Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 05/08/2025

Wannan shafi ne da ke kao muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 05/08/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Nabeela Mukhtar Uba da Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Jama'a a nan muka kaw ƙarshen wannan shafin namu na labaran kai-tsaye.

    Sai kuma gobe idan Allah ya nuna mana.

    Mu kwana lafiya.

  2. Gwamnatin Amurka ta fitar da rahoto kan haɗarin jirgin ruwa na Titan

    Jami'an tsaron gabar tekun Amurka sun fitar da wani rahoto mai muni kan mummunar hadarin na jirgin ruwan nan na Titan da ya nitse a lokacin da ya nufi tarkacen jirgin ruwan Titanic da ke karkashin teku a shekarar 2023.

    Ya ce kamfanin jirgin ruwan, Oceangate ya keta dokokin tsaron rayuka, tare da yin watsi da wasu bincike masu muhimmanci.

    Duka mutane biyar da ke cikin jirgin sun mutu nan take a lokacin da jirgin ruwan ya nitse bayan ya kai zurfin kusan kilomita hudu a cikin teku. Iyalan dan kasuwar Birtaniya Shahzada Dawood, wanda ya mutu tare da dansa Suleman, sun ce babu wani rahoto da zai iya shafe bakin cikin da hadrin ya janyo masu

  3. Majalisar Amurka ta gayyaci Clinton kan alaƙa da mai safarar yara

    Wani kwamitin majalisar dokokin Amurka ya bayar da sammaci kan tsohon shugaban kasar Bill Clinton da matarsa, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton.

    Gayyatar na cikin wani bangare na bincike harkokin Jeffrey Epstein wanda aka zarga da laifin safarra kananan yara don a yi lalata da su.

    Suna cikin kusan tsaffin jami'ai goma da aka kira don ba da shaida a gaban kwamitin wanda ya yi fatali da kiran da Donald Trump na yin watsi da bukatar neman karin bayani dangane da shari'ar tsohon dan kasuwar.

    Wakiliyar BBC ta ce sammacin ya shafi jami'ai da dama da suka jagoranci ma'aikatar shari'a a lokacin gwamnatocin Obama da wa'adin Trump na farko da kuma Biden har ila yau ya kuma hada da tsohon darektan FBI James Comey da tsohon lauyan gwamnati Merrick Garland.

    Sammacin ya yi ikirarin cewa Bill Clinton ya shiga jirgin Epstein a lokuta da dama kuma ya taba bayyana shi a matsayin abokinsa na kwarai.

  4. Kwamitin tsaro na MDD ya fara zama kan waɗanda Hamas ke garkuwa da su

    Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya fara zauna domin tattaunawa buƙatar da Isra'ila ta miƙa mata na duba halin da waɗanda Hamas ke garkuwa da su ke ciki a Gaza.

    Kwamitin ya saurara bayanai daga wani mai suna Ilay David, wanda ƴan Hamas ɗin suka yi garkuwa da ɗan'uwansa mai suna Evyyatar a cikin wani hali na tashin hankali a makon jiya, lamarin da ya tayar da hankalin Isra'ilawa da gwamnatin ƙasar.

    Ya ce waɗanda ake garkuwa da su ɗin suna fuskantar barazanar mutuwa saboda wahalar da suke ciki, sannan iyalansu na cikin tashin hankali da rashin tabbas.

    Isra'ila dai na ta ƙoƙarin mayar da hankali kan batun ƴan ƙasarta ɗin da ke hannun Hamas a daidai lokacin da ƙasashen duniya ke matsa mata lamba kan halin da Falasɗinawa ke ciki a Gaza.

  5. Netanyahu ya buƙaci sojoji su kuɓutar da waɗanda Hamas ke garkuwa da su

    Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya shaida wa sojojin da ke wata cibiyar horaswa cewa dole ne a fatattaki Hamas gaba ɗaya domin kuɓutar da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.

    An sa ran Firaministan zai yi wani taron majalisar ministocin ƙasar domin tattauna wani shiri na mamaye zirin Gaza baki ɗaya, sai dai kuma an ɗage shi sakamakon adawar da ya ke fuskanta musamman daga babban hafsan sojin ƙasar Janar Eyal Zamir da kuma iyalan wadanda aka yi garkuwa da su.

    A yayin wata ziyara da ya kai wa sojoji a Gaza Ministan tsaron Isra'ila, Isreal Katz ya tabbatar da cewa sojojin ƙasar za su aiwatar da umarnin gwamnati.

  6. Kotun tsarin mulki ta tabbatar da hana jagoran adawa na Kamaru takara

    Kotun tsarin Mulki ta Kamaru ta yanke hukunci kan cire Maurice Kamto daga zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa ta hanyar yin watsi da ƙarar da ya shigar kan matakin hukumar zaɓen ƙasar na cire shi daga cikin jerin ‘yan takarar.

    Kotun ta fitar da hukuncinta ne a yau, wanda kuma ba za a iya kalubalanata ba.

    Hukumar zaɓen ƙasar ta yanke hukuncin cire Kamto ɗan jam'iyyar MANIDEM saboda ''ƴantakara masu yawa,'' bayan wani ɗan takara daga wani tsagen jam'iyyar ya miƙa buƙatar tsayawa takara, wanda ya sa ake nuna damuwa kan halaccin shugabancin jamiyyar.

    Bayan gabatar da hukuncin, Kamto wanda da alama bai ji daɗin hakan ba, ya fice daga harabar kotun ba tare da magana da ƴan jarida ba.

    Lauyoyinsa waɗanda ba su yi ƙarin bayani kan mataki da za su ɗauka ba, sun ce Kamto mai shekara 71 ne zai bayyana matakin da zai ɗauka.

    A ranar litinin, an ɗan sami wani ɗan rikici tsakanin ƴansanda da mutanen da ke neman shiga harabar kotun domin bibiyar tattaunawar.

    Maurice Kamto, wanda ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2018, ya kasance babban abokin hamayya da zai iya karawa da Shugaba Paul Biya a zaɓen wannan shekara.

    Masu suka na ganin cewa akwai wata maƙarƙashiya ne na kawar da ɗan siyasar daga zaɓen.

  7. Gwamnan Texas ya buƙaci a kama ƴanmajalisar Democrats 50

    Gwamnan jihar Texas, Greg Abbott, ya bayar da umarnin kama ‘yanmajalisar jiha na jam’iyyar Democrat fiye da 50, waɗanda suka fice daga jihar a wani yunƙuri na dakatar da kaɗa ƙuri’a kan sabuwar taswirar majalisar da za ta ƙarfafa goyon bayan ‘yan Republican

    Matakin wanda ya shafi sake tsarin dokokin zaɓe wanda 'yan jam'iyyar Republican a Texas masu rinjaye a majalisar suka ƙaddamar a makon da ya gabata tare da goyon bayan Shugaba Trump, zai samar da sabbin kujeru biyar na Republican a majalisar.

    Wakilin BBC ya ce Gwamna Abbott ya bai wa yansanda umarnin kama su bayan zargin su 'yan majalisar na Democrat da yin watsi da aikinsu.

  8. An kama aku da tsuntsayen kanari 1,600 a Legas da ake ƙoƙarin safarar su

    Hukumar hana fasa-ƙawri ta Najeriya ta ce ta kama tsuntsayen aku da kanari 1,600 a filin jirgin sama na Legas waɗanda ake ƙoƙarin safarar su ba tare da izini ba.

    Hukumar ta ce ta kama tsutsayen ne a ranar 31 ga watan Yuli, a lokacin da ake ƙoƙarin safarar su zuwa Kuwait, kuma shi ne kame mafi girma irinsa da suka yi cikin shekaru.

    Shugaban kula da hana fasa-ƙawri a filin jirnin saman, Micheal Awe, ya ce masu safarar ba su da takardar izini ta CITES da ke nuna cewa sun samo tsuntsayen ne ta hanyar da ta dace.

    Awe ya ce hukumar su na binciken waɗanda ke da hannu a ciki, kuma za a miƙa tsuntsayen ga hukumar kula da gandun daji ta ƙasar.

    Rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya na 2024 kan dabbobi ya bayyana cewa Aku, da wasu tsuntsaye kamar songbird na daga cikin tsuntsayen da aka fi safarar su domin yin kasuwancin su ga masu siya su ajiye a gida ko kuma masu siyan fukafukinsu.

  9. Ana ci gaba da aikin ceto bayan ambaliyar ruwa a Indiya

    Ana ci gaba da aikin ceto a jihar Uttarakhand da ke arewacin Indiya bayan da wata ambaliyar ruwa ta mamaye wani ƙauye.

    Rahotannin sun ce aƙalla mutane huɗu ne suka mutu sannan wasu da dama suka ɓace.

    Ambaliyar dai ta auku ne a ƙauyen Dharali, da ke yankin tsaunukan Himalayas.

    Wakiliyar BBC ta ce wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda ruwa ke kwarara daga saman wani tudu inda ya mamaye gine-gine a ƙauyen.

    Babban Ministan jihar Uttarakhand (Pushkar Singh Dhami) ya ce hukumomin na aiki tuƙuru domin gano waɗanda suka ɓace.

    Yankin tsaunukan Himalayas yana fuskantar ƙarin ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasa, wanda wasu masana ke alaƙantawa da sauyin yanayi.

  10. Ƴanbindiga sun sace mutum 150 cikin kwana huɗu a Zamfara

    Rahotonnin daga jihar Zamfara a yankin arewa maso yammcin Najeriya na cewa ƴanbindiga sun sace mutum 150 a jerin hare-haren da suka kai wasu garuruwan jihar cikin kwanaki huɗu da suka gabata.

    Kakakin gwamnatin jihar Zamfara, Mahmud Mohammed Dantawasa ya tabbatar wa da BBC kai hare-haren, kodayake bai yarda ko musanta adadin ba, sai dai ya ce gwamnati na ƙoƙarin kuɓutar da mutanen.

    Mazauna garuruwan sun ce ƴanbindigar ɗauke da muggan makamai sun kai jerin hare-hare cikin kwana huɗu a ƙauyukan Sabon Garin Damri da Dakko Butsa (da ke iyaka da Sokoto), da Tungar Abdu Dogo da Tungar Sarkin Daji da Sadeda kuma Tungar Labi.

    Ƴanbindigar na bin dare ko lokacin ruwan sama domin auka wa ƙauyukan a lokacin da mutane ke tsaka da barci.

    Bayanai sun ce rashin kyawun titunan jihar na taimaka wa ƴanbindigar, inda jami'an tsaro ke fuskantar ƙalubale wajen zuwa wuraren da ƴanbindigar ke cin karensu babu babbaka a kan lokaci.

  11. MDD ta yi gargaɗi kan matsananciyar yunwa a Sudan

    Hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutanen da suka kwashe sama da shekara guda suna maƙale a birnin El Fasher suna fuskantar matsananciyar yunwa, yayin da babu wata alamar kawo ƙarshen ƙawanyar da dakarun RSF suka yi wa birnin.

    Kungiyar RSF ta yi ƙoƙarin ƙwace birnin na yankin Darfur daga hannun sojojin Sudan, kuma ta yi masa ƙawanya tun a watan Afrilun shekarar da ta gabata, inda ta hana dubban mutane samun kayayyain agaji.

    Wakiliyar BBC ta ce shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗin cewa mazauna yankin na fuskantar yunwa bayan da ƙungiyar RSF ta kwashe fiye da shekara guda tana kewaye da birnin.

    Shirin dai ya ce sojojin Sudan sun bayar da izinin shigar da ayarin motocin agaji cikin birnin, amma har yanzu ba a ji komai daga ɓangaren RSF ba.

  12. Gwamnati za ta soke kuɗin makarantar nazare a China

    Gwamnatin China ta ce za ta janye kuɗin makaranta na ɗaliban da ke ajin ƙarshe a makarantun nazare a wani ɓangare na ƙara karkato da hankalin iyaye a ƙasar su ƙara haihuwa.

    China dai tana fama da raguwar haihuwa.

    Ƙwararru sun zargin cewa tsadar kuɗin kula da yara da na ilimi da kuma rashin samun ayyukan yi na bayar da gudummawa a matsalar rashin haihuwa a China.

    A makon da ya gabata ne, gwamnati ta ɓullo da tsarin bai wa yara ƴan ƙasa da shekara uku tallafi.

  13. An kama ƴan'uwa da kitsa garkuwar ƙarya don karɓar kuɗi a wajen mahaifinsu

    Rundunar ƴansandan Najeriya, reshen Abuja, babban birnin ƙasar ta cafke mutum huɗu kan zargin shirya garkuwar ƙarya don karɓar naira miliyan biyar a hannun wani dattijo wanda ƴaƴansa mata da wasu suka kitsa.

    Cikin wata sanar wa da kakakin rundunar ƴansanda Abuja, SP Josephine Adeh ta fitar ta ce wani Mista Innocent ne ya kai ƙarar ɓacewar ƴarsa mai shekara 16 da ta bar gida a ranar 18 ga Yulin 2025 don zuwa rubuta jarabawa a makarantar sakandare ta gwamnati da ke Karu.

    Daga bisani kuma, a cewarsa, ya samu kiran waya daga wasu mutane suna neman da ya biya kuɗin fansa don su sake ta.

    Bayan samun labarin ne kuma, jami'in ɗansanda mai muƙamin DPO a ofishin ƴansanda na Jikwoyi ya gaggauta ƙaddamar da bincike kan lamarin inda kuma aka bibiyar lambar wayar da aka kira mahaifin matashiyar har aka gano waɗanda suka kira na zaune a wani gida da ke yankin na Jikwoyi Phase II.

    ''Daga nan ne kuma ƴansanda suka je gidan inda suka gano matashiyar tare da mai ɗakin wani Mayowa Adedeji'', kamar yadda sanarwar ta yi karsin haske.

    SP Adeh ta kuma ce an ga mutanen biyu suna cin abinci suna kuma tattaunawa, abin da ke nuna babu wata alama ta damuwa tattare da ita.

    ''Binciken da aka ƙara gudanarwa kuma ya kai ga cafke babbar yar matashiyar da saurayinta'', in ji ta.

    An dai gano yayar ta haɗa baki da saurayinta wajen shirya garkuwar ƙaryar da suka yi wa ƙanwarta da burin su karɓi kuɗi kimanin naira miliyan biyar daga hannun mahaifinsu.

    Ƙarin binciken da aka yi ya bayyana cewa matashiyar da aka yi garkuwar da ita, tana da masaniyar abin da aka shirya kuma ta amince za ta zauna a gidan waɗanda ake zargi yayin da kuma yayarta za ta ci gaba da zama a gidan mahaifinsu inda za ta nuna ba ta da masaniyar abin da ke faruwa.

    Rundunar ta ce duka mutanen huɗu da ake zargi suna hannun ƴansanda kuma sun bayyana cewa suna da hannu a lamarin.

    Za dai a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.

  14. Zanga-zanga ta ɓarke a China saboda cin zalin wata ɗaliba

    Zanga-zanga ta ɓarke a kudancin China sakamakon cin zarafin wata ɗaliba ƴar shekara 14 inda mutane ke ta neman a yi mata adalci.

    A makon da ya gabata ne wani bidiyo da a ciki wasu sa'annin yarinyar suke zabga mata mari da kuma tilasta mata tsayawa kan gwiwoyinta ya karaɗe shafukan sada zumunta a birnin Jiangyou da ke Lardin Sichuan.

    Ƴansanda sun ce yaran da ake zargi da cin zarafin ɗalibar - dukkansu mata ne ƴan shekara 13 da 14 da kuma 15, kuma an tura biyu daga cikinsu makarantu na musamman domin gyara masu tarbiyya.

    Bayan da labarin yarinyar ya bazu a shafukan sada zumunta, wasu da dama na ganin an yi sassauci a matakin da aka ɗauka kan waɗanda ake zargi - musamman bayan iƙirarin da ke nuna cewa an ɗaɗe ana cin zarafin yarinyar kuma mahaifiyarta, wadda kurma ce, ta roƙi hukumomi su yi wa ɗiyarta adalci.

    Lamarin dai ya fusata mutane da dama har ma zanga-zanga ta ɓarke a wajen ofisoshin ƙaramar hukumar dake Jiangyou.

    Fiye da mutum 1,000 ne suka taru kan titi jiya Litinin inda suka kai har tsakaddare a wajen, kamar yadda masu shaguna da ke wurin suka bayyana.

    Ɗaya daga cikinsu ya shaida wa BBC cewa "lamarin ya ƙazanta" bayan da ƴansanda suka tarwatsa mutanen da suka taru.

  15. Ko Trump da Putin sun raba gari ne?

    Alamu na nuna akwai yiwuwar shugaban Amurka, Donald Trump da Vladimir Putin sun raba gari kamar yadda wata fitacciyar jaridar ƙasar Rasha, Moskovsky Komsomolets take hasashe.

    Jaridar ta nuna cewa shugabannin guda biyu da ta kwatanta da jiragen ƙasa waɗanda babu makawa za su yi taho-mu-gama domin babu ɗayansu da ke shirin kaucewa ɗayan ko ya tsaya masa.

    Jaridar ta ce shi Putin ya kasance mutumin da ya ƙuduri niyyar cigaba da yaƙin da yake yi a Ukraine na tsawon lokaci kasancewar yana taƙama da ƙarfin soji.

    A ɗaya hannu kuma shi Trump na ƙara matsa wa Rasha lamba wajen ganin ta kawo ƙarshen yaƙin inda yake ƙara barazanar sanya wa Rashar takunkumai da ma wasu ƙasashe ƙawayen Rashar kamar China da India.

    Haka kuma a ƙarshen makon da ya gabata ne shugaban na Amurka ya bayar da umarnin jibge jiragen yaƙi na ruwa a kusa da Rasha.

    Abin da ya shigarwa jama’a duhu yanzu shi ne yadda ake ƙoƙarin yi wa juna barazanar yaƙi a daidai lokacin da jakada na musamman na shugaban Amurka, Steve Witkof ya kai ziyara Moscow.

  16. 'Burina na zama injiniya ya daƙushe saboda jinyar mahaifina'

    Umar Harun, yaro mai shekara 16 a Kaduna da ke Najeriya ya zaɓi yin sana'ar jari-bola domin taimaka wa iyalinsa da abin da za su ci.

    Umar ya ce tun da asubahi yake fita tare da abokan sana'ar tasa domin shafe tsawon kilomitoci wajen neman ƙarafuna a gefen titi domin ya rufawa kansa da iyayensa asiri.

    Ya ce da wannan kuɗi ne muka cin abinci da sauran bubuwan buƙatun rayuwa.

    ''Sai mun fita mun samo sannan ake samun abin da ake dafawa a gidanmu, duk ranar da ban fita wannan sana'a ba, to ba za a ci komai ba a gidanmu'', in ji shi.

    Yaron ya ce mahaifinsa ya shefe fiye da shekara 10 yana fama da jinya, haka ma babban yayansa, don haka dole ɗawainiyar gidan ta koma kansa.

    ''Ƙannena su yara ne abin da nake kawowa idan yayi saura da shi ake biya musu kudin makarantar islamiyya, kodayake ta boko ma ta gwamnati suke zuwa'', in ji Umar.

    Yaron ya ƙara da cewa h alin da gidansu ke ciki ne ya sa ya haƙura da karatu ya koma nema wa iyalinsa abin da za su ci su kuma biya sauran buƙatun rayuwa.

    Umar ya ce a duk lokacin da ya fita sana'arsa ya kuma ci karo da yaran da ke zuwa makaranta sai ya ji yana sha'awar hakan, inda zuciyarsa ke cike da burin watarana shi ma ya samu ya koma makaranta.

    ''Bana jin daɗi a zuciyata idan na ga abokaina suna zuwa makaranta ni kuma babu halin hakan'', in ji shi.

    ''A halin yanzu idan na ce zan koma makaranta to za mu rasa abin da za mu ci a gidanmu''.

    Umar ya ce ya kafin ɗawainiyar gidansu ta hau kansa ya samu kammala makaratar Firamare.

    Ya ƙara da cewa idan da zai samu dama zai koma makaranta, domin cika burinsa na kammala digiri domin zama babban injiniya.

  17. Isra'ilawa sun soki ƙudirin Netanyahu na son mamaye Gaza

    Ƴan'uwan Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su a Gaza sun bayyana fushinsu kan rahotannin da ke cewa Firaiminista Benjamin Netanyahu na son sojoji su mamaye gaba ɗaya yankin har da wuraren da waɗanda ke tsaren suke.

    Hukumar Falasɗinawa ita ma ta yi tur da rahoton wanda zuwa yanzu ba a tabbatar da shi ba.

    Rahotannin da aka samu zuwa safiyar yau Talata sun nuna cewa aƙalla Falasɗinawa 12 aka kashe a sabbin hare-haren da Isra'ila ta kai har da mutum uku da suka jiran abinci kusa da Rafah a kudancin zirin.

    A jiya Litinin, rahotanni sun bayyana kisan mutane da dama.

  18. Kotu za ta yanke hukunci kan makomar takarar Kamto a babban zaɓen Kamaru

    A yau Talata ne Kotun Tsarin mulki a Kamaru za ta yanke hukunci kan ƙarar da jagoran ƴan hamayyar ƙasar, Maurice Kamto ya shigar na ƙalubalantar matakin soke damarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a watan Oktoba.

    Shi ne mutumin da ya zo na biyu a zaɓen 2018 da aka gudanar kuma ana ganinsa a matsayin babban abokin karawar shugaba Paul Biya mai shekara 92 wanda ya shafe shekaru arba'in yana mulki.

    Hukumar zaɓen Kamaru ta ce jam'iyyar Mista Kamto ta MANIDEM ta gabatar da ƴan takara biyu da za su yi mata takara ba bisa ƙa'ida ba.

    Lokacin da jagororin jam'iyyar suka yi ƙoƙarin gudanar da taron manema labarai domin musanta hakan, sai jami'an tsaro suka hana su.

  19. Ƴan Bangladesh na taron cika shekara guda da kifar da mulkin Sheikh Hasina

    Dubban mutane na hallara a Dhaka, babban birnin Bangladesh domin yin gangami da bukukuwa da kuma taron addu'oi na cika shekara ɗaya da hamɓarar da gwamnatin tsohuwar Firaiminista Sheikh Hasina sakamakon gagarumar zanga-zanga da ɗalibai suka gudanar.

    Gaba a yau ne Shugaba mai riƙon ƙwarya, Muhammad Yunus zai bayyana abin da ya kira taswirar samar da sauye-sauye a dimokraɗiyya.

    Dakta Yunus ya ce masu mulkin kama-karya da aka hamɓarar da masu mara masu baya, har yanzu suna haɗa baki kan yadda za su daƙile ci gaban Bangladesh.

    Ya ƙara da cewa ya zama tilas a kare damar samar da sauye-sauye a ƙasar ta kowane hali.

  20. Manufofin Tinubu sun ƙara jefa miliyoyin ƴan Najeriya cikin talauci - Falana

    Fitaccen lauyan nan a Najeriya mai kare haƙƙin bil adama, Femi Falana ya caccaki manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu inda ya ce "manufofin masu tsauri" sun shafe masu matsakaicin samu tare da ƙara jefa miliyoyin mutanen ƙasar cikin talauci.

    Falana ya ce duk da cewa a baya-bayan nan shugaban ƙasar ya fito ya bayyana cewa ya san irin halin ƙunci da ƴan Najeriya ke ciki, manufofinsa sun ƙara talauta al'umma.

    Lauyan mai muƙamin SAN ya shaida hakan ne a hirar da ya yi a gidan Talabijin na Channels inda kuma ya ga baiken yadda gwamnati ke cefanar da kamfanoni ga ƴan kasuwa lamarin da a cewarsa ya ci karo da ƙoƙarin da ake na magance bambancin samu a tsakanin ƴan Najeriya.

    Ya ƙara da cewa ya zama dole gwamnati ta sake nazari kan manufofinta tare da samar da tallafi ga ƴan Najeriya masu rauni musamman waɗanda suke yankunan karkara.

    Lauyan ya bayyana cewa galibin ƴan Najeriya a yanzu ba sa iya cin abinci sau uku a rana.

    "Dole gwamnati ta sake yin nazari kan waɗannan manufofin musamman waɗanda Bankin Duniya da Asusun ba da lamuni na duniya suka bijiro da su, domin ci gaban ƴan Najeriya. Ya kamata gwamnati ta sake nazarin waɗannan manufofin ba tare da ɓata lokaci ba." in ji shi.

    Tun bayan da ya hau karagar mulki a Mayun 2023, Tinubu ya sanar da wasu manufofin tattalin arziki ciki har da cire tallafin mai da barin kasuwa ta tsaida farashin naira.

    Janye tallafin man dai ya janyo hauhawar farashin man abin da ya ƙara ta'azzara yanayin talauci da kuma ƙaruwar farashin sufuri har ma da hauhawar farashin kayan masarufi.