Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 30/09/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran muhimman abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/09/2024.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Umar Mikail da Nabeela Mukhtar Uba

  1. Likitocin manyan asibitoci a Kano za su fara yajin aiki

    Kungiyar likitoci da ke aiki a manyan asibitocin gwamnatin jihar Kano sun yi barazanar tsundunma yajin aiki na tsawon mako biyu daga gobe Talata.

    Kungiyar ta ce gazawar da gwamnatin Kano da ke arewacin Najeriya ta yi wajen aiwatar da wasu daga cikin yarjejeniyar da suka cim ma tun a Satumban 2023, da ƙarancin likitoci a jihar na daga cikin dalilan shiga yajin aiki.

    Kazalika, ƴan ƙungiyar sun ce akwai batutuwan da suka shafi rashin kayan aiki, da ƙarancin ma'aikata, da kuma ƙarancin albashi.

    Shugaban ƙungiyar Dr. Anas Idris Shanono ya faɗa wa BBC cewa 4 ga watan Agusta suka kafa kwamatin tattaunawa da gwamnatin.

    "Idan ka kalli likitocin da ke Kano 600 ne da 'yan kai, hakan na nufin kowane likita na kula da sama da mutum 30,000 kenan," in ji shi. Ya ƙara da cewa sun lura albashin da ake biyan likitocin a wasu jihohi ya zarta na Kano.

    Sai dai ƙungiyar ta ce duk da cewa da gwamnatin baya suka cim ma yarjejeniyar ya kamata gwamnatin yanzu ƙarƙashin jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya ta saurare su.

  2. Rwanda na bin sawun mutum 300 bayan cutar Marburg ta kashe mutum takwas

    Hukumomi a Rwanda sun ce sun tsaurara bin sawun mutum mutum 300 bayan annobar cutar Marburg ta kashe mutum takwas cikin 26 da aka tabbatar sun kamu da ita, a cewar gidan talabijin na ƙasar Rwanda TV.

    Ministan Lafiya Sabin Nsanzimana ya ce mutum 18 ne ke jinya yayin da gwmanati ta mayar da hankali kan gwaji da kuma wayar da kan al'umma game da cutar da aka tabbatar da ɓullarta ranar 27 ga watan Satumba.

    Nsanzimana ya nemi 'yan ƙasar da ke jin alamomi kamar zazzaɓi, da ciwon gaɓoɓi, da gudawa ko amai da su kai rahoto zuwa asibiti mafi kusa da su.

    "Abu ne mai muhimmanci idan kuka ji waɗannan alamomi ku sanar da hukumomi ta lambar waya 114 da kuma tuntuɓar hukumomin lafiya," a cewar ministan.

    Wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a Rwanda, Brian Chirombo, ya ce an tura ƙwararru bakwai domin talafa wa gwamnatin ƙasar shawo kan annobar.

  3. Guguwar Helene ta kashe mutum fiye da 90 a Amurka

    Sama da mutum 90 aka tabbatar sun mutu a sassan Amurka sakamakon guguguwar Helene da ke tafe da iska da ruwan sama mai karfin gaske.

    Hukumomi sun ce a North Carolina kadai mutane sama da 30 ne suka rasa rayukansu.

    Guguwar tafe da tsawa ta tafka ta'adi sosai a jihohin Florida da Georgia. Akwai kuma birane da dama da tittunan da suka lalace sakamakon ambaliya, haka kuma akwai milyoyin mutane da lantarkinsu ya katse.

    Shugaba Biden ya ce zai ziyarci wasu daga cikin yankunan da suka fuskanci wannan iftila'i

  4. Jam'iyyar Freedom ta yi zarra a zaɓen Austria

    A karon farko tun bayan yaƙin duniya na biyu, jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta yi zarra a babban zaben Austria.

    Jam'iyyar Freedom da Herbert Kickl ke jagoranta ta samu kashi 29 cikin 100 na kuri'un da aka kada, inda ta doke ta masu ra'ayin mazan jiya mai kashi 26 da masu matsakaicin sassaucin ra'ayin, da suka samu kashi 20. Sai dai jam'iyyar ba ta samu rinjaye kafa gwamnati ba.

    Wakilin BBC a birnin Vienna, ya ce Misa Kickl ya kasance mutum mai raba kawuna da kwata-kwata ba shi da farin-jini tsakanin sauran shugabannin jam'iyyar, da kuma suka ki yarda da gwamnati hadaka a karkashin jagoranci.

    Shugaba Alexander Van der Bellen - wanda zai jagoranci kafa gwamnati - shi ma ya caccaki jam'iyyar Freedom kan ki alla-wadai da mamamayar Rasha a Ukraine.

  5. Sojojin Nijar sun ce sun yi nasarar kashe ƴanbindiga fiye da 60

    Sojoji a Jamhuriyar Nijar sun yi nasarar kashe 'yan bindiga sama da 60 da kuma ƙwato shanu 250 da 'yan bindigar suka sace.

    Sojojin sun samu wannan nasara ne a wani aiki da suka aiwatar na haɗin-gwiwa a jihar Tillabery da kuma taimaka wa manoman yankin gudanar da ayyukansu cikin tsaro a gonaki.

    Dakarun dai na samun nasara a kan ƴanbindigar da ke addabar al'ummar ƙasar kamar yadda maƙwabciyar ƙasar Najeriya ke samun irin wannan nasara ta kamawa da kashe gomman ƴanbindigar.

  6. Hezbollah a shirye take idan Isra'ila ta kai samame ta ƙasa - Sheikh Naim Qassem

    Mataimakin shugaban Hezbollah Sheikh Naim Qassem ya ce ƙungiyar a shirye take don tunkarar dakarun Isra'ila idan suka auka kudancin Lebanon ta ƙasa.

    Yayin da yake jawabi kai-tsaye a safiyar yau, Sheikh Qassem ya ce za su ci gaba da ayyukan da suke yi yana mai cewa har yanzu "kaɗan ne", kamar yadda kamfanin labarai na Reuters ya fassara jawabin nasa.

    Ya kuma ƙara da cewa yaƙin zai iya ɗaukar tsawon lokaci.

    Ya kammala jawabin nasa da neman a "yi haƙuri".

    A ranar Juma'a da ta wuce Isra'ila ta kai hari kan hedikwatar ƙungiyar da ke birnin Beirut, inda ta kashe shugabanta Hassan Nasrallah tare da wasu manyan kwamandoji, ciki har da wani janar ɗin sojin Iran.

  7. An harba makaman roka zuwa arewacin Isra'ila

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce an harba rokoki 35 daga Lebanon zuwa arewacin ƙasar a safiyar yau.

    An kakkaɓe wasu daga cikinsu yayin da wasu suka sauka a filayen da babu kowa, in ji rundunar sojin.

    Zuwa yanzu Hezbollah ba ta ce komai ba - amma tana ci gaba da harba makaman roka a 'yan kwanakin nan duk da hare-haren da Isra'ila ke kai wa maɓoyar makamanta.

  8. Bankin Duniya ya amince da bai wa Najeriya bashin dala biliyan 1.57

    Bankin Duniya ya amince da kashe kuɗi dala biliyan 1.57 domin tallafa wa gwamnatin Najeriya wajen inganta ayyukan kyautata rayuwar 'yan ƙasa, da yaƙi da sauyin yanayi, da lafiyar mata.

    Za a kashe kuɗin ne a mataki uku kan abubuwan da suka haɗa da rage aukuwar bala'i kamar ambaliya da fari ta hanyar inganta lafiyar madatsun ruwa a ƙasar, da kuma noman rani.

    Sabon ƙunshin tallafin ya kuma ƙunshi dala miliyan 500 na kyautata harkar koyo da koyarwa da lafiya, da miliyan 570 na inganta cibiyoyin lafiya a matakin farko, da kuma miliyan 500 na samar da lantarki mai ɗorewa da noman rani a Najeriya.

    Ana sa ran ɓangaren ilimi da na lafiya a matakin farko za su amfana ta hanyar kyautata ayyuka, da ɗaukar ma'aikata.

    Kazalika, ana sa ran 'yan Najeriya 950,000 za su amfana da tallafin ta hanyar noman rani da ba shi da matsala ga muhalli.

  9. Gwamnatin Najeriya ta bai wa 'yanƙwadago da ɗalibai motoci masu amfani da gas 64

    Gwamnatin Najeriya ta miƙa wa ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC da ku ma ta ɗalibai NANS motocin bas masu amfani da iskar gas 64 a jiya Lahadi.

    An gudanar da bikin miƙa motocin ne a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja a matsayin wani ɓangare na bikin cika shekara 64 da samun 'yancin kai.

    Da yake magana yayin bikin, Ministan Kuɗi Wale Edun ya ce wannan ɗaya ne daga cikin yunƙurin gwamnatin na sauƙaƙa farashin zirga-zirga wanda ya hauhawa tun bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023.

    "Babban abin da muka saka a gaba shi ne zirga-zirgar jama'a," in ji ministan.

    Ya ƙara da cewa hikimar ba da motocin a jajiberin bikin 'yancin kai ita ce saka ɗambar fito da su da yawa, yana mai cewa sun tsara raba sama da 500 da kuma masu amfani da lantarki 100.

  10. Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ce sojoji sun kai wa ofishin jakancinta hari a Sudan

    Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ce an kai hari kan gidan jakadanta da ke Khartoum da jiragen sojin Sudan.

    A wata sanarwa da ta fitar a shafin sada zumunta, ma'aikatar harkokin ƙetare na cewa za ta shigar da ƙorafinta a duk wuraren da ya kamata ciki har da Majalisar Ɗinkin Duniya.

    A baya an sha zargin Daular da taimaka wa dakarun RSF da makaman da suke amfani da su wajen yaƙi da sojojin Sudan a kazamin yaƙin da ake gwabzawa a kasar. Sai dai ƙasar ta sha musanta wannan zargi.

    A jiya Lahadi, mayaƙan RSF, sun fito suna cewa babu batun sulhu da sojoji domin kawo ƙarshen yaƙin watanni 17.

    Sai dai kuma sojojin ƙasar ta Sudan sun yi watsi da iƙirarin na UAE cewa dakarunsu sun kai harin bam gidan jakadanta a Khartoum.

  11. Isra'ila ta faɗaɗa hare-hare a Lebanon da Yemen

    Isra'ila ta faɗaɗa hare-haren da take kaiwa a Lebanon cikin 'yan sa'o'i da suka gabata,inda ta sanar da cewa ta ruguza gwamman cibiyoyin Hezbollah.

    Sojojinta sun ce jiragensu na yaƙi sun yi luguden wuta a cibiyar harba makaman roka da rumbin ajiyar makamai da ke tsaunin Bekaa, da wasu yankunan Hezbollah da ke kudancin Lebanon.

    Wata ƙungiyar a-ware da ke fafutukar kafuwar Falasdinu ta ce akwai shugabanninta uku da aka kashe a hare-haren Isra'ila a unguwar Kola da ke birnin Beirut.

    Wakilin BBC ya ce Firaminista Netanyahu ya ce ba za su sarara ba har sai sun ga bayan Hezbollah.

    A jiya Lahadi kuma, sojojin Isra'ila sun kai hare-hare ta sama a yankin da Houthi ke iko da shi a Yemen.

    Jiragen yaƙinta sun yi ruwan bama-bamai a cibiyar makamashi da tashar ruwan Hodeidah.

  12. Isra'ila ta kashe shugaban Hamas a Lebanon

    Ƙungiyar Hamas ta Zirin Gaza ta sanar da cewa an kashe shugabanta a Lebanon, Fateh Sherif Abu el-Amin, tare da wasu 'yan'uwansa sakamakon harin Isra'ila a kudancin Lebanon.

    Hamas ta ce harin ya faɗa kan gidansa da ke sansanin Al-Bass.

    Tun da farko kamfanin labarai na gwamnatin Lebanon ya ruwaito harin a kusa da garin Tyre.

    Duk da cewa Hamas a Gaza take al'amuranta - inda Isra'ila ke kai hare-hare tun ranar 7 ga watan Oktoba - tana kuma gudanar da ayyuka a Lebanon.

    Iran ce ke taimaka wa Hezbollah da Hamas.

  13. Maraba

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye.

    Za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya, musamman a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma yaƙin da ake yi tsakanin Hezbollah da Isra'ila a Lebanon.

    Ku biyo mu domin sanin halin da ake ciki.