Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 30/09/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran muhimman abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/09/2024.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Umar Mikail da Nabeela Mukhtar Uba

  1. Mu kwana lafiya!

    Masu bin mu a wannan shafi, da haka muka kawo ƙarshen labaran da muke kawo maku daga sassan duniya a wannan shafi na Kai Tsaye.

    Za mu sake dawowa gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Kafin nan, kuna iya ƙara duba ƙasa domin karanta labaran da muka wallafa maku tsawon yinin wannan rana ta Litinin.

    Nabeela Mukhtar Uba, a madadin sauran abokan aiki nake cewa asuba ta gari.

  2. Mayaƙan Houthi sun yi iƙirarin kakkaɓo jirgin Amurka mara matuƙi

    Mayaƙan Houthi a Yemen sun ce sun harbo wani jirgi marar matuƙi na Amurka a yankin Saada da ke arewacin ƙasar.

    Ƙungiyar ta yi iƙirarin cewa shi ne jirgi na 11 da ta kakkaɓo.

    Mai magana da yawun ƴan Houthi ya ƙara da cewa mutum biyar suka rasu tare da jikkata ƙarin wasu hamsin sakamakon harin jiya Lahadi da Isra'ila ta kai tashar Hodeidah da ke ƙasar.

    Isra'ila ta ce harin martani ne na harin da makami mai linzami da ƙungiyar ta kai a filin jirgin Tel Aviv a ranar Asabar.

    Mayaƙan Houthi na kai hare-haren makamai masu linzami kan Isra'ila da kuma tekun Bahar Maliya, a matsayin nuna goyon baya ga Falasɗinawa a Gaza.

  3. Mun janye tuhumar halasta kuɗin haram kan Bobrisky a bisa doka – EFCC

    Wata mai gabatar da ƙara a hukumar yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa zagon ƙasa a Najeriya, Bilkisu Bala ta shaida wa kwamitin majalisar wakilan ƙasar da ke bincike kan zarge-zargen cin hanci da ake yi wa wasu jami'an hukumar da na hukumar kula da gidajen gyaran hali cewa an janye tuhume tuhumen halasta kuɗin haram da ake yi wa Bobrisky da aka fi sani da Idris Okuneye bisa doka.

    EFCC ta bayyana haka ne cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na X.

    Bilkisu Bala ta shaida wa kwamitin cewa an janye tuhume-tuhumen la'akari da bayanan wani sashen hukumar na musamman da ke yaƙi da halasta kuɗin haram da ya ce kamfanin Okuneye mai suna Bob Express ba kamfani bane na hada-hadar kuɗi ko na kasuwanci don haka ba za a iya hukunta shi a matsayin wanda ya saɓa wa dokar halasta kuɗin haram ta 2022.

    Tun farko mun tuhume shi da laifuka shida kan cin mutuncin takardar naira da kuma halasta kuɗin haram la'akari da jawabin da ya yi cewa kamfaninsa Bob Express ba shi da rajista da sashen na musamman da ke yaƙi kan halasta kuɗin haram sannan kuma ba ya samar masa da wata riba.

    Mai gabatar da ƙarar ta yi fatali da iƙirarin cewa janye tuhume-tuhumen na da nasaba da zargin bayar da cin hanci abin da ta ce bai faru ba.

    Bilkisu Bala, wadda ta bayyana gaban kwamitin majalisar wakilan bisa rakiyar wasu manyan jami'an EFCC ta buƙaci kwamitin da ya sake yin nazari kan batutuwan da EFcc ta yi sannan kuma ya gabatar wa jama'a sakamakon bincikensa domin tabbatar da adalci.

  4. An haramta wa Eto'o halartar wasannin Kamaru

    Kwamitin ladabtarwa na hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, Fifa ya haramta wa shugaban Kungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Kamaru, Samuel Eto'o halartar duk wasannin da ƙasarsa za ta buga.

    An ɗauki matakin kan tsohon ɗanwasan Barcelona da Chelsea sakamakon saɓa dokokin Fifa da suka shafi ladabtarwa.

    Haramcin na da alaƙa da wasan da Kamaru ta buga da Brazil ranar 11 ga watan Satumba a gasar cin kofin duniya ta ƴan ƙasa da shekara 20 inda Brazil ɗin ta doke Kamaru da ci 3 da 1 bayan ƙarin lokaci.

    A yanzu, an haramta wa Eto'o zuwa wasannin da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar ƙasa - mata da maza za su buga.

    Fifa ta ce matakin zai soma aiki nan take kuma tuni aka sanar da Eto'o.

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kamaru. ɓangaren maza za ta kara da Kenya a watan Oktoba a wasan neman tikitin zuwa gasar cin kofin Afirka ta 2025.

    Eto'o ya jagoranci wani taro a Douala yau Litinin domin tattaunawa kan shirye-shiryen tunkarar wasan ranar 11 ga watan na Oktoba.

    An tuntuɓi hukumar ƙwallon ƙafa ta Kamaru domin jin martaninta kan matakin da aka ɗauka kan Eto'o.

  5. Isra'ila ta ce za ta sake kai wa Hezbollah hari

    Akwai ƙwararan alamu da ke nuna cewa Isra'ila za ta ƙaddamar da farmaki ta ƙasa kan Hezbollah a Lebanon.

    Manyan tankunan yaƙi sun yi jerin gwano a arewacin iyakar Lebanon da kuma wasu wurare uku da aka ayyana a matsayin wuraren aikin soja.

    Tunda farko sakataren tsaron Isra'ila, Yoav Gallant ya ce nan ba da jimawa ba za su ƙaddamar da sabon salo a yaƙin da suke da Hezbollah, ta hanyar amfani da sojojinsu na ruwa da sama da kuma ƙasa, domin tabbatar da mayar da ƴan Isra'ila dubu sittin da suka tsere daga muhallansu zuwa gidajensu.

    Mataimakin shugaban Hezbollah ya yi iƙirarin cewa ƙungiyar a shirye take wajen tunkarar Isra'ila.

  6. Sojin saman Najeriya na binciken kuskuren kashe fararen hula 24 a Giwa

  7. Ana binciken kamfanin abinci na McDonalds kan safarar mutane zuwa Birtaniya

    Wani binciken BBC ya gano cewa kamfanin abincin maƙulashe na McDonalds ya gaza wajen hana cin zarafin wasu mutane tara da aka yi safararsu zuwa Ingila daga Jamhuriyar Czech.

    Dukkanin mutanen na aiki ne a wuri guda na wani sashe na kamfanin kuma mutanen da suka kawo su Birtaniya ne ke karɓe albashinsu.

    Kamfanin da sauran rukunansa sun gaza gano cewa ana amfani da mutanen ne wajen bautar zamani - ciki har da yadda ake biyan albashin mutanen tara a asusu guda, kuma kowanne mutum guda na aikin sa'o'i 100 a mako guda.

    Ɗaya daga cikin ma'aikatan ya bayyana yanayin uƙubar da suka tsinci kansu, inda har yake cewa da ma mutuwa ya yi.

    Kamfanin da abokan hulɗarsa, sun ce sun ƙaddamar da bincike domin gano irin waɗannan barazanar a nan gaba da kuma cewa suna aiki tuƙuru wajen taimaka wa kowane ma'aikancinsu da suka fuskanci alamar cin zarafi.

  8. Abin da ƴan Najeriya ke cewa kan ci gaba da faɗuwar darajar naira

  9. MSF na jinyar gomman matan da aka yi wa fyaɗe a Kongo

    Kungiyar agaji ta Likitocin duniya, MSF, ta ce ta yi jinyar fiye da mutum dubu 25 galibinsu mata da suka samu raunuka sakamakon azabtarwa da fyade a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

    Ƙungiyar ta ce waɗannan alƙaluman duka sun faru ne a shekarar 2023, inda hakan ke nuni da cewa akan yi wa mata biyu fyaɗe a cikin kowace sa'a.

    Wannan adadi shi ne mafi girman da MSF ta taɓa tattara bayanansu a Kongo.

    Wakilin BBC ya ce mata da ƙananan yara na shiga babban hatsari a duk lokacin da suka fita daga sansanin ƴan gudun hijira domin ɗebo ruwa da itace.

    Wuraren da abin ya fi ƙamari shi ne arewacin Kivu inda shekara uku da ta gabata yaƙi ya ɓarke tsakanin kungiyar 'yantawayen M23, da sojojin Kongo, da kawayensu.

  10. Iran za ta rushe nan ba da jimawa ba – Netanyahu

    Firaiministan Isra'ila Benyamin Netanyahu, ya yi jawabi ga al'ummar Iran a cikin wani bidiyo inda ya ce ƙasarsa na tare da su.

    Ya zargi shugabannin Iran da ƙara jefa ƙasar cikin duhu da kuma barazanar yaƙi ta hanyar goyon bayan Hezbollah da Hamas.

    Ya ce babu inda dakarunsa ba za su kutsa ba wajen kare al'ummar ƙasar, kuma nan ba da jimawa ba jamhuriyar musulunci ta Iran za ta ruguje da sauri fiye da yadda mutane suka yi tsammani.

    Firaiministan ya ce idan ƴan Iran suka samu ƴanci za a kawo ƙarshen kashe biliyoyi kan yaƙi, za kuma a tabbatar da zaman lafiya tsakanin Yahudawa da ƴan Iran ɗin.

    Ya ce ku yi tunannin ina ma maƙudan kuɗaɗen da gwamnatinku ke ɓarnatarwa don samar da makamin nukiliya da kitsa yaƙe-yaƙe a ƙasashen duniya, a ce ana amfani da su wajen bunƙasa ilimin ƴaƴanku da inganta kiwon lafiyarku da samar da ababen more rayuwa da dukkan buƙatunku.

  11. Mece ce makomar Hezbollah da Lebanon?

  12. An ceto yara 19 da aka yi safarar su daga Kebbi zuwa Cross River

    Gwamnatin jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya ta ce ta yi farin ciki da nasarar da aka samu ta ceto wasu yara 19, ƴan asalin jihar da masu fasaƙaurin mutane suka sace suka kai su Cross River da ke kudancin ƙasar.

    Gwamnan jihar Kwamred Nasir Idris ne ya bayyana haka yayin bikin karɓar yaran da aka yi a gidan gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi, tare da shan alwashin ƙin amince wa da irin wannan al’ada ta safarar mutane a jiharsa.

    A cewar gwamna Nasir Idris, an samu nasarar ƙwato yaran ne da haɗin gwiwar hukumar NAPTIP mai hana fasaƙaurin mutane.

    Ya ce yaran waɗanda adadinsu ya kai 19 dukkansu babu wanda ya wuce shekara 11.

    Gwamnan ya ƙara da cewa hukumar NAPTIP ta bibiya labarin sannan ta sanar da gwamnati inda kuma suka yi tattaki zuwa birnin Calabar tare da gano yaran da wanda ake zargi da jagorancin safarar yara a jihar.

    "Abin baƙin ciki, bincike da hukumar lafiya ta yi a asibiti ya nuna cewa ana kwana da ƙananan yaran ƴan shekara 10 zuwa ƙasa, wannan ba al'adar mu ba ce." in ji gwamna Nasir Idris.

    Gwamnan Nasir Idris ya ci gaba da cewa iyaye da dama na sakaci suna ba da yaransu da sunan za a kai su makaranta, sai dai saɓanin haka ne ke faruwa da yaran.

    Ya kuma ce kowanne mahaifi ya sani abin tambaya ne ga kiwon yayansa da ubangiji ya bashi a matsayin kyauta.

    Najeriya na daga cikin ƙasashen da ke fama da masu fasaƙaurin mutane na cikin gida da kuma na ƙetare.

    Ko a ƙarshen makon jiya sai da hukumar NAPTIP ta miƙa wasu yan mata takwas ‘yan Najeriya da aka yi fasaƙaurinsu zuwa ƙasar Ghana ga iyayensu.

  13. Ƴansanda sun kama mutum 89 kan zargin aikata miyagun laifuka a Kano

    Rundunar ƴansandan jihar Kano ta ce ta kama waɗanda ake zargi ɓatagari ne su 89 har da masu fashi da makami 15 da wasu mutum 10 da ake zargi dilolin miyagun ƙwayoyi ne da kuma mutum guda da ake zargi mai safarar mutane ne.

    Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya ce jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kuɓutar da mutum biyu da aka yi safararsu da ƙarin biyu da suka tsinci kansu a hannun masu garkuwa da mutane.

    SP Kiyawa ya ƙara da cewa rundunar ƴan sandan ta kuma ƙwato haramtattun miyagun ƙwayoyi da muggan makamai da kuma muhimman takardu da aka sace har da kwalabe 538 na maganin Bacardi da kuma ƙunshin busassun ganyayyaki da ake zargi tabar wiwi ce.

    Sanarwar ta ce rundunar ta gudanar da waɗannan ayyukan ne tsakanin 12 da 30 ga watan Satumban bana.

    Kiyawa ya bayyana cewa dabarun da jami'an rundunar ta ɗauka ne ya kai ga nasarorin inda kuma tuni aka tisa ƙeyar mutum 43 da ake tuhuma zuwa kotu yayin da ake gudanar da bincike a kan wasu 46.

    Kakakin rundunar ya kuma bayar da tabbaci cewa rundunarsu ta kammala dukkan matakan tsaron da suka dace yayi da kuma bayan bikin ranar ƴancin kai da za a yi gobe, Talata.

  14. VeryDarkMan ya gabatar da hujjoji kan zargin Bobrisky da ba jami'an gwamnati cin hanci

    Martins Vincent Otse da mutane suka fi sani da Verydarkman ya gurfana gaban kwamitin majalisar wakilan Najeriya da aka kafa domin yin bincike kan zarge-zargen cin hanci kan wasu jami'an hukumar kula da gidajen yari da na hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa zagon ƙasa.

    A kwanan nan ne Verydarkman ya yi wata fallasa inda ya saki sautin muryar da ya ce ta Bobrisky ce da ke iƙirarin biyan wasu jami'an EFCC maƙudan kuɗi domin janye wasu tuhume-tuhume da ake masa inda kuma ya yi iƙirarin cewa bai zauna a gidan yari ba tsawon hukuncin aka yanke masa.

    Wannan bankaɗa ta sa hukumomi kafa kwamiti domin gudanar da bincike lamarin da ya kai ga dakatar da wasu manyan jami'an hukumar kula da gidajen yari saboda zarginsu da hannu a lamarin.

    Hukumar gudanarwar kula da gidajen yari da shige da fice da gobara ta Najeriya ta ce ta ɗauki matakin dakatar da jami'an ne domin ba da sararin gudanar da bincike kan zargin da ake masu.

    A ranar Litinin ne Verydarkman ya bayyana gaban kwamitin inda ya yi zargin cewa Bobrisky wanda asalin sunansa Idris Okuneye yana yi wa mutumin da ake zargin ya ba shi rancen kuɗi barazana.

    Verydarkman ya gabatar da jawabinsa gaban kwamitin inda kuma ya gabatar da wasu takardu da a cewarsa hujjojinsa ke nan.

    Ya yi iƙirarin cewa ya yaɗa sautin muryar a shafukan sada zumunta bayan da ya saurari sautin ya kuma ga cewa wasu jami'an EFCC suna da hannu a lamarin.

    A cewar Verydarkman ya yi haka ne saboda barazanar da Bobrisky ke yi wa mutumin da ya ba shi rancen naira miliyan huɗu - "mutumin ya ba shi rance kuma da lokacin karɓar rancen ya yi, Bobrisky ya ƙi biyansa, ya kuma ɓuge da yi masa barazana,".

    "Abokina ne ya aiko da rasiti, Sai Bobrisky ya riƙa roƙon abokin nawa sannan ya biya amma da na saurari sautin, sai na ajiye shi."

    Tun farko Verydarkman ya shaida wa kwamitin cewa ba zai yi magana ba matuƙar Bobrisky da shugaban EFCC Ola Olukoyede ba su bayyana gaban kwamitin ba, sai dai daga baya ya yi magana bayan da kwamitin ya nemi Verydarkman ya yi bayani kan sautin da ya yaɗa ranar 23 ga Satumba wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta.

  15. Za a fara zaman sauraron shari'a kan Marine Le Pen

    Za a fara zaman sauraran shari'a kan Marine Le Pen, shugabar masu ra'ayin rikau a Faransa, kan zargin kashe kuɗaɗen tafiyar da majalisar Turai ba bisa ƙa'ida ba.

    Akwai kuma wasu manyan jami'ai sama da 20 a jam'iyyarta da suma ke fuskantar irin wannan tuhuma.

    Wakilin BBC ya ce, ana zarginsu da ɗaukan mataimaka da ke aikin da ya shafi jam'iyyarsu da sunan majalisar Turai da ke biyansu albashi.

    Idan aka same ta da laifi, za a ci ta tara ko ɗaureta a gidan yari, Kuma za a hanata neman wani muƙami a gwamnati na tsawon shekara biyar.

    Wannan na iya zama naƙasu ga muradinta na zama shugabar ƙasa.

    Jam'iyyarta ta musanta waɗannan zarge-zarge.

  16. MSF ta yi jinyar mata fiye da 25,000 da aka yi wa fyaɗe a Congo a 2023

    Kungiyar agaji ta Likitocin duniya, MSF, ta ce ta yi jinyar fiye da mutum dubu 25 galibinsu mata da suka samu raunuka sakamakon azabtarwa da fyade a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

    Ƙungiyar ta ce waɗannan alƙaluman duka sun faru ne a shekarar 2023, inda hakan ke nuni da cewa akan yi wa mata biyu fyaɗe a cikin kowacce sa'a.

    Wannan adadi shi ne mafi girman da MSF ta taba tattara bayanansu a Kongo.

    Galibin wadanda abin ya shafa an yi musu magani ne a yankunan da aka tsugunnar da su a kusa da Goma, kuma wannan adadi na ci gaba da karuwa saboda faɗan da ake yi tsakanin kungiyar 'yantawayen M23, da sojojin Kongo, da kawayensu.

  17. Rundunar sojin Sudan ta musanta zargin kai wa jakadan Daular Larabawa hari

    Rundunar sojin Sudan sun musanta zargin da Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi na cewa sun kai hari kan gidan jakadanta a birnin Khartoum.

    Rundunar ta dora alhakin kai harin kan abokan gwabzawarsu wato dakarun RSF, inda suka yi tir da harin.

    Da yammacin jiya Lahadi ne ma'aikatar harkokin wajen Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce za ta gabatar da ƙorafinta a gaban Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da duk inda ya dace.

    Wakilin BBC ya ce sojoji sun sha zargin Daular da taimaka wa dakarun RSF da makaman da suke amfani da su wajen yaƙi da su. Sai dai Daular ta sha musanta wannan zargi.

  18. Sama da mutum 100,000 ne suka tsere daga Lebanon zuwa Syria - MDD

    Hukumar ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce sama da mutum 100,000 ne suka yi hijira daga Lebanon zuwa Syria tun bayan ƙazancewar yaƙin Isra'ila da Hezbollah a makon da ya gabata.

    Hukumar ta ce yawancin mutanen ƴan asalin ƙasar Syriyar ne wadanda suka guje wa yaƙin basasa a ƙasarsu.

    Shugaban hukumar, Filippo Grandi ,ya ce adadin mutanen da ke gudun hijirar ya ninka cikin kwana biyu.

    Firaministan Lebanon Najib Miƙati ya ce mutane kusan miliyan ne yaƙin ya raba da muhallansu a Lebanon.

  19. Harin Isra'ila ya kashe sojan Lebanon

    Wani harin Isra'ila ya kashe sojan ƙasar Lebanon da ke tafe a kan babur a kudancin ƙasar, a cewar rundunar sojan ƙasar.

    Rundunar ta ce harin na jirgi maras matuƙi ya hari babur ɗin ne lokacin da yake wucewa kusa da wani wurin duba ababen hawa a yankin Wazzani da ke kusa da iyakar Isra'ila.

    Wata majiyar sojin ta faɗa wa kamfanin labarai na AFP an hari mutum biyu ne 'yan Syria da ke kan babur, inda ɓaraguzai suka shafi sojan kuma ya rasu.

    Zuwa yanzu Isra'ila ba ta ce komai ba game da harin.

  20. Tinubu ya rantsar da Kudirat Kekere-Ekun babbar mai shari'a ta Najeriya

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da Mai Shari'a Kudirat Olatokunbo Kekere-Ekun domin kama aiki a matsayin babbar mai shari'a ta ƙasa a ranar Litinin bayan Majalisar Dattawa ta amince da naɗin nata.

    Ita ce mace ta biyu da take riƙe muƙamin a tarihi, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana.

    An yi bikin rantsuwar ne a gaban tsofaffin manyan alƙalai huɗu, ciki har da mace ta farko da ta riƙe muƙamin Mariam Aloma Mukhtar.

    "Fannin shari'a babban ginshiƙi ne da ke tallafe da tsarin dimokuɗaiyarmu, kuma tsawon shekaru fannin shari'ar Najeriya ya sha nuna tasirinsa na mai shiga tsakani domin tabbatar kowa ya bi doka," a cewar Shugaba Tinubu yayin taron.

    "Matsayinki na zama wuri na ƙarshe da talaka zai samu adalci yana da muhimmanci wajen saka wa mutane ƙwarin gwiwa kan dimokuraɗiyya," in ji shi.