Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 07/03/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 07/03/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza, Isyaku Muhammad, Usman Minjibir, da Umar Mikail

  1. EFCC ta gayyaci tsohuwar ministar matan Najeriya, Uju Kennedy

    Jami'an hukumar EFCC, mai yaƙi da cin hanci da Rashawa a Najeriya sun gayyaci tsohuwar ministar matan ƙasar, Uju Kennedy-Ohanenye domin amsa tambayoyi.

    Kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ce hukumar na zargin Ms Kennedy da karkatar da naira miliyan 138.4 cikin kuɗin da aka ware wa ma'aikatar a kasafin kuɗin 2023, da ɓarnatar da kuɗi da kuma saɓa ƙa'ida wajen gudanar da wasu lamurra.

    Hukumar na zargin tsohuwar ministar da karkatar da kuɗin domin amfanin ƙashin kanta, ciki har da kuɗaɗen da aka ware domin shirin tallafa wa mata na P-BAT.

    Tsohuwar ministan ta isa harabar hukumar da safiyar ranar Alhamis, domin amsa tambayoyi, kuma bayanai na cewa har yanzu ana ci gaba da yi mata tambayoyin, kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

    Uju Kennedy-Ohanenye na ɗaya daga cikin ministoci biyar da Shugaban Ƙasar, Bola Tinubu ya sallama daga aiki a watan Oktoban 2024.

    A watan Agustan 2023 ne shugaban ya naɗa ta a matsayin ministar kula da al'amuran matan ƙasar, matayin da ta riƙe na tsawon wata 15.

  2. Zelensky zai je Saudiyya don tattauna batun tsagaita wuta

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce zai je Saudiyya a mako mai zuwa - inda aka tsara jami'an Ukraine da na Amurka za su tattauna kan tsagaita wuta da Rasha.

    Mista Zelensky ya ce gwamnatinsa na aiki cikin hikima domin tabbatuwar zaman lafiya mai ɗorewa a cikin gaggawa.

    Matakin na zuwa ne bayan Donald Trump ya tattauna kai-tsaye da shugaba Rasha, Vladimir Putin da kuma daina bai wa Ukraine bayanan sirri da taimakon soji.

    A gefe guda kuma shugabannin Tarayyar Turai sun alƙawarta mara wa Ukraine baya bayan wani taro da suka gudanar a birnin Brussels na ƙasar Belgium, inda suka alƙawarta ƙara yawan kuɗin da suke kashewa kan tsaro.

    Shugabannin sun kuma amincewa duka cewa Rasha da ƙawarta Belarus na yi wa ƙasashensu barazana.

    Shugaban ƙasar Hungary, Viktor Orban ya jaddada cewa babbau yadda za yi tattaunawar kawo ƙarshen yain Ukraine ba tare da sanya ƙasar a ciki ba.

  3. Majalisar wakilan Najeriya na son a ƙwace ikon yi wa jam'iyyu rajista daga wurin INEC

    Majalisar Wakilan Najeriya ta gabatar da wani ƙudirin da zai ƙwace wa hukumar zaɓen ƙasar ikonta na yi wa jam'iyyun siyasar ƙasar rajista da kula da ƙa'idojin jam'iyyun.

    ƙudurin - wanda kakakin majalisar wakilan ƙasar Hon.Tajudeen Abbas tare da haɗin gwiwar Hon Marcus onobun daga jihar Edo suka gabatar - ya buƙaci a samar da wata hukuma mai zaman kanta da za ta kula da batun yi wa jam'iyyu rajista da kula da ƙa'idojinsu da ɗaukar nauyin jam'iyyun.

    Tuni dai ƙudirin ya wuce karatu na biyu a zauren majalisar.

    Haka kuma ƙudirin ya buƙaci da kafa kotu ta musamman don sauraron ƙorafe-ƙorafen jam'iyyu domin magance rigingimu tsakanin mambobin jam'iyyu.

    Yayin da yake gabatar da ƙudirin, Hon. Onobun ya ce matakin ya zama wajibi, la'akari da yadda ake yawan samun rigingimun tsakanin jam'iyyu da mambobinsu

  4. 'China na cikin matsanancin yanayin kasuwanci'

    Sabbin Alkaluman kasuwanci da China ta fitar na nuna matsanancin yanayi da ƙasar - wadda ita ce ta biyu mafi girman arziki a duniya - ke ciki.

    Shigar da kayayyaki ya ragu da sama da kashi takwas cikin 100 a watan Janairu da Fabarairu idan aka kwatanta da bara, yanayin da ke nuna tafiyar hawaniya a ɓangare masana'anatu.

    Sannan fitar da kayayyakin bai kai yadda aka yi tsammani ba.

    Bayanan na zuwa ne kwana guda, bayan masu hasashe a gwamnati na ganin ƙasar za ta samu haɓɓaka tattalin arziki da kashi biyar cikin 100 a nan gaba a wannan shekara, duk da tarin ƙalubalen da ke tunkarosu.

  5. Trump ya amince da samar da rumbun ajiyar kuɗaɗen kirifto na Amurka

    Shugaba Trump ya sanya hannu kan dokar zatarwa domin samar da kuɗaɗen ajiya na crypto.

    Babban Jami'in da ke kula da harkokin crypto a fadar White House, David Sacks, ya ce za a samar da kuɗaɗen ajiyar ne ta kuɗaɗen da aka ƙwace daga hannun masu aikata laifi da kadarorin da gwamnati ta ƙwato daga hannun mutane.

    A farkon wannan makon ne Mista Trump ya zayyano kuɗaden crypto biyar da ya ce Amurka za ta mayar da hankali a kansu a kuɗaɗenta na ajiya, yanayin da ya ara darajar da tashin kuɗaɗen a kasuwa.

  6. Marabanku

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar ranar Juma'a da Hausawa ke yi wa kirari da Haji babbar rana.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kuna iya zuwa shafukanmu na sada zumunta domin bayyana ra'ayoyinku kanlabaran da muke wallafawa.