Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Sauye-sauyen da hukumar Premier League za ta kawo a ɓangaren VAR

Wannan shafi na kawo muku rahotonni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni na ranar 6 ga watan Yuni, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotonnin kenan

    Nan za mu rufe wannan shafi da muka kawo wasu rahotonni game da wasanni.

    Mu haɗu da ku gobe domin samun wasu labaran.

    Kafin lokacin, kuna iya sauraron labarin wasanni a shriye-shiryenmu na rediyo da ƙarfe 8:30 na dare agogon Najeriya. Sai kuma 6:30 da 7:30 na safiya.

    Umar Mikail ke muku fatan alheri.

  2. Sauye-sauyen da hukumar Premier League za ta kawo a ɓangaren VAR

    Duk da cewa ƙungiyoyin Premier League sun amince a ci gaba da amfani da na'urar VAR mai taimaka wa alƙalin wasa yanke hukunci, a bayyane take cewa akwai buƙatar gyara.

    Hukumar gasar ta amince cewa za ta ɓullo da wasu matakai don inganta aikin na'urar, ciki har da sanar da 'yan kallo dalilin da ya sa aka ɗauki wani mataki.

    Fannonin da hukumar ta amince za ta kawo gyara sun ƙunshi:

    • Ƙara yawan matakan da za a bi kafin a nemi taimako daga VAR
    • Rage yawan jiran hukunci saboda za a ƙirƙiro sabuwar gano satar gida da ake kira SAOT
    • Rage wa magoya baya rashin jin daɗi ta hanyar rage ɗaukar lokaci da kuma ba su sanarwar dalilin da ya sa aka ɗauki wani mataki
    • Yin aiki tare da ƙungiyar alƙalan wasa wajen ba su horo a kan VAR don kada a samu tsaiko
    • Ƙara yawan bayanai da kuma rage ƙumbiya-ƙumbiya a harkokin VAR
  3. An cire Grealish da Maguire daga tawagar Ingila ta Euro 2024

    Ana sa ran ɗan wasan gaba na Manchester City Jack Grealish, da ɗan bayan Manchester United Harry Maguire ba za su buga wa Ingila gasar Euro 2024 ba.

    Zuwa yanzu ba a tabbatar da hakan ba a hukumance, amma kocin Ingila Gareth Southgate zai yi taron manema labarai da ƙarfe 6:00 kafin wasansu da Iceland a filin wasa na Wembley ranar Juma'a.

    Sai dai kuma, an fahimci cewa Magiure bai warke ba yadda ya kamata daga raunin da ya ji a bayan ƙwaurinsa a watan Afrilu, wanda ya sa bai buga wa United wasan ƙarshe na FA da ta cinye City ba.

    Grealish bai buga wasan ba gaba ɗaya kamar yadda babu shi a manyan wasnnin City da ta buga da Tottenham da kuma West Ham a ƙarshen gasar.

    Tsohon ɗan wasan na Aston Villa ya buga wa Ingila wasan da ta ci Bosnia-Herzegovina 3-0 ranar Litinin, har ma aka dinga yabonsa.

    Grealish d a Maguire na cikin tawagar 'yan wasa 33 kafin a rage mutum bakwai daga cikinsu zuwa 26 domin buga gasar ƙasashen Turai ta Euro 2024.

    Tun da farko a ranar Alhamis an tabbatar cire ɗan wasan tsakiyar Tottenham James Maddison mai shekara 27 daga tawagar, da na Liverpool Curtis Jones mai shekara 23.

    Ingila za ta buɗe wasanninta ne a Runin C da Serbia ranar 16 ga watan Yuni kafin ta kara da Denmark, da kuma Slovenia.

  4. Sai yau 'yan wasan Afirka ta Kudu suka isa masaukinsu

    Yayin da ya rage ƙasa da kwana biyu a take wasa tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu, sai da tsakar ranar yau Alhamis 'yan wasan tawagar ta Bafana Bafana suka isa masaukinsu a jihar Akwa Ibom.

    Wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, tawagar Afirka ta Kudun ta ce sai a jiya Laraba suka isa filin jirgin sama na jihar Ribas kafin daga baya su shiga mota zuwa birnin Uyo na Akwa Ibom.

    "Mun shafe awa 18 a kan hanya kuma har yanzu ba mu isa masauki ba. Yanzu haka muna filin jirgi na Fatakwal...an rufe filin jirgi na Uyo lokacin da muka so mu tashi zuwa can," in ji wani saƙo da ta wallafa jiya.

    Sai kuma da ranar yau ta sake wallafa wani saƙon cewa: "Daga ƙarshe dai Bafana Bafana sun isa masaukinsu a Uyo."

    Wannan ne zagayen farko na wasan neman shiga gasar Kofin Duniya da za su kara, inda za a buga zagaye na biyun a Afirka ta Kudu cikin shekarar 2025.

  5. Shirin da Super Eagles ke yi, Najeriya v Afirka ta Kudu

    Tawagar Super Eagles ta Najeriya da Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu na ci gaba da shirin fafatawa da juna a wasan neman gurbin gasar Kofin Duniya ta 2026.

    Za a buga wasan gobe Juma'a da misalin ƙarfe 8:00 na dare agogon Najeriya da Nijar a filin wasa na Godswill Akpabio da ke birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.

    Yayin da 'yan wasan Najeriya ke ci gaba da atasaye a sansaninsu, sai a yau Alhamis tawagar Bafana Bafana ta isa masaukinta a Uyo.

  6. Za a ci gaba da amfani da VAR a Premier League

  7. Euro 2024: Ban ji daɗi ba da aka cire ni daga tawagar Ingila - Maddison

    Ɗan wasan tsakiyar Tottenham, James Maddison, ya ce ya "kaɗu sosai" bayan an cire shi daga tawagar Ingila da za ta buga gasar Euro 2024.

    An saka ɗan wasan mai shekara 27 cikin babbar tawagar mutum 33 da aka ware amma sai aka sanar da shi cewa yana cikin 'yan wasa bakwai da za su koma gida.

    Hakan na nufin ba shi cikin tawagar mutum 26 da za su buga wasan zumunta na ƙarshe a gobe da Iceland kafin fara gasar ta ƙasashen Turai.

    "Na yi atasaye da kyau kuma na mayar da hankali amma idan zan faɗa wa kaina gaskiya, ƙoƙarina a Tottenham bayan na dawo daga jinya bai kai abin da ake buƙata ba wanda koci Gareth Southgate ya yi amfani da shi wajen ɗaukar mataki," in ji Maddison.

  8. Jita-jitar a kasuwar saye da musayar 'yan wasan Turai

    Atletico Madrid ta tuntubi ƴan ukun Argentina, wato Angel Correa, Rodrigo de Paul da kuma Nahuel Molina, a kan ɗan wasan, gaba na Manchester City Julian Alvarez mai shekara 24.(Marca - in Spanish), external

    Paris St-Germain ma na son Alvarez.(Fabrizio Romano)

    Manchester United ta bi takwararta Liverpool a son dan wasan tsakiya na Faransa Leny Yoro mai shekara 18, wanda kuma yake taka wa Lille leda. (Marca - in Spanish)

    Sai dai da alama ba lallai Manchester United ta samu dan wasan ba, yayin da Real Madrid ke sahun gaba kan dauko dan wasa Yoro. (Mail)

  9. Barkanmu da rana

    Ma'abota wasanni barkanmu da tsakar ranar Alhamis.

    Umar Mikail ne zai kasance da ku a wannan rana don kawo muku yadda take kasancewa a duniyar wasanni kai-tsaye.

    Ku biyo ni kawai.