Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi 16 ga watan Agustan 2026

Taƙaitattu

  • Sabon shugaban Hamas ya isa Alkahira domin tattaunawa kan Gaza
  • Iran ta gargaɗi Trump ya damu da tsaron kansa maimakon mashigar Hormuz
  • INEC ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Osun
  • Mun kama wanda ake zargi da harbi a wajen biki a Kano - Ƴansanda
  • Atiku ya taya Adeleke murnar sake lashe zaɓen gwamnan Osun
  • Tinubu ya taya ni murnar lashe zaɓe - Adeleke
  • Lokuta huɗu da siyasa ta raba Kannywood

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammed

  1. Iran ta buƙaci Qatar ta bari ta bincika ɓacewar direbobin jirginta uku a ƙasar

    Rundunar sojin Iran ta ce ya kamata Qatar ta ba ta damar tura tawagar bincike domin gano abin da ya faru da matuƙan jiragen saman sojin Iran guda uku da suka ɓace.

    Qatar ta musanta kwata-kwata cewa tana tsare da mutanen ukun, wadanda Tehran ta ce an harbo jiragen da suke tukawa a farkon yakin da ta yi da Amurka.

    Wani kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar ya ce an gano gawar daya daga cikin matukan, kuma an gayyaci Iran domin karbar ragowar gawar.

    Wannan musantawar ta Qatar ta zo ne bayan wani janar din Iran, wanda ke jagorantar kwamitin sojin Iran mai neman mutanen da suka bace a yakin, ya yi zargin cewa an kama matukan jiragen ukun da ransu bayan jiragensu sun yi hatsari a watan Maris.

  2. MURIC ta zargi Inec da hana masu hijabi yin zabe a Osun

    Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC) ta zargi Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da hana dubban mata Musulmi masu sanya hijabi kaɗa ƙuri’arsu a zaɓen gwamnan jihar Osun da aka gudanar ranar 15 ga Agusta, 2026.

    A cikin wata sanarwa da daraktan ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar, MURIC ta yi ikirarin cewa lamarin ya faru a wurare da dama na jihar, inda ta ce an hana wasu mata masu hijabi yin zaɓe sai bayan sun cire hijabinsu.

    Kungiyar ta bayyana hakan a matsayin tauye haƙƙin zaɓe da kuma cin mutuncin mata Musulmi.

    MURIC ta ɗora alhakin lamarin kan shugabancin INEC, tana mai cewa hukumar ta gaza wayar da kan jami’anta na dindindin da na wucin gadi game da ’yancin addini.

    Kungiyar ta kuma ce tana da bidiyon wata mata mai hijabi da ta yi korafin cewa an hana ta yin zaɓe saboda suturar da take sanyawa.

    Kungiyar ta sake kira da a cire shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, tare da zargin cewa abin da ta kira tsoratar da mata Musulmi masu hijabi ya yi tasiri a sakamakon zaɓen.

    Haka kuma MURIC ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta binciki zarge-zargen, tana mai gargadin cewa irin wannan matsala na iya sake faruwa a babban zaɓen shekarar 2027 idan ba a ɗauki mataki ba.

  3. Tsohon shugaban Iran Khatami ya goyi bayan yarjejeniyar ƙasar da Amurka

    Tsohon shugaban Iran, Mohammad Khatami, ya kare yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da Amurka, yana mai cewa ta haifar wa ƙasar da al'ummarta wata babbar dama da bai kamata a bari ta wuce ba.

    Khatami ya yaba wa Majalisar Koli ta Tsaron Ƙasa da kuma kwamandojin sojin Iran kan amincewa da yarjejeniyar, tare da yaba wa shugaban ƙasar Massoud Pezeshkian saboda abin da ya kira jarumtaka wajen tunkarar lamarin.

    Ya ce ko da yake ba za a iya amincewa da Amurka gaba ɗaya ba, ya kamata a tafiyar da irin waɗannan batutuwa cikin hikima da diflomasiyya.

    Ya kuma yi kira da a samar da "zaman lafiya mai mutunci" tare da magance matsalolin tattalin arzikin da ke addabar jama'a.

    Khatami ya yi gargadin cewa gibin da ke tsakanin gwamnati da al'umma ya ƙara faɗaɗa a cikin 'yan shekarun nan, yana mai cewa rasa wannan dama na iya ƙara tsananta barazanar da ƙasar ke fuskanta.

  4. Nijar ta ƙulla yarjejeniyar gina matatar mai ta dala biliyan $1.9 da kamfani a Canada

    A ranar 15 ga Agusta 2026, gwamnatin Nijar ta sanya hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (PPP) da Zimar Group ta Canada, domin gina katafaren matatar mai da sauran albarkatun man fetur a birnin Dosso, kudancin kasar.

    Muhimman abubuwan yarjejeniyar

    • Za a gina matatar mai mai ikon tace gangar mai 100,000 a rana.
    • Aikin zai gina bututu da sauran kayayyakin more rayuwar masana'antu.
    • Zimar Group da abokan hulɗarta ne za su samar da kuɗin aikin na tsawon shekara 16.
    • Bayan shekara 16, za a miƙa mallakar aikin ga gwamnatin Nijar ƙarƙashin tsarin Build-Operate-Transfer (BOT).
    • Kamfanin yana da wata 4 na neman kuɗin aikin da kammala cikakken tsarin injiniya, yayin da dole ne a kammala samar da kudin aikin gaba daya cikin watanni 12.

    Wannan yarjejeniya ta samo asali ne daga yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da aka rattaba hannu a kanta a Oktoba 2024.

  5. Majalisar Iran ta amince da ƙudirin daƙile tasirin ƙasashen waje a ƙasar

    Majalisar dokokin Iran ta amince da ainihin tsarin wani kudiri da ake cewa zai taimaka wajen dakile tasirin hukumomin leƙen asiri, gwamnatoci da cibiyoyin ƙasashen waje a cikin ƙasar.

    Kakakin majalisar, Abbas Goodarzi, ya ce an gabatar da ƙudirin ne domin kare Iran daga duk wani tasirin waje da ka iya shafar harkokin siyasa, tsaro da zamantakewa na ƙasar.

    Tun a watan Yulin bara ne aka fara bayyana ƙudirin a gaban majalisar, sannan Kwamitin Tsaro da Harkokin Waje na majalisar ya amince da shi da rinjayen kuri'u a watan Oktoba.

    Kakakin kwamitin, Ebrahim Rezaei, ya ce manufarsa ita ce ƙarfafa garkuwar Iran daga abin da ta ke kallon katsalandan daga ƙasashen waje.

    Jami'an Jamhuriyar Iran sun sha bayyana damuwa a cikin shekarun baya kan abin da suke kira yunƙurin hukumomin leƙen asirin ƙasashen waje na yin tasiri a harkokin siyasa, zamantakewa da tsaro na ƙasar.

  6. Iran ta sa ladan dala 60,000 ga duk wanda ya kashe ko ya kama sojan Amurka

    Babban kwamandan sojojin Iran, Amir Hatami, ya sanar da cewa ƙasar za ta bai wa duk macen da ta kashe ko kama sojan Amurka sannan ta miƙa shi ga hukuma ladan dala 60,000.

    Hatami ya ce ga maza kuwa za su samu ladan dala 30,000 idan suka yi hakan wanda ya ce ya yi daidai da biliyan biyar na toman.

    Ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka gudanar domin bikin Ranar 'Yan Jarida.

    Ya kuma ƙara da cewa za a sayi makamin duk wanda ya yi nasarar kashe sojan Amurka da ninki biyu na kuɗinsa, sannan a ba shi sabon makami.

    Kazalika, ya ce za a ajiye makamin a wani gidan tarihi da aka tanada domin tunawa da irin waɗannan ayyuka.

  7. Yadda ɗaliban jami'ar ABU Zaria suka kece raini a Bikin Baje-kolin Al'adu

    Ga wasu hotuna da ke nuna yadda ɗaliban Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya suka kece raini a bikin baje-kolin al'adu, inda suka fito sanye da kayan gargajiya iri-iri da ke nuna al'adu da al'adun ƙabilu daban-daban na Najeriya.

    Bikin ya kasance cike da ƙayatattun kaya, raye-raye da kuma abubuwan da suka nuna yalwar al'adun ƙasar.

    Hotunan da shafin AbuInsight ya wallafa a dandalin X sun nuna yadda ɗalibai suka yi ado cikin kayan Hausawa, Yarbawa, Ibo da sauran ƙabilu, tare da baje kolin abinci, kiɗa da al'adun gargajiya.

    Bikin ya jawo hankalin mutane da dama, inda ɗaliban suka yi amfani da damar wajen nuna haɗin kai da kuma bikin bambancin al'adun da ke haɗa al'ummar jami'ar.

  8. Ƴansanda sun ce mutum biyar sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a Neja

    Mutum biyar ne suka mutu bayan da wani kwale-kwale ya kife a Kogin Kudi da ke ƙauyen Shaba Woshi a ƙaramar hukumar Katcha ta jihar Neja, a cewar rundunar ’yan sandan jihar.

    A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce jami’anta sun garzaya zuwa wurin da hatsarin ya faru bayan samun rahoton lamarin.

    Ta ƙara da cewa hatsarin ya yi sanadin mutuwar mutum biyar, kuma an samu nasarar gano gawarwakin dukkansu daga kogin.

    Rundunar ta bayyana cewa an yi jana’izar mamatan.

    Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Minna na ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin.

  9. An ɗaure direban Canter wata daya bayan rufe fasinja da tamfal

    Wata kotun tafi-da-gidanka a jihar Abia ta yanke wa wani direba hukuncin ɗaurin wata guda a gidan gyaran hali bayan da Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta gano fasinjoji 15 da aka ɓoye ƙarƙashin tamfal na wata motar Canter a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

    FRSC ta ce jami'anta sun tare motar ne a Nyanya bayan sun yi zargin cewa ana ɓoye wani abu a cikinta.

    Bayan bincike, sun gano mutane 15 da babura takwas da aka lulluɓe da kaya ƙarƙashin tamfal, lamarin da hukumar ta ce ya sa rayuwar fasinjojin cikin haɗari.

    An kuma kama direban motar, Umar Muhammadu, wanda ake zargi da ƙoƙarin bai wa wani jami'in FRSC cin hanci tare da kasa gabatar da sahihin lasisin tuƙi.

  10. APC ta fice daga cibiyar tattara sakamakon zaɓen gwamnan Osun

    Wakilin jam'iyyar APC ya fice daga cibiyar tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Osun, kuma bai sanya hannu kan sakamakon ƙarshe da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana ba.

    Bayan kammala tattara sakamakon zaɓen da kuma ayyana Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen, wakilan jam'iyyun siyasa sun kasance a wurin domin sanya hannu kan takardun sakamakon da aka tattara daga ƙananan hukumomin jihar.

    Sauran wakilan jam'iyyun da suka halarta sun ci gaba da kasancewa a wurin yayin gudanar da ayyukan kammala tattara sakamakon zaɓen.

  11. Tinubu ya taya ni murnar lashe zaɓe - Adeleke

    Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ce Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kira shi domin taya shi murnar nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan jihar.

    Adeleke ya bayyana hakan ne yayin da yake gode wa shugaban ƙasar kan yadda ya ce ya tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin tsarin dimokuraɗiyya.

    Adeleke ya samu nasarar sake lashe zaɓen gwamna bayan ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jam'iyyar APC.

    Nasarar ta ba shi damar ci gaba da jagorantar al'ummar jihar Osun na wani wa'adi na shekara huɗu.

  12. Atiku ya taya Adeleke murnar sake lashe zaɓen gwamnan Osun

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya taya Ademola Adeleke murnar nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan jihar Osun.

    A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, Atiku ya ce nasarar Adeleke ta nuna ƙarara zaɓin al'ummar jihar Osun, wanda suka bayyana ta hanyar ƙuri'un da suka kaɗa a zaɓen.

    Ya kuma yaba wa al'ummar jihar kan yadda suka fito cikin lumana tare da nuna himma wajen gudanar da zaɓen.

    Atiku ya ce yana yi wa Adeleke fatan samun ƙarin nasara yayin da yake ci gaba da yi wa mutanen Osun hidima a matsayinsa na gwamna.

  13. Mun kama wanda ake zargi da harbi a wajen biki a Kano - Ƴansanda

    Rundunar ’yansandan Kano ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da harbin mutane a wajen bikin aure a Tudun Yola Bajallabe.

    A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafin sada zumuntarta na X, ta ce jami’anta sun gaggauta isa wurin bayan samun kiran neman agaji, inda suka kama wanda ake zargin tare da kwacd bindigar da aka yi amfani da ita wajen harbin.

    Ta ƙara da cewa an garzaya da mutane huɗu da suka jikkata zuwa sakamakon harbin zuwa asibiti domin samun magani, sai dai likita ya tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikinsu.

    Rundunar ta ce sashen binciken manyan laifuka na SCID da ke Bompai na ci gaba da binciken lamarin.

  14. Yadda Davido ya yi murnar sanar da kawunsa ya lashe zaɓen gwamnan Osun

    Ga wani bidiyo da ke nuna yadda shahararren mawaƙin Najeriya, Davido, ya yi murnar nasarar kawunsa, Ademola Adeleke, bayan da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Osun.

    An ga mawaƙin cikin farin ciki yayin da yake shagulgulan nasarar tare da waɗanda ke tare da shi.

    Bidiyon, wanda Davido ya wallafa a shafinsa na X, ya nuna yadda mawaƙin da wasu mutane ke murna da raye-raye bayan sanar da sakamakon zaɓen.

    A sakamakon da INEC ta sanar, Adeleke ya samu ƙuri'u 511,067 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jam'iyyar APC, wanda ya samu ƙuri'u 444,815. Sakamakon ya tabbatar da ci gaba da zamansa gwamnan jihar Osun.

    Faifan bidiyon ya yi ta samun martani a kafafen sada zumunta, inda magoya baya da sauran masu amfani da shafukan intanet suka rika taya Davido da kawunsa murnar wannan nasara a zaɓen gwamnan jihar.

  15. Iran ta nemi Qatar ta ba ta damar binciken batun matukan jiragenta da ke tsare a ƙasar

    Iran ta nemi Qatar ta ba ƙwararrun rundunar sojin saman ƙasarta damar shiga ƙasar domin gudanar da bincike kan makomar matukan jiragenta uku da ta ce ana tsare da su.

    Kwamandan kwamitin neman mutanen da suka ɓace na rundunar sojin Iran, Mohammad Bagherzadeh, ya ce ƙwararrun Iran sun shafe watanni suna jiran izinin shiga Qatar, yana zargin hukumomin Qatar da jinkirta binciken.

    Ya kuma buƙaci Red Cross ta gaggauta bibiyar lamarin, tare da bayyana damuwa kan wasu ƴan Iran huɗu da ya ce ana tsare da su a Kuwait.

    Qatar ta musanta cewa tana tsare da matukan jiragen uku. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen ƙasar, Majid Ansari, ya ce matuƙan sun shiga sararin samaniyar Qatar a watan Maris, kuma Qatar ta ɗauki matakin kare ƙasarta bisa dokokin kasa da kasa.

  16. INEC ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Osun

    Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana gwamnan jihar Osun mai ci, Ademola Adeleke, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar 14 ga watan Agusta.

    A sakamakon da hukumar ta bayyana, Adeleke na jam'iyyar Accord ya samu ƙuri'u 511,067, inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa Bola Oyebamiji na jam'iyyar APC, wanda ya samu ƙuri'u 444,815. Hakazalika, ɗan takarar jam'iyyar ADC, Najeem Salaam, ya zo na uku bayan samun ƙuri'u 17,180.

    Sakamakon zaɓen daga ƙananan hukumomi daban-daban na jihar ya nuna cewa Adeleke ya yi nasara a mafi yawan yankunan da aka kaɗa ƙuri'a, lamarin da ya taimaka masa wajen samun gagarumar rinjaye da kuma ci gaba da zama gwamnan jihar Osun na wani wa'adi.

  17. Iran ta gargaɗi Trump ya damu da tsaron kansa maimakon mashigar Hormuz

    Shugaban Kwamitin Tsaro da Harkokin Waje na Majalisar Iran, Ebrahim Azizi, ya mayar da martani ga kalaman Donald Trump kan mashigar Hormuz, yana mai cewa shugaban na Amurka ya kamata ya damu da tsaronsa maimakon ci gaba da yin barazana game da mashigin ruwan.

    Kalaman na sa sun zo ne a matsayin martani ga abin da Donald Trump ya faɗa a jiya inda ya ce zai ayyana mashigar Hormuz a matsayin na Amurka.

    Daga baya fadar White House ta ce kalaman Trump shaci faɗi ce amma kalaman nasa sun jawo ce-ce-ku-ce a kafafen yaɗa labarai da kuma tsakanin jami'an gwamnati da 'yan siyasar Iran.

    Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar man fetur a duniya, lamarin da ke sa duk wata magana a kansa ta ja hankalin ƙasashen duniya..

  18. Sabon shugaban Hamas ya isa Alkahira domin tattaunawa kan Gaza

    Sabon shugaban ungiyar Hamas Khalil al-Hayyah, ya isa birnin Alkahira na Masar domin tattaunawa da jami'an ƙasar kan halin da ake ciki a Gaza, a cewar majiyoyin Hamas.

    Tashar Al Jazeera ta ruwaito cewa ana sa ran al-Hayyah zai gana da Hassan Rashad, shugaban hukumar leƙen asirin Masar, a safiyar Lahadi.

    Wannan ita ce ziyararsa ta farko zuwa Masar tun bayan da ya karɓi jagorancin Hamas a ƙarshen watan Yuli.

    Ziyarar tasa na zuwa ne gabanin wata tafiya da Jared Kushner, surukin shugaban Amurka Donald Trump, zai kai yankin.

    Ana sa ran Kushner zai ziyarci Isra'ila da Masar a mako mai zuwa domin ƙoƙarin rage saɓanin da ke akwai kan wani shiri da ya shafi Gaza, wanda Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da shi.

    Haka kuma, ana sa ran wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da harkokin zaman lafiya a Gaza, Nickolay Mladenov, zai raka Kushner a wannan tafiya.

  19. Assalamu alaikum!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da Safiyar ranar Lahadi.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.