Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/02/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza

  1. Majalisa ta gayayci shugaban hukumar Kwastam kan ƙin yi wa wasu ritaya

    .

    Asalin hoton, Others

    Kwamitin majalisar wakilan Najeriya, da ke karbar koken al'umma ya gayyaci shugaban hukumar Kwastam na kasa, Adewale Adeniyi a gabanta kafin ranar Talatar mako mai zuwa.

    Gidan talabijin ta Channels ya rawaito cewar, Chooks Oko, ya ce tilas ne Adeniyi ya bayyana a gaban kwamitin don ya kare kansa daga wani koke da ake yi akan nasa na gaza yi wa wasu jami'an hukumar ritaya, duk da cewar lokacin barinsu aiki ya cika.

    Gidauniyar Obasi-Pherson ce dai ta shigar da koken ta gaban majalisar ta 10, inda suka yi zargin cewar mataimakan kontirola da lokacin ajiye aikinsu ya yi har yanzu sun ki ajiyewa.

    A wani ci gaban kuma Sanarwar ta Oko ta kuma ce kwamitin ya yi barazanar bayar da umarnin da aka kama shugaban hukumar katin dan kasa NIMS ida ta gaza bayyana a gabanta don amsa wasu tambayoyi, da suka shafi gaza biyan kudin aikin da wani kamfani mai zaman kansa ya yi.

  2. Trump da Putin sun tattauna ta waya kan yaƙin Ukraine

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Donald Trump na Amurka ya ce ya yi wata doguwar tattaunawa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, wanda a yayin tattaunawar ya amice da yin aiki tare da shi wajen kawo karshen yakin Ukraine.

    Trump ya ce dukkaninsu sun amince cewar dole ne a kawo karshen kisan da ake yi. Ya ce wakilai daga Amurka da Rasha zasu fara tattaunawa na take. Shugaban Amurka ya godewa Mr Putin, sannan ya ce zasu ziyarci kasashen juna.

    Fadar Kremlin ta ce ta yi maraba da shawarar, da lokacin yazo da za za ai aiki tare.

    Ganawar karshe da aka yi a tsakanin shugabanin Rasha da Amurka ita ce wadda suka yi shekaru hudu da suka gabata, tun gabanin Rasha ta fara kaddamar da fara kai hari tare da mamaye Ukraine.

  3. Kwamitin gudanarwa na Jam'iyyar PDP ya tabbatar da Udeh-Okoye a matsayin Sakataren ta na kasa

    .

    Asalin hoton, PDP

    Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP ya tabbatar da Sunday Ude-Okoye a matsayin sakataren jam'iyyar na kasa.

    Jarridar The Punch ta ce hakan dai na cikin wata sanarwa da kwamitin gudanarwar ya fitar mai ɗauke da sa-hannun sakataren yada labarai na jam'iyyar ta PDP na kasa Debo Ologunagba ya fitar a ranar Laraba.

    Sanarwar ta ce ta dauki wannan mataki ne domin yin biyayya ga hukuncin da kotun daukaka kara ta yi kan batun.

    Haka kuma sanarwar ta ambato, cewar tuni ta aikawa da hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, matsayar da suka cimma na tabbatar da Sunday Udeh-Okoye a matsayin halastacen sakataren jam'iyyar tasu na kasa, da sauran dukkan hukumomin da suka kamata, kamar yadda hukuncin kotun daukaka karar ya bayar da hukunci.

    "Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP a zaman da muka yi a yau Laraba, 12 ga watan Fabarairun, 2025, mun amince da wannan takarda mai kwanan watan 11 ga watan Fabarairun, 2025, ga shugaban jam'iyyarmu na riko, kan dukkan wani batu da ya shafi dambarwar sakataren jam''iyyar PDP.

  4. Mun kashe manyan "ƴanta'adda" a jihohin Zamfara da Sokoto - Sojoji

    ..

    Asalin hoton, NDH

    Rundunar Fansan yamma da ke yaƙi da ƴan bindiga a jihohin Zamfara da Sokoto ta ce ta samu gagarumar nasarar karya lagon "yanta'adda" daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Fabrairun 2025.

    Rundunar wadda ta shaida hakan a wata sanarwa da ta fitar ta hannun mai magana da yawunta, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, ta ce aikin da rundunar ta yi ya ci galaba kan "ƴanta'adda" da suka haɗa da manyan ƴanbindiga.

    A yayin aikin rundunar, dakarun soji sun yi nasarar kashe gomman "ƴanta'adda" da suka haɗa da manyansu irin su Kachalla na Faransa da Dogon Bakkwalo da Auta Gobaje da Dan Mai Dutsi.

    Sanarwar ta ce yawancin ƴanbindigar na addabar al'ummar yankunan da ke ƙananan hukumomin Shinkafi da Zurmi da ke jihar Zamfara da kuma ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto

  5. Dole ɓangarori biyu su munta yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza - Guterres

    Guterres

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakatare Janar na Mjalaisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres- ya buƙaci Isra'ila da Hamas su tabbatar da cewa yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza ta kai ga gaci.

    Guterres ya yi kira ga Hamas da ta saki waɗanda take garkuwa da su ranar Asabar inda ya yi kira ɓangaren Isra'ila da ya mutunta yarjejeniyar ta hanyar komawa kan teburin sulhu a Doha a zango na biyu na yarjejeniyar.

    A wata sanarwa da aka fitar a birnin Geneva ranar Talata, Guterres ya ce "dole ne mu guji mayar da hannun agogo baya a Gaza domin hakan zai haifar da mummunan bala'i."

    Guterres ya ƙara da cewa buƙatar Majalisar Ɗinkin Duniya ita ce shigar kayan agaji Gaza wanda ake da buƙata sosai.

  6. Wakilan Hamas sun isa Alqahira domin tattaunawar tsagaita wuta

    Wata tawagar wakilan ƙungiyar Hamas ta isa birnin Alƙahira domin tattaunawa kan yarjejeniyar tsagaita wuta kamar yadda kafar watsa labara mai goyon bayan Hamas ta rawaito.

    Tuni dai tawagar ta fara tattaunawa da jami'an ƙasar Misra dangane da yadda za a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar.

    Ƙasar Masar ce dai kan gaba wajen sasantawa a yarjejeniyar da ake yi tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hamas.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito wani jami'in Hamas yana cewa " tawagar za ta tattauna hanyoyin warware taƙaddamar da ta dabaibaye yarjejeniyar da kuma tabbatar da kawo ƙarshen mamaya."

    Tunda farko dai ƙungiyar Hamas ta saki wata sanarwa cewa tana godiya ga Jordan da Masar bisa watsi da suka yi da batun kwashe Falasɗinawa daga Gaza da Trump ke son yi.

  7. Ƙungiyar ƙwadago ta nemi ƴan Najeriya su ƙaurace wa kamfanonin sadarwa

    Joe Ajero

    Asalin hoton, Others

    ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, NLC ta nemi kamfanonin sadarwar na da ke aiki a Najeriya da su janye sabon farashin su kuma koma wa tsohon farashi cikin gaggawa.

    A wata takardar bayan taro da ƙungiyar ta fitar wanda ta gudanar ranar Talatar nan a birnin Lokoja na jihar Kogi, NLC ta ɗauki wasu matakai guda bakwai kan al'amarin kamar haka:

    • Janye ƙarin farashin da komawa tsohon farashi har zuwa lokacin da kwamitin da ƙungiyar ta kafa ya kammala gudanar da bincike.
    • Ƙungiyar ta buƙaci ma'aikatan Najeriya da sauran ƴan ƙasa da su ƙaurace wa kiran waya ko amfani da datar kamfanonin MTN da Airtel da Glo a kowacce rana daga ƙarfe 11:00 na safe zuwa ƙarfe 2:00 na rana na kowace rana har zuwa ƙarshen watan Fabrairu.
    • Ta umarci ƴan Najeriya da su daina sayen data daga kamfanonin
    • Ƙungiyar na buƙatar kamfanonin su dawo wa Najeriya da kuɗaɗen da suka kwashewa ƴan ƙasar
    • Ƙungiyar za ta jagoranci rufe ayyukan kamfanonin ranar 1 ga watan Maris idan dai har ba su janye sabon ƙarin da suka yi ba ya zuwa ƙarshen watan Fabrairu.
    • Ƙungiyar ta umarci dukkannin rassanta na jihohi da su zaburar da mambobinsu gabanin 1 ga watan na Maris.
    • Ƙungiyar ta umarci dukkan sauran sassanta da su ja hankalin mambobinsu wajen ƙaurace wa kira ko amfani da datar kamfanoni a sa'o'in da aka ayyana
  8. Ƙudirin haraji ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilan Najeriya

    'yan majalisa

    Asalin hoton, NASS

    Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da ƙudirin haraji a karatu na biyu, bayan zazzafar muhawara kan ƙudirin tsakanin 'yan majalisar.

    Tun da farko majalisar ta haɗe duka ƙudurorin harajin huɗu da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya aike mata a shekarar da ta gabata zuwa ƙuduri guda kafin fara muhawara a kansa.

    Shugaban masu rinjaye na majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere ne ya jagoranci muhawarar, wanda ya ce kuɗurin zai taimaka wajen farfaɗo da fannin karɓar haraji na ƙasar.

    Farfesa Ihonvbere ya yaba wa ƙoƙarin ƙungiyar gwamnonin bisa kwaskwarimar da suka yi wa ƙudurin, da nufin ,magance matsalolin da aka yi fargabarsu tun da farko.

    Ƙudirin harajin ya haifar da zazzafar muhawara takanin 'yan ƙasar, musamman waɗanda suka fito daga yankin arewacin ƙasar, inda suka riƙa zargin cewa sabon ƙudirin zai cutar da yankin.

    A farkon wannan shekarar ne ƙungiyar gwamnonin ƙasar suka amince da kuɗurin bayan sun yi masa kwaskwarima dangane da yadda za a raba harajin VAT.

  9. Babban layin lantarkin Najeriya ya sake samun matsala

    Lantarki

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban layin lantarki na Najeriya ya samu wata matsala, lamarin da ya haifar da ɗaukewa lantarkin a wasu sassan ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da kamfanin rarraba wutar lantarki na birnin Abuja ya fitar a shafinsa na X, ya ce matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safe.

    Sai dai kamfanin ya ce masu ruwa da tsaki na aiki tuƙuru domin maido da wutar da zarar an magance matsalar.

    Babban layin lantarki na Najeriyar ya saba samun matsalolin faɗuwa, musamman a shekarar da ta gabata, wani abu da ke haifar da matsalar ɗaukewar wutar a faɗin ƙasar.

  10. Kongo ta maka Rwanda a kotu kan tallafa wa ƙungiyar ƴan tawaye

    Ƙasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ta maka takwararta ƙasar Rwanda a gaban kotun 'yancin ɗan'adam bisa zargin ayyukan take haƙƙin bil'adama da Rwandar aikata a Kinshasa.

    Zargin na da alaƙa da faɗan da ake ci gaba da ake yi a gabashin DR Congo, inda ƴantawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda ke kai hare-hare.

    Sauraron ƙarar da aka yi a birnin Arusha na ƙasar Tanzaniya, ya mayar da hankali kan ko kotun take haƙƙin bil-adamar ta Afirkan, na da hurumin sauraron ƙasar.

    Rwanda ta ce kotun ba ta da hurumin sauraron ƙasar, tana mai cewa an kafa ta ne domin sauraron ƙararrakin da ɗaiɗakun mutune ko ƙungiyoyi suka shigar, amma ba ƙasashe ba.

  11. Hukumomin Ghana na farautar tsohon ministan kuɗin ƙasar ruwa-a-jallo

    Tsoffin ministan

    Asalin hoton, MINISTRY OF FINANCE/FACEBOOK

    Ofishin mai shigar da ƙara na musamman na Ghana, ya ayyana neman tsohon ministan kuɗin ƙasar, Ken Ofori-Atta, kan zargin hannu a manyan badaƙalar cin hanci a ƙasar.

    Toshon ministan na fuskantar bincike kan haifar wa ƙasar asarar kuɗi, bayan da aka bayar da rahoton cewa ya kashe dala miliyan 58 wajen aikin gina babbar majami'ar ƙasar, ba tare da ganin wani aikin kirki ba da kuma wasu sauran laifuka.

    Mai shigar da ƙara na musamman na ƙasar, Kissi Agyabeng, ya ce tsohon ministan ya fice daga ƙasar domin guje wa bincike.

    Mista Agyabeng ya kuma ce tuni hukumomin ƙasar suka bai wa tsohon ministan wa'adin komawa ƙasar domin fuskantar tuhume-tuhumen da ake yi masa.

    “Ko dai ka dawo ƙasar bisa raɗin kanka domin fuskantar zarge-zargen da ake yi maka, ko kuma ofishin OSP ya tilasta dawowarka.''

    Wannan zargi na daga cikin manyan zarge-zargen cin hanci da ake yi wa gwamnatin Akufo-Addo da ta gabata.

    Shugaban ƙasar, John Mahama ya kafa kwamitin da aka yi wa laƙabi da ''kwamitin ƙwato duka abubuwan da aka ɓarnata', wanda kawo yanzu ya karɓi ƙorafe-ƙorafen cin hanci fiye da 200 da suka kai na fiye da dala biliyan 20.

    Shugaba Mahama ya umarci babban lauyan gwamnati da ministan shari'ar ƙasar su fara gudanar da bincike kan zarge-zargen, yana mai cewa Ghana ba za ta taɓa zama mafakar masu cin hanci ba.

    Sai dai wasu 'yan ƙasar na sukar Shugaba Mahama saboda ƙin ci gaba da shari'o'in cin hanci da ake da ake yi wa tsoffin muƙarrabansa.

  12. 'Jordan na aiki da Masar kan shirin sake gina Gaza'

    Firaministan Jordan, Jafar Hassan, ya ce ba wanda zai raba Falasɗinawa daga Gaza.

    Ya kuma ce ganawar da Sarki Abdullah na Jordan ɗin ya yi da shugaban Amurka, Donald Trump a jiya ta ƙara jaddada matsayin Jordan na sake gina Gaza, ba tare da Falasɗinawa sun fice daga Gaza ba.

    ''Jordan na aiki da Masar da kuma Falasɗinu domin fito da daftarin sake gina Gaza'', kamar yadda ya bayyana.

    Tun da farko mun bayar da rahoton cewa, ita ma Masar ta ce za ta gabatar da ''cikakken kundin'' sake gina Gaza.

  13. Gwamnan Neja zai karya farashin kayan abinci saboda azumi

    Umaru Mohammed Bago

    Asalin hoton, Umaru Mohammed Bago/facebook

    Gwamnan jihar, Mohammed Umar Bago ya bayyana aniyar gwamnatinsa na bayar da tallafi domin rage farashin kayan abinci a lokacin watan ramadan.

    Bago ya bayyana hakan ne a lokacin da wakilan gidauniyar Gates suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin jihar da ke Minna, kamar yadda sakataren yaɗa labaran gwamnan, Bologi Ibrahim ya bayyana cikin sanarwar da ya fitar.

    Gwamnan ya ce matakin zai kawo wa al'ummar jihar sauƙin sayen kayan abinci a lokacin azumin.

    Umar Bago ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta noma tan miliyan guda na masara, yana mai cewa ta hanyar abincin da jihar ta noma ya taimaka wajen daidai farashin kayan abinci a faɗin ƙasar.

    Hakazalika ya jaddada buƙatar samun haɗin kan gidauniyar Gates ta fuskar noman rani wanda ya bayyana a matsayin sana’ar da za ta iya amfanar da al'umma da magance sauyin yanayi.

    Jagoran ayyukan noma na gidauniyar Gates, Obai Khalifa ya ce tun kafuwar gidauniyar, shekara 25 da suka gabata, ta himmatu wajen gina rayuwar al'umma.

    Mista Khalifa ya bayyana noma a matsayin muhimmin abu ba kawai a mahangar tsaro ba, har ma da samar da abinci mai gina jiki.

  14. Kotu ta ƙi bayar da belin Farfesa Yusuf Usman

    Hoton motar ɗaukar ɗaurarru zuwa kotu

    Asalin hoton, Ladan Salihu/Facebook

    Babbar kotun Abuja ta yi watsi da buƙatar belin da lauyoyin, tsohon shugaban Hukumar Inshoran Lafiya ta Najeriya, Farfesa Usman Yusuf.

    Hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa ce dai ta gurfanar da Farfesan bisa zargin bayar da kwangila ba bisa ƙa'ida ba a lokacin da yake jan ragamar hukumar.

    Kama tsohon shugaban hukumar Inshorar ya haifar da zazzafar muhawara a ƙasar, inda wasu ke zargin bi-ta-da-ƙulli ne.

    A yanzu dai kotun ta ɗage sauraron buƙatar belin zuwa ranar 27 ga watan Fabrairun da muke ciki.

  15. Ɗaliban Jamhuriyar Nijar na alhinin kisan ƴan'uwansu

    Daliban Nijar

    Asalin hoton, Getty Images

    Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ɗalibai ta Nijar (USN), ta shirya wani gagarumin taro domin tunawa da ɗaliban ƙasar uku da aka kashe a lokacin wata zanga-zangar lumana a 1990.

    Ƙungiyar na kiran hukumomin ƙasar su yi adalci ga tsoffin ɗaliban da aka kashen.

    Miliyoyin ɗaliban ƙasar ne suka suka taro a birnin Yamai domin gangamin neman adalciga ɗaliban.

    Babban sakaten haɗakar ƙungiyar ta USN, Effred Mouloul Alhassane ya ce suna kira kira ga hukumomin mulkin sojin ƙasar su yi adalci ga kisan ɗaliban da aka yi a 1990.

    Kuma ce ''a wannan lokaci na yaƙi da barazanar ƙasashen Yamma masu mulkin mallaka, muna sahun gaba a yaƙin da ake yi da zaluncin Najeriya da Benin da kuma Faransa''.

  16. Ƴan Najeriya na kokawa kan ƙarin kuɗin data da na waya

    Wani mutum ke kiran waya

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu amfani da wayoyin sadarwa a Najeriya na ci gaba da kokawa kan ƙarin kuɗin kiran waya da na data da kamfanonin sadarwa a ƙasar suka yi.

    A farkon makon nan kamfanin MTN - kamfanin sadarwa mafi girma ƙasar - ya ninka farashin kiran waya da na data har kusan sau uku, yayin da ake sa ran sauran kamfanoni su aiwatar da ƙarinsu cikin kwanaki masu zuwa.

    Ƙarin farashin na zuwa ne bayan amincewar da hukumar sadarwar ƙasar ta yi wa kamfanonin na ƙarin kashi 50 cikin 100.

    Lamarin zai yi matuƙar tasiri ga ƴan ƙasar - waɗanda ke fama da tsadar rayuwa - yayin da hauhawar farashi ta kai mataƙin da da a taɓa gani ba cikin shekara 30.

  17. Dakarun RSF sun kai samame sansanin ƴangudun hijira mafi girma a Sudan

    Sansanin ƴangudun hijira na gundumar al-Huri a birnin Gedaref

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotonni daga Sudan na cewa dakarun RSF sun kai samame sansanin ƴangudun hijira na Zamzam a jihar Darfur ta Arewa.

    Ƴangudun hijirar da ke zaune a sansanin sun ce an lalata sansanin tare da cinna wuta a wata kasuwa da ke kusa da wurin.

    Tun a shekarar da ta gabata ne sansanin ke fuskantar hare-haren makamai ta sama.

    To sai dai wannan ne karon farko da aka zargi RSF da aika dakaru ta ƙasa zuwa sansanin, tun bayan fara yaƙin basasar ƙasar kusan shekara biyu da suka gabata.

    Ana kallon wannan samame a matsayin wani mataki na faɗaɗa mamayar da mayaƙan ke yi daga birnin El Fasher da ke kusa da sansanin, ɗaya daga cikin wuraren da yaƙin ya fi ƙamari.

    Akwai ƴangudun hijira kusan rabin miliyan a sansanin na Zamzam, waɗanda ke fama da matsananciyar yunwa.

  18. Majalisa ta buƙaci rundunar ƴansandan Najeriya ta yi bayani kan ɓatan bindigogi

    Makamai

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Dattawan Najeriya na bincike kan rahotonnin ɓacewar fiye da bindigogi 178,000, yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da addabar wasu yankunan ƙasar.

    Haka kuma majalisar ta ce za ta gudanar da bincike kan rarraba kwangilar sayen makamai da ya kai na naira biliyan 1.1, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.

    Cikin wani rahoton bincike da ofishin babban mai binciken kuɗi na ƙasar ya gabatar wa majalisar a 2019, ya ce ya gano yadda aka rarraba kwangilar sayen makaman.

    Rahoton ya bayyana cewa "a watan Disamban 2018 akwai bindigodi 178,459 ciki har da ƙirar AK-47 88,078 da ba a san inda suke ba.

    Haka ma zuwa watan Janairun 2020, aƙalla bindigogi da pistol 3,907 ne suka ɓata.

    Ƴan majalisar dattawan sun ce suna fargabar bindigogin su faɗa hannun ɓata-gari, da ke ƙara dagula matsalar tsaro musamman a ƙasar da ke fama da rikicin Boko Haram da ƴanfashin daji da masu garkuwa da mutane.

    Yayin da yake jawabi a madadin Babban Sifeton Ƴandan ƙasar, Mataimakan sifeton ƴansandan ƙasar, AIG Abdul Sulaiman ya ce wasu daga cikin bindigogin an sace su ne a lokacin fashi da hare-haren da ake kai wa ƴansanda.

    Ya kuma buƙaci kwamitin majalisar dattawan ya ba shi ƙarin lokaci, domin gabatar da cikakken rahoto kan bindigogin da ba a san inda suken ba.

  19. Majalisar Wakilan Najeriya ta buƙaci a janye ƙarin kuɗin kiran waya da na data

    ƴanmajalisar wakilai

    Asalin hoton, NASS

    Majalisar wakilan Najeriya ta buƙaci hukumar da ke kula da kamfanonin sadarwa ta ƙasar, NCC ta janye karin kuɗin kira da na data da kamfanonin sadarwar suka yi.

    Karin kuɗin kiran na kashi 50 cikin 100 da Kamfanonin sadarwar suka yi ya soma aiki cikin makon nan.

    Sai dai majalisar wakilan ta ce yin ƙari a wannan lokacin ba adalci ba ne saboda ƴanƙasar na cikin matsin rayuwa.

    Hon. Umar Ajilo daga jihar Kaduna ya shaida wa BBC cewa majalisar ba za ta amince da wannan ƙarin ba.

    ''Duba da irin wannan yanayi da ƴanƙasa ke ciki na matsin rayuwa da rashin aikin yi da rashin abubuwan more rayuwa, ba yadda za a yi, a yi musu ƙari, wannan bai kamata ba'', a cewar ɗan majalisar.

    Ya ƙara da cewa la'akari da rashin kyawun sadarwar da ake fama da ita a ƙasar, ƙarin bai dace ba.

    Ya ci gaba da da cewa maalisar wakilan ta buƙaci hukumar NCC ta zauna domin janye wannan mataki.

    Hon Umar Ajilo ya ce idan abin ta citura, majalisar ka iya gayyato jagororin hukumar NCC domin su zo su yi mata bayani kan dalilin ƙin janye matakin.

  20. Ba sabuwar budurwata ce ta raba ni da matata ba - 2Baba

    Mawaƙi da 'yar majalisa

    Asalin hoton, natashairobosa_oi/Instagram

    Fitaccen mawaƙin nan na Najeriya 2Baba da aka baya a ka fi sani da 2face, ya ce ba sabuwar budurwa da ya yi ce ta raba shi da matarsa ba.

    Wani bidiyo da mawaƙin ya wallafa a shafinsa sada zumunta ranar Litinin tare da ƴarmajalisar dokokin jihar Edo, Natasha Osawaru ya karaɗe shafukan sada zumunta.

    A makonnin baya ne dai 2Baba ya bayyana rabuwa da matarsa, Annie Macaulay Idibia bayan fiye da shekara 10 suna tare.

    Bayyanar sabon bidiyon nasa da ƴar majalisar jihar ta Edo, ya sa wasu sun riƙa zargin cewa ita ce sanadin rabuwarsu da matar tasa.

    To amma mawaƙin mai shekara 49 ya musanta zarge-zargen cikin wani bidiyon na daban da ya wallafa, yana mai cewa ba ta da hannu a rabuwarsa da matar tasa.

    ''Na ga wasu mutane suna ta soki-burutsu da zarge-zarge marasa tushe kan rabuwata da matata, inda suke ɗora alhakin hakan kan Honorable Natasha''.

    ''Amma magana ta gaskiya, Natasha ba ta san komai ba kan rabuwarmu da matata, ita budurwa ce da ba ruwanta da wani, budurwa ce mai hazaƙa da basira'', a cewar mawaƙin.

    Sai dai mawaƙin ya ce ba zai hana mutane ci gaba da zarge-zargen da suke yi ba.