Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/02/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza

  1. Hamas za ta saki waɗanda take garkuwa da su idan yanayi ya daidaita - Jami'an ƙungiyar

    Hamas ta ce "tana ci gaba da jajircewa kan aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta" amma ta jaddada cewa Isra'ila ce ke da ''alhakin duk wani rikici ko jinkiri da za a samu''.

    Wani babban jami'in ƙungiyar, Basem Naim ya shaida wa BBC cewa ƙofar ƙungiyar a buɗe take ga Amurka da Qatar da kuma Masar masu shiga tsakani, da su sanya baki domin komawa aiki da yarjejeniyar.

    "Ba ma fatan wannan yarjejeniya ta wargaje," a cewarsa. "Muna yin duk mai yiwuwa don kauce wa duka wani abin da zai kawo tarnaƙi ko barazana ga yarjejeniyar, don haka a shirye muke mu miƙa fursunonin da ke hannunmu a ranar Asabar mai zuwa idan masu shiga tsakanin suka daidaita lamura''.

    Haka kuma ƙungiyar ta yi fatali da shirin Donald Trump na ''karɓe ikon'' Gaza, tana mai kiran kalaman shugaban da ''wariyar layunin fata'', sannan ta ce shirin ba zai yi nasara ba.

  2. Isra'ila ta bai wa Hamas wa'adin sakin ƴanƙasarta ko ta koma yaƙi

    Isra'ila ta ce za ta koma yaƙi tare da fatali da yarjejeniyar tsagaita wuta, matsawar Hamas ba ta saki Isra'ilawan da ke take garkuwa da su ba a ranar Asabar.

    Firaministan Isra'ila Benjami Netanyahu bai fayyace ko yana nufin duka mutanen da Hamas din ke garkuwa da su, ko kuma ukun da aka tsara saki a ranar ƙarƙashin yarjejeniyar.

    Netanyahu ya umarci dakarun ƙasarsu su taro a ciki da kewayen Gaza, yayin da Hamas ke cewa Isra'ila ce ''ta janyo duk abin da ya faru na jinkirin da aka samu''.

    Ƙungiyar ta ce ta jinkirta sakin mutanen da aka tsara za ta saki a ƙarshen makon da muke ciki, bayan da ta zargi Isra'ila da saɓa wa sharuɗan yarjejeniyar, sai dai ta ce har yanzu tana son ci gaba da aiki da yarjejeniyar.

    An fahimci cewa ƙasashen Larabawa na matsa wa ƙungiyar lamba kan komawa aiki da yarjejeniyar.

    Tun da farko shugaban Amurka, Donald Trump ya yi gargaɗin cewa idan ba a saki Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su a Gaza ba ''za a yi duk bala'in da za a yi'', matakin da Netanyahu ya yi maraba da shi a ranar Talata.

    Kawo yanzu Falasɗinawa da suka koma Gaza byan fara aiki da yarjejeniyar, na cikin fargaba da tashin hankali.

  3. Birtaniya ta tsaurara dokokin shige da fice

    Gwamnatin Birtaniya ta tsaurara dokokin shige da fice, lamarin da ya sa mutanen da suka isa ƙasar a cikin ƙananan kwale-kwale zai musu matuƙar wahala kafin su samu takardar shaidar zama ƴan ƙasar.

    A ƙarƙashin sabuwar dokar, duk wanda ya shiga Birtaniya ba bisa ƙa'ida ba, duk daɗewar da zai yi ba zai samu shaidar zama ɗan ƙasar ba.

    Hukumar ƴan gudun hijira ta Birtaniyar da wasu daga cikin ƴan jami'iya mai mulki ta Labour sun yi Allah wadai da matakin.

  4. Masar ta ce za ta gabatar da kundin sake gina Gaza

    Masar ta ce za ta gabatar da cikakken kundin da za a yi amfani da shi wajen sake gina Gaza ba tare da an raba Falasɗinawa da Zirin ba.

    Hakan na zuwa ne bayan tattaunawar da shugaba Trump ya yi da sarkin Jordan a jiya Talata.

    Trump ya shaida wa ƴan jarida cewa Amurka na da ikon mallakar Gaza, yayin da sarki Abdallah ya dage cewa mafita guda ita ce a samar da ƙasashe biyu domin tabbatar da zaman lafiya a Gaza.

    Sarki Abdallah ya ce dole ne mu san cewa akwai wani shiri daga Masar da sauran ƙasashen Larabawa da ke yi.

    Sarkin na Jordan ya ce Yariman Saudiyya, Muhammad bin salman ya gayyaci shugabannin ƙasshen Larabawa zuwa Riyad domin tattauna batun ta hanyar lalabo hanyar da za a bi, ayi gyara ba tare ran kowa ya ɓaci ba.

  5. Asslamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkamu da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Muna fatan sake kasancewa da ku a wannan lokaci domin kawo muku yadda duniyar ta wayi gari.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.