Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 12 ga watan Agustan 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Usman MINJIBIR

  1. Dalilan da suka sa na nace kan zaɓen Muslim-Muslim - Sheikh Jingir

    Shugaban majalisar malamai ta ƙungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce ya yi tsammanin zai sha suka lokacin da ya yi wasu kalamai game da takarar Muslim-Muslim. Jingir ya kuma ce ba ya da na sanin matsayarsa.

  2. A shirye muke mu ɗauki tsawon lokaci muna yaƙi - Iran

    Iran ta ce a shirye take ta ɗauki tsawon lokaci tana yaƙi idan buƙatar hakan ta taso, tare da ci gaba da gudanar da ayyukan soji na tsawon lokaci.

    Mataimakin babban jami’in gudanarwa na rundunar sojin ƙasar, Alireza Sheikh, ya bayyana cewa Iran na da ƙarfin da za ta iya mayar da martani ga duk wata barazana, har ma da ɗaukar matakan kariya.

    A wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Mehr, Alireza Sheikh ya ce dabarun da Iran ke amfani da su sun tilasta wa Amurka sake nazarin manufofinta akai-akai, yana mai cewa Tehran na ci gaba da taka muhimmiyar rawa a fagen siyasa da tsaro.

    Ya kuma ce Iran ta sauya daga tsarin kare kai zuwa tsarin hana barazana da kuma ɗaukar matakai kai tsaye idan hali ya buƙata, yana mai jaddada cewa ƙasar na da isassun kayan aiki da dabarun ci gaba da yaƙi na dogon lokaci.

    Jami'in ya ƙara da cewa ikon Iran na ƙera makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa na daga cikin manyan abubuwan da ke ƙarfafa shirinta na ci gaba da gudanar da ayyukan soja cikin dogon lokaci.

  3. 'Iran ta ce babu tattaunawar tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka'

    Wani babban jami’in gwamnatin Iran ya ce babu wata tattaunawa da ake yi da Amurka domin tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Tehran da Washington in ji kamfanin dillancin labaran Reuters.

    Jami’in, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya ce babu abin da Iran za a tsawaita, domin a cewarsa Amurka ta karya yarjejeniyar wucin-gadi sa’o’i 48 bayan ƙulla ta, sannan ta janye daga cikinta bayan wasu kwanaki.

    Wannan na zuwa ne yayin da ministan harkokin cikin gida na Pakistan, Mohsen Naqvi, ya kai ziyara Tehran inda ya gana da shugaban Iran da kuma ministan harkokin wajen ƙasar, a wani yunƙuri da ake dangantawa da ƙoƙarin sasanta rikicin da kuma sake buɗe mashigar Hormuz.

    A ranar 17 ga Yuni ne Amurka da Iran suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna wadda ta tanadi tsagaita wuta da kuma wa’adin kwanaki 60 na tattaunawar kawo ƙarshen yaƙi.

    Sai dai bayan sabbin rikice-rikice da musayar hare-hare, ɓangarorin biyu sun zargi juna da karya yarjejeniyar.

  4. Ghana ta kafa sabuwar dokar ƴaƙi da fashin teku a Gulf na Guinea

    Gwamnatin Ghana ta kafa wata sabuwar doka da nufin magance matsalolin tsaro a yankin Tekun Gulf na Guinea.

    Dokar wadda Majalisar Dokokin ƙasar ta amince da ita, za ta taimaka wajen yaƙi da fashin teku, fashi da makami a ruwa da sauran laifukan da ke barazana ga harkokin jiragen ruwa.

    Hukumar Kula da Harkokin Teku ta Ghana ta ce ta yi aiki tare da Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi da Laifuka (UNODC) da Tarayyar Turai domin wayar da kan hukumomin tsaro kan yadda za a aiwatar da sabuwar dokar.

    Mataimakin darakta janar na hukumar, Mubarick Masawudu, ya bayyana dokar a matsayin wani babban mataki na daƙile ayyukan masu laifi da ke kawo cikas ga harkokin sufurin teku.

    Sai dai masana sun yi gargaɗin cewa doka kaɗai ba za ta wadatar wajen kare yankin ruwan Ghana ba.

    Wani masanin harkokin tsaro na Ghana, Adib Sana, ya shaida wa BBC cewa nasarar dokar za ta dogara ne da ingantaccen sa ido, musayar bayanan sirri tsakanin hukumomi, haɗin gwiwa da maƙwabtan ƙasashe, da kuma ƙarfafa ikon gurfanar da masu laifi a gaban kotu.

    Ya kuma nuna damuwa kan yadda wasu jiragen ruwa na Rasha da ake kira shadow fleet ke amfani da tutocin ƙasashe masu tasowa domin kauce wa takunkuman ƙasa da ƙasa.

  5. Tinubu ya amince da farfaɗo da rijiyoyin man fetur da ke tsakiyar teku

    Gwamnatin Najeriya ta amince da wani sabon tsarin haraji da dokoki da nufin farfaɗo da harkar hako man fetur da iskar gas daga rijiyoyin mai da ke tsakiyar teku.

    Gwamnatin ta yi imanin cewa matakin zai iya jawo jarin da ya kai dala biliyan 50 cikin harkar mai da gas, tare da ƙara samar da ayyukan yi da kuma kuɗaɗen shiga ga ƙasar.

    Babban gwajin wannan sabon tsarin shi ne ko kamfanonin mai daga ƙetare za su amince su ci gaba da aikin Bonga South West-Aparo, wani shiri da ya kwashe kimanin shekaru 30 ana shirin aiwatar da shi.

    Ana sa ran aikin zai buƙaci jarin farko na kusan dala biliyan 10, kuma idan aka kammala shi zai iya samar da ganga 150,000 na ɗanyen mai a kowace rana.

    Gwamnatin Najeriya na sa ido kan ko kamfanin Shell, wanda ke gudanar da rijiyar man Bonga, zai yanke shawarar fara aikin a shekarar 2027.

    Hakan na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar raguwar saka jari a harkar mai da gas sakamakon satar mai, rashin tsaro da kuma ficewar wasu manyan kamfanonin mai daga wasu rijiyoyin da ke kan tudu.

    A lokaci guda, gwamnati na kuma shirin sauya wasu ƙa'idojin rarrabawa da farashin ɗanyen mai ga matatun mai na cikin gida, domin rage musu tsadar samar da mai.

    Ana sa ran matakan za su taimaka wajen ƙara yawan man da ake haƙowa da jawo ƙarin jari da kuma tabbatar da cewa ana sarrafa mafi yawan ɗanyen man Najeriya a cikin ƙasar.

  6. Abin da ya sa muka bai wa gwamnoni wa'adi kafin shiga yajin aiki - ASUU

    Ƙungiyar Malaman Jami'o'in Najeriya (ASUU) ta umarci malaman jami'o'i 20 da su fara shirye-shiryen shiga yajin aikin gama-gari, bisa zargin cewa gwamnatin tarayya da wasu gwamnatocin jihohi sun gaza cika alƙawuran da suka ɗauka a yarjejeniyar da aka ƙulla da ƙungiyar tun a shekarar 2025.

    Ƙungiyar ta ce ta bai wa gwamnatocin da abin ya shafa wa'adin mako biyu domin magance matsalolin da suka rage.

    Shugaban ASUU na shiyyar Kano, Dakta Abdulrazaq Ibrahim Fagge, ya ce an ɗauki matakin ne bayan taron da uwar ƙungiyar ta gudanar a Abuja sakamakon ƙorafe-ƙorafen da ta samu daga wasu jami'o'i, musamman na jihohi.

    Ya ce duk da yarjejeniyar da aka cimma a watan Disambar 2025 kan sabbin alawus-alawus da wasu sauye-sauye a tsarin tafiyar da jami'o'i, har yanzu wasu gwamnatocin jihohi ba su aiwatar da abin da suka amince da shi ba.

    ASUU ta ce yayin da gwamnatin tarayya ta fara cika nata alƙawuran tun daga watan Janairun wannan shekarar, wasu gwamnoni sun gaza yin haka.

    Ƙungiyar ta zargi wasu gwamnatocin jihohi da fifita ayyukan da ba su da muhimmanci fiye da ilimi, tana mai cewa babu shirin sake zama da gwamnati a yanzu saboda an shafe watanni takwas ana tattaunawa ba tare da samun ci gaba ba.

    Ta gargadi cewa rassan da abin ya shafa za su shiga yajin aiki idan wa'adin mako biyun ya cika ba tare da an warware matsalolin ba.

  7. Iran za ta jima bata ƙera makamin mukiliya ba - Isra'ila

    Tsohon shugaban hukumar leƙen asirin Isra'ila ta Mossad, Yossi Cohen, ya ce duk da cewa Iran na da sinadarin uranium mai wadatar kaso 60 cikin 100, hakan ba yana nufin tana gab da ƙera makamin nukiliya ba.

    Ya ce har yanzu ƙasar na da sauran aiki mai yawa kafin ta kai matakin kera irin wannan makami.

    Yossi Cohen ya bayyana haka ne a wani taro da aka gudanar ranar Talata, inda ya ce hukumar Mossad ta shafe lokaci tana bibiyar cibiyar nukiliyar Fordow ta Iran da ke ƙarƙashin ƙasa tare da gudanar da bincike mai zurfi game da ita.

    Sai dai tsohon shugaban leƙen asirin bai yi ƙarin bayani kan irin bayanan da suka tattara daga cibiyar ta Fordow ba.

  8. NiMet ta yi gargaɗin ambaliya a Sokoto, Kaduna, Neja da wasu jihohi 10 a watan Agusta

    Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargaɗin yiwuwar aukuwar ambaliyar ruwa a jihohi 13 tsakanin ranar 11 da 20 ga watan Agustan 2026.

    Jihohin da ta ce ke fuskantar barazanar sun haɗa da Sokoto, Zamfara, Kebbi, Neja, Kaduna, Nasarawa, Adamawa, Filato, Benue, Kogi, Taraba, Cross River da Akwa Ibom.

    Hukumar ta ce hasashen ya samo asali ne daga nazarin yawan ruwan sama da ake sa ran samu, yanayin danshin ƙasa, ƙarfin magudanan ruwa, yanayin ƙasa da kuma yanayin madatsun ruwa.

    Ta yi gargaɗin cewa ambaliyar ka iya shafar yankunan da ke fama da ambaliya, ƙananan wurare, birane da kuma al'ummomin da ke kusa da koguna, lamarin da zai iya haddasa rufe hanyoyi da tsaikon sufuri.

    NiMet ta kuma ce ambaliyar na iya lalata gonaki, amfanin gona da dabbobi tare da shafar wutar lantarki da hanyoyin sadarwa.

    Hukumar ta shawarci jama'a su riƙa bibiyar hasashen yanayi da gargaɗin ambaliya, su guji wucewa ta hanyoyin da ruwa ya mamaye, yayin da ta buƙaci hukumomin agajin gaggawa da manoma su ɗauki matakan kariya domin rage illolin da ka iya tasowa.

  9. 'Yan Pakistan uku sun mutu a harin Houthi kan wani jirgin ruwa

    Ministan Harkokin Wajen Pakistan, Mohammad Ishaq Dar, ya sanar a ranar Laraba cewa 'yan ƙasar Pakistan uku sun mutu sakamakon harin da mayaƙan Houthi suka kai kan wani jirgin ruwa a Tekun Bahar Maliya.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Ishaq Dar ya ce: "'Yan ƙasar Pakistan uku sun rasa rayukansu, yayin da mutum guda ya jikkata a wannan lamari."

    Kalaman nasa sun zo ne kwana guda bayan hukumomin tsaron gaɓar tekun Yemen suka tabbatar da cewa aƙalla mutum shida ne suka mutu a harin da mayaƙan Houthi suka kai kan wani jirgin ruwa a gaɓar ƙasar.

    Har yanzu ba a bayyana ƙarin cikakkun bayanai kan mutanen da suka mutu ko kuma yanayin jirgin ruwan da harin ya rutsa da shi ba.

  10. Sabon jirgin da aka sauya min ya ma fi haɗarin fuskantar harin Iran - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sabon jirgin sojin da aka sauya masa a lokacin da yake komawa Amurka daga Turkiyya ya fi haɗarin fuskantar harin Iran fiye da jirgin shugaban ƙasar Amurka Airforce one da ya bari.

    Da yake magana da manema labarai, Trump ya ce ya bi shawarar hukumomin tsaro inda ya koma Amurka ta wani jirgin daban bayan halartar taron ƙungiyar NATO a Turkiyya kusan wata guda da ya wuce.

    Rahotannin kafofin yaɗa labaran Amurka sun ce jami'an tsaro sun gano wata babbar barazana daga Iran ta yiwuwar harba makami mai linzami kan jirgin Trump lamarin da ya sa ya sauya jirgi a asirce.

    Trump ya kuma yi iƙirarin cewa Amurka ce ke da cikakken iko da Mashigar

  11. Za mu farmaki cibiyoyin Amurka da na ƙawayenta idan aka sake kai mana hari - Iran

    Jami'in dakarun juyin juya halin Iran (IRGC), Hossein Mohebi, ya ce Amurka da ƙawayenta za su fuskanci hare-hare kan muhimman cibiyoyinsu idan aka sake kai wa Iran hari.

    Ya yi gargaɗin cewa Iran za ta iya kai farmaki kan tashoshin samar da wutar lantarki, layukan isar da makamashi da sauran muhimman tsare-tsaren Amurka da na ƙawayenta.

    Mohebi ya kuma ce, manyan sassan cibiyoyin sadarwa na duniya da ke da alaƙa da intanet na iya fuskantar barazana idan aka sake kai wa Iran hari.

    Ya ƙara da cewa a halin yanzu babu wani jirgin ruwa na Amurka da ke cikin ruwan Tekun Fasha.

    Kalaman kakakin IRGC na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba yarda da Iran domin, a cewarsa, tana yi masa ƙarya.

    Trump ya kuma jaddada cewa Mashigin Hormuz yana ƙarƙashin ikon Amurka kuma mallakin Amurka ne.

  12. Assalamu alaikum

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye.

    Kamar kullum, yau ma za mu muku labaran abubuwan da ke faruwa game da yaƙin Iran da wasu muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a wannan rana ta Laraba.

    Aisha Babangida ce za ta saka kasancewa da ku daga yanzu zuwa ƙarfe 4 na yamma.

    Za ku iya yin tsokaci a shafukanmu na sada zumunta: Facebook, X, instagram, YouTube da kuma zaurenmu na WhatssApp.

    Ku kasance da mu.