Masana sun yi gargaɗi kan barazanar Maleriya
Masana Kimiyya sun yi gargadin cewa rayuwar miliyoyin mutane na cikin hadari idan ba a dauki matakin gaggawa ba wajen dakatar da zazzabin Malariya da ke bijirewa magani wanda kuma ke yaduwa a nahiyar Afirka kamar yadda ya yi shekaru 50 da suka wuce lokacin mace-macen da ya ninka har sau uku.
Kwayoyin Malariya wadanda ke bijirewa muhimmin maganin na artemisinin, yanzu ba su a gabashin Afirka.
Bijirewa magungunan cutar ta malariya yanzu ya karu a wasu yankuna daga kashi daya cikin 100 zuwa fiye da kashi 20 cikin 100.
Wasu masana kimiyya sun ce daga kasashe 10, yaduwar irin nau'in wannan cuta ya wuce kima ba tare daukar matakin da ya dace ba.