Jam'iyyar gamayyar ƴan'adawa a Najeriya - ADC - ta soki lamirin sauya sheƙar da wasu gwamnonin jihohin ƙasar ke yi daga jam'iyyun adawa zuwa APC mai mulki.
Jam'iyyar ta bayyana haka ne ƴan sa'o'i bayan gwamnoni biyu daga babbar jam'iyyar adawa ta ƙasar PDP sun sauya sheƙa zuwa APC.
Wata sanarwa da ta samu sa hannun sakataren ƴaɗa labaran ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi a yau Laraba ta ce: "Yayin da APC ke ganin kamar ta ƙara samun yawan gwamnoni, gaskiyar abin da ya faru shi ne waɗannan gwamnoni sun yi watsi ne da al'ummarsu domin haɗa kai da jam'iyya mai mulki wajen ƙuntata wa al'umma."
A yau Laraba ne gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya fice daga jam'iyyarsa ta PDP tare da sanar da komawarsa jam'iyyar APC, yayin da a jiya Laraba takwaransa na Enugu, Peter Mbah, ya fice daga PDPn tare da komawa APC.
Hakan ya ƙara zabtare yawan ƙusoshin siyasa da jam'iyyun adawa na Najeriya ke da su yayin da babban zaɓen ƙasar na 2027 ke ƙaratowa.
A Najeriya ana kallon gwamnoni a matsayin masu matuƙar tasiri wajen nasarar jam'iyyu a matakin jihohi da kuma tarayya a lokacin zaɓuka.
Sai dai tun bayan babban zaɓen Najeriya na 2023, ƙarfin ƴan hamayya a Najeriya na raguwa ta hanyar sauya sheƙar ƴaƴansu zuwa jam'iyya mai mulki.
Jam'iyyun adawar a lokuta da dama sun zargi APC mai mulki da yin amfani da tsoratarwa ko barazana wajen tursasa wa ƴan'adawa komawa cikinta.
Haka nan sukan zarge ta da shafa wa ƴan adawar zuma a baki.
Sai dai jam'iyyar ta APC ta musanta duk waɗannan zarge-zarge, tana cewa tsari mai kyawu na gwamnati mai ci ne ke sanya ƴan adawar sauya sheƙa zuwa cikinta.
Haka nan a cikin sanarwar ADCn ta yau Laraba, jam'iyyar ta zargi APC da ci gaba da yunƙurin mayar da Najeriya ƙasa mai bin tsarin jam'iyya ɗaya.
"Komawar gwamnonin Enugu da Bayelsa zuwa jam'iyyar APC mai mulki ya gaskata gargaɗin da jam'iyyar ADC ta daɗe tana yi na cewa Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin mayar da Najeriya ƙasa mai amfani da tsarin jam'iyya ɗaya," in ji sanarwar.