Farashin mai ya tashi bayan gaza cimma matsaya a
tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran, da kuma sanarwar da
Washington ta yi cewa za ta rufe mashigar tekun Iran baki ɗaya.
Farashin ɗanyen mai na Brent ya tashi da fiye da
kashi bakwai cikin ɗari, inda ya kai dala 103 kowacce ganga.
Iran dai ta yi gargaɗin cewa za ta kai hari kan
duk wani jirgin ruwan soji da ya doshi mashigar Hormuz.
Sa'o'i bayan alwashin Shugaba Trump na hana
zirga-zirgar jiragen ruwan, rundunar sojin Amurka ta yi ƙarin haske kan batun,
inda ta ce matakin zai shafi jiragen ruwa ne da kodai suka tashi daga gaɓar
tekun Iran ko kuma suke kan hanyar zuwa can.
Ta ce sojojin Amurka ba za su hana jiragen ruwa
daga wasu tashoshin wucewa ta mashigar Hormuz ba.
Birtaniya dai ta ce ba za ta shiga yunƙurin
aiwatar da matakin na Amurka ba.
Duk da yawan dakarun sojin Amurka a Gabas ta
tsakiya, Iran ta yi nasarar jigilar miliyoyin gangar manta zuwa sassan duniya a
lokacin da ake ci gaba da yaƙin, wani abu da fadar White House ta sha alwashin
daƙilewa.
A nata ɓangaren, rundunar sojin Iran ta yi
gargaɗin cewa duk wani jirgi da ke ƙoƙarin kutsa kai ta mashigar Hormuz zai
ɗanɗana kuɗarsa.
Mista Trump ya shaida wa manema labarai cewa ko
kaɗan bai damu ba da matakin da Iran za ta ɗauka, kodai ta koma a ci gaba da
tattaunawa ko kuma ta yi biris, yana mai cewa zabi ya rage mata.