Rufewa
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne dake kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/08/2025
Isiyaku Muhammed da Ahmad Bawage
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Kafofin yaɗa labaran Lebanon sun ce sojojin ƙasar biyar sun mutu yayin da suke ƙoƙarin kwashe abubuwan fashewa daga wata cibiyar tsaro ta Hezbollah da ke kudancin ƙasar.
Bayanai na cewa an bar abubuwan fashewar ne a wajen bayan yaƙin baya-bayan nan tsakanin Isra'ila da Hezbollah.
A farkon wannan makon, gwamnatin ƙasar ta tattauna yadda za a aiwatar da shawarar da Amurka ke goyon baya ta ƙwace makaman ƙungiyar a wani ɓangare na mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a Nuwambar bara.
Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU na shirin sake komawa yajin aiki bayan da ta zargi gwamnati da rashin cika alkawarinta na biya musu bukatunsu da suka daɗe suna nema.
Wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Christopher Piwuna ya fitar, ƙungiyar ta nuna damuwa kan rashin kula da walwalar mambobinta, rashin kuɗaɗen gudanarwa da kuma rashin cika alkawura da aka amince da su.
Gargaɗin na zuwa ne bayan da ministan ilimin ƙasar Dakta Tunji Alausa, ya ce "babu wata jami'a ko malaman ASUU da za su sake shiga yajin aiki a ƙasar nan." Inda ya ce za a iya ƙauce wa hakan idan aka cika alkawuran malaman da kuma shiga tattauna.
Sai dai ASUU ta ce idan ana son kauce wa yajin aiki to a cika musu alkawura da aka amince da su.
Ƙungiyar ta ce yawancin malamai na koyarwa ne ba tare da wani abu ya shiga cikinsu ba, kuma suna gudanar da bincike-bincike ba tare da samun abubuwan da suka kamata ba.
"Lamarin ya kai wasu mambobinmu ba sa iya biyan kuɗin mota zuwa wurin aiki, ba sa biya wa kansu buƙatu har ma da kuɗin makarantar ƴaƴansu," in ji ASUU.
Wata motar bas ɗauke da ƴan jana'iza ta yi hatsari, inda ta hallaka mutum 25 a yammacin ƙasar Kenya, a cewar jami'ai a yankin.
Motar ta ƙwace wa direban, ta ƙauce hanya sannan ta faɗa gefen hanya - a kan babbar hanyar Kisumu-Kakamega ranar Juma'a, kamar yadda rahoton ƴansanda wanda BBC ta gani ya bayyana.
Yankin ya kasance wuri da aka fi samun munanan haɗura.
Ƴansanda sun ce mata 10 da maza 10 da kuma karamar yarinya sun mutu nan take a wurin, inda fasinjoji 20 suka jikkata, biyar daga ciki munana. Huɗu daga cikinsu sun mutu a asibiti daga bisani, a cewar jami'ai.
Fasinjojin na komawa gida ne bayan wata jana'iza da suka halarta kuma an ce dukkansu sun fito daga gida guda.
Ba a dai san abin da ya janyo hatsarin ba kawo yanzu, in ji ƴansanda.
Motar ta kasance ta wata makaranta ce sai dai babu ɗalibai a ciki lokacin da lamarin ya faru.
Shugaban jam'iyyar APC a jihar Kebbi, Abubakar Kana, ya ce sabuwar haɗaka ta jam'iyyar ADC ba ta taka kara ta ƙarya ba a jihar.
Kana ya ce matasan da ba su san me suke yi bane ke yaɗa manufofin ADC.
Ya bayyana haka ne lokacin kaddamar da shirin rabon taki da sauran kayan noma da aka yi a mazaɓar Bagudu/Suru, a karamar hukumar Bagudu na jihar, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Ya nanata cewa har yanzu jam'iyyar APC ce ke da rinjaye a jihar Kebbi.
Sai dai ya nuna damuwa kan ɗabi'un wasu ƴaƴan jam'iyyarsu ta APC waɗanda ke riƙe da mukamai a gwamnati, inda ya zarge su da yin watsi da mutanensu.
Ya yi gargaɗin cewa muddin wannan ɗabi'a ta ci gaba, to ba su da wani zaɓi illa bai wa gwamnan jihar shawara ya sallami masu riƙe da mukamai waɗanda suka ki taimaka wa ƴan mazaɓarsu.
Zanga-zanga ta ɓarke a ƙasar Côté -D'Ivoire domin nuna adawa da matakin shugaban ƙasar, Alassane Ouattara na neman mulki wa'adi na huɗu.
Zanga-zangar na zuwa ne bayan Ouattara mai shekara 83, ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takara a zaɓen da za a yi ranar 25 ga Oktoban 2025.
Sugabannin ƴan adawa a ƙasar sun yi Allah-wadai da matakin, suna zargin cewa gwamnatinsa ta yi wa dokar zaɓe garambawul ne domin durkusar da manyan abokan hamayya.
An cire sunayen tsohon shugaban ƙasar Laurent Gbagbo, da tsohon Firaminista Guillaume Soro, da kuma tsohon minista Tidjane Thiam daga rajistar masu zaɓe, lamarin da ya hana su tsayawa takara.
Ƙungiyoyin fararen hula da shugabannin addinai, ciki har da ƙungiyar limaman cocin Katolika, sun nuna fargaba game da ƙaruwar rikice-rikicen siyasa, inda suka yi gargadin cewa za a iya samun sake ɓarkewar tashin hankali.
Fitaccen ɗan TikTok kuma mawaƙi a arewacin Najeriya, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da GFresh Al'amin ya ce shi ko kaɗan ba ya jin komai a irin yanayin yadda yake gudanar da harkokinsa a kafofin sadarwa, domin a cewarsa yana nishaɗantar da kansa, yana nishaɗantar da wasu, sannan kuma yana samun kuɗi.
Gfresh ya bayyana haka ne a zantawarsa da shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, wanda ya zo tare da matarsa, Maryam Ahmad Yola.
A game da yadda ya fara samun ɗaukaka, mawaƙin ya ce da wahala ya fara harkokinsa har ya kai matakin da yake kai na ɗaukaka.
''Ni ne mawaƙin da yake waƙa ya haɗa kaset na CD ya bi tituna yana tallatawa. Dama can ina da masoya waƙoƙina, da TikTok ta fito kawai sai na ɗaura daga inda na tsaya, inda na cigaba da soki-burutsuna."
Latsa nan don karanta cikakken labarin....
An ruwaito mutuwar ƙarin mutum 11 sakamakon rashin abinci mai gina jiki a Gaza, a cewar ma'aikatar lafiya a yankin.
Wannan ya kawo alkaluman waɗanda suka mutu sakamakon rashin abinci a Gaza zuwa 212, ciki har da yara 98.
Hare-haren Isra'ila sun hallaka aƙalla mutum 38 da jikkata 491 a cikin sa'o'i 24 da suka wuce.
Alkaluman waɗanda ke mutuwa na ta ƙaruwa a daidai lokacin ake ruwaito cewa Isra'ila ta bai wa mazauna Gaza wa'adi zuwa 10 ga Oktoban 2025 da su fice daga yankin, bayan wani shiri da ƙasar ke yi na mamaye zirin Gaza - lamarin ya janyo Alla-wadai da kuma ce-ce-ku-ce daga faɗin duniya.
Sabon tsarin, wanda majalisar ministocin Isra'ila suka amince da shi ranar Juma'a, ya bayar da jerin sharuɗa biyar da za su kawo karshen yaƙin Gaza, inda ɗaya daga ciki ya kasance "karɓe iko da tsaron yankin".
Rahotannin kafafen yaɗa labaran Isra'ila sun ce an kuma amince za a mayar da mazauna Gaza aƙalla miliyan ɗaya zuwa kudancin yankin.
Tsohon ministan noma na Najeriya, Audu Ogbeh ya rasu yana da shekara 78
A wata sanarwa da iyalan mamacin suka fitar, sun ce ya rasu a ranar 9 ga watan Agustan 2025.
''Muna alhinin sanar da rasuwar babanmu kuma kakanmu, Cif Audu Ogbeh.''
Iyalan sun ce ya rasu ne ba tare da wata doguwar jinya, ''amma ya rasu ya bar mana baya mai kyau na tarihin gaskiya da riƙon amana da jajircewa. Duk da muna jimamin rashinsa, amma muna samun sauƙi na ganin irin rayuwar mutanen da ya taɓa da sadaukarwarsa wajen aiki."
Sun ce za su sanar da tsare-tsaren jana'izar mamacin nan da wani lokaci na gaba.
Ogbeh ya fara siyasa ne a shekarar 1979, inda ya zama ɗanmajisar jihar Benue, har ya zama mataimakin shugaban majalisar.
Daga baya ya yi minista sau uku: Sau ɗaya a zamanin Shehu Shagari, da kuma sau biyu a zamanin Muhammadu Buhari.
Haka kuma ya taɓa zama shugaban Jam'iyyar PDP a zamanin Olusegun Obasanjo.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da sallamar masu taimaka masa guda biyu bisa laifuffuka daban-daban, sannan aka wanke guda ɗaya bayan kwamitocin bincike sun gabatar da rahoton binciken su.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Musa Tank Muhammad ya fitar.
Sanarwar ta ce gwamnan ya amince da sallamar Abubakar Umar Sharada, babban mai taimaka wa gwamna kan tattara jama'a bayan kwamitin binciken ya gano shi ne ya kitsa yadda aka yi belin wanda ake zargi da fataucin miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
Haka kuma gwamnan ya amince da sallamar Tasiu Al'amin Roba bayan kwamitin bincike ya tabbatar da hannunsa a kwana da kayan tallafin a rumbun gwamnati na Sharaɗa, wanda kuma tuni aka gabatar da shi a gaban shari'a.
Sai dai kuma gwamnatin ta amince da rahoton kwamitin bincike da ya wanke Musa Ado Tsamiya mai ba gwamnan shawara kan magudanan ruwa.
Gwamna Abba ya nanata cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci rashin amana ba, sannan ya yi kira ga dukkan jami'an gwamnatin da su ƙara ƙaimi wajen riƙe gaskiya da amana.
Shugab Trump ya ce za su haɗu da shugaban Rasha, Vladimir Putin ranar Juma'a mai zuwa a Alaska - inda za su tattauna batun yaƙin Ukraine.
Gwamnatin Rasha ta ce ta zaƙu ranar taron yazo, sannan ta ce itama ta gayyaci shugaban na Amurka wani lokaci na gaba zuwa Rasha.
A lokacin da yake magana da 'yan jarida a Fadarsa ta White House, Mista Trump ya ce tattaunawar Alaska za ta bukaci gwamnatin Moscow da Kyiv su yi musayar yankuna.
Ya ce ina magana ne kan yankunan da ake ta faɗa a kansu tsawon shekara uku da rabi yanzu.
Mutane da dama daga ɓangaren Rasha da Ukraine sun rasa rayukansu, don haka ban yi tunanin akwai wasu hanyoyi na daban na kawo karshen wannan yaƙi ba.
Rahotanni daga yakin ƙaramar hukummar Bukuyum na jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, sun ce ƴanbindiga sun kashe jami’an da ke samar da tsaro goma sha uku (13) a cikin mazabar Adabka, yayin da suke tsaka da gudanar da sintiri.
Harin wanda ƴanbindigar suka kai a jiya Juma’a, sannan suka ƙi bari a shiga domin a kwaso gawarwakin jami’an da suka kashe domin yi musu sutura.
Hamisu A Faru, shi ne ɗan majalisar jihar, mai wakiltar Bukuyum ta Kudu, a zantawarsa da BBC ya buƙaci gwamnatin tarayya ta gaggauta kai musu ɗauki, bisa la’akari da girman matsalar.
Ya ce al'ummar mazaɓarsa na cikin tashin hankali, "musamman ganin waɗanda suke taimaka musu wajen ba su kariya ne aka kashe. Ka ga ke nan me ya rage? ai sai gudun hijira, dama tuni wasu sun gudu zuwa Zuru."
Ɗan majalisar ya ƙara da cewa kashi 70 na mazaɓar Bukuyum ta Kudu, a ƙarƙashin mulkin ƴanbindiga yake.
A ƙarshe ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tura jiragen yaƙi a shiga dazukan, "a yi luguden wuta sansanonn ƴanbindigar."
An gudanar da taron cika shekara 80 da Amurka ta kai harin nukiliya karo na biyu a Nagasaki na Japan.
An soma taron ne da tsit na minti guda, kana tawagen kararawar cocin birnin suka buga a tare a karo na farko tun bayan jefa wannan hari, wanda sako ne aka aike wa duniya na haɗakai domin tabbatar da zaman lafiya.
An kiyasata cewa harin ya yi ajalin mutane aƙalla dubu 74, kuma masu sharhi na cewa ya taka rawa wajen gaggauta kawo karshen yaƙi duniya na biyu.
Galibin waɗanɗa suka tsira daga harin sun yi ta fama da Kansar jini, da sauran wasu cututtuka masu haɗari sakamakon turirin nukiliyar.
Gwamnatin soji a Nijar ta ƙwace katafaren cibiyar mahaƙar zinare ɗaya tilo da ke ƙasar, bayan ta zargi Kamfanin Australia da ke tafiyar da harkokin cibiyar da saɓa dokoki.
Kamfanin McKinel na Australia ke tafiyar da harkokin mahakar tun 2019.
Amma gwamnatin sojin da ta ƙwace mulki shekaru biyu da suka gabata, ta ce McKinel ya gaza wajen tabbatar da shirin zuba jari na dala miliyan 10 yanayin da ya jefa mahaƙar cikin barazanar tattalin arziki.
Ko a watan Yuni wannan shekarar sai da gwamnatin Sojin ƙasar ta ƙwace harkar tafiyar da Uranium na Orano daga hannun Faransa.
Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ne ya fi dacewa da zama ɗan takarar jam'iyyar PDP a babban zaɓen shekarar 2027, inda ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jam'iyyar da su yi duk mai yiwuwa wajen jawo hankalin tsohon shugaban a kan ya koma jam'iyyar ya tsaya takara.
"Ina tunanin ya kamata PDP ta janyo shi: shi ne ya fi dacewa ya mata takara. Duk wani ɗantakara da PDP za ta tsayar, ƴan Najeriya za su zaɓe shi," in ji tsohon gwamnan kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da tashar Channels.
Lamido ya bayyana Jonathan a matsayin wanda ya fahimci ƙasar kasancewar ya yi mulki a baya, kuma ya san yadda zai yi mu'amalanci mulkin ƙasar.
Ya ce ba su da wani ɗantakara daga kudancin Najeriya da ya fi tsohon shugaban ƙasar idan ana batun wanda za su tsayar a zaɓen wanda ke tafe.
"Ni dai a nawa tunanin, duk da cewa ba wai ina raina sauran ƴan jam'iyyarmu ba ne, amma lallai Jonathan ne ya fi dacewa da yin takara a PDP."
Wannan jawabin na Lamido na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da yaɗa raɗe-raɗin cewa Jonathan zi tsaya takara a zaɓen mai zuwa domin fafatawa da Bola Tinubu.
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Asabar daga wannan shafin namu na labaran kai-tsaye daga nan sashen Hausa na BBC.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa irin su Facebook da X da Instagram da ma zaurenmu na Whatsapp domin karanta wasu labaran da ma tafka muhawara.
Ku kasance tare da mu.