Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 05/08/2025

Wannan shafi ne da ke kao muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 05/08/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Nabeela Mukhtar Uba da Abdullahi Bello Diginza

  1. Ƙasashe fiye da 170 na taro kan taƙaita samar da robobi a duniya

    Wakilan ƙasashe sama da 170 na taro a birnin Geneva wanda ake ganin shi ne zagaye na ƙarshe na tattaunawa domin cimma yarjejeniyar taƙaita samar da robobi a duniya.

    Kusan ɗari daga cikin ƙasashen na son taƙaita amfani da roba.

    Sai dai suna fuskantar tirjiya daga ƙasashe masu arzikin mai irinsu Saudiyya da Rasha, wadanda suke son a bi matakan sake sarrafa robobin maimakon taƙaitawa.

    Masu jagorantar tattaunawar na fargabar janyewar Amurka daga ayyukan kare muhalli, kan iya kawo cikas ga ƙoƙarin amincewa da yarejejniyar.

  2. Sojoji sun halaka mayaƙan Boko Haram 17 a Borno

    Sojojin Najeriya da ke aiki ƙarƙashin rundunar Operation Haɗin Kai a yankin arewa maso gabashin ƙsar sun halaka mayaƙan Boko Haram 17 yayin samamen da suka kai a sassan yankunan jihohin Borno da Adamawa.

    Muƙaddashin Darakta a sashen hulɗa da jama'a na rundunar, Kyaptin Reuben Kovangiya, cikin wata sanarwa ya ce mayaƙan sun jima suna cin karensu babu babbaka a ƙananan hukumomin Bama da Konduga da Gwoza da Magumeri da Biu duka a jihar Borno da kuma Michika a jihar Adamawa.

    Daily Trust ta ruwaito jami'in na cewa sojojin sun kuma gano tare da kwance fiye da abubuwan fashewa 14 da ƴan Boko Haram ɗin suka dasa a wurare da dama.

    A cewarsa, abubuwan fashewar da aka dasa domin illata farar hula da sojoji, an yi nasarar kwance su a yayin samamen na jami'an soji.

    Kovangiya ya ƙara da cewa a tsukin lokacin, sojoji sun samu damar maido da fiye da ƴangudunhijira 987 zuwa yankunansu a Mandaragau da ke ƙaramar hukumar Biu.

    Ya ƙara da cewa matakin ya yi daidai da ƙudirin gwamnatin jihar Borno na sake tsugunar da mutanen yankin da kuma dawo da harkokin kasuwanci," in ji shi.

  3. Rwanda ta amince ta karɓi baƙi 250 da Amurka ta kora

    Gwamnatin Rwanda ta ce ta amince ta karɓi baƙin haure kusan 250 daga Amurka.

    A ƙarƙashin yarjejeniyar, da jami'an Rwanda suka amince, za a ba baƙin hauren horo na aiki da kiwon lafiya da kuma tallafin masauki yayin da suka isa ƙasar.

    An bayar da rahoton cewa tuni Amurka ta aika da sunayen farko na mutum 10 domin tantancewa.

    Gwamnatin Trump na ci gaba da tsaurara aniyarta na korar miliyoyin baƙin haure da suka shiga Amurka ba bisa ka'ida ba.

  4. Man Utd da Newcastle sun nace wa Sesko, Rodrygo ba ya son barin Madrid

    Newcastle na shirin sabunta buƙatarta kan ɗanwasan baya na Ingila Marc Guehi inda ta yi sabon tayi na fam miliyan 40, yayin da Crystal Palace ke son fam miliyan 50 kan ɗanwasan mai shekara 25. (Times - subscription required)

    Newcastle da Manchester United na hamayya kan ɗanwasan gaba na RB Leipzig da Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 22. (Bild - in German)

    Kocin Everton David Moyes na son ƙara shiga kasuwa domin ƙara cefanen ƴanwasa shida da suka ƙunshi ƴanwasan tsakiya guda biyu. (Telegraph - subscription required)

    Barcelona ta shaida wa Tottenham cewa sai ta biya fam miliyan 26 kafin ɗauko ɗanwasanta na tsakiya da Spain Marc Casado, mai shekara 21. (Sport - in Spanish)

    Ɗanwasan gaba na Brazil Rodrygo, mai shekara 24, na son ci gaba da taka leda a Real Madrid duk da ribibinsa da Tottenham da Arsenal da Liverpool ke yi. (AS - in Spanish).

    Karanta ƙarin bayani a nan.

  5. Tsoffin jami'an tsaron Isra'ila sun roƙi Trump ya dakatar da yaƙin Gaza

    Wata tawagar jami'an tsaron Isra'ila da suka yi ritaya su 600 ciki har da tsaffin shugabannin hukumomin leƙen asiri sun aika wa Shugaban Amurka, Donald Trump wasiƙa domin neman ya matsa wa Isra'ila da ta gaggauta kawo ƙarshen yaƙin da ake a Gaza.

    Jami'an sun ce "tunaninmu ne cewa Hamas ta daina zama wata barazana ga Isra'ila".

    "Amincin da kake da shi a wajen Isra'ilawa zai ƙara ba ka damar sanya Firaiminista [Benjamin] Netanyahu da gwamnatinsa a kan hanya daidaitacciya: A kawo ƙarshen yaƙin, a dawo da mutanen da ke tsare a kuma daina gallaza wa Falasɗinawa," kamar yadda suka rubuta.

    Roƙon nasu na zuwa ne daidai lokacin da rahotanni ke cewa Netanyahu na ƙoƙarin faɗaɗa ayyukan soji a Gaza yayin da tattaunawar tsagaita wuta da Hamas ke fuskantar cikas.

    Isra'ila ta ƙaddamar da mummuman yaƙi a Gaza sakamakon hare-haren Hamas a Kudancin Isra'ila ranar 7 ga Oktoban 2023 inda aka kashe kusan mutum 1,200 sannan aka yi garkuwa da mutum 251 a Gaza.

    Fiye da mutum 60,000 aka kashe sakamakon yaƙin da Isra'ila ta ƙaddamar a Gaza tun lokacin, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Hamas ta shaida.

  6. Kwamitin sulhu na MDD zai gana kan makomar ƴan Isra'ila da ke hannun Hamas

    Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya zai tattauna yau Talata kan makomar sauran mutanen da ake ci gaba da garkuwa da su a Gaza.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu rahotanni ke cewa Isra'ila na nazarin mamaye yankin Gaza baki ɗaya.

    Wakiliyar BBC ta ce an kira taron na Majalisar Ɗinkin Duniya bayan mayaƙan Falasɗinawa sun fitar da wani bidiyo da ke nuna biyu daga cikin waɗanda suke tsare da su cikin mawuyacin hali.

    Iyalan mutanen sun bayyana damuwa kan bayanan da ke nuna cewa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na shirin mamaye ɗaukacin yankin Gaza ciki har da wuraren da ake tsare da mutanen.

    Sai dai wasu rahotanni na cewa wasu shugabannin sojin Isra'ila sun bayyana adawa da matakin, a yayin da halin jin ƙai a Gaza ya kasance mai matuƙar muni.

  7. Barka da Safiya

    Masu bibiyar mu ta wannan kafa da muke kawo maku wainar da ake toyawa a Najeriya da maƙwabtanta da ma sassan duniya, barka da warhaka.

    Da fatan za ku kasance da mu tun daga yanzu har zuwa lokacin da za mu naɗe tabarma.

    Nabeela Mukhtar Uba tare da sauran abokan aiki ke maku lale maraba.