ta ce za ta bari a shigar 'Abincin da aka fi buƙata' zuwa Gaza

    Isra'ila ta ce za ta bari a shigar da 'abincin da aka fi buƙata' zuwa Gaza domin tabbatar da cewa ''ba a samu matsalar yunwa ba'', bayan hana shigar da agaji na tsawon mako 10 zuwa yankin.

    Cikin wata sanarwa daga ofishin firaministan ƙasar, ta ce an ɗauki matakin ne bisa shawarar rundunar sojin ƙasar IDF.

    "Isra'ila za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin agajin bai faɗa hannun mayaƙan Hamas ba, domin hana ƙungiyar yin iko da agajin,'' in ji sanarwar.

    Isra'ila ta riƙa fuskantar matsain lamba domin ta ɗage hana shigar da agajin, inda aka hana abinci da man fetur da kuma magunguna.

    Sanarwar na zuwa ne sa'o'i bayan sojojin Isra'ila sun ce sun fara kai hare-kare ta ƙasa a duka faɗin Gaza.

  7. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin, Mande tushen aiki ko da Nasara na tsoronki, kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza tare da Zubairu Ahmad ke fatan sake kasancewa da ku a wannan shafi domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kuna iya kasancewa da mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.