Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 07/01/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Ahmad Bawage

  1. Nijar ta ƙwace izinin zama ɗan ƙasa na makusantan Bazoum uku

    Gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar ta ɗauki sabon matakin soke takardar izinin zama ɗan ƙasa ga ƙarin wasu ƴan ƙasar da ake zargi da hannun a cikin ayyukan ta'addanci ko neman hargitsa ƙasar.

    Sabon matakin da shugaban majalisa mulkin sojan ƙasar ya ɗauka a jiya ya shafi wasu ƴan Nijar guda biyu na kusa da hamɓararren Shugaban Ƙasa, Mohamed Bazoum.

    Wannan shi ne karo na uku da gwamnatin mulkin soja ta Nijar ke ɗaukar irin wannan mataki inda zuwa yanzu ta soke takardar izinin zama ɗan ƙasa ga ƴan Nijar kusan 20, akasarinsu makusantan Bazoum.

  2. Cutar HMPV: Najeriya ta fara gwada fasinjojin da ke shiga ƙasar

    Gwamnatin Najeriya ta ƙara ƙaimi wajen sa ido a manyan filayen jiragen ƙasar domin hana yaɗuwar cutar HMPV da ta ɓulla a ƙasar China a ƙasar.

    Daily Trust ta ruwaito cewa ministan lafiya na ƙasar, Muhammad Ali Pate, ya umarci ma'aikatan lafiya da ke filayen jirage su fara gwada fasinjojin da ke shiga ƙasar domin gano ko suna ɗauke da cutar, inda jaridar ta ce an fara gwajin ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas da na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

    A lokacin da cutar Covid-19 ta ɓulla a shekarar 2020, wani fasinja mai shekara 44 ɗan asalin ƙasar Italiya ne ya shigar da cutar Najeriya ta filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a ranar 24 ga Fabarairun 2020.

    Cutar ta HMPV, wadda ta fara ɓulla a China, yanzu ta fara yaɗuwa a Indiya da Malaysia da Kazakhstan, sannan aƙalla mutum 5,000 ne ake tunanin cutar ta kwantar a Birtaniya.

  3. Magoya bayan Peter Obi sun yi alla-wadai da barazana ga rayuwarsa

    Magoya bayan jagoran jam'iyyar LP a Najeriya, Peter Obi, wato Obidients sun yi alla-wadai da barazanar da ya ce ana yi wa rayuwarsa.

    A wata sanarwa da Yunusa Tanko ya fitar a madadinsu, ya ce suna takaici kan jawabin sakataren watsa labaran APC mai mulki, Felix Morka.

    Sanarwar ta ce, "maganarsa cewa Peter Obi ya wuce gona da iri barazana ce ga rayuwarsa, kuma barazana ce ga zaman lafiyar Najeriya.

    "Wannan na nuna yadda Najeriya take ƙara faɗawa cikin mulkin kama-karya a wannan gwamnatin, domin a ce irin wannan jawabin na fitowa daga bakin kakakin jam'iyya mai mulki bai da ce ba, kuma tamkar kira ne ga tayar da zaune tsaye.

    A jawabinsa na sabuwar shekara, Peter Obi ya soki gwamnatin ƙasar kan rashin taɓuka abin a zo a gani domin tsamo ƴan Najeriya daga matsin tattalin arziƙi, tare da sukar wasu manufofin ƙasar.

    Sai dai tsokacin da jami'in hulɗa da jama'a na jam'iyyar APC, na cewa "Obi ya tsallake iyaka" ya janyo suka daga ɓangarori da dama.

    Najeriya na fama da matsalar tashin farashin kayan masarufi tun bayan da shugaban ƙasar ya ɗauki wasu matakai game da tattalin arziƙin ƙasar.

    Ya cire tallafin man fetur, tare da barin kasuwa ta tantance darajar naira, lamarin da ya haifar da tsadar sufuri da kayan masarufi.

  4. 'Hukumar yaƙi da cin hanci ta Nijar ta ƙwato sama da CFA biliyan 57 a shekara ɗaya'

    A jamhuriyar Nijar hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta COLDEFF ta gabatar da rahoton aikinta na shekara.

    A cikin rahoton, hukumar ta bayyana cewa ta yi nasarar karɓo kudi sama da CFA biliyan 57 Daga hannun mutanen da aka samu da laifin almundahana.

    Sai dai an samu ra'ayoyi mabambanta a ƙasar, inda wasu suke ganin ya kamata a fallasa sunayen waɗanda aka ƙwato kuɗaɗen a hannunsu, wasu kuma suke tunanin ba sai an fallasa ba.

  5. Aƙalla mutum 95 sun rasu a girgizar ƙasa a China

    Wata mummunar girgizar ƙasa ta afku a kusa da iyakar Tibet da Nepal.

    Aƙalla mutum 95 ne aka tabbatar da mutuwarsu, sannan sama da 130 sun jikkata a girgizar, wadda ta afku a ranar Talata.

    Girgizar ta kuma ƙetara zuwa yankin Nepal da ke ƙasar Indiya, wanda ke maƙwabtaka da Tibet na ƙasar China.

    Girgizar ƙasar ta lalata gine-gine a birnin Shigatse na Tibet, lamarin da ya sa jama'a su riƙa kwararowa kan tituna domin tsira.

    Tuni sojojin ƙasar suka fara aikin ceto, inda suka aika jirage marasa matuƙa zuwa wani yanki mai nisa a kusa da tsaunin Everest.

  6. Ana barazana ga rayuwata - Obi

    Jagoran Jam'iyyar LP a Najeriya, Peter Obi, ya ce ana yi wa rayuwarsa barazana saboda sukar gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Tinubu da ya yi a saƙonsa na sabuwar shekara.

    A saƙon nasa na sabuwar shekarar, Obi ya bayyana cewa Najeriya na fama da taɓarɓarewar tattalin arziki da rashin tsaro da rashin ingantaccen kiwon lafiya.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya ce, "shin na wuce gona da iri? na yi wannan tambayar ce saboda ana yi wa rayuwata da ta iyalina barazana saboda jawabin da na yi na sabuwar shekara. Bayan barazanar kuma wani mai suna Mr Felix Morka ya zarge ni da wuce gona da iri, sannan ya yi barazanar zan ɗanɗana kuɗata," in ji shi.

    Obi ya ƙara da cewa idan har da gaske ya karya doka, a nuna masa, inda ya ƙara da cewa, "amma ba zan daina faɗin gaskiya ba, musamman a wannan lokacin da ƙasarmu ke ƙara shiga cikin ruɗu."

  7. 'Damar gyara jarabawar WAEC zai rage ɓata lokaci'

    Masana harkoki ilimi sun fara bayana ra'ayinsu kan matakin hukumar shirya jarabawar fita daga sakadare ta WAEC na bai wa ɗaliba damar zama domin gyara darussan da suka faɗi jarabawar ba sai sun jira shekara ta zagayo ba.

    Masana harkokin Ilimi a Najeriya irin su Dr Aliyu Tilde wanda tsohon kwamishinan Ilimi ne a jihar Bauchi, na da ra'ayin cewar wannan tsari zai baiwa ɗalibai damar gyara wasu daga cikin darusan da suka faɗi, ba tare da sun ɓata lokaci ba.

    Hukumar shirya jarabawar WAEC ce ta fitar da tsarin, inda ta fitar da wani sabon tsarin da zai ba ɗalibai dama su riƙa zama su zauna domin gyara darussan da suka faɗi a jarabawa ba tare da sun jira wani zangon jarabawar ba.

  8. Ayyukan agaji a Gaza na fuskantar tsaiko - MDD

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa aikin da take yi na isar da kayan agaji ga al'ummar Gaza na cikin tsaka mai wuya, sakamakon abin da ta ta kira ayyukan zagon ƙasa da sojojin Isra'ila da ƴan daban Falasɗinawa ke gudanarwa.

    Sakataren MDD mai kula da harkokin jin ƙai Tom Fletcher, ya zargi sojojin Isra'ila da kai hari a kan ayarin motocin Majalisar Ɗinkin Duniya a tsakiyar Gaza tare da kai farmaki kan wani sanannen wurin rarraba abinci.

    Ya kuma zargi gungun Falasɗinawa masu ɗauke da makamai da yin awon gaba da wasu tankokin mai guda shida.

    Mista Fletcher ya yi kira ga mambobin Majalisar Dinkin Duniya da su dage kan kare dukkan ayyukan jin kai.

  9. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu riƙa kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa irin su X da Facebook da Instagram domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.