Rufewa
Masu bibiyar mu a nan muke sallama da ku, sai kuma gobe Juma'a idan Allah ya kai mu, za mu ci gaba da kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Umar Mika'il da Rabiatu Kabir Runka ke maku fatan alheri.
Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya, 19/12/2024
Usman Minjibir, Aisha Aliyu Ja'afar, Badamasi Abdulkadir Mukhtar
Masu bibiyar mu a nan muke sallama da ku, sai kuma gobe Juma'a idan Allah ya kai mu, za mu ci gaba da kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Umar Mika'il da Rabiatu Kabir Runka ke maku fatan alheri.
Birtaniya da Amurka sun kakabawa manyan jami'an tsaro Georgia takunkumi, saboda amfani da karfi fiye da kima kan mazu zanga-zangar son kasar shiga kungiyar Tarayyar Turai.
Ofishin harkokin wajen Birtaniya ya ce cikin jami'an biyar har da ministan cikin gida da za a haramta masa shiga Birtaniya ko tsoma baki kan harkokin tattalin arziki.
Amurka a na ta bangaren ta sanar da takunkumi kan jami'an Georgia biyu.
Sama da mutane 500 aka cafke a Georgia tun daga lokacin da aka fara zanga-zangar makonni 3 da suka gabata, lokacin da gwamnati ta jingine shirin ta na shiga Tarayyar Turai.
Rahotonni daga jihar Neja a arewacin Najeriya na cewa wasu bama-bamai da suka tashi sun yi sanadiyyar kashe mutum ɗaya da raunata wasu 'yan gida ɗaya.
Jaridu a ƙasar sun ruwaito cewa bam na farko da ya tashi a yau Alhamis a yankin Bassa na ƙaramar hukumar Shiroro ya kashe wani mai suna Dauda Haruna.
Wasu mazauna yankin sun faɗa wa Daily Trust cewa bam ɗin ya tashi daidai lokacin da mutanen huɗu ke kan hanyar zuwa gonarsu kuma ya raunata su.
Mahaifin yaran mai suna Enoch ya faɗa wa jaridar cewa yaran suna kan babur lokacin da lamarin ya faru, yayin da shi da mahaifiyarsu ke tafe a ƙafa.
An garzaya da mutanen zuwa asibitin ƙwararru na IBB da ke binrin Minna domin kula da su.

Asalin hoton, Reuters
Shugaba Putin na Rasha ya ce a shirye ya ke ya rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Volodymyr Zelensky -- amma da sharadin sai an sake zabar shi a matsayin shugaban Ukraine.
A taron da ya ke jagoranta na karshen shekara, Vladimir Putin ya ce ba lallai ne Zalensky ya kasance halastaccen shugaban da ya dace su rattaba hannu kan yarjejeniyar ba, saboda ya na jagorantar kasar ne karkashin dokar shugaban kasa tun bayan karewar wa'adin mulkinsa.
Sai dai Mista Putin bai ce uffan kan sukar da ake yi ma sa kan sake zaben shi na cike da aringizon kuri'u.
Shi ma da ya ke maida martani daga Brussels, Mr Zelensky ya ce Ukraine ba ta amince da duk wani shadari da Rasha ta gindaya ba shekaru biyu da suka gabata lokacin da Kremlin ta yi tayin Kyiv ta yanke sojinta kuma kar ta shiga kungiyar tsaro ta NATO.

Asalin hoton, Bola Tinubu/Facebook
Shugaba Bola Ahmed ya bayyana baƙin cikinsa kan mummunan turmutsutsun da aka samu a wajen taron shekara na al'ada, wanda ya yi sanadiyar mutuwar yaran da basu ji ba ba su gani ba, tare da jikkata wasu da dama.
Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriyar, Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu a yau Alhamis,
Shugaba Tinubu ya miƙa ta'aziyyarsa ga gwamanti da la'ummar jihar Oyo, da kuma iyalan wadanda lamarin ya ritsa da su.
Shugaba Tinubu ya ba hukumomi umarni nan take da a gudanar da bincike domin gano yadda lamarin ya faru, ya kuma umarci gwamnatin jihar Oyo da ta yi duk mai yiyuwa domin ganin wani bau makamancin hakan bai sake faruwa ba.
Ministan harkokin wajen gwamnatin soji ta Myanmar ya ce hukumomin kasar na shirin gudanar da zabe a shekara mai zuwa amma bai fadi takamaimai lokacin ba.
Than Swe ya yi jawabin ne a wani taro da aka gudanar a birnin Bangkok na ƙasar Thailand mai makwabtaka, wanda kasashen China da Indiya da Thailand suka halarta.
Sai dai babu tabbacin ko gwamnatin sojin da gaske take yi kan batun mayar da kasar kan turbar dimukuradiyya.
A baya dai sun sha dage lokacin zaben tun bayan juyin mulkin da suka yi shekara huɗu da suka gabata.
A bangare guda kuma, 'yantawayen da ke goyon bayan mulkin Dimkuradiyya na ci gaba da kai hare-hare a kasar.

Asalin hoton, NASS
Majalisar Wakilan Najeriya ta ce za ta gabatar wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kuɗin da suka tara daga albashinsu domin ba da tasu gudummawar wajen rage wa 'yan Najeriya raɗaɗin tsadar rayuwa.
Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas ne ya bayyana hakan yayin zaman majalaisar a yau Alhamis, yana mai cewa kuɗin sun kai naira miliyan 704.91.
Ya ce za su yi hakan ne a ranar 31 ga watan Disamban 2024. Tun a watan Yuli ne 'yanmajalisar suka yi alƙawarin sadaukar da rabin albashinsu domin taimakawa saboda cire tallafin man fetur.
"Ina farin cikin shaida muku cewa zuwa yanzu mun tara naira N704,907,578.82," in ji Tajudeen.
"A ranar 31 ga watan Disamba, zan jagoranci shugabannin majalisa domin kai wa shugaban ƙasa kuɗin da zimmar yin amfani da su wajen tallafa wa mabuƙata."

Asalin hoton, EPA
Gwamnatin Iraƙi ta ce a yau Alhamis za ta fara mayar da sojojin Syria da suka tsallaka kasar lokacin da 'yan tawayen Hayat Tahrir al-Sham (HTS) suka kaddamar da farmakin hambarar da mulkin Bashar al-Assad a farkon watan nan.
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin da yawansu ya kai kusan 250 za su koma Syria bisa radin kansu bayan gwamnatin riko ta HTS ta sanar da yin afuwa ga sojojin tsohuwar gwamnatin ta Assad.
An shaida musu su mika makaman da suke dauke da su ga hukumomi.
An sha mamaki a lokacin da gwamnatin Iraƙi da mabiya mazhabar Shi'a suka fi yawa a ciki, da kuma ta kasance aminiyar Assad, ta yi saurin nesanta kan ta daga halin da ake ciki a Syriar, jim kadan bayan hambarar da mulkin Assad na shekaru 24.
Ana nuna damuwa kan karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin ƴan tawayen da ke goyon bayan Turkiyya da na ɓangaren Kurdawa da Amurka ke mara wa baya.
Amurkar ta ce sanar da tsawaita yarjkejeniyar zuwa karshen makon nan, amma Turkiyya ta musanta hakan.
Mayakan Kurdawa ma sun yi watsi da sulhun, tare da shan alwashin ci gaba da yakar Turkiyya da kungiyoyin da ta ke goyon baya a Kobani.
A jiya Laraba an kashe sama da 20 cikin mayakan da ke mara wa Turkiyya baya, a taho mu gamar da suka yi da Kurdawa a kusa da garin Manjib da ke arewa maso gabashin birnin Aleppo.

Asalin hoton, Julien Goldstein/Getty Images
Kotu a Faransa ya samu Dominique Pelico da laifin yi wa matarsa, Gisele mummunan fyade, tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari.
Mr Pelico ya shafe fiye da shekara 10 yana shirya yadda maza suke yi wa matarsa, Gisele Pelicot fyaɗe, inda ya riƙa bugar da ita da kayan maye kafin a yi mata fyaɗen.
Kotun ta samu dukkan mutane 51 da ake zargin da aikata fyaɗen da laifi kuma ta yanke masu hukuncin ɗauri a gidan yari na tsawon shekara uku zuwa 15.
Mutane da dama a cikin kotun sun zubar da hawaye a yayin zaman kotun.
Kotun ta ruɗe da ihu da sowar murna a lokacin da alkalin ya sanar da hukuncin, amma Lauyan Dominique Pelico, ya ce za su duba yiwuwar ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
Dukkan sauran mata 50 da suka yi wa matar shi fyade, an yake musu hukuncin zaman kaso tsakanin shekara 3 zuwa 15.

Asalin hoton, AFP
Wata kotu a Guinea ta yanke wa tsohon ministan ƙasar hukuncin zaman shekara biyar a gidan yari saboda laifin rashawa da almubazzaranci da kuɗi.
Mohamed Diane ya riƙe muƙamin minista a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2021 a ƙarƙashin gwamnatin shugaba Alpha Condé, kafin sojoji su ƙwace mulki.
An kuma ci shi tarar $58.5m (£46m) tare da rufe asusun ajiyar sa na banki, da ma wasu ƙaddarorinsa a Conakry da Kankan.
Alƙalin ya ce an ƙwace ƙaddarorin ne saboda babu tabbacin hanyar da aka mallake su.
Tun a watan Mayun 2022 ake tsare da Diane a gidan yari, lokacin da gwamnatin mulkin soji ta ƙaddamar da bincike kan aikata rashawa a ƙasar.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Shugaba Putin ya ce dakarun Rasha sun kama hanyar cimma nasara a yaƙin da suke da Ukraine.
Da ya ke jawabi a wajen taron da ya saba yi kowacce shekara, Mista Putin ya ce dakarunsa suna ci gaba da mamaye muhimman wurare a Ukraine.
Amma bai bayyana haƙiƙanin kusancin da Rasha ta kai ga cimma muradin ta na yaƙin ba.
Shugaban Rashan ya kuma bayyana aniyar sa ta ganawa da Donald Trump a duk lokacin da zaɓabben shugaban Amurkan ya shirya.
Ya kuma yi iƙirarin cewa tattalin arzikin Rasha yana bunƙasa cikin sauri fiye da na Amurka da kuma tarayyar Turai.

Asalin hoton, ALIKO DANGOTE
Matatar mai ta Dangote ta ce ta rage farashin litar man fetir zuwa naira 899.50 gabanin bikin kirsimati da sabuwar shekara.
Kakakin matatar Anthony Chiejina, ya ce an rage farashin litar man ne domin rage tsadar sufuri ga jama'a, a lokacin shagulgulan ƙarshen shekara.
A cikin watan Nuwamba ma, matatar man mai zaman kanta ta rage farashin litar mai zuwa naira 970.
Ya ce “Domin samar da sauƙi kan sufuri a lokacin hutun ƙarshen shekara, matatar mai ta Dangote ta fara sayar da mai a kan ragin farashi. Daga yau za a riƙa sayar da man a kan naira 899.50 a kowacce lita, daga mtatar man tamu.''
Chiejina ya jaddada cewa matatar ta jajirce wajen tabbatar da ganin an samarwa jama'ar Najeriya man fetir mai inganci kuma cikin farashi marar tsada.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Emmanuel Macron ya isa tsibirin Mayotte, yankin da ke ƙarƙashin Faransa da mummunar guguwar Chido ta yi ɓarna.
Mista Macron ya isa Mayotte ne da safiyar yau Alhamis, tare da kayan agaji da suka haɗa da kayan abinci da na kiwon lafiya.
Hukumomin Faransa sun ce mutane aƙalla 31 ne guguwar ta kashe, yayin da wasu dubbai suka ɓace a annobar da ta faɗawa tsibirin a ranar Asabar.
Tuni dai aka ayyana dokar ta ɓaci domin kai agaji Mayotte.
Sanata mai wakiltar Mayotte, Salama Ramia ta shaidawa BBC cewa kai agajin abinci na gaggawa ne abin da suka bai wa fifiko a yanzu.
Ta ce "Ɗaya daga cikin shagunan yankin biyu ya buɗe kuma yana sayar da kayayyaki, amma ba kowa ke da kuɗi ba, kuma shi ma shagon ba zai daɗe ba kayan cikin sa za su ƙare, don haka akwai buƙatar samar da abinci cikin gaggawa."

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni sun ce mayaƙan RSF na Sudan sun kashe mutum 10 a wani hri da suka kai garin al-Fashir a arewacin Darfur, lamarin da ya kai jimilar mutanen da mayaƙan suka kashe zuwa 70 a cikin mako guda.
Hukumomi a al-Fashir sun ce bayan mutane 10 da mayakan RSF suka kashe a harin na ranar 18 ga watan Disamba, a wani asibitin Saudiyya, akwai kuma wasu 20 da suka jikkata.
Sun ce "Kawo yanzu yawan mutanen da suka mutu a hare-haren RSF ya kai 71, kuma wasu gommai sun jikka'' Inji hukumomin.
A bana dai an kai hare-hare da dama asibitin, lamarin da ya janyo asara mai yawa.
Ƙungiyoyin kare ƴancin ɗan Adam sun daɗe suna zargin RSF da yin lugude wauta kan mazaunin fararen hula a al-Fashir, a ƙoƙarin ta na ƙwace iko a yankin.
Ƙungiyar ta musanta wannan zargi.

Asalin hoton, Reuters
Sojojin Isra'ila sun ce jiragen yakinsu sun kai hare-hare ta sama a kasar Yemen.
Kakakin rundunar IDF, Daniel Hagari, ya ce wuraren da aka kai harin, wurare ne da mayakan Houthi da ke samun goyon bayan Iran ke amfani da su wajen gudanar ayyukan soji.
Kafofin yada labarai da ke karkashin ikon kungiyar Houthi sun ce an kai hari kan tashoshin samar da wutar lantarki a Sanaa babban birnin kasar, da kuma wata cibiyar haƙar mai da ke kusa da Hodeida a tekun Bahar Maliya.
Sa'o'i kadan kafin hare-haren, Isra'ila ta dakile wani makami mai linzami da aka harba daga Yemen zuwa birnin Ramat Gan.

Asalin hoton, AFP
Shugaban kungiyar da ke mulkin Syria Ahmed al-Sharaa ya ce ba shi da niyyar mayar da kasar ta zama kamar Afghanistan a ƙarkashin mulkin kungiyar Taliban inda ya ce kashen biyu na da matukar bambanci.
A wata hira da ya yi BBC a Damascus, shugaban kungiyar Hayat Tahrir al Sham ya ce Syria a ƙarƙashin ƙungiyarsa, ba barazana be ce ga duniya, domin haka ya kamata a cire kungiyar daga jerin kungiyoyin ƴan ta'adda.
Ya ce ''Ba mu aikata wani laifi da zai sa a ayyana mu a matsayin kungiyar ta’addanci ba.
''A cikin shekaru 14 da suka gabata ba mu kai hari kan wani yankin fararen hula ba.''
Ya kuma bayyana cewa dukkan al’ummomin da addinai za su samu wakilci a sabuwar gwamnatin da za a kafa kuma ba za a hana mata neman ilimi ba.

Asalin hoton, PDP
Jam'iyyar PDP ta soki kasafin kuɗin da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya gabatar wa majalisar dokokin ƙasar, wanda ta bayyana a matsayin wani abu da ''ba zai yiwu ba'' kuma wanda ''babu gaskiya a ciki''.
Sakataren yaɗa labaran PDP Debo Ologunagba, a cikin wata sanarwa a kan kasafin kuɗin, ya ce kasafin kuɗin ya shafi abubuwan da za su ƙara jefa jama'a cikin ƙangin talauci da kuma matsalar tsaro.
Shugaba Tinubu ya gabatarda kasafin na 2025, na naira tiriliyan 49.7 ga majalisar dokokin Najeriya, inda ya sha alwashin bayar da fifiko ga ɓangaren da samar da ayyukan raya ƙasa da fannin kiwon lafiya da kuma ilimi.
Sai dai jam'iyyar PDP mai adawa a ƙasar ta ce gabatar da kasafin kuɗin ba wani abu bane illa alƙawurran da ba za a iya cikawa ba.
Jma'iyyar adawan da zargi gwamnatin shugaba Tinubu da gazawa wajen samar da muhimman abubuwan more rayuwa ga jama'ar ƙasa.
Barkanmu da safiyar Alhamis daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu riƙa kawo muku labaran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Za kuma ku iya leƙawa shafinmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo, har ma ku tafka muhawara.