Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

  • 'Ƴan Najeriya miliyan 30 za su fuskanci matsalar yunwa a 2026'
  • Kotun ƙoli ta yi watsi da tuhumar da ake wa Al-Mustapha kan kisan Kudirat Abiola
  • Ba za a bai wa waɗanda ba ƴan APC ba muƙamin siyasa – Shugaban APC
  • Latsa nan domin shiga zaurenmu na Whattsapp
  • Mazauna Kurmin Wali sun zargi hukumomi da rufa-rufa bayan sace jama'a
  • An samu wata ƴar jarida da laifin tallafawa ayyukan ta'addanci a Philippines
  • An kashe ƴan jarida uku a wani harin da Isra'ila ta kai a Gaza
  • 'Ba zan huta ba, sai mun ceto mutanenmu da aka sace'

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Ibrahim Yusuf Mohammed, Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. An kashe ƴan jarida uku a wani harin da Isra'ila ta kai a Gaza

    Ma’aikatan bayar da agajin gaggawa sun ce an kashe falasɗinawa ƴan jarida guda uku a wani harin da Isra'ila ta kai a tsakiyar Gaza.

    Hukumar kare haƙƙin farar hula a Gaza ta ce an kashe ƴan jaridan ne bayan an kai wa motarsu hari a yankin al-Zahra inda ta bayyana sunayensu da Mohammed Salah Qashta da Anas Ghneim da kuma Abdul Raouf Shaat. An fahimci cewa suna aiki ne da wata ƙungiyar agaji ta Masar.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari kan wasu da ake zargi da yin amfani da wani jirgi mara matuki da ke da alaka da Hamas... ta hanyar da ke barazana ga dakarunta. Inda ta ƙara da cewa tana kan gudanar da bincike kan lamarin.

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta sanar da cewa, an kashe wasu mutane takwas, biyu daga cikinsu yara kanana da makaman atilare na Isra'ila a Gaza a ranar Laraba.

    Likitoci sun ce mutane uku ciki har da wani yaro ɗan shekara 10, sun mutu sakamakon Harbin da tankokin yaƙin Isra'ila suka yi a wani wuri a tsakiyar Gaza, kuma wani yaro dan shekara 13 da wata mata sun mutu sakamakon harbin da sojojin Isra'ila suka yi a kudancin yankin Khan Younis, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Aƙalla Falasdinawa 466 ne aka kashe a Gaza tun bayan da aka fara tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas a ranar 10 ga Oktoba, a cewar ma'aikatar lafiya.

  2. 'Ba zan huta ba, sai mun ceto mutanenmu da aka sace'

    Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya dace domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Kurmin Wali da ke ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar.

    Gwamnan ya ce yana bibiyar ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi game da batun, kuma ba zai gajiya ba har sai an yi nasarar ceto dukkan mutanen da aka sace.

    A ranar Lahadi wasu mahara suka shiga ƙauyen Kurmin Wali inda rahotanni ke cewa sun yi garkuwa da mutane fiye da 170 tare da jefa al'ummar yankin cikin ruɗani.

    Da farko ƴansanda da jami'an gwamnatin jihar Kaduna sun musanta faruwar lamarin amma daga baya suka fitar da sanarwar da ke tabbatar da shi, duk da cewa kawo yanzu babu haƙiƙanin bayani kan ko mutane nawa ne aka sace a ƙauyen.

    Amma a hirar shi da BBC a Kaduna, gwamna Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta karkata ne ga aikin ceto mutanen, don haka sanin yawan su wani abu ne da zai iya zuwa daga baya domin a cewarsa masu ''siyasantar'' da batun tsaro ne ke mayar da hankali kan yawan mutanen da aka sace.

  3. Trump ya ce an tattauna tsarin yarjejeniya kan Greenland bayan ya janye barazanar ƙaƙaba haraji

    Shugaba Donald Trump ya ce Amurka na nazarin yiwuwar ƙulla yarjejeniya kan Greenland bayan tattaunawa da ƙungiyar tsaro ta NATO yayin da ya janye barazanar sanya haraji kan ƙawayensa na Turai da suka yi adawa da shirin Amurka na mallakar tsibirin.

    A saƙonnin da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Trump bai bayar da cikakkun bayanai game da tattaunawar tsakaninsa da NATO ba, amma ɓangarorin biyu sun bayyana tattaunawar a matsayin "mai matuƙar tasiri".

    Sai dai babu wani abin da ya yi nuni da cimma yarjejeniyar da za ta biya buƙatar Trump na "mallakar" Greenland, burin da ya sake jaddadawa a taron tattalin arzikin duniya a Switzerland, yayin da ya yi watsi da batun amfani da ƙarfin soja.

    Bayan ganawa da Sakatare Janar na NATO Mark Rutte a Switzerland, Trump ya shaidawa manema labarai cewa akwai yiwuwar yarjejeniyar za ta iya ƙunsar batun mallakar ma'adinan da ke tsibirin.

  4. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara kan labaran da mu ke wallafawa.