Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya - Litinin 18/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye

Taƙaitattu

  • Jihar Sokoto na horar da ɗalibai mata 151 don rubuta jarrabawar shiga jami'a
  • Hayaƙin masana'antu ya sa an rufe yawancin makarantu a birnin Delhi na India
  • Jam'iyya mai mulki a Senegal ta yi iƙirarin samun nasara a zaɓen majalisar dokoki
  • Najeriya ta roƙi Chadi kada ta janye daga rundunar ƙasashe ta yaƙi da Boko Haram
  • Yau za a fara allurar rigakafin ƙyandar biri a Najeriya

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad

  1. Muna da buƙatar Inganta dangantaka tsakanin Birtaniya da China - Starmer

    Starmer da Xi

    Asalin hoton, Reuters

    Sir Keir Starmer ya gana da shugaba Xi Jinping a taron kasashe 20 masu ƙarfin tattalin arziki na G20, inda ya jaddada muhimmancin "dangantakar Birtaniya da China" ga kasashen biyu.

    Ganawar ita ta farko da wani firaministan Birtaniya ya yi da shugaban na China tun shekarar 2018, bayan da dangantaka ta yi tsami a baya-bayan nan.

    Sir Keir ya taɓo batun ɗan rajin kare dimokradiyya a Hong Kong, Jimmy Lai da ake tsare da shi, yana mai cewa ya damu da rahotannin "tabarbarewar" lafiyarsa.

    Har ila yau, firaministan ya nuna sha'awar samun babban haɗin gwiwar kasuwanci, musamman kan "bangarorin da za su inganta kasashen biyu" kamar zaman lafiyar ƙasa da ƙasa, da sauyin yanayi da ci gaban tattalin arziki.

    Sir Keir ya gana da shugaba Xi a gefen taron G20 a birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil, kuma yayin da yake magana a farkon taron, ya ce: "Muna son dangantakarmu ta kasance mai ɗorewa kuma amintaciya, kamar yadda muka amince, da kaucewa duk abubuwan da za su iya sanyawa mu shammaci juna, idan har za mu iya."

    Yayin da batun goyon bayan da China ke bai wa Rasha a yaƙinta da Ukraine ya haifar da suka daga Birtaniya da sauran ƙasashen yammacin duniya, Firaministan ya kuma ce yana son a tattauna cikin aminci a kan ɓangarorin da ƙasashen biyu ba su sami jituwa a kai ba, da suka hada da batun Hong Kong, da hakkin ɗan'Adam da yaƙin Rasha da Ukraine. .

  2. Taron G20 zai mayar da hankali kan matsalar yunwa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, ya bude taron shekara shekara na kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a Duniya wato G20, a birnin Rio de Janeiro inda aka kaddamar da batun hadin kan duniya wajen shawo kan yunwa da talauci.

    Kasashe 81 suka sanya hannu kan batun ciki har da na kungiyar tarayyar Turai da kuma na kungiyar kasashen Afirka dama wasu kungiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa.Shugaba Lula ya kira yunwar da ake fama da ita a duniya a matsayin abin kunya ga al'ummar duniya.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum miliyan dari bakwai da talatin da uku ne suka yi fama da yunwa a bara.

    Nan gaba shugabannin kasashen kungiyar ta G20 zasu tattauna a kan yadda za a kara tara kudade wajen yaki da dumamar yanayi a taron.

  3. Amurka ta miƙa wa Lebanon daftarin shirin tsagaita wuta tsakanin Hezbollah da Isra'ila

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Yunƙurin tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah ya tsananta, inda ake sa ran gwamnatin Lebanon za ta mayar da martani kan daftarin yarjejeniyar da Amurka ta gabatar, a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare ta sama a faɗin ƙasar.

    Hare-hare cikin makon da ya gabata, wanda suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a Lebanon, da alama yana da nufin matsin lamba ne kan ƙungiyar Hezbollah da gwamnatin Lebanon kan amincewa da yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin da ya shafe sama da shekara guda ana gwabzawa.

    Ba a fayyace cikakkun bayanai ba game da daftarin da jakadan Amurka a majalisar dokokin Lebanon Nabih Berri ya gabatar a makon da ya gabata, wanda Hezbollah ta amince ya gudanar da tattaunawar.

    Tun bayan da rikicin ya tsananta a ƙarshen watan Satumba, mahukuntan ƙasar Lebanon sun ce duk wata yarjejeniya ne kan kza ta kasance ne kan ƙudurin kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya mai lamba 1701, wanda ya kawo ƙarshen yaƙin 2006 tsakanin Hezbollah da Isra'ila.

  4. An yi awon gaba da motocin dakon kayan abinci 100 a Gaza - MDD

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ƴan gudun hijirar Falasdinawa (UNRWA) ta bayyana cewa, an kaiwa ayarin motocin agaji sama da dari hari tare da wawashe su a Gaza a ranar Asabar.

    Shaidu sun ce wasu mutane da suka rufe fuskokinsu ne suka jefa gurneti yayin da suka afka wa motocin - wanda yawancinsu aka yi awon gaba da su baki daya.

    Da yake magana a wani taron manema labarai, shugaban UNRWA, Philippe Lazzarini, ya ce halin da ake ciki na jin kai a kudancin Gaza yana da matuƙar tsanani.

    Ya ce: “Mun daɗe muna gargaɗi game da rugujewar tsarin rayuwar jama’a, har zuwa watanni hudu ko biyar da suka gabata, muna da mutanen da ke raka ayarin motocin, amma yanzu babu ko ɗaya.''

    A cewar UNRWA, idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, matsalar karancin abinci za ta ƙara tsananta ga mutane miliyan biyu da suka dogara kan taimakon jin kai don tsira.

  5. Ambaliyar ruwa ta mamaye wasu ƙauyuka a Honduras

    Ambaliya a Honduras

    Asalin hoton, Reuters

    Mamakon ruwan sama da guguwar Sara ta haddasa ya janyo ambaliya da ta mamaye al'ummomi sama da 1,700 a Honduras.

    Ya zuwa yanzu dai jami’an ƙasar Honduras sun tabbatar da mutuwar mutum ɗaya amma sun ce sama da mutane 110,000 ne lamarin ya shafa.

    Masu hasashen yanayi sun ce mai yiyuwa ne guguwar Sara ta kara rage ƙarfi a ranar Litinin yayin da take ratsa jihar Quintana Roo da ke kudancin Mexico.

    Guguwar ta yi tafiyar hawainiya, inda ta haddasa ruwan sama mai yawa a arewacin Honduras na tsawon kwanaki huɗu kafin ta nufi arewa zuwa Belize da Mexico.

    Wasu wuraren sun ga ruwan sama mai yawar mm 500 (inci 19.7) wanda ya sa koguna suka tumbatsa.

    Ma'aikatan agajin gaggawa na Honduras sun ce gadoji tara ne suka dagargaje sakamakon ruwan da ke kwarara cikin sauri sannan wasu 19 suka lalace.

    Shugabar ƙasar Honduras Xiomara Castro ta gargadi ƴan ƙasar da ke zaune a kusa da koguna tun ranar Alhamis da su fake a wani wuri kuma dubbai sun saurari kiran nata.

  6. Ana kitsa shirin mallake arewacin Najeriya daga Legas - Kwankwaso

    Kwanklwaso

    Asalin hoton, Other

    Tsohon gwamnan jihar Kano Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya yi iƙirarin cewa sabon ƙudurin dokar haraji da gwamnatin tarayya ta gabatar zai daƙile kuɗaɗen shiga da ake samu a jihohi irinsu ƙano ta hanyar harajin VAT.

    Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin da ya ke jawabi a taron yaye ɗalibai karo na uku da jami’ar skyline University ta gudanar ranar litinin.

    Jagoran jam'iyyar NNPP, ya ƙara da cewa ''A yau muna ganin a bayyane yadda a ke wani yanƙuri daga ɓangaren Legas na neman ta mamaye yankin arewacin Najeriya, muna ganin yadda wasu 'matasa' daga Legas ke neman su ƙakaba mana haraji domin su tattara kuɗaden shiga da mu ke samu daga harajin VAT da Kano da ɓangaren arrwacin ƙasar nan zuwa Legas'.

    Kwankwaso ya ƙara da cewa ''hatta [kiran] waya da mu ke yi da rajisata a nan Kano, akwai yunƙurin a kwashe duka harajin a mai da su Legas''

    Ya koka kan yadda ake tilastawa kamfanoni har ma da bankuna da ake buɗewa a sauran sassan ƙasar nan dasu su kai hedikwatarsu Legas,

    Tsohon gwamnan na Kano ya kuma yi tsokaci kan bambancin da ke tsakanin masu hannu da shuni da kuma talakawa, inda ya ce, “Mun ga irin ƙoƙarin da wasu ke yi na ganin cewa talaka ya ci gaba da dawwama cikin talauci yayin da masu hannu da shuni ke ci gaba da yin arziki, kuma na yi imanin hakan ya fi hadari. ''

    Kwankwaso ya yi kira ga ƴan majalisar da suka fito daga yankin Arewacin ƙasar da su farka su tabbatar ba a yi wa yankin sakiyar da babu ruwa ba kowace hanya.

    “A halin yanzu ina kira ga ɗaukacin ƴan majalisar mu na ƙasa da su bude ido don kada su yi wani abu da zai al’ummacutar da Arewacin Najeriya, musamman a nan Kano.'' in ji shi

  7. An garƙame wani ɗan TikTok bisa laifin cin mutuncin shugaban Uganda

    Emmanuel Nabugodi

    Asalin hoton, Swaibu Ibrahim / BBC

    Wani matashi ɗan shekara 21 ya zama ɗan TikTok na baya bayan nan da aka tura gidan yari a Uganda bayan ya wallafa wani bidiyo da aka ce yana cin mutuncin shugaba Yoweri Museveni.

    Emmanuel Nabugodi ya bayyana ne a gaban kotu a ranar litinin bayan ya amsa laifinsa a makon da ya gabata kan wasu tuhume-tuhume guda huɗu da suka haɗa da kalaman nuna ƙiyayya da yaɗa munanan bayanai game da shugaban ƙasar.

    An yanke masa hukuncin ɗaurin watanni 32 a gidan yari.

    Nabugodi, wanda ya shahara wajen wallafa abubuwan barkwanci ga mabiyansa 20,000, ya yi bidiyo na wani shari'ar izgili da ake yi wa shugaban ƙasa. A ciki ya yi kira da a yi wa Museveni bulala a bainar jama'a.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun yi ta korafin yadda ake tauye ƴancin faɗin albarkacin baki a ƙasar, suna masu zargin cewa shugaban - wanda ke kan karagar mulki tun 1986 - ba ya lamuntar suka a gare shi.

    A watan Yuli, an yankewa Edward Awebwa hukuncin shekaru shida akan irin wannan tuhuma da aka yi wa Nabugodi. Wasu uku kuma suna jiran hukunci kan abubuwan da suka wallafa a shafukan sada zumunta sada zumunta.

    A lokacin da take zartar da hukuncin Nabugodi, Stellah Maris Amabilis, babbar alƙaliyar kotun Entebbe, ta ce bai yi nadama ba, kuma hukuncin zai taimaka wajen daƙile sukar da ake kai wa miutane a shafukan sada zumunta ciki har da na shugaban ƙasa.

  8. Har yanzu ba mu ɗauki matsaya kan ƙudurin harajin Tinubu ba - Kakakin Majalisa

    Abbas Tajudeen

    Asalin hoton, OTHERS

    Shugaban majalisar wakilan Najeriya, Abbas Tajudeen, ya ce har yanzu majalisar ba ta ɗauki matsaya ba a kan sabon ƙudirin haraji na gwamnatin Tinubu.

    Ya bayyana hakan ne kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a jawabinsa na buɗe tattauna kan sabon ƙudirin harajin a zauren majalisar da ke Abuja a yau Litinin.

    Sai dai kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ya ce majalisar za ta yi aikin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na tantancewa duk tanadin ƙudurin tare da yin gyara inda ya zama wajibi.

    A watan da ya gabata ne fadar shugaban ƙasar ta aika wa majalisun dokokin ƙasar ƙudurorin, amma kuma majalisar zartarwa ta bayar da shawarar janye ƙudurorin saboda wasu taƙaddamomi da suke ɗauke da su.

    To amma kuma Shugaba Bola Tinubu ya ƙi janyewa yana mai cewa duk waɗanda suke son bayar da gudummawarsu a kan ƙudurin za su iya yin hakan a lokacin zaman sauraron ra'ayin jama'a a majalisar.

  9. 'Yanbindiga sun kashe jami'in tsaro na sintiri na jihar Anambra huɗu

    'Yansanda

    Asalin hoton, AFP

    'Yanbindiga sun kashe 'yan ƙungiyar sintiri ta tsaro na jihar Anambra huɗu a yau Litinin.

    Uku daga cikin 'yansintirin an kashe su ne a garin Ukpo da ke ƙaramar hukumar Dunukofia, yayin da ɗayan aka kashe shi a Abatete, da ke ƙaramar hukumar Idemili ta Arewa.

    Jarida Daily Trust ta ruwaito cewa 'yanbindigar sun yi dirar-mikiya ne a garin na Abatete, inda suka buɗe wuta suna harbin kan-mai-uwa-da-wabi, inda suka kashe mutum ɗaya.

    Sun kai harin ne bayan da gwamnan jihar Charles Soludo ya bayar da umarni ga 'yankasuwa su yi watsi da umarnin 'yan haramtacciyar kungiyar a-ware ta Biafra na zaman gida a duk ranar Litinin, su ci gaba da harkokinsu.

    Wani da ya ga yadda aka kai harin ya ce, bayan da 'yanbindigar suka kashe 'yan sintirin uku a Ukpo sai suka cinna wa motarsu wuta suka kuma kama mutum wajen bakwai suka tsere da su, tare da raunata wasu da dama.

    Kakakin rundunar 'yansandan jihar ta Anambra SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce babban jami'in 'yansanda na Ukpo na gudanar da bincike a kai.

    A mako biyu da ya gabata Gwamna Soludo ya bayar da umarnin a riƙa buɗe dukkanin kasuwanni a jihar a ranar Litinin, wato a yi watsi da hanin da ƙungiyar ta IPOB ta yi.

  10. Jihar Sokoto na horar da ɗalibai mata 151 don rubuta jarrabawar shiga jami'a

    Gwamna Ahmed Aliyu

    Asalin hoton, AHMED ALIYU FACEBOOK PAGE

    Asusun raya limi na jihar Sokoto ya zaɓi ɗalibai mata 151 daga makarantu daban-daban na jihar, inda yake ba su horo kan yadda za su rubuta jarrabawar shiga jami'a, mai zuwa.

    Shirin wanda kwamishinan ilimi matakin farko da kuma sakanadire na jihar, Mohammad Tukur Alkali, ya ƙaddamar na da nufin bai wa matasan mata ilimi da ƙwarewar da za su iya yin fice a fannin ilimi.

    Matsaloli da dama na zama kalubale ga burin 'ya'yan mata na samun karatu na Najeriya.

    Matsalolin kwa sun haɗa da talauci, wanda ke sa iyaye fifita ilimin 'ya'ya maza a kan na mata, inda ake yi wa matan aure suna da ƙananan shekaru saɓanin takwarorinsu maza.

    Matsalar tsaro, na daga ƙalubalan da ke zama barazana ga ilimin 'ya'ya mata a Najeriya, musamman a arewacin ƙasar, inda 'yanbindiga da sauran 'yan ta'adda kan kai hari makarantu su yi garkuwa da ɗalibai musamman mata, kuma wannan na tsoratar da wasu iyayen kai 'ya'yansu manyan makarantu.

  11. Hayaƙin masana'antu ya sa an rufe yawancin makarantu a birnin Delhi na India

    Hayakin masana'antu a birnin Delhi

    Asalin hoton, Getty Images

    Yawancin makarantu a babban birnin India, Delhi, sun koma koyarwa ta hanyar intanet har sai abin da hali ya yi, sakamakon ƙaruwar hayaƙi mai guba na masana'antu a birnin.

    An shawarci kamfanonin da suke da ofisoshi a birnin da yankunan da ke kewaye da shi da su bar rabin ma'aikatansu su riƙa aiki daga gida.

    Hayaƙin ya ƙaru inda ya zarta ninki sittin na abin da hukumar lafiya ta duniya ta bayar da shawara ya kai, a kullum idan har abu ya ci tura.

    An haramta wa duk wasu manyan motoci masu amfani da man dizil shiga birnin sai dai masu ɗauke da kaya masu muhimmanci .

    Sannan kuma an dakatar da ayyukan gine-gine da kere-kere a wurare na gwamnati.

    Mutanen da ke aiki a waje sun ce idanuwansu na ta zafi duk tsawon kwanakin nan.

    An shawarci mutane dama masu yawan shekaru ko tsofaffi da yara da waɗanda suke da larura ta numfashi da kada su fito waje.

  12. Jam'iyya mai mulki a Senegal ta yi iƙirarin samun nasara a zaɓen majalisar dokoki

    Magoya bayan jam'iyya mai mulki a Senegal

    Asalin hoton, AFP

    Alamu sun nuna cewa jam'iyya mai mulki a Senegal ta kama hanyar samun gagarumin rinjaye bayan zaɓen da aka yi na majalisar dokoki a jiya Lahadi.

    Jam'iyyar Pastef ta Shugaba Bassirou Diomaye Faye, ta bayar da rata sosai, bayan da aka ƙirga yawancin ƙuri'u.

    Sai a gobe Talata za a sanar da sakamakon amma kuma tuni manyan jam'iyyun hamayya biyu sun amsa shan kaye.

    A watan Maris aka zaɓi Faye shugaban ƙasa da niyyar gudanar da gagarumin sauyi a fannonin ƙasar - tattalin arziƙi da yaƙi da cin hanci da rashawa da samar da aiki ga matasa da sauransu, to amma ba shi ga rinjayen majalisa da zai yi sauye-sauyen.

    Tsohon shugaban ƙasar Macky Sall, wanda ke jagorantar wata haɗaka ta 'yan hamayya da ake kira Takku Wallu, daga inda yake zaune a Moroko ya yi zargin tafka maguɗi a zaɓen ba tare da bayar da cikakken bayani ba.

    Masu rijistar zaɓe miliyan 7.3 na Senegal na zaɓen 'yan majalisar dokoki 165 a tsawon shekara biyar.

  13. Shugaba Biden ya yi alƙawarin ƙara kuɗi don yaƙi da sauyin yanayi

    Biden da wani jami'i a dajin Amazon

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Biden na Amurka ya yi alƙawarin ƙara zuba kuɗi wajen yaƙi da sauyin yanayi a lokacin da ya kai ziyara ta farko da shugaban ƙasa mai ci na Amurka ya taɓa kai wa katafaren dajin Amazon.

    Wakiliyar BBC ta ce babban abin da ya bayyana a cikin jawabin da ya yi shi ne zai ƙara yawan kuɗin da ake samarwa domin kula da dajin daga dala miliyan 50 hamsin zuwa dala miliyan 100.

    Mista Biden ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa ta samar da iska ingantacciya ta yadda babu wani wanda zai iya sauyawa ko dakatar da shirin.

    Ya kuma yi gargaɗi kan haɗarin da ke akwai na ɗumamar yanayi da duniya ke fuskanta, lamarin da tsohon shugaban Amurka kuma mai jiran-gado a yanzu, Trump ya sha suka a baya.

  14. Najeriya ta roƙi Chadi kada ta janye daga rundunar ƙasashe ta yaƙi da Boko Haram

    Dakarun MNJTF

    Asalin hoton, MNJTF

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tura wata tawaga mai ƙarfin gaske zuwa N'Djamena, babban birnin Chadi bayan da Shugaban Chadin ya yi barazanar janye dakarun ƙasarsa daga rundunar haɗaka ta yaƙi da 'yanta'adda a yankin Sahel.

    A jiya Lahadi ne tawagar ta Najeriya ta je N'Djamena, inda a can hedikwatar rundunar (MNJTF), da ta ƙunshi dakarun Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Benin, take.

    Shugaba Deby ya yi barazanar janye sojojin ƙasarsa ne bayan da mayaƙan da ake zargi na ƙungiyar Boko Haram ne suka kashe dakarun ƙasarsa 40 a tsibirin Barkaram, da ke yankin tafkin Chadi a ranar 27 ga watan Oktoba.

    Saboda wannan barazana ne shugaban na Najeriya ya tura tawagar ƙarƙashin jagorancin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, domin tattauna batun haɗin kan tsaron.

    Rahotanni sun ce, bayan gabatar da ta'aziyyar Shugaba Tinubu ga Shugaban na Chadi kan rasa sojojin, tawagar ta tabbatar wa da shugaban na Chadi samun cikakken goyon bayan Najeriya wajen yaƙi da ta'addanci.

    Babban hafsan hafsoshin Najeriya Janar Christopher Musa, wanda shi ma yake cikin tawagar ya ce ƙudurin sojin ƙasashen biyu zai tabatar da nasarar yaƙi da 'yanta'adda.

  15. Trump ya naɗa mai rajin tabbatar da faɗin albarkacin baki muƙami

    Brenden Carr
    Bayanan hoto, Brenden Carr mai rajin tabbatar da faɗin albarkacin baki ne a Amurka

    Shugaban Amurka mai jiran-gado, Donald Trump ya zaɓi Brenden Carr a matsayin wanda zai jagoranci hukumar kula da sadarwar ƙasar.

    Hukumar ta gwamnatin tarayya, ita ce ke kula da kafofin yaɗa labarai da hanyoyin sadarwa na Intenet a Amurka.

    Mista Carr shi ne babban ma'aikaci ɗan jam'iyar Republican a ma'aikatar kuma babban aboki ne ga attajirin nan Elon Musk.

    Haka kuma yana kan gaba wajen fafutukar tabbatar da 'yancin faɗin albarkacin baki a Amurka.

  16. Bayan kama shugabansa kamfanin haƙar ma'adanai na Australia zai biya Mali haraji

    Shugaban kamfanin Austaliya Terence Holohan

    Asalin hoton, X: Resolute Resources

    Bayanan hoto, Hukumomin Mali sun tsare Terence Holohan da wasu ma'aikatan kamfanin

    Wani kamfanin haƙar ma'adanai na Australiya ya ce zai biya gwamnatin Mali harajin dala miliyan 160.

    Kamfanin ya sanar da hakan ne bayan da ba zato ba tsammani aka tsare shugaba da wasu ma'aikatansa biyu tsawon kwana goma a lokacin da suka kai ziyara ƙasar da ke yammacin Afirka domin aiwatar da wasu tsare-tsaren kamfanin.

    Kamfanin ya yi alƙawarin fara biyan dala miliyan tamanin nan take, yayin da zai cika sauran cikin 'yan watanni masu zuwa.

    Mali na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi samar da zinare a Afirka.

  17. Amurka ta ba wa Ukraine damar amfani da makamanta masu cin dogon zango a kan Rasha

    makami mai linzami

    Asalin hoton, Ukraine Armed Forces

    Jami'ai a Amurka sun ce shugaba Biden ya ba Ukraine izinin amfani da makamai masu cin dogon zango na Amurkar domin kai hare-hare har cikin ƙasar Rasha.

    Matakin wani koma-baya ne ga manufofin Amurka, kodayake Shugaba Biden din da zai miƙa wa Donald Trump mulki a watan Janairu bai bayar da sanarwar hakan a hukumance ba.

    Wani babban ɗan siyasa a Rasha ya nuna ɓacin rai kan matakin.

    Wakilin BBC ya ce babban sanatan Rashar ya ce wannan wani mataki ne na haddasa yaƙin duniya, sai dai Shugaba Putin bai ce komai kan hakan ba.

  18. An fara allurar rigakafin ƙyandar biri a Najeriya yau Litinin

    Ana yi wa wani allura

    Asalin hoton, Getty Images

    A yau Litinin ne aka fara allurar riga-kafin ƙyandar biri a wasu jihohi bakwai a Najeriya., wanda hakan zai sa ƙasar ta zama ta uku da za ta yi riga-kafin bayan Rwanda da Jamhuriyar Dumukuraɗiyyar Kongo.

    Wannan shi ne karon farko da Najeriya za ta yi riga-kafin a kan cutar ta ƙyandar biri bayan ɓarkewarta.

    Ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta ce za a fi mayar da hankali ne a kan ma'iakatan lafiya da sauran rukunan jama'a da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar.

    A watan Agusta Najeriya ta karɓi allurarn riga-kafin na farko da aka bai wa Afirka, wanda kuma a wannan watan ne hukumar lafiya ta duniya ta ayyana cutar a matsayin annoba ta duniya

    Amurka ta bai wa Najeriya kwalaban allurar sanfurin Jynneos (MVA), 10,000.

    Hannu da kyandar biri

    Asalin hoton, Getty Images

    Tun daga farkon shekarar nan rahotanni sun tabbatar da mutum 118 a jihohi 28 daga cikin 36, da kuma Abuja. ne suka kamu da cutar a Najeriya, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya, WHO ta sanar.

    Hukumar yaki da bazuwar cutuka ta Najeriya ta ce, zuwa yanzu a wannan shekara daga watan Oktoba, 27, akwai mutane 1,442 da ake zargin sun kamu da cutar daga jihohi 36 da kuma Abuja.

    Kasashen Afirka 20 sun tabbatar da bullar cutar a kasarsu a wannan shekara, kuma aranar Asabar ne Angola ta bayar da rahoton mutum na farko da ta tabbatar ya kamu a kasarta.

  19. Harin Isra'ila ya kashe jami'an yaɗa labaran Hezbollah

    Jami'an Hezbollah sun ce hare-haren Isra'ila ta sama a tsakiyar Lebanon sun kashe jam'in yaɗa labaran ƙungiyar.

    Muhammad Afif na ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar ƙalilan da suka rage.

    A ranar Litinin da ta wuce ne aka yi wa mista Afif ganin ƙarshe a wani taron manema labarai a wajen kudancin Beirut, inda ƙungiyar take.

    Haka kuma sojojin Isra'ilar sun kai hari kan wani wajen sojin Lebanon inda suka kashe soja ɗaya da raunata wasu uku a kudancin ƙasar.

    Wannan wata alama ce da ke ƙara nuna cewa babu wani tudun mun tsira a Beirut, saboda an kai wannan harin ne ba tare da wani gargaɗi ba.

  20. Buɗewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, muna muku maraba a wannan safiya ta Litinin -18/11/2024.

    Ni Muhammad Annur Muhammad zan kasance da ku daga yanzu zuwa wani lokaci a nan gaba. A yi jimirin kasancewa da mu.

    Mu fara da wannan karin maganar - Da sanyin safiya ake kama fara