'Amurka na fuskantar ƙarancin makamai masu linzami sakamakon yaƙin Iran'
Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Amurka CBS sun nuna cewa ƙasar na fuskantar ƙarancin wasu muhimman makamai masu linzami bayan yawan amfani da su a yaƙin da aka yi da Iran.
Wasu majiyoyi sun shaida cewa sojojin Amurka sun yi amfani da kusan dukkan makaman ATACMS a hare-haren da suka kai wa Iran lamarin da ya jawo damuwa kan adadin makaman da suka rage a ma'ajiyarsu.
Rahoton ya kuma ce ana ƙara nuna damuwa kan raguwar makaman kariya na Patriot da THAAD.
Sai dai jami'an Pentagon sun musanta cewa lamarin ya kai matakin barazana, suna cewa har yanzu Amurka na da isassun makamai da ƙarfin soja da za su ba ta damar kare muradunta da gudanar da ayyukanta a duk inda ake buƙata.
Batun ya sake tayar da muhawara a Washington kan ko masana'antun tsaron Amurka za su iya ci gaba da samar da makamai cikin sauri idan aka shiga wani yaƙi mai ɗaukar dogon lokaci.