Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/12/2025.

Wanna shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/12/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Ya za a kwatanta ƙarfin sojin Najeriya da na ƙasashen Afirka ta yamma?

    Tun bayan ɗauki da sojojin saman Najeriya suka kai ƙasar Benin inda suka taimaka wajen daƙile yunƙurin juyin mulki da sojoji suka so yi, da kuma amincewar da majalisar dokoki ta yi na buƙatar Bola Tinubu na aikewa da rundunar soji zuwa Benin ɗin domin wanzar da zaman lafiya, ƴan Najeriya da ma Afirka sanin irin karfin da Najeriya ke da shi idan aka kwatantan da sauran ƙasashen Sahel.

    Alƙaluman World Factbook sun nuna cewa dakarun Najeriyar 180 na Sudan da Sudan ta Kudu, inda ta aike da dakaru 200 zuwa Gambia a ƙarƙashin ƙungiyar Ecowas sai kuma 150 da ke Guinea-Bissau nan ma a ƙarƙashin ƙungiyar Ecowas.

    Wannan ne ya sa ƴan Najeriya da ma Afirka ke tambayar shin Najeriyar ce ta fi kowace ƙasa ƙarfin soji? Yaya za a kwatanta ƙarfin sojin na Najeriya da sauran ƙasashen Afirka ta yamma?

  2. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya a jiya na labaran kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a cikin Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.