KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 14/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 14/07/2026

Taƙaitattu

  • Dangote ya fara sayar da man fetur da dala
  • An ji ƙarar manyan abubuwan fashewa a Iran
  • Sojojin Jordan sun ce sun kakkaɓo makaman Iran
  • Ƙasashen Gulf za su fara biyan kuɗin tsaron da muke ba su - Trump
  • Iran ta ce ta kai hare-haren kan manyan jiragen dakon mai a mashigar Hormuz
Skip Bidiyo and continue reading
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Jami'an kashe gobara na fafatawa da gobarar daji a Faransa

    Gobarar daji

    Asalin hoton, Frank Desprez / SDIS 77 via EPA

    Gobarar daji da ke ci gaba da bazuwa a wani daji da ke kudancin birnin Paris ta mamaye kusan murabba’in kilomita ashirin, yayin da jami’an kashe gobara ke fatan shawo kanta a yau.

    Ministan harkokin cikin gidan Faransa ya ce an kama mutum biyu bisa zargin haddasa gobarar da gangan.

    Ɗaya daga cikinsu matashi ne mai shekara 18, wanda rahotanni suka ce an kama shi ɗauke da abin kunna wuta, yayin da hannayensa ke cike da toka.

    A faɗin ƙasar, an kama mutane 59 bisa zargin haddasa gobara da gangan ko kuma sakaci.

    A karon farko a yankin Paris, an tura jiragen sama na musamman da jirage masu saukar ungulu masu zubar da ruwa domin taimakawa wajen dakile gobarar.

  2. Wa zai kai wasan ƙarshe tsakanin Faransa da Spain?

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Kylian Mbappe da Lamine Yamal za su fuskanci junansu karo na 11, sai dai wannan ne karawa mafi muhimmanci saboda suna neman zuwa wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya.Ga wasu bayanai kan hamayyar da ke tsakanin ƴan wasan da kuma ƙasashensu.

  3. An gargaɗi jiragen Turai game da keta sararin samaniyar ƙasashen Gulf

    Hoton jirgi

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da kariyar jiragen sama ta Tarayyar Turai ta gargaɗi jiragen sama kan keta sararin samaniyar ƙasashen Bahrain da Kuwait da Qatar UAE da kuma ratsawa ta saman tekun Oman.

    Hukumar ta ce ta yi gargaɗin ne saboda halin rashin tabbas da ake ciki a yankin kan ƙaruwar ayyukan soji ciki har da yiwuwar samun makamn linzami da jirage marasa matuƙa.

    ''Akwai yiwuwar fuskantar hatsari wajen ketawa ta saman wannan yanki'', in ji hukumar.

    Hukumar ta ce za a ci gaba da aiki da wannan shawara har zuwa ranar 29 ga watan Yulin, inda ta ce za ta ci gaba da sanya idanu kan lamarin.

    Ƙasashen yankin na fama da hare-haren Iran kan sansanonin sojin Amurka a yankin, yayin da Amurka ke amfani da ƙasashen wajen kai wa Iran hare-hare.

  4. Farashin ɗanyen man fetur ya zarce dala 85

    gangar mai

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin da yaƙi tsakanin Amurka da Iran ke ci gaba da zafafa, farashin man feutur a kasuwannin duniya na ci gaba da yin tashin gwauron zaɓo.

    A ranar Talata farashin ya tashi da kusan kashi uku cikin ɗari, lamarin da ya sa man ya yi tsada mafi yawa cikin mako huɗu.

    Tashin farashin ba ya rasa nasaba da barazanar Amurka na datse tasoshin ruwan Iran.

    Barazanar na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen biyu ke zafafa hare-haren ramuwar gayya kan kan ƙoƙarin ƙwace iko da mashigar Hormuz.

  5. ADC da Atiku sun ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Koli

    Atiku

    Asalin hoton, Atiku/X

    Jam'iyyar ADC a Najeriya da kuma ɗantakararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar sun yanke shawarar ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙolin Najeriya kan hukuncin shugabancin jam'iyyar.

    A ranar Litinin ne kotun ɗaukaka ƙara da umarci hukumar zaɓen ƙasar INEC ta daina amincewa da tsagin David Mark a matsayin shugabannin jam'iyyar.

    Cikin wasu mabambantan sanarwa da ADC da Atiku suka fitar, sun ce za su ƙalubalanci hukuncin a Kotun Ƙolin ƙasar.

    Kotun ɗauka ƙarar ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya wadda ta hana INEC amincewa da tarukan jam'iyyar na ƙasa da jihohi, wanda a nan ne aka zaɓi shugabannin ɓangaren David Mark.

    Atiku da ADC sun buƙaci lauyoyinsu su tattara duka bayanan da suke buƙata domin ɗaukaka ƙarar.

    ADC ta jima tana fama da rikicin shugabanci, wani abu da masana ke gani a matsayin barazana ga shirye-shiryen jam'iyyar don tunkarar zaɓen 2027.

    Atiku Abubakar

    Asalin hoton, Atiku Abubakar

  6. An kai hare-hare a wurare huɗu a birnin Bushehr na Iran

    Mataimakin gwamnan lardin Bushehr mai kula da harkokin tsaro ya ce an kai hare-hare a wurare huɗu da ke cikin birnin Bushehr.

    Ehsan Jahanian ya ce hare-haren sun faru ne da yammacin ranar Litinin agogon ƙasar Iran.

    Ya ce binciken farko da aka gudanar, sun nuna cewa babu rahoton asarar rayuka sakamakon hare-haren.

    Tun da farko kuma, gidan talabijin na ƙasar Iran ya ruwaito cewa an ji ƙarar fashewa har sau biyar a yammacin birnin Bandar Abbas.

    Hare-haren sun faru ne sa'o'i kaɗan bayan Rundunar Sojin Amurka ta CENTCOM ta sanar da kammala wani sabon jerin hare-haren da ta kai kan Iran.

  7. Dangote ya dakatar da sayar da man fetur da naira

    Dangote

    Asalin hoton, Dangote Refinery

    Matatar Dangote ta sanar da dakatar da sayar da mai ga masu sari da kuɗin Najeriya naira.

    A ranar 1 ga watan Oktoban 2024 ne dai Dangote ya fara sayar da mai na naira ga kwastomominsa a Najeriya, bayan cimma wata yarjejeniya da gwamnatin ƙasar, kan wadata ƙasar da man fetur.

    A lokacin an cimma yarjejeniyar cewa gwamnatin Najeriya za ta riƙa sayar masa da ɗanyen mai da naira yayin da shi ma zai riƙa sayar da wanda ya tace da naira.

    Kawo yanzu dai babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da Dangoten ya bayar dangane da wannan mataki, to amma wasu jaridun ƙasar na ambato wasu majiyoyi a matatar na cewa a yanzu gwamnati na sayar da matatar ɗanyen mai ne da dala, kuma ba ta sayar mata wanda zai wadace ta.

  8. An ji ƙarar manyan abubuwan fashewa a Iran

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayar da rahoton jin ƙarar abubuwan fashewa a birnin Bandar Abbas mai gaɓar ruwa, yayin da yaƙi tsakaninta da Iran da Amurka ya tsananta kan iko da mashigar Hormuz.

    Amurka ta ce ta ƙaddamar da hare-hare kan cibiyoyin soji a faɗin Iran cikin dare, domin ruguza ƙarfinta wajen kai wa jiragen ruwa hare-hare.

    A nata ɓangare Iran ta ce ta kai hare-hare kan cibiyoyin sojin Amurka a Bahrain da Jordan, bayan wasu hare-hare da ta kai wa wasu manyan jiragen ruwa a mashigar Hormuz

  9. Sojojin Jordan sun ce sun kakkaɓo makaman Iran

    Rundunar sojin Jordan ta bayyana cewa ta kakkaɓo wasu makaman linzami huɗu da Iran ta harba mana.

    Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce dakarun juyin juya halin Iran sun tabbatar da kai hari kan sansanin sojin Amurka da ke Jordan.

    A ƴan kwanakin nan Iran ta riƙa kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da ƙasashen yankin Gulf, a matsayin martani kan hare-haren da Amurka ta kai mata.

    Ko a safiyar yau Talata sai da rundunar IRGC ta bayyna cewa ta kai hari kan cibiyar sadarwar tauraron ɗan'adam ta Amurka da sansanin sojin Amurka da ke Bahrain.

  10. Ƙasashen Gulf za su fara biyan kuɗin tsaron da muke ba su - Trump

    Donald Trump

    Asalin hoton, Aaron Schwartz/CNP/Bloomberg via Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce dole ne ƙasashen yankin Gulf su biya Amurka saboda kariyar da za ta ba su daga hare-haren Iran.

    Iran ta fara kai hare-hare kan sansanonin sojij Amurka da ke ƙasashen yankin, a matsayin martani kan hare-haren Amurka.

    Yayin da yake magana game da batun a Fadar White House, Shugaba Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da bai wa ƙasashen na yankin Gulf tsaro, amma kuma dole ne su biya.

    "Ina so su biya, saboda muna aikin kare yanki mai arziki ne a duniya, don haka ya kamata a biya mu wannan aiki,'' in ji shi.

    Shugaban na Amurka ya ci gaba da cewa ƙasashen na buƙatar taimakon Amurka.

    "Za mu samu kuɗi daga ƙasashe irin su Saudiyya da UAE da Qatar da Bahrain da Kuwait da sauran ƙasashen, Ba mu muke buƙatarsu ba, su ne suke buƙatarmu. Mu muna da wadataccen mai, ciki har da na Venezuela,'' kamar yadda ya yi ƙarin haske.

    Shugaban na Amurka ya kuma bayyana cewa ƙasarsa za ta rufe tasoshin ruwan Iran.

    Ya kuma bayyana cewa za a ɗora wa kowane jirgin dakon mai da zai wuce ta mashigar Hirmzu harajin kashi 20.

  11. Iran ta ce ta kai hare-haren kan manyan jiragen dakon mai a mashigar Hormuz

    jirage

    Asalin hoton, Reuters

    Dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran sun ce suna kai hare-hare kan manyan tankokin dakon mai a mashigar Hormuz da kuma wuraren da ke da alaƙa da Amurka a ƙasar Bahrain, yayin da rikici a tsakanin Iran da Amurka ke ƙara kamari.

    Dakarun sun ce sun lalata wasu jiragen ruwan dakon mai bayan sun yi watsi da gargaɗin da aka yi musu tare da kashe na’urorin da ke nuna inda suke zirga-zirga.

    A nata ɓangaren, rundunar sojin Amurka ta ce dakarunta sun kai hare-hare kan wuraren da sojoji suke a sassan Iran.

    Rundunar ta kuma ce a yanzu suna da sojoji dubu 50 da aka jibge a yankin Gabas ta Tsakiya.

  12. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku kasance da mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.