PSG za ta cefanar da Donnarumma, Jackson ba ya son barin Ingila

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Paris St-Germain na dakon tayi daga Chelsea da Manchester United ko Inter Milan kan mai tsaron ragarta daga Italiya, Gianluigi Donnarumma mai shekara 26. (ESPN)

Newcastle na fatan inganta tayin fam miliyan 30 da ta gabatar kan ɗan wasan Brentford mai shekara 28 daga DR Congo, Yoane Wissa. (Times - subscription required)

Newcastle ta shiga tattaunawa da PSG kan ɗan wasanta na gaba daga Faransa, Randal Kolo Muani mai shekara 26. (Florian Plettenberg)

Ƙungiyar kuma na nazari kan ɗan wasan Porto da Sifaniya, Samu Aghehowa mai shekara 21. (Athletic - subscription required)

Ɗan wasan gaba a Senegal Nicolas Jackson mai shekara 24, baya son barin ƙungiyoyin Firimiyar Ingila ko da ya bar Chelsea a wannan kaka, kuma ana ganin Newcastle zai je. (Sun)

Jackson zai so ya gwada sa'arsa a wasu ƙungiyoyi bayan barin Chelsea a wannan kaka, yayinda AC Milan da Juventus ke nuna kwaɗayinsu. (Mail)

Manchester United na nazarin sayen ɗan wasan tsakiya da kuma sabon mai tsaron raga, yayinda suke kokarin karkare tattaunawa kan ɗan wasan Slovenia, Benjamin Sesko mai shekara 22 daga RB Leipzig. (Telegraph - subscription required)

Southampton na gudanar da tattaunawa kan yarjejeniyar fam miliyan 50 da ɗan wasan Ingila, Tyler Dibling mai shekara 19, yayinda Everton ke fatan cimma yarjejeniya. (Liverpool Echo)

Ƙungiyar Lille na Faransa na zawarcin ɗan wasan Spurs da Czech, Antonin Kinsky. Ɗan wasan mai shekara 22 na cikin waɗanɗa ake hari musamman a lokacin da ake ganin a iya rasa Lucas Chevalier da zai je PSG. (L'Equipe - in French)

Brentford na son ɗan wasan Bournemouth Dango Ouattara. Ɗan wasan mai shekara 23 daga Burkina Faso sau 32 ya haska a Firimiya a kakar da ta gabata. (Sky Sports)

Ƙungiyar Leeds United na zawarcin ɗan wasan tsakiya a Brighton, Facundo Buonanotte mai shekara 20. Ɗan wasan na Argentina ya kasance wanda ita ma Borussia Dortmund ke hari. (Yorkshire Evening Post)