Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/10/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/10/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotonni

    Mun kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Alhamis.

    Umar Mikail ke fatan za ku kasance da mu gobe da safe domin samun wasu sababbin rahotonnin kai-tsaye a wani shafi daban.

  2. Shugaban Ukraine ya nemi ƙasashen Turai su bai wa ƙasarsa kuɗaɗen Rasha

    Vladmir Zelensky

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya buƙaci ƙasashen Turai ƙawayensa da su amince da shirin yin amfani da kadarorin Rasha da aka dakatar domin taimaka wa Kyiv a yaƙin da take yi da Rashar.

    Da yake magana a birnin Brussels, Mista Zelensky ya ce "muna buƙatar duk wani kudi daga Rasha domin samar da kayyayaki a Ukraine".

    Ana tattauna wannan batun a taron da shugabannin ƙasashen Turai ke yi a Brussels, inda Belgium ƙasar da nan ce ke rike da mafi yawan kadarorin Rashan, ke ƙalubalntar halaccin matakin a mahangar shari'a.

    Mista Zelensky ya kuma yi watsi da duk wata shawara da ke bukatar Ukraine ta yi musayar yankuna da Rasha domin samun zaman lafiya.

  3. Shugaban Amurka ya yi wa mutumin da ya kafa Binance afuwa

    Chanpeng Jao Zhao

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa mutumin nan da ya kafa shafin hada-hadar kuɗin kirifto na Binance, Chanpeng Jao Zhao afuwa, wanda ake tuhuma da karya dokokin da ke hana tallata kudaden haram.

    Fadar gwamnatin Amurka ta ce gwamnatin Biden ce ke ta bibiyar Mista Zhao a wani abu da ta kira ''yaki da kuɗin Kirifto'' wanda fadar White House ta ce a yanzu an kawo karshensa.

    Mista Zhao ya zauna a gidan yari tsawon wata huɗu a shekarar da ta gabata, kuma shi da shafin kirifto din na Binance sun biya tarar biliyoyin dala.

    Wakilin BBC ya ce afuwar da aka yi masa za ta buɗe masa hanyar dawowa Binance da kuma duniyar hada-hadar kirifto.

  4. Gwamnonin PDP a Arewa sun amince da Tanimu Turaki ɗantakararsu

    Kabiru Tanimu Turaki

    Asalin hoton, @kabiruturakisan

    Wasu jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya daga yankin arewacin ƙasar sun amince da tsohon minista Kabiru Tanimu Turaki a matsayin ɗantakararsu a babban taron da jam’iyyar da za ta gudanar cikin watan Nuwamba.

    Jam’iyyar ta bayyana cewa sun cimma wannan maslaha ne bayan tuntuɓa da tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki.

    Ibrahim Abdullahi, shi ne mataimakin sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa, kuma ya faɗa wa BBC cewa gwamnonin jam'iyyar na arewacin Najeriya suka yanke shawarar.

    Matakin na nufin shi ne ɗantakarar da za su saka a gaba yayin jefa ƙuri'ar shugabancin jam'iyyar a taron na ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari hira da Ibrahim Abdullahi:

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari hira da Ibrahim Abdullahi:
  5. An kama taurarin ƙwallon kwando kan caca ba bisa ƙa'ida ba a Amurka

    Sanannun yanwasan kwallon kwando biyu da ke tashe a Amurka na daga cikin mutum 34 da aka kama a cikin wani bincike da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ke yi kan caca ba bisa ƙa'ida ba.

    Ana zargin mai horar da tawagar Portland Trail Blazers, Chauncey Billups, da buga wasannin karta da aka yi maguɗi a cikinsu a New York.

    Magudin ya hada da amfani da fasahar X-ray da ke iya nuna wa mutum kati, da kuma na'urorin lale katin da aka yi magudi a kansu.

    Wani bincike ya kuma bankado rahotannin yin ƙarya a lokacin wasannin kwandon da kuma yin caca a kan wasannanin, kuma cikin wadanda ake tuhuma har da tauraron kungiyar Miami Heat, Terry Rozier.

    Daraktan FBI Kash Patel ya ce "yaudara ce mai girma ta miliyoyin daloli, da sata, da fashi".

  6. Tinubu ya nemi sabon shugaban Inec Amupitan ya yi aiki da gaskiya

    Farfesa Joash Ojo Amupitan

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da Farfesa Joash Ojo Amupitan a matsayin shugaban hukumar zaɓe Inec na shida.

    An yi bikin rantsuwar ne a ɗakin taro na Council Chamber da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja, inda shugaban ya umarce shi da ya yi aiki "bisa gaskiya".

    A ranar 16 ga watan Oktoba ne majalisar dokokin ƙasar ta amince da naɗa Farfesa Amupitan a matsayin shugaban hukumar ta Independent National Electoral Commission (Inec).

    "Miƙa sunanka da tantancewar da majalisa ta yi maka hujja ce ta ƙwarewarka da kuma yardar da aka yi da majalisar ministoci da ta dokoki suka yi da kai," in ji Tinubu bayan rantsuwar.

    Ɗaya daga cikin ƙalubalen da ke gaban sabon shugaban shi ne gudanar da babban zaɓe na 2027 wanda kowane ɓangare zai amince da shi, yayin da aka shafe shekaru ana zargin maguɗi a dukkan zaɓukan Najeriya.

    Farfesa Joash Ojo Amupitan

    Asalin hoton, State House

  7. Uwargidan tsohon Shugaban Ghana Jerry Rawlings ta rasu

    Nana Konadu Agyeman-Rawlings

    Asalin hoton, Getty Images

    Uwargidan tsohon Shugaban Ghana Jerry John Rawlings ta rasu tana da shekara 76 da haihuwa.

    Fadar shugaban ƙasar Ghana ta ce Nana Konadu Agyeman-Rawlings ta mutu a yau Alhamis bayan wata gajeriyar jinya.

    Yayin da take uwargidan shugaban ƙasa, ana kallon Nana Konadu a matsayin ɗaya daga cikin na gaba-gaba wajen nema wa matan Afirka 'yanci da kuma inganta rayuwarsu.

    A 1982, ta kafa ƙungiyar fafutika ta 31st December Women’s Movement (DWM), wadda ta dinga aikin tallafa wa mata a fannin tattalin arziki, da zamantakewa, da kuma siyasa.

    Mijinta Jerry Rawlings ya yi shugaban ƙasa a tsarin dimokuraɗiyya sau biyu daga 1993 zuwa 2001.

  8. Ɓarayi sun sake sace silallan zinare da azurfa a Faransa

    Silallan zinare

    Asalin hoton, Maison des Lumières

    Silalla na zinare da azurfa kusan 2,000 ne aka sace a wani fashi da aka sake yi a wani gidan ajiye kayan tarihi na Faransa, waɗanda suka kai darajar dala 100,000.

    An yi satar ne 'yan awanni bayan satar kayan tarihi a gidan tarihi na Louvre ranar Lahadi.

    Bayan gidan tarihin na Maison des Lumières ya buɗe a ranar Talata, ma'aikata sun lura da wata adaka da aka fasa kuma suka ankarar da mahukunta.

    Wata sanarwa ta ce an zaɓi silallan ne "cikin ƙwarewa mai girma, kamar yadda hukumomin yankin da ke arewacin Faransa suka bayyana.

    Silallan tun na shekarun 1790 ne zuwa 1840 kuma suna cikin waɗanda aka gano a 2011 lokacin da ake aikin sake gina ginin da gidan tarihin ke ciki a yanzu.

  9. Hukumomi sun katse intanet a Kamaru

    Kamaru

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mazauna biranen Kamaru na zanga-zangar jinkirin sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa

    Rahotanni na cewa an samu katsewar intanet a sassa da dama na kamaru, yayin da 'yan ƙasar ke ci gaba da jiran sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka yi kusan mako biyu da suka wuce.

    Wata ƙungiya mai sanya ido kan harkokin Intanet mai suna NetBlocks ta ce katsewar intanet din ta shafi har wasu ƙasashe makwaftan Kamaru.

    Masu amfani da intanet sun ce sun samu sako daga kamfanonin sadarwa cewa katsewar ta wucin gadi ce.

    Katsewar intanet din na zuwa ne a yayin zaman ɗarɗar ke ƙaruwa a kasar, inda ƙungiyoyin 'yan'adawa ke kiran a ci gaba da gudanar da zanga-zanga idan har majalisar kundin tsarin mulkin kasar ta bayyana abin da suka kira sakamakon ƙarya.

    Hukumomi sun haramta duk wani taro, da zirga-zirgar babura da tasi a birane da dama, yayin da ake jiran sakamakon zaben a ranar Litinin mai zuwa.

  10. Boko Haram ta kai samame a sansanonin sojin Najeriya huɗu cikin dare

    Janar Christopher Musa

    Asalin hoton, X/Defence Headquarters

    Bayanan hoto, Babban hafsan sojojin Najeriya Janar C.G Musa

    Rundunar sojin Najeriya ta ce masu iƙirarin jihadi sun ƙaddamar da hare-hare lokaci ɗaya kan sansanoninta huɗu da ke arewa maso gabashin ƙasar, sai dai ta samu nasarar murƙushe su.

    Sanarwar da rundunar haɗin gwiwa ta 'Joint Task Force' ta fitar a yau Alhamis, tare da sa hannun jami'in yaɗa labaran rundunar Laftanar Kanar Sani Uba, ta ce mayaƙan sun dirar wa sansanonin ne ta hanyar buɗe wuta da ƙoƙarin cimma musu wuta.

    Sanarwar ta ce "tsakanin tsakiyar dare zuwa ƙarfe huɗu na asuba, ƴan ta'adda sun ƙaddamar da wani shiryayyen farmaki kan dakarunta da ke Dikwa, da Mafa, da Gajibo da kuma Katarko a jihar Borno da kuma Yobe.

    "A dukkanin hare-haren dakarun sun tsaya tsakin-daka, suka yi artabu cikin karsashi, suka murƙushe harin, inda suka yi wa ƴan ta'adda mummunar ɓarna".

    A lokacin wannan artabu, a cewar rundunar "martanin sojojin ya kai ga halaka ƴan ta'adda 50. Haka nan dakarun sun ƙwato bindigar AK-47 guda 38, da bindigar labarbar bakwai, da bindigar tarwatsa tankokin yaƙi guda biyar, da bindigar GPMG biyu da tarin gurneti da dubban harsasai.

    "Bugu da ƙari dakarun Najeriya na ci gaba da neman sama da mutum 70 cikin waɗannan ƴan bindiga da aka raunata," in ji sanarwar.

    A ɓangare ɗaya "wasu daga cikin dakarun Najeriya sun samu rauni yayin artabun amma suna samun kulawa kuma ba sa cikin haɗari. Wasu motoci da kuma gine-gine sun ƙone sanadiyyar ruwan wuta daga jirage marasa matuƙa masu ɗauke da makamai da ƴan ta'addan suka yi amfani da su da kuma wutar manyan bindigogi, musamman a Mafa da Dikwa," kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

    Najeriya ta shafe sama da shekara 15 tana yaƙi da ƙungiyar Boko Haram wadda ke kai hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula a arewa maso gabashin ƙasar, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa dubban rayuka da tarwatsa miliyoyi, tare da haifar da mummunar matsalar jin-ƙai.

    Alƙaluman ƙungiyar ACLED mai sanya ido kan tsaro sun nuna cewa ya zuwa yanzu Boko Haram ta kai hari sau 333 a yankin arewa maso gabashin Najeriya cikin wannan shekara.

    Wani abu da masana tsaro ke nuna damuwa a kai shi ne yadda ƙungiyar ke amfani da fasahar zamani wajen kai hare-hare, kamar amfani da jirage marasa matuƙa masu ɗauke da makamai ko kuma wajen tattara bayanai.

  11. Tchiroma Bakary ya buƙaci a ci gaba da zanga-zangar lumana a Kamaru

    ...

    Asalin hoton, Facebook/Tchiroma

    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa a Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya yi kira ga magoya bayansa su ci gaba da zanga-zangar lumana domin nuna adawa da abin da ya bayyana a matsayin "nasarar da aka sace" a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Oktoba.

    Tchiroma ya yi wannan kiran ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar 22 ga Oktoba.

    Ya yi gargadi cewa, "idan Kwamitin Tsarin Mulki ya tabbatar da sakamakon zaɓe na ƙarya, hakan zai zama laifin cin amana, kuma mutanen Kamaru ba za su yarda da hakan ba."

    Ya ce shi ne ya lashe zaɓen da fiye da kashi 50 cikin 100 na kuri’u, inda ya yi kira ga Shugaba mai ci, Paul Biya da ya amince da rashin nasara kuma ya tabbatar da sauyin mulki cikin lumana.

    Tchiroma ya yi kira ga dukkan 'yan Kamaru, a cikin ƙasa da ƙasashen waje, da su haɗu cikin lumana domin nuna goyon bayan su.

    Ya ce: "Mu haɗu a matsayin ɗaya, cikin lumana da ƙaunar ƙasa. Mu yi zanga-zangar neman ‘yanci kuma mu karɓi nasararmu."

    Haka kuma, ya yi kira ga jami’an tsaro da sojoji da kada su yi amfani da makaman su kan fararen hula, inda ya ce: "wahalar da mutanen ƙasa suka sha, naku ne." Wannan jawabi ya fito ne a daidai lokacin da zanga-zanga ke ci gaba a babban birnin ƙasa, Yaoundé, da kuma a Garoua, garin da Tchiroma ya fito.

  12. Najeriya za ta bai wa jihohi naira biliyan 32.9 don ingata lafiyar al'ummominsu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za ta bai wa jihohi da cibiyoyin lafiya naira biliyan 32.9 kafin ƙarshen watan Oktoba domin inganta kiwon lafiyar jama'a.

    Ta dalilin wannan ne gwamnati ta kaddamar da wasu tsare-tsare na wani asusu da aka tanada domin kula da harkokin lafiya a matakin farko BHCPF da nufin tabbatar da cewa kuɗin da za a raba za a yi amfani da su yadda ya dace domin inganta ayyukan kiwon lafiya a ƙasar.

    Ministan lafiya da walwalar Jama’a, farfesa Muhammad Pate, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, yayin ƙaddamar da sabon tsarin BHCPF 2.0, wanda ke mayar da hankali kan gaskiya da inganci da biyan sakamako bisa aiki.

    Ya ce "Wannan mataki yana da nasaba da umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da gaskiya da amfani da kuɗaɗen gwamnati da na abokan hulɗa ta hanya mai inganci."

    Gwamnati ta bayyana cewa yawan cibiyoyin lafiya da ke amfana da kuɗin BHCPF zai ƙaru daga 8,800 zuwa 13,000.

  13. Ana neman gwamnati ta yi bincike kan ɓacewar manyan alƙalai a Burkina Faso

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Human Rights Watch ta yi kira ga gwamnatin sojin Burkina Faso da ta yi gaggawar bincike kankan ɓacewar wasu manyan alƙalai shida da masu shari’a, da kuma lauya guda ɗaya bayan da ake zargin an ɓatar da su da karfi da yaji.

    Wannan lamari ya haifar da tsoro cewa za a iya samun sabon matakin tsangwama ga tsarin shari’a da ‘yan jarida a ƙasar.

    Human Rights Watch ta ce ɓacewar waɗannan jami’an shari’a da lauya tun daga 10 ga Oktoba, 2025, na iya zama an sace su ne kuma akwai yiwuwar an tilasta su shiga rundunar soji ba tare da bin doka ba.

    Al’amuransu da na wasu ‘yan jarida hudu da aka tsare sannan aka sake su tsakanin 13 zuwa 18 ga Oktoba suna nuna alaka da wani yunƙurin take hakkin bil’adama da gwamnatin soji ke yi ga shari’a da kafofin watsa labarai.

    Ilaria Allegrozzi, babbar mai bincike kan Sahel na Human Rights Watch, ta ce: “Yanayin hakkin bil’adama a Burkina Faso ya kara taɓarɓarewa ta hanyar ɓacewar mutane da tsarewa ba bisa ka’ida ba, da tilasta shiga soji ga masu sukar gwamnati da masu rajin kare hakki.”

    Ta yi kira ga gwamnatin soja da ta gaggauta gano waɗanda suka ɓace, ta bayyana inda suke, kuma ta sake su idan ba a tuhume su da wani laifi ba.

  14. Gwamantin Nijar ta yi ƙarin albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikatanta

    Shugaban mulkin soja na Jamhuriyar Nijar Abdourahamane Tiani

    Asalin hoton, Presidence De La Republique Du Niger

    Bayanan hoto, Shugaban mulkin soja na Jamhuriyar Nijar Abdourahamane Tiani

    Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da yin ƙarin albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikata daga cfa 30,000 zuwa cfa 42,000, wanda ya yi daidai da naira 108,780 a Najeriya.

    Wannan ƙarin albashi na daga cikin matakan gwamnatin domin inganta rayuwar ma’aikata da ƙarfafa su wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum, kamar yadda gwamnatin ta sanar.

    Majalisar Ministocin gwamnatin ce ta ɗauki wannan mataki a taron da ta gudanar jiya Laraba, inda kuma minsitocin suka tattauna hanyoyin da za a tabbatar da cewa ƙarin albashin zai shafi dukkan ma’aikatan gwamnati ba tare da rarrabewa ba.

    Wannan mataki ya zo ne bayan da gwamnatin ta lura da ƙaruwar farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi a ƙasar.

    Gwamnatin ta bayyana cewa wannan ƙarin albashi zai taimaka wajen rage wahalhalu da ma’aikata ke fuskanta, musamman wajen biyan bukatun yau da kullum kamar abinci, sufuri, da kuma ilimin yara.

  15. Nnamdi Kanu ya kori lauyoyinsa

    ...

    Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya kori dukkan lauyoyinsa tare da bayyana cewa zai kare kansa da kansa a gaban kotu.

    Kanu ya bayyana hakan ne a lokacin zaman kotu yayin da yake shirin fara kare kansa kan tuhumar da gwamnati take masa kan cin amanar ƙasa.

    A lokacin zaman kotun da aka gudanar a ranar Alhamis, babban lauyan Kanu, Sanata Kanu Agabi (SAN), ya sanar wa kotu cewa shi da sauran manyan lauyoyin Kanu sun janye daga kare shi a wannan shari’ar.

    Mai shari’a James Omotosho ya amince da bukatar janyewar lauyoyin.

    Bayan haka, alƙalin ya tambayi Kanu ko yana da sabon lauya da zai kare shi, sai Kanu ya amsa da cewa: “Zan tsaya da kaina na kare kai na, bana buƙatar lauya.” Daga nan sai Mai shari’a Omotosho ya umurci sauran ƙananan lauyoyi ba da su bar dakin kotu.

    A halin yanzu, labari na cewa Nnamdi Kanu ya saka sunayen tsofaffi da kuma wasu jami’an gwamnati masu aiki a matsayin shaidu da zai gabatar wajen kare kansa.

    Cikin jerin sunayen da ya ambata akwai tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami; tsohon babban hafsan sojojin Najeriya, Janar Tukur Buratai; tsohon Ministan Tsaro, Janar Theophilus Danjuma; da kuma gwamnonin jihohin Legas da Imo — Babajide Sanwo-Olu da Hope Uzodinma, tare da wasu mutune da dama.

  16. Ƴunkurin Isra’ila na ƙwace Gaɓar Yamma barazana ce ga zaman lafiya a Gaza - Rubio

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce duk wani yunƙuri da Isra’ila za ta yi na ƙwace Gaɓar yammacin Kogin da ta mamaye daga hannun Faladinawa na iya zama barazana ga yarjejeniyar zaman lafiyar Gaza da Donald Trump ya jagoranci cimmawa.

    Ana sa ran Rubio zai je Isra'ila daga baya don matsa wa jami'an gwamnatin Lamba su ci gaba da tattaunawa kan aiwatar da ƙarashen yarjejeniyar.

    A ranar Laraba ne wani ƙuduri da masu tsattsauran ra'ayi suka gabatar a majalisar dokokin Isra'ilar da ke neman ƙasar ta ƙwace iko da gabar yammacin kogin Jordan din ya samu tsallakewa.

    Rubio ya nanata kalamin shugaba Trum na baya, cewa Amurka ba za ta taba lamuntar wannan yunkuri ba.

    Da aka tambaye shi game da karuwar tashin hankalin da yan kama-wuri-zaunar Isra'ila ke yi, sakataren harkokin wajen Amurkar ya ce Washington na adawa da duk wani tashin hankali.

  17. Amurka ta ƙaƙaba wa Rasha sabbin takunkumai

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ƙaƙaba wa Rasha sabbin takunkumai kan manyan kamfanonin man fetur na ƙasar, a matsayin mataki na farko kai tsaye da gwamnatinsa ta ɗauka kan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

    Wannan mataki, wanda aka bayyana a matsayin sabon salo a manufofin gwamnatin Trump, an ɗauke shi ne domin tilasta wa shugaban Rasha, Vladmir Putin, ya kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Ukraine.

    Matakin ya zo ne gabanin taron shugabannin Tarayyar Turai da za a fara a yau a birnin Brussels.

    Ukraine dai ta yi marhabin da wannan matakin na Amurka.

    Taron zai mayar da hankali ne kan miƙa wa Ukraine kadarorin Rasha da aka kwace domin taimaka mata wajen farfaɗo da tattalin arzikinta.

    Takunkumin dai shi ne na farko kai-tsaye da gwamnatin Trump ta ƙaƙaba Kremlin kan mamayar da ta yi wa Ukraine.

    A taron na kwanaki biyu da za a yi a Brussels, ana sa ran shugabannin Tarayyar Turai za su yi tunanin bai wa Ukraine rancen sama da dala biliyan 160 da aka kwace daga Rasha.

  18. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya a jiya na labaran kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a cikin Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.