Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/08/2025.

Taƙaitattu

  • Latsa nan ku shiga tasharmu ta WhatsApp
  • Rundunar sojin Najeriya ta musanta yunƙurin juyin mulki
  • Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 21 daga hannun 'yanbindiga a jihar Kwara
  • Shugaba Tinubu ya koma Najeriya bayan taron Italiya
  • 'An kashe Falasɗinawa 11 a Gaza'
  • Ba zan yi takarar shugaban ƙasa da Tinubu ba - Wike
  • An gano hanyar gwajin cutar kansa a matakin farko

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Rufewa

    A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin namu na labaran kai-tsaye.

    Da fata kun ji daɗin kasancewa tare da mu.

    Sai kuma gobe Litinin.

  2. 'Tattaunawar Trump da Putin babbar nasara ce'

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Galibin kafafen yaɗa labaran duniya na kallon ganawar da aka yi tsakanin Donald Trump da Vladmir Putin a matsayin wata nasara ta diflomasiyya ga shugaban Rasha.

    Sai dai jakadan shugaban Amurka na musamman a Ukraine, Steve Witkoff ya shaida wa kafar yada labarai ta CNN cewa ɓangarorin biyu sun amince da akasarin batutuwa ban da batun miƙa yankuna abin da ya ce zaɓi ne ga Ukraine.

    Ya kuma ce akwai yarjejeniya kan tabbacin tsaro a gaba ga Ukraine yayin da Amurka da Turai za su samar da tsaro makamancin na Nato.

  3. Shugaban Botswana ya buƙaci ƙasashen Afirka su haɗa kai a cinikayya

    Shugaban Botswana ya ce akwai buƙatar ƙasashen Afirka su ƙara azamar yin cinikayya a tsakaninsu domin gujewa matsalar tattalin arziki idan manyan ƙasashen duniya suka bijiro da sabbin manufofi.

    Duma Boko yana magana ne a wani taron shugabanni daga sassan Kudancin Afirka a wani taro a Madagascar.

    Harajin da Amurka ta ƙaƙaba a baya-bayan nan ya shafi kayayyakin da ake fitarwa daga Afirka baya ga batun rage kuɗaɗen tallafi daga ƙasashe masu arziki.

    Mista Boko ya ce yawan dogaro kan kasuwanci da wasu manyan ƙasashen ya sanya ƙasashen Afirka sun zama masu rauni.

  4. Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun yi Allah-wadai domin hukuncin kisa na RSF

    RSF

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama sun yi Allah-wadai da zartar da hukuncin kisa kan wani farar hula da dakarun RSF suka yi a yankin Darfur.

    Wani bidiyo wanda BBC ba ta tantance sahihancinsa ba ya nuna wani ɗan RSF ya titsiye wani mutum yana masa tambayoyi.

    Daga bisani kuma sai aka harbe shi. Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Darfur Network for Human Rights ta ce mutumin ya nuna cewa shi farar hula ne daga wata ƙabila da ba ta Larabawa ba.

    Ana zargin RSF da kashe mutane da dama a shekaru biyun da aka shafe ana yaƙin. Wata kungiyar kare haƙƙin bil adaman kuma ta zargi sojoji da azabtar da ɗaurarru a Khartoum, babban birnin ƙasar.

  5. Tinubu ya taya waɗanda suka yi nasara a zaɓukan cike gurbi murna

    Tinubu

    Asalin hoton, Bayo Onanuga

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya waɗanda suka samu nasara a zaɓukan cike gurbi da aka yi a Najeriya murna, sannan ya yaba da ƙoƙarin INEC wajen gudanar da zaɓukan.

    Tinubu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, inda a ciki ya ce shugaban ya taya dukkan waɗanda suka samu nasara a kujeru 16 da aka fafata a jihohi 12 na ƙasar.

    "Tinubu ya yaba da ƙoƙarin Hukumar INEC wajen gudanar da zaɓen ba tare da hargisti sosai ba."

    Haka kuma ya taya shugaban APC, Farfesa Nentawe Yilwatda murna "bisa gagarumar nasarar da APC ta samu a zaɓukan."

    A zaɓukan da aka gudanar guda 16, APC ta lashe guda 12, APGA biyu, PDP ta ɗaya, sannan NNPP ta lashe ɗaya.

  6. Shugabannin turai za su raka Zelensky ganawa da Trump

    Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabannin ƙasashen turai sun ce za su raka Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky zuwa fadar shugaban Amurka domin ganawa da shugaban ƙasar, Donald Trump.

    A gobe Litinin ne dai Trump zai gana da shugaban Ukraine, Zelensky, zaman da zai zo kwana kaɗan bayan gawanar Trump da Putin a Alaska.

    Ganawar Trump da Putin dai ba ta haifar da wani sakamako mai kyau ba, ganin yadda aka tashi ba tare da cimma wata yarjejeniyar kirki ba.

    An yi tunanin ganawar ce za ta buɗe ƙofar shiga yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Ukraine.

  7. Falasɗinawa na tserewa daga Birnin Gaza saboda hare-haren Isra'ila

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Dubban Falasɗinawa na ciga ba da tserewa daga yankunan Birnin Gaza saboda tsanantar hare-hare da Isra'ila ke kaiwa.

    Kakakin yankin gundumar Zeitoun ya shaida wa BBC cewa yanayi na bala'i da ake ciki bayan shafe kusan mako ana kai hare-hare ta sama babu ƙaƙƙautawa, waɗanda ke rusa gidaje.

    Yanki ne da ke ɗauke da mutane kusan 50,000 kuma ba su samun abinci da ruwan sha.

    Ma'aikatar lafiyar a Gaza ta ce aƙalla mutum 36 aka kashe a hare-haren Isra'ila a jiya Asabar. Sannan akwai mutum 11 da yunwa ta yi ajalinsu.

  8. Zaɓen Kano: NNPP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Ghari da Tsanyawa

    Hashimu Sulaiman Dungurawa

    Asalin hoton, Social Media

    Bayanan hoto, Shugaban jam'iyyar NNPP a Kano Hashimu Dungurawa ya yi taron manema labarai a yau Lahadi

    Jam'iyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya ta yi watsi da sakamakon zaɓen cike gurbi na ɗanmajalisar jiha da aka gudanar a mazaɓar Ghari da Tsanyawa.

    Da yake yi wa manema labarai jawabi a yau Lahadi, shugaban NNPP na Kano Hashim Dungurawa ya zargi abokan hamayya da haɗa kai da jami'an hukumar zaɓe domin "aikata maguɗi".

    Hukumar zaɓe ta ayyana APC mai adawa a jihar ce ta samu nasara a zaɓen da aka gudanar a jiya Asabar, yayin da kuma aka doke ta a ɗaya zaɓen na mazaɓar Bagwai/Shanono - wanda ta nemi a soke ita ma.

    "An gudanar da zaɓe a rumfuna 10 na ƙaramar hukumar ta Ghari lafiya, amma kuma wasu 'yansiyasar APC sun haɗa kai da jami'an hukumar zaɓe wajen sanar da ɗantakarsu a matsayin wanda ya yi nasara," in ji shi.

    Jam'iyyar ta kuma soki hukumar zaɓe saboda "sanar da sakamakon a hedikwatarta ta jiha" maimakon "cibiyar tattara sakamako".

  9. Kalli yadda Sifaniya ke fama da gobarar daji

    Gobarar daji a Sifaniya

    Asalin hoton, EPA

    Dubban ma'aikatan kashe gobara ne ke aikin kashe wutar daji a Sifaniya da Portugal ranar Asabar yayin da kudancin nahiyar Turai ke ci gaba da fama da gobarar daji.

    Hukumar kula da yanayi ta Sifaniya Aemet ta ce yanayin zafi ya zarta 44C a wurare da yawa ranar Asabar.

    Faɗin murabba'in kilomita 1,500 ne gobarar ta mamaye a Sifaniya, kuma tuni mutum bakwai suka mutu.

    Latsa hoton ƙasa ku kalli bidiyo:

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
  10. APC ta lashe zaɓukan cike gurbi a jihar Kaduna

    Uba Sani

    Asalin hoton, KDSG

    Bayanan hoto, Jam'iyyar APC ce ƙarƙashin Gwamna Uba Sani ke mulkin jihar ta Kaduna

    Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta lashe duka zaɓukan cike gurbi uku da aka gudanar a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar, kamar yadda hukumar zaɓe ta Inec ta sanar.

    Sakamakon da aka gudanar a mazaɓar majalisar tarayya ta Chikun/Kajuru ya nuna cewa Felix Bagudu na APC ɗin ya samu ƙuri'a 34,580 kuma ya doke na PDP da ya zo na biyu da ƙuri'a 11,491.

    Kazalika, APC ta yi nasarar cin zaɓen 'yanmajalisar jiha na mazaɓun Zaria/Kewaye da kuma Basawa.

    Baturen zaɓe na Zaria Kewaye Balarabe Abdullahi ya sanar cewa ɗantakarar APC Haruna Ihamo ne ya cinye da ƙuri'a 26,613, yayin da abokin hamayya na SDP Nuhu Sada ya samu 5,721.

    A zaɓen Basawa kuma, baturen zaɓe Farfesa Nasiru Rabiu ya ce APC ta samu ƙuri'a 10,926 kuma ta doke PDP mai 5,499.

    Da ma APC ce ke mulkin jihar ta Kaduna bayan ɗantakararta Uba Sani ya lashe zaɓen gwamna na watan Maris ɗin 2023.

  11. Isra'ilawa na yajin aiki saboda adawa da yaƙin Gaza

    Tel Aviv

    Asalin hoton, EPA

    A yau wasu Isra'ilawa ke yin yajin aikin kwana ɗaya domin nuna adawa da shirin gwamnatin ƙasarsu na ƙwace iko da zirrin Gaza.

    Iyalai da 'yan'uwan mutanen da har yanzu Hamas riƙe da su a Gaza ne ke jagorantar yajin aikin domin nuna wa gwamnati haɗarin da ke tattare da matakinta.

    Ranar Asabar da dare mahaifin ɗaya daga cikin mutanen da ake rike da su a Gaza, Itzik Horn, ya shaida wa dubban masu zanga-zanga a Tel Aviv cewa ya zama tilas su yi wannan bore saboda kare martabar Isra'ila.

    Ya ce yajin aiki ne na farar hula kuma kamfanoni da mutane da dama za su shiga a duk faɗin ƙasar.

  12. Sarkin Zuru Muhammadu Sami ya rasu yana da shekara 81

    Manjo Janar Muhammadu Sami II

    Asalin hoton, Masarautar Zuru

    Sarkin Zuru Manjo Janar Muhammadu Sami II mai ritaya ya rasu yana da shekara 81 da haihuwa.

    Sakataren yaɗa labarai na gwamantin jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa sarkin ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Landan ranar Asabar da dare.

    Sarkin tsohon gwamnan mulkin soja ne na jihar Bauchi lokacin mulkin marigayi Janar Muhammadu Buhari a 1984 zuwa 1985.

    Sanarwar ta ce Gwamnan Kebbi Nasir Idris ya siffanta marigayin a matsayin "uban ƙasa mai cike da hikima kuma wanda ya sanya hidimar al'ummarsa a gaba".

    Sarkin ya rasu ya bar mata huɗu da 'ya'ya bakwai.

  13. APC ta lashe zaɓen cike gurbi a jihar Jigawa

    Jam'iyyar APC

    Asalin hoton, Getty Images

    Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta yi nasarar lashe zaɓen cike gurbi na ɗanmajalisar tarayya da aka gudanar a jiya Asabar, kamar yadda hukumar zaɓe ta bayyana.

    Baturen zaɓe Fafesa Salisu Ibrahim ya ce Rabiu Mukhtar na APC ne ya lashe zaɓen na mazaɓar Garki-Babura da ƙuri'a 38,449.

    A cewar baturen zaɓen, ɗantakarar jam'iyyar PDP Auwalu Isa ne ya zo na biyu bayan ya samu ƙuri'a 13,519.

  14. NNPP da APC sun lashe zaɓukan cike gurbi a jihar Kano

    Zaɓe

    Jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya zaɓen cike gurbi na ɗanmajalisar jiha a mazaɓar Bagwai da Shanono.

    A gefe guda kuma, APC mai adawa ce ta lashe ƙarashen zaɓen ɗanamajlisa da aka yi a ƙaramar hukumar Gari da Tsanyawa.

    Da yake sanar da sakamakon a cikin daren da ya gabata, baturen zaɓe Farfesa Hassan Adamu Shitu ya sanar da Ali Hassan Kiyawa na NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen na Bagwai da Shanono da ƙuri'a 16,198.

    Sakamakon ya nuna cewa ya doke ɗantakatarar APC mai adawa Ahmad Muhammad Kadamu, wanda ya zo na biyu da ƙuri'a 5,347.

    Tun kafin gama kaɗa ƙuri'a APC ta nemi a soke zaɓen saboda abin da ta kira "tayar da hankali da lalata kayayyakin zaɓe".

  15. Yaƙin Ukraine: Shugabannin Turai za su gana bayan Trump ya janye sharuɗɗan tsagaita wuta

    Ukraine

    Asalin hoton, PA Media

    Shugabannin Faransa da Jamus da Birtaniya za su gana ta waya anjima kaɗan bayan Donald Trump ya janye sharuɗɗan tsagaita wuta a Ukraine.

    Sun yi maraba da ƙoƙarin da Mista Trump ke nunawa na kawo ƙarshen yaƙin.

    Amma akwai damuwa da suka nuna cewa goyon bayan wasu abubuwan da Vladimir Putin ya nema a yarjejeniyar zaman lafiyar tamkar Amurka za ta ƙara wa Rasha ƙarfi ne.

    Wakilin BBC a birnin Moscow ya ce magoya bayan gwamnati na ta murna, inda suke ganin Putin ya yi nasara a ganawar Alaska.

    Shugabannin ƙasashen Turai sun mara wa Shugaba Zelensky baya, wanda ya tubure cewa ba zai miƙa yankunansu da Rasha ta mamaye ba ta haramtacciyar hanya.

    Shi ma Zelensky zai gana da Mista Trump gobe Litinin a birnin Washington.

  16. Maraba

    Barkanmu da sake haɗewa a shafin rahotonni kai-tsaye na ranar Lahadi.

    Ni ne Umar Mikail zan kawo labaran daga yanzu zuwa ƙarfe 4:00 na rana.

    Ku biyo mu.