Tauraron ɗan wasan Argentina Lionel Messi ya ce ba zai shiga cikin tawagar ƙasarsa ta 'yan ƙasa da shekara 23 ba yayin gasar wasanni ta Olympics.
A madadin haka, Messi mai shekara 37 zai mayar da hankali kan buga gasar Copa America da za a fara a watan nan.
"Na faɗa wa kociya Mascherano kuma gaskiya mun fahimci matsalar," kamar yadda Messi ya faɗa wa kafar yaɗa labarai ta ESPN.
"Da wuya [mutum ya dinga tunanin Olympics yanzu] saboda Copa America ne a gabanmu. Zai zama wata biyu ko uku zan yi ba tare da ƙungiyar [Inter Miami] ba kenan, kuma yanzu shekaruna sun wuce a ce na shiga komai da komai.
"Ya kamata na duba da kyau, abin zai yi yawa idan na buga gasa biyu a jere. Na yi sa'a sosai da na buga Olympics kuma na lashe gasar tare da Mascherano."
Argentina da Messi za su fara kare kofin Copa America da suka ɗauka a gasar da ta gabata kuma za su fara wasa da Canada a ranar 20 ga watan Yuni. Za a buga wasan ƙarshe na gasar ranar 14 ga watan Yuli, kwana 10 kacal kafin fara Olympics ɗin a birnin Paris na Faransa.
Tun bayan da matasan na Argentina suka yi nasarar samun gurbi a Olympics aka fara yaɗa labarai cewa Messi zai shiga cikinsu a matsayin ɗaya daga cikin 'yan wasa uku masu shekaru da yawa kamar yadda doka ta bai wa kowace tawaga dama.
Mascherano ya ce ƙofar Messi a buɗe take ta shiga tawagar, kodayake dai ya amince da abubuwan da ke gaban ɗan wasan mai kambin gwarzon ɗan ƙwallon duniya bakwai.
Newcastle ta ɗauki Lloyd Kelly a kyauta
Asalin hoton, Newcastle United
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Newcastle ta sanar da ɗaukar Lloyd Kelly a kyauta.
Ɗan wasan bayan mai shekara 25 ya bar Bournemouth a ƙarshen kakar da aka kammala bayan kwantaraginsa ya ƙare a kulob ɗin.
Newcastle ta ce ɗan ƙwallon ya saka hannu kan yarjejeniya mai tsawo.
Sai dai Sky Sports ta fahimci cewa ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar da kuma zaɓin tsawaita ta da shekara ɗaya.
Abubuwan da suka kamata ku sani kan gasar Euro 2024
Asalin hoton, Getty Images
Idan ba ku san lokuta da kuma yadda gasar ƙasashen Turai ta Euro 2024 za ta kasance ba, to ga yadda abin yake:
Yaushe za a fara gasar kuma a ina?
Gobe ne (Juma'a) da misalin ƙarfe 8:00 agogon Najeriya da Nijar. Mai masaukin baƙi Jamus ce za ta buɗe gasar da wasa tare da Scotland a rukunin A a birnin Munich.
Yaya sauran jadawalin gasar yake?
Tawagar ƙasa 24 ne za su nemi lashe kofin gasar karo na 17 kamar haka:
Akasarin masu sharhi na ganin Ingila, da Faransa, da Jamus, da Portugal, da Sifaniya a matsayin waɗanda ke kan gaba. Amma komai zai iya faruwa.
A waɗanne filayen wasa za a buga wasannin?
Filayen wasa 10 ne za su karɓi baƙuncin wasannin a faɗin Jamus, ciki har da Berlin, da Dortmund, da Hamburg, da kuma Munich.
Yaushe za a kammala gasar?
Za a buga wasan ƙarshe a birnin Berlin ranar 14 ga watan Yuli.
Messi zai yi ritaya a Inter Miami
Asalin hoton, USA Today Sports
Lionel Messi ya yanke shawarar yin ritaya a Inter Miami - sai dai kawo yanzu bai tsara lokacin da zai bar taka leda ba.
Mai shekara 36, mai kyautar Ballon d'Or takwas, ya koma buga gasar tamaula ta Amurka a kakar 2022/23, bayan da kwantiraginsa ya kare a Paris St-Germain.
Kyaftin din tawagar Argentina ya nuna kansa a Barcelona, inda ya lashe Champions League hudu da La Liga 10 a kungiyar da ke Sifaniya.
Wanda ya dauki kofin duniya a 2022 da Argentina a Qatar a 2022, yana da sauran kunshin yarjejeniya da za ta kare a Inter Miami zuwa karshen kakar 2025.
Kawo yanzu Messi yana wasa kan ganiya ba za ka ce zai yi ritaya kwanan nan ba, wanda ya ci kwallo 12 da bayar da 13 aka zura a raga a wasa 12 a gasar ta Amurka.
Dortmund da kocinta Terzic sun raba gari a tsakaninsu
West Ham ta kammala ɗaukar Guilherme daga Brazil
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta West Ham ta kammala ɗaukar Luis Guilherme daga Palmeiras ta ƙasar Brazil.
Matashin ɗan wasan mai shekara 18 ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar da kulob ɗin na birnin Landan da ke buga gasar Premier League.
Ya buga wa babbar ƙungiyar Palmeiras wasa 40, inda har ya lashe babbar gasar ƙasar ta Brazilian Serie A.
Zai isa Landan ne bisa sharaɗin tantancewa da samun takardun biza da kuma na izinin aiki a Ingila.
Wace ƙasa ce za ta lashe gasar Euro 2024?, Hasashen Jose Mourinho
Asalin hoton, Getty Images
Game da hasashen ƙasar da za ta zama lashe gasar ƙasashen Turai ta Euro 2024, shahararren mai horarwa Jose Mourinho ya faɗi wadda yake ganin za ta jinjina kofin gasar.
Kocin wanda ya shafe akasarin shekarun sana'arsa a gasar Premier League ta Ingila, ya ce yana ganin ƙasarsa ta haihuwa Portugal ce za ta yi nasara, inda za ta doke Ingila a wasan ƙarshe.
Mourinho ya ƙara da cewa Harry Kane ne zai lashe takalmin zinare na ɗan wasan da ya fi kowa cin ƙwallaye, sai kuma abokin wasansa Jude Bellingham da zai zama gwarzon ɗan wasan gasar.
Game da kambin Ballon d'Or kuma, Jose na ganin ɗan wasan Real Madrid da Brazil, Vinicious Jr ne zai yi wuf da ita a wannan shekarar.
Ɗan bayan Ingila Stones ya koma atasaye, Euro 2024
Asalin hoton, Reuters
Ɗan bayan Ingila John Stones ya koma atasaye bayan jinyar da ya yi.
Ya shafe wunin Laraba a ɗakinsa na otel don kauce wa yaɗa cutar ga sauran abokan wasansa.
Ingila za ta buɗe wasanninta na Euro 2024 da Serbia a Gelsenkirchen na Jamus ranar Lahadi.
Sau ɗaya Stones ya taɓa buga cikakkun minti 90 cikin wata biyu da suka wuce, amma ya buga minti 45 a wasan Ingila na ƙarshe da Iceland kafin gasar a ranar Juma'a.
Ingila na cikin rukuni na C mai ƙunshe da Denmark, da Slovenia, da kuma Serbia.
Jita-jita a kasuwar saye da musayar 'yan wasan Turai
Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich ta nuna sha'awarta a kan dan wasan bayan Liverpool Joe Gomez, Chelsea na tunanin sabunta kwantaragin Conor Gallagher, AC Milan na zawarcin Matty Cash na Aston Villa.
Bayern Munich na zawarcin dan wasan bayan Liverpool da Ingila Joe Gomez, mai shekara 27(Mirror)
Chelsea na tunanin sake sabon kwantaragin dan wasan tsakiyar Ingila Conor Gallagher, mai shekara 24, wanda Aston Villa da Tottenham ke nema.(Guardian)
AC Milan ta tattauna da Aston Villa kan daukar dan wasan bayan Poland Matty Cash mai shekara 26.(Talksport)
Sai dai farashin fam miliyan 30 da Villa ta sanya na iya kawo cikas a tattaunawar.(Athletic)
Ana shirin nada tsohon kocin Lille da Roma Paulo Fonseca a matsayin sabon kocin AC Milan.(Sky Sports)
Wakilin dan wasan tsakiya na Aston Villa Douglas Luiz, mai shekara 26, ya tuntubi daraktan wasanni na Barcelona Deco yayin da dan wasan na Brazil ke tantance kungyar da ya kamata ya koma a bazara.(Sports Spanish)
Barkanmu da rana
Maraba da sake haɗuwa a shafin lalabarin wasanni na kai-tsaye.
Za mu kawo muku yadda take kasancewa a duniyar wasanni a yau Alhamis tare da ni Umar Mikail.