Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 09/07/2025

Wanan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 09/07/2025

Rahoto kai-tsaye

Umaymah Sani Abdulmumin, Abdullahi Bello Diginza, da Umar Mikail

  1. Gwamnati na shirin sake kara kuɗin lantarki a Najeriya

    Ministan Lantarki a Najeriya, Adebayo Adelabu, ya ce gwamnatin Najeriya na nazarin ƙarin kuɗin lantarki a kokarin cike giɓin bashin naira tiriliyan huɗu da ake bin ɓangaren.

    Adebayo da ke waɗannan bayanai a taron masu ruwa da tsaki a Abuja, ya ce ta wannan hanya ce kaɗai za a iya ceto ɓangaren da kuma cigaba da gudanar da ayyukansa.

    Duk da karin ƙudin lantarki da aka yi wa kwastamomi da ke tsarin Band A, 'yan Najeriyar na kokawa ganin cewa wutar ba ta waɗatar da su.

    Amma Adelabu ya ce matakin na da muhimmanci wajen inganta tattalin arziki da cigaban ƙasar.

    Wannan dai na nufin gwamnatin za ta kawo ƙarshen tsarin tallafin da ake bai wa ɓangaren lantarki, yanayin da zai tilasta ƙarin kuɗin wuta ga kowa.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta rawaito cewa a watannin shida na farkon wannan shekarar gwamnati ta biya tallafin naira tiriliyan ɗaya da miliyan ɗaya domin cike gibin da masana'antar ke fuskanta, wannan ƙari ne kan tiriliyan huɗu.

  2. BBC ta gano Sheikh Hasina da take haƙƙin bil adama

    Wani bincike da BBC ta gudanar ya gano cewa tsohuwar Firaministar Bangladesh, Sheikh Hasina, ta bai wa jami'an tsaronta izinin yin amfani da karfi domin murkushe masu zanga-zangar da aka yi a bazarar da ta gabata.

    Kimanin mutane dubu ɗaya da dari hudu ne aka kashe yayin da aka jikkata wasu dubu goma sha biyu a zanga-zangar da dalibai suka yi na nuna adawa da sabuwar dokar da ta taƙaita guraben samun ayyukan gwamnati.

    A wata murya da aka naɗa kuma BBC ta tabbatar da sahihancinta, an ji Sheikh Hasina na cewa ta bai wa jami’an tsaronta izinin harbin masu zanga-zangar a duk inda aka same su.

    Tuni dai hukumomin Bangladesh suka tuhume ta da laifin cin zarafin bil adama.

  3. Har yanzu ba a ga mutum 160 bayan ambaliyar Texas

    Gwamnan jihar Texas ta Amurka ya ce sama da mutane 160 ne har yanzu ba a gano ba sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a ranar Juma'ar da ta gabata.

    Greg Abbott ya ce wannan adadi na lardin Kerr ne kaɗai, ɗaya daga cikin wuraren da lamarin ya fi muni.

    Hukumomi dai sun bayar da rahoton mutuwar fiye da mutum 100.

    Masu aikin ceto na aiki a sannu a ƙoƙarin kawar da tarkacen da ruwan ya janyo domin gano ko akwai mutanen da ke maƙale a ƙarƙashinsu musamman a yankin gaɓar kogin Guadalupe.

    A jihar New Mexico da ke makwabtaka da Texas, ruwa ya tafi da wani gida inda wani uba ke zaune da 'ya'yansa biyu a yankin Ruidoso, kuma har anzu ana kan nemansu

  4. Assalam alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiya.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a fain duniya.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.