Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 9/08/2026

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi 9 ga watan Agustan 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. Rundunar sojin ruwan Najeriya ta kama man fetur da aka tace ba bisa ƙa’ida ba

    Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ƙara tsaurara matakanta na yaƙi da satar ɗanyen mai da safarar mai ba bisa ka’ida ba, inda ta tarwatsa wata sabuwar matatar mai ta haramtacciyar hanya tare da kama wani jirgin ruwa mai dauke da kusan lita 17,000 na man fetur da ake zargin an tace ba bisa ka’ida ba a yankin Neja Delta.

    Jaridar The Guardian ta ruwaito a ranar 8 ga watan Agusta cewa rundunar ta ce a wani samame daban a jihar Rivers da ke kudancin Najeriya, ta kuma kama kusan lita 24,000 na wani abu da ake zargin ɗanyen mai ne da aka sata, tare da tarwatsa wasu wurare da ake zargin an kafa domin satar ɗanyen mai.

    Kakakin rundunar, Kyaftin Abiodun Folorunsho, ya ce kamen ya nuna ƙudurin rundunar na dakile hanyoyin safarar man fetur ba bisa ka’ida ba, hana masu yin zagon ƙasa ga tattalin arzikin ƙasa samun damar gudanar da ayyukansu, da kuma kare muhimman ababen more rayuwa na man fetur da iskar gas daga amfani da su wajen aikata laifuka.

    Ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da samame bisa bayanan sirri domin tarwatsa wuraren tace mai ba bisa ka’ida ba, yaƙi da satar ɗanyen mai da kuma safarar mai ba bisa ƙa’ida ba, kare muhallin teku da kuma kare muradun tattalin arzikin Najeriya.

    Rundunar ta ce ayyukan nata sun fi mayar da hankali ne kan muhimman wuraren da ake aikata laifuka a yankin Neja Delta, ciki har da jihohin Rivers da Delta.

    Najeriya na asarar miliyoyin gangar ɗanyen mai a kowace shekara sakamakon yawaitar satar mai, huda bututun mai ba bisa ka’ida ba da kuma lalata ababen more rayuwa a yankin Neja Delta.

  2. Netanyahu ya yi watsi da shirin zaman lafiya a Gaza

    Firaministan Isra’ila ya yi watsi da wani shirin zaman lafiya na Amurka kan Gaza, wanda Shugaba Donald Trump ya yaba da shi.

    Benjamin Netanyahu ya ce Isra’ila ta ƙi amincewa da takardar mai ɗauke da maki 15, wadda Hamas ta amince da cewa za ta kwance makamanta a matakai, bisa sharadin cewa Isra’ila za ta janye dakarunta daga yankin Falasɗinu a lokaci guda.

    Ya ce rundunar sojin Isra’ila (IDF) ba za ta janye daga Gaza ba har sai Hamas ta miƙa dukkan makamanta.

    Wani babban jami’in Hamas ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ƙungiyar har yanzu tana nan kan matsayinta na bin shirin zaman lafiyar da aka cimma a birnin Alkahira a watan da ya gabata.

    Isra’ila dai ta ci gaba da kai hare-hare ta sama kan Gaza tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta farko a yankin a watan Oktoban bara.

  3. Abianosa de Muñoz: Ƙauye a ƙasar Spain da za a yi dare biyu a rana ɗaya

    Ƙauyen Abianosa de Muñoz na ƙasar Spain na shirin fuskantar wani dare na musamman, duk da cewa a yanzu kusan babu mazauna a ƙauyen, babu gidajen cin abinci, kuma ba kasafai baƙi ke ziyartarsa ba.

    Akwai ƙauyuka da ke cike da natsuwa da kwanciyar hankali, kuma wannan ƙaramin ƙauyen na Abianosa de Muñoz na cikinsu, kuma yana lardin Burgos a arewacin ƙasar Spain ne.

  4. Muna tattaunawa da Oman game da mashigar Hormuz - Iran

    Iran ta ce tattaunawar da take yi da Oman kan sababbin tsare-tsaren gudanar da zirga-zirga a Mashigar Hormuz na tafiya yadda ya kamata.

    Sai dai babban jami'in tsaro na Tehran, Mohammad Bagher Zolghadr, ya yi gargaɗin cewa ba za a sake buɗe mashigar ruwan ba har sai Amurka ta amince da wasu sharuɗɗa guda shida.

    Daga cikin sharuɗɗan akwai sassauta takunkumin tattalin arziki da aka ƙaƙaba wa Iran, da biyan diyya kan asarar yaƙi, da kuma kawo ƙarshen toshe tashoshin jiragen ruwan ƙasar da Amurka ke yi.

    Wakilin BBC ya ce abin da muka ji daga shugaban tsaron shi ne sai an cimma wadannan bukata idan har za a sake bude Mashigar Hormuz Tun da farko, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya ce Iran da Oman sun yi kusa sosai da cimma yarjejeniya kan wata sabuwar hanya ta zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar ta Hormuz.

    A halin da ake ciki kuma, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta ce Iran ta kai harin makami mai linzami kan ɗaya daga cikin jiragen ta na ruwa na dakon mai.

  5. Gwamnan Kano ya buƙaci waɗanda suka ci moriyar auren gata su zauna lafiya

    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci ma’aurata 1,500 da suka amfana da shirin aure gata na jihar da su zauna lafiya da juna bisa haƙuri da fahimtar juna.

    Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin da yake jawabi ga ma’auratan, inda ya tunatar da su cewa aure ibada ne, don haka ya kamata su gudanar da shi bisa koyarwar Alƙur’ani da Sunnar Annabi Muhammad (SAW).

    Ya kuma buƙace su da su yi adalci da mutunta juna tare da tabbatar da zaman lafiya a gidajensu, sannan su yi amfani da abubuwan da suka koya yayin shawarwarin da aka ba su kafin aure.

    Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah Ya albarkaci aurensu, Ya kuma ba su ’ya’ya nagari wadanda za su amfani iyalansu, al’umma da bil’adama.

  6. Hukumar NDLEA ta gargadi iyaye kan biskit da alewa da ake sanya miyagun ƙwayoyi

    Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta gargadi iyaye da su sanya ido sosai kan yadda ƴaƴansu ke sha’awar cin biskit da alewa mai laushi, tana mai cewa wasu daga cikin kayayyakin maƙulahen na iya ƙunsar miyagun ƙwayoyi da ake safararsu zuwa ƙasar.

    TVC News ta ruwaito a ranar 9 ga watan Agusta cewa daraktan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana haka ne a ranar 8 ga watan Agusta cewa samamen baya-bayan nan da hukumar ta gudanar ya bankaɗo ƙoƙarin masu safarar miyagun ƙwayoyi na ɓoye haramtattun abubuwa cikin kayan zaƙi na yau da kullum.

    Babafemi ya ce iyaye su ƙara kula idan suka lura ’ya’yansu da matasa na yawan sha’awar biskit da alewa, domin akwai yiwuwar kayayyakin suna ɗauke da wasu abubuwa da suka wuce abin da ake zato.

    Gargadin ya biyo bayan ƙwace kwantena biyu masu tsawon ƙafa 40 da hukumar ta yi a Legas, inda aka gano ɗimbin kayayyakin da aka haɗa da tabar wiwi, waɗanda aka ɓoye a cikin kayayyakin shigo da kaya na halal, ciki har da motocin da aka yi amfani da su, janareto, batura da yadudduka.

    Kayan da aka ƙwace sun haɗa da dubban fakitin alewa mai laushi da aka sanya tabar wiwi, da kuma wasu nau’ikan biskit da ke ɗauke da tabar wiwi.

  7. 'Ɗan shekara 14 ya kashe kakanninsa bayan kallon bidiyon harbe-harbe a intanet'

    Wani matashi mai shekara 14 a Thailand ya kashe kakanninsa biyu, sannan ya yi harbin kan mai uwa da wani a makarantarsa da ke kusa da birnin Bangkok a ranar Juma’a, bayan da ya kalli wasu bidiyoyin rigingimu a intanet, kamar yadda masu binciken ‘yan sanda suka bayyana.

    Matashin ya kashe malamai biyar kafin daga bisani ya kashe kansa. Sannan wata yarinya mai shekaru 12 da aka harba a kai ta mutu daga baya a asibiti.

    Ƴansandan Thailand sun ce matashin ya nuna sha’awar mallakar bindigogi tsawon shekara daya ko biyu da suka gabata, kuma ya yi amfani da kafafen sada zumunta wajen koyon yadda ake amfani da bindigar hannu.

    Ya kasance yana zaune tare da kakanninsa tun bayan rabuwar iyayensa.

    ‘Yan sanda sun ce matashin ya fuskanci matsin lamba a makaranta, yayin da kakarsa kuma ta kasance mai tsauri wajen bibiyar karatunsa.

  8. An ayyana dokar ta-ɓaci kan gobarar daji a yammacin Canada

    An ayyana dokar ta-baci a lardin British Columbia da ke yammacin Kanada, bayan gobarar daji da ta gagara kashewa ta tilasta wa dubban mutane tserewa daga gidajensu.

    Shugaban gwamnatin lardin, David Eby, ya bukaci duk mutumin da aka umarta na yatashi , da ya gaggauta tashi nan take, yana mai gargaɗin cewa gobarar na ci gaba da bazuwa cikin sauri sosai.

    Ya ce gobarar ta lalata wasu gidaje da kadarori, yayin da aka ceto wasu mazauna da suka makale sakamakon yadda wutar ta kewaye su.

    Garin Summerland da ke kudancin lardin na daga cikin yankunan da abin ya fi shafa, inda wutar ke ta ci ganga-ganga ba kakkautawa tun ran Juma.a Jami'ai sun ce gobarar, yanzu ta mamaye fiye da fili mai fadin murabba'in kilomita 100.

  9. FIFA ta yi zargin akwai wasu shirya muzanta shugabanta Infantino

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA, ta yi tsayin daka wajen kare shugabanta Gianni Infantino, tana mai cewa akwai wani “tsari da aka shirya kuma ake ci gaba da aiwatarwa daga wasu ɓangarori” domin muzanta shi.

    Wakilin BBC ya ce Gianni Infantino ya sha bincike da dama a lokacin shugabancinsa na shekara goma.

    Shugaban na fuskantar suka a cikin makon nan bayan ya yi watsi da shirinsa na sayar da hannun jari a bangaren wasan cin kofin duniya, ga masu zuba jari.

    Tun da farko, FIFA ta ce Mista Infantino ya yi fatali da zarge-zargen da ke cewa hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA ta biya wata mata da ake bayyana a matsayin wadda ake zargin tana da alaƙa ta soyayya da shi, a lokacin da yake jagorantar hukumar ƙwallon ta Turai.

    UEFA ta ce kuɗin da aka biya matar ya yi daidai da ƙa’idojin da ke aiki a lokacin. Sai dai hukumar ta ƙara da cewa an ƙara tsaurara waɗannan ƙa’idoji tun daga lokacin.

  10. An yi jana’izar mutum 16 da aka kashe a wani hari a Benue

    An gudanar da jana’izar jama’a a ranar 8 ga watan Agusta a ƙauyen Efeyi da ke jihar Benue, arewa ta tsakiyar Najeriya, inda aka yi wa mutum 16 da ake zargin wasu ƴanbindiga suka kashe jana’iza, kamar yadda jaridar Vanguard mai zaman kanta ta ruwaito.

    Rahotanni sun ce an kashe mutanen ne lokacin da aka kai hari a ƙauyen a ranar 28 ga watan Yuli, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici tare da tilasta wa da dama daga cikinsu tserewa domin tsira da rayukansu.

    Mazauna kauyen sun bayyana harin a matsayin mummunan hari da aka kai ba tare da wani dalili ba.

    Harin ya faru ne watanni bayan da wasu ‘yan bindiga suka kashe mutane da dama a wasu kauyuka da ke cikin gundumar Ugboju, a ƙaramar hukumar Otukpo.

    A wajen jana’izar, ’yan uwa, shugabannin al’umma, sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa da malaman addini sun hallara domin yin bankwana da wadanda aka kashe.

    Wani limamin Cocin Katolika ne ya jagoranci addu’o’in jana’izar, kafin a sauke akwatunan gawarwakin wadanda aka kashe cikin kaburburansu, yayin da ’yan uwa da makusanta ke kuka da alhini.

    Jihar Benue, wadda ke yankin Middle Belt na Najeriya, na fama da rikice-rikice da suka samo asali musamman daga hare-haren ramuwar gayya da satar shanu tsakanin makiyaya, wadanda galibinsu Musulmi ne, da manoma, wadanda galibinsu Kiristoci ne.

  11. An jefa bama-bamai a Colombia ranar da sabon shugaban ƙasa ya kama aiki

    An kai hare-haren bama-bamai biyu a Colombia a ranar farko da sabon shugaban ƙasar mai ra'ayin mazan jiya, Abelardo de la Espriella, ya kama aiki.

    Rundunar sojin kasar ta dora alhakin ɗaya daga cikin hare-haren kan wasu mayaƙan ƙungiyar FARC da suka balle daga yarjejeniyar sulhu.

    Daya daga cikin fashewar ta lalata wurin karɓar kuɗin hanya a kusa da birnin Cali, inda aka gudanar da bikin rantsar da shugaban ƙasar a shekaran jiya Juma’a.

    Jami’an tsaro biyu sun jikkata sakamakon harin. A wani hari na biyu da aka kai kan wani caji ofis da jirgin sama maras matuki a gundumar Cesar da ke arewacin ƙasar, an kashe wani ɗan sanda.

    Shugaba Abelardo de la Espriella, wanda ya sha alwashin ɗaukar tsauraran matakai kan abin da ya kira “ta’addancin masu safarar miyagun ƙwayoyi”, ya ce waɗanda suka kai hare-haren ba za su samu mafaka a ko’ina ba.

  12. Mayaƙan Houthi sun kai hari kan matatar man fetur ta Saudiyya

    Mayaƙan Houthi na Yemen sun ce sun kai harin jirgin sama mara matuƙi kan wata matatar man fetur ta Saudiyya da ke gaɓar Bahar Maliya.

    Kakakin rundunar sojin ƙungiyar, Yahya Saree, ya ce harin da aka kai kan matatar man fetur ta Aramco da ke Jazan, martani ne kan kutsen da Saudiyya ke yi a arewa maso yammacin Yemen.

    Ma'aikatar makamashi ta Saudiyya ta ce jami'an kashe gobara sun yi nasarar kashe gobarar da ta tashi a wurin.

    Mayaƙan Houthi sun sanar da kafa katanga ta ruwa kan Saudiyya a watan da ya gabata, lamarin da ya sake rura wutar rikicin tare da ƙara matsin lamba kan samar da makamashi a duniya, wanda yaƙin Iran ya haifar.

    A gefe guda kuma, babbar hukumar tsaron Iran ta yi gargadin cewa ba za a bude mashigar ruwan Hormuz ba har sai Amurka ta amince da wasu bukatu guda shida, ciki har da sassauta takunkuman da aka ƙaƙaɓawa Iran, biyan diyya kan barnar yakin, da kuma kawo karshen katangar da aka sanya wa tashoshin jiragen ruwa na Iran.

  13. Mutum 22 sun rasu a haɗarin mota a Nijar

    Mahukunta a Nijar sun ce aƙalla mutum 22 ne suka rasu, wasu kusan 40 kuma suka ji rauni bayan wasu motocin bas biyu sun yi taho-mu-gama a kusa da garin Madawa da ke kudancin ƙasar.

    Ma’aikatar Sufuri ta Nijar ta ce aƙalla mutum 17 daga cikin waɗanda suka mutu sojoji ne da ke tafiya a ɗaya daga cikin motocin.

    Har yanzu ba a san musabbabin haɗarin ba, amma jami’ai sun ce ana ci gaba da bincike domin gano abin da ya haddasa afkuwar lamarin.

    Hatsarin ya faru ne a daidai lokacin da hukumomin Nijar ke gudanar da shiri na wayar da kan jama’a kan bin dokokin kiyaye haɗurran hanya.

    Haɗurran hanya na yawan afkuwa a kan titunan ƙasar ta Nijar, wadda ke yankin Sahel mai faɗin gaske, inda sama da mutum 1,200 suka mutu sakamakon irin waɗannan haɗurra a shekarar da ta gabata - 2025

  14. Farawa

    Jama'a masu bibiyar wannan shafi na kai-tsaye daga BBC Hausa.

    A wannan shafi za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na Facebook da X da kuma Whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.