Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 15/10/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 15/10/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Tarayyar Afirka ta dakatar da Madagascar bayan juyin mulki

    Sojojin Madagascar

    Asalin hoton, Getty Images

    Tarayyar Afirka (AU) ta dakatar da ƙasar Madagascar daga ƙungiyar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar Talata.

    Dakatarwar ta fara aiki ne nan take.

    Hakan na zuwa ne bayan majalisar dokokin ƙasar ta tsige shugaban ƙasar Andry Rajoelina bayan ya tsere daga ƙasar sanadiyyar ƙazancewar zanga-zanga.

    Ba da daɗewa ba ne wata tawagar sojoji ta karɓe iko da ƙasar, inda ta yi alƙawarin gudanar da zaɓe cikin shekara biyu.

    Zanga-zangar ce rikicin siyasa mafi muni da ya dabaibaye ƙasar cikin shekarun baya-bayan nan, bayan kwashe makonni ana zanga-zanga kan matsanancin ƙarancin lantarki da ruwa, inda masu zanga-zangar suka buƙaci shugaba Rajoelina ya sauka daga mulki.

  2. Gwamnonin da ke sauya sheƙa zuwa APC sun ci amanar talakawa - ADC

    Tambarin jam'iyyar ADC

    Asalin hoton, X/ADC Vanguards

    Bayanan hoto, Tambarin jam'iyyar ADC

    Jam'iyyar gamayyar ƴan'adawa a Najeriya - ADC - ta soki lamirin sauya sheƙar da wasu gwamnonin jihohin ƙasar ke yi daga jam'iyyun adawa zuwa APC mai mulki.

    Jam'iyyar ta bayyana haka ne ƴan sa'o'i bayan gwamnoni biyu daga babbar jam'iyyar adawa ta ƙasar PDP sun sauya sheƙa zuwa APC.

    Wata sanarwa da ta samu sa hannun sakataren ƴaɗa labaran ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi a yau Laraba ta ce: "Yayin da APC ke ganin kamar ta ƙara samun yawan gwamnoni, gaskiyar abin da ya faru shi ne waɗannan gwamnoni sun yi watsi ne da al'ummarsu domin haɗa kai da jam'iyya mai mulki wajen ƙuntata wa al'umma."

    A yau Laraba ne gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya fice daga jam'iyyarsa ta PDP tare da sanar da komawarsa jam'iyyar APC, yayin da a jiya Laraba takwaransa na Enugu, Peter Mbah, ya fice daga PDPn tare da komawa APC.

    Hakan ya ƙara zabtare yawan ƙusoshin siyasa da jam'iyyun adawa na Najeriya ke da su yayin da babban zaɓen ƙasar na 2027 ke ƙaratowa.

    A Najeriya ana kallon gwamnoni a matsayin masu matuƙar tasiri wajen nasarar jam'iyyu a matakin jihohi da kuma tarayya a lokacin zaɓuka.

    Sai dai tun bayan babban zaɓen Najeriya na 2023, ƙarfin ƴan hamayya a Najeriya na raguwa ta hanyar sauya sheƙar ƴaƴansu zuwa jam'iyya mai mulki.

    Jam'iyyun adawar a lokuta da dama sun zargi APC mai mulki da yin amfani da tsoratarwa ko barazana wajen tursasa wa ƴan'adawa komawa cikinta.

    Haka nan sukan zarge ta da shafa wa ƴan adawar zuma a baki.

    Sai dai jam'iyyar ta APC ta musanta duk waɗannan zarge-zarge, tana cewa tsari mai kyawu na gwamnati mai ci ne ke sanya ƴan adawar sauya sheƙa zuwa cikinta.

    Haka nan a cikin sanarwar ADCn ta yau Laraba, jam'iyyar ta zargi APC da ci gaba da yunƙurin mayar da Najeriya ƙasa mai bin tsarin jam'iyya ɗaya.

    "Komawar gwamnonin Enugu da Bayelsa zuwa jam'iyyar APC mai mulki ya gaskata gargaɗin da jam'iyyar ADC ta daɗe tana yi na cewa Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin mayar da Najeriya ƙasa mai amfani da tsarin jam'iyya ɗaya," in ji sanarwar.

  3. Hauhawar farashi ta ragu zuwa kashi 18 a watan Satumba - NBS

    kayan kasuwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS ta ce an samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar zuwa kashi 18 cikin 100 a watan Satumban da ya gabata.

    Cikin rahoton wata-wata da hukumar ke fitarwa ta ce an samu raguwar hauhawar farashin da kashi 2.1 a watan daga kashi 20.12 cikin 100 da yake a watan Agustan da ya gabace shi.

    Rahoton hukumar ya nuna saukar farashin abinci da kashe 2.34 cikin 100 a watan na Satumba, inda ya koma kashi 19.53 maimakon kashi 21.87 da yake a watan Agusta.

  4. Raguwar samun kuɗi ya tilasta mana rage tallafin da muke bayarwa - WFP

    wasu jami'ain WFI na duba wasu buhunan abinci

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Samar da Abinci ta Duniya ta ce ƙarancin kuɗi ya tilasta mata rage tallafin abinci da take bai wa mutane sama da miliyan 13.

    Lamarin zai iya mayar da hannun agogo baya kan ayyukan da aka shafe shekaru da dama ana yi domin kawo ƙarshen yunwa a duniya.

    Daraktar hukumar ta WFP, Cindy McCain, ta ce raguwar kuɗin na nufin ƙananan yara ba za su samu abinci ba ko kuma iyaye mata ba za su samu abincin da za su ci ba.

    Hukumar ta MDD ta ce tana sa ran samun tallafi kasa da kashi 40 cikin 100 a wannan shekara, kuma ta yi gargaɗiin cewa ayyuka shida masu muhimanci za su fuskanci tsaiko.

    Kashi ɗaya bisa huɗu na waɗanda aka bai wa tallafin a wannan watan da muke ciki a Jamhuriyar Dimokardiyyar Kongo da Sudan suke, yayinda za a rage wa Sudan ta Kudu yawan abinci da take samu saboda abincin da aka adana ya ƙare

  5. An ayyana makokin kwana bakwai a Kenya bayan rasuwar Odinga

    Kenya ta ayyana zaman makoki na kwanaki bakwai domin nuna alhihin mutuwar tsohon firaministan ƙasar.

    Raila Odinga, wanda ya mutu yana da shekara tamanin a duniya.

    Shugaba William Ruto ya bayyana Odinga a matsayin wani jigo a harkar dimokuradiyyar ƙasar kuma mai gwagwamayar ƙwato 'yanci da ba shi da tsoro.

    Mista Odinga ya tsaya takarar shugaban ƙasar Kenya har sau biyar amma duka bai samu nasara ba.

    Zanga-zangar da aka yi bayan zaɓen shekarar 2007 da aka ta yi taƙaddama a kai ta yi sanadin mutuwar mutum fiye da 1,000 a rikicin siyasa mafi muni da aka taɓa gani a ƙasar tun bayan da ta samu yancin kai

  6. Gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri ya fice daga PDP

    Douye Diri

    Asalin hoton, Douye Diri/X

    Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya fice daga jam'iyyarsa ta PDP.

    Diri ya bayyana haka ne ranar Laraba a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Yenagoa lokacin taron majalisar zartarwarsa.

    Cikin wata sanarwar ta sakataren yada labaran gwamnan, Daniel Alabrah ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce gwamnan ya fice daga PDP ne tare da ƴan majalisar dokokin jihar 19, ciki har da kakakin majalisar.

    Kawo yanzu dai Gwamnan bai bayyana jam'iyyar da ya koma ba.

    Ficewar gwamnan na zuwa ne kwana guda bayan da takwaransa na Enugu, Peter Mbah, ya fice daga PDPn tare da komawa APC.

    A wannan shekarar kaɗai babban jam'iyyar hamayyyar ta PDP ta rasa gwamnoni uku, wani abu da masana ke kallo a matsayin babbar barazana ga jam'iyyar.

  7. Gwamnan Edo ya gargaɗi kwamishinoninsa kan rashin saka hular Tinubu

    Monday Okpebholo da wasu daga cikin muƙarrabansa

    Asalin hoton, Monday Okpebholo/X

    Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya gargaɗi kwamishinoninsa game da rashin saka irin hular da shugaban Najeriya Bola Tinubu ke sakawa.

    Mista Okpebholo ya bayyana haka ne a lokacin rantsar da wasu sabbin kwamishohinsa.

    Yayin sa yake jawabi a wurin rantsar da kwamishinonin, Gwamna Okpebholo - wanda ke sanye da irin hular Tinubun - ya ce ba zai yafewa duk kwamishinan da ya je ofis ba tare da hular Tinubu ba.

    ''Kun ga wannan hular, ba zan yafewa duk wanda ya zo aiki ba tare da ita a kansa ba'', in ji shi.

    Ya ƙara da cewa ''indai ba kwat za ta saka ba, matsawar tufafin da za ka saka irin na al'ada ne da ke buƙatar sanya hula, to dole ku saka irinta''.

    Gwamnan ya ce duk wanda ya saɓa dokar to zai koma gida.

  8. Al-Sharaa ya isa Moscow don ganawa da Putin ''da nufin karɓo Assad''

    Shugaban Syria, Ahmed al-Sharaa ya isa Moscow domin ganawa da Shugaba Putin na Rasha.

    Jami'ai sun ce al-Sharaa ya je Rasha ne da nufin gabatar da buƙatar karɓo tsohon shugaban ƙasar Syria, Bashar al-Assad, da ya hamɓarar da gwamnatinsa watanni 10 da suka gabata.

    Jami'an sun ci gaba da cewa al-Sharaa zai so karɓa Assad ne domin mayar da shi Syria don ya fuskanci hukunci kan laifukan yaƙi da ake tuhumarsa da su.

    Fadar gwamnatin Rasha ta ce shugaba Putin zai tattauna da al-Sharaa klan makomar sansanonin sojojin Rasha da ke ƙasar.

  9. 'Ɗaya daga cikin gawarwakin da Hamas ta mayar wa Isra'ila ba nata ba ne'

    Motar Red Cross

    Asalin hoton, Reuters

    Sojojin Isra'ila sun ce gwajin da aka yi wa gawarwakin Isra'ilawa huɗu da Hamas ta mayar jiya, ya nuna cewa ɗaya daga cikinsu ba ya cikin waɗanda Hamas ɗin ta yi garkuwa da su.

    Rundunar IDF ta sake jaddada kira ga Hamas ta yi duk mai yiwuwa domin mayar da duka gawarwakin mutanen da ta yi garkuwa da su a harin 7 ga watan Oktoban 2023.

    A ranar Talata ne aka mayar da gawarwakin mutum huɗu, yayin da ake sa ran mayar da huɗu a yau.

    Aikin mayar da gawarwakin daga Gaza da aka ruguza na da matuƙar wahala, inda aka yi amanna cewa wasu gawarwakin na ƙarƙashin ɓaraguzai.

    Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce za a buɗe muhimmiyar mashigar Gaza a yau domin shigar da agaji zuwa Gaza, idan aka mayar da ƙarin gawarwakin.

  10. Kano ta zama ta huɗu a kula da sauyin yanayi a Najeriya

    ..

    Asalin hoton, Hashim/Facebook

    Jihar Kano ta ɗauki matsayi na 4 a fannin samar da hanyoyin daƙile illolin sauyin yanayi a jadawalin jihohi masu kula da fannin na sauyin yanayi na 2025.

    A shekarar da ta gabata dai jihar Kano ce ta zo ta 35, inda jihar Zamfara ke biye mata.

    Sabon matsayin da ƙungiyar da ke kula da ingancin yanayin duniya ta Society for Planet and Prosperity, SPP bisa haɗin gwiwar jami'ar Bristol da ke Burtaniya suka ayyana, ya fayyace irin rawar da jihar ta Kano take takawa dangane da abin da ya shafi gudanarwa a fannin sauyin yanayi da ingancin muhalli.

    Kwamishinan Muhalli na jihar ta Kano, Dakta Dahiru hashim ya alaƙanta nasarar da irin ƙudirin gwamnatin jihar da take da shi kan muhalli da sauyin yanayi.

    Hashim ya lissafa matakan da ya ce su ne suka kai su ga nasarar da suka haɗa da tsare-tsaren gwamnatin jihar Kano kan sauyin yanayi da mayar da hankali wajen amfani da makamashi maras gurɓata muhalli da shirin gwamnati na sake ƙawata birane ta hanyar dasa itatuwa da kuma katafaren shirin gwamnati na dashen bishiyoyi a faɗin jihar.

  11. Ina Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara yake?

    ..

    Asalin hoton, Sheikh Abduljabbar

    Ƴan uwa da magoya bayan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wanda ke tsare a gidan yarin Kurmawa na Kano bisa tuhumar "ɓatanci" ga Annabi Muhammadu SAW, tuhumar da Malamin ya musanta kuma yake ƙoƙarin ɗaukaka ƙara, sun shiga ruɗani saboda rashin sanin halin da malamin ke ciki a yanzu haka.

    Mabiya da iyalan Malamin dai sun shiga ruɗun a ranar Talata bayan da suka kai masa ziyara a gidan yarin amma sai suka tarar ba ya nan kuma ba su samu wata gamsasshiyar amsa ba daga jami'an gidan kason.

    A ranar 15 ga watan Disambar 2022 ne dai wata babbar Kotun Shari'ar Musulunci ta Jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi tuhume-tuhumen da aka yi masa.

  12. Gwamnan Nasarawa ya nuna damuwa kan ɓullar sabuwar ƙungiyar ƴanbindiga ta Wulowulo

    Gwamnan Nasarawa

    Asalin hoton, Nasarawa State Govt

    Gwamman jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana damuwarsa kan ɓullar wani reshe na ƙungiyar Boko Haram a yankin arewa ta tsakiyar Najeriya.

    Abdullahi Sule ya bayyana haka ne a lokacin zaman majalisar tsaron jihar da ya jagoranta, inda ya koka kan barazanar tsaro musamman daga jihohin makwabta, kamar yadda gidan talbinin na Channels ya ruwaito.

    “Kamar yadda kuka sani, sabuwar ƙungiyar Wulowulo, wadda ta ɓalle daga Boko Haram ta fara ɓulla a yankin arewa ta tsakiya, muna buƙatar ɗaukar tsauraran matakai'', in ji shi.

    “Dole mu ɗauki matakai domin kare jiharmu daga samun shigowar wannan ƙungiyar'', kamar yadda ya bayyana a lokacin zaman majalisar tsaron jihar.

    Gwamnan ya buƙaci kwamishinan ƴansandan jihar da kuma darakta hukumar tsaro ta DSS su zurfafa bincike game da lamarin.

  13. Tinubu ya buƙaci majalisar dattawa ta amince da naɗin sabon shugaban INEC

    Shugaba Tinubu

    Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya aike wa majalisar dattawan ƙasar wasiƙar neman tantance tare da tabbatar da naɗin Farfesa Joash Amupitan (SAN) a matsayin sabon shugaban hukumar zaɓen ƙasar, INEC.

    Shugaban Majalisar Dattawan ƙasar, Sanata Godswill Akapbio ne ya bayyana haka, yayin da ya karanto wasiƙar Shugaba Tinubu a zaman majalisar na ranar Talata.

    Matakin na zuwa ne bayan amincewar majalisar magabatan ƙasar a makon da ya gabata.

    Shugaba Tinubu ya buƙaci ƴanmajalisar su bai wa tantancewar ''muhimmancin gaske''.

    Tinubu ya naɗa Farfesa Amupitan ne bayan ƙarewar wa'adin tsohon shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu.

  14. Gwamnatin Najeriya ta cire darasin Lissafi cikin sharuɗan samun gurbin karatun Jami'a ga wasu ɗaliban

    wata mata

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta cire wajibcin cin darasin lissafi cikin sharuɗaɗan samun gurbin karatu a jami'a ga ɗaliban da za su karanci kwasa-kwasan da na na kimiyya ba.

    Cikin wata sanarwar da ma'aikatar ilimin ƙasar ta fitar ta ce daga yanzu ɗaliban da ke son karanta kwasa-kwasan da ba su da kusanci da kimiyya ko fasaha ba, cin darasin lissafi a sakandire bai zame musu wajibi ba.

    Kwasa-kwasan sun haɗa da nazarin ilimin harsuna da zane-zane da nazarin wasannin kwaikwayo da kaɗe-kaɗe, amma dole sai sun ci darasin Ingilishi a sakandire.

    Sai dai sanarwar ta jaddada wajibcin darasin lissafin ga sauran kwasa-kwasan da suka shafi kimiyya da fasaha da nazarin zamantakewa.

    Ma'aikatar ta ce ta ɗauki matakin ne domin ɗalibai da dama su riƙa samun damar shiga jami'a.

    ''Matakin zai samar da ƙarin guraben karatu 300,000 a kowace shekara, domin rage yawan ɗaliban da ba sa samun guraben karatu, tare da ƙarfafa sana'o'in dogaro da kai'', in ji sanarwar.

  15. Tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga ya rasu

    Raila Odinga

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon Firaminsitan Kenyan, Raila Odinga ya mutu a Indiya.

    Wata majiya daga iyalansa ta shaida wa BBC cewa marigayin mai shekara 80 ya rasu ne bayan yi masa aiki a wani asibitin Indiya.

    A ƴan makaonnin nan an yi ta yaɗa jita-jita game da rashin lafiyarsa, duk da cewa iyalansa da abokan siyasarsa sun riƙa yin watsi da rahotonnin da ke nuna cewa yana fama da matsananciyar jinya.

    Odinga ya kasance jigo a siyasar Kenya, inda ya sau biyar yana tsayawa takarar shugaban ƙasar, sai dai bai taɓa samun nasara ba, kodayake ya riƙa watsi da sakamakon, ya ma taɓa cewa ƙwace masa zaɓen ake yi.

  16. 'Kayan abinci na ci gaba da ƙarewa a El Fasher'

    wasu mata

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafofin watsa labaran cikin gida a Sudan sun ba da rahoton cewa kayan abinci na ci gaba da ƙarewa a El Fasher, tun bayan da dakarun RSF sun yi wa birnin ƙawanya tare da tsananta kai hare-hare.

    Rahotanni sun ce ƙungiyoyin ba da agaji da ke taimaka wa mutane da abinci sun fice a ƙarshen mako, kana kasuwanni sun zama tamkar kufai.

    Masu aiko da rahotanni sun ce ba za a iya shigar da kayayyakin jin kai a halin da ake ciki ba, duk da kasancewa birnin a matsayin tunga ta ƙarshe ta dakarun gwamnati a yankin.

    Duk tsawon wannan lokaci luguden wutar da RSF ke yi na ci gaba da tsananta a yayin da ta ba da himma wajen ganin ta kwace iko da birnin da shi kadai ne ba ya karkashin ikonta a yammacin Sudan.

  17. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba, ''ta bawa ranar samu'' kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kada ku manta da shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.

    Ku biyo mu....