Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya, Lahadi, 23/02/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sassan duniya kai tsaye, Lahadi, 23/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad da Isiyaku Muhammed

  1. Ƙasashen Sahel sun ƙaddamar da tutar ƙawance

    AES

    Asalin hoton, Burkina Faso Presidency

    Gamayyar ƙasashen Sahel da suka haɗa da Mali da Burkina Faso da Nijar sun ƙaddamar da tutar ƙawancen ƙasashen a birnin Bamako na Mali.

    Wannan matakin ya biyo bayan amincewar da shugabannin ƙasashen ƙungiyar suka yi a ranar 22 ga watan Fabrairu.

    An gabatar da tutar ce a wajen wani taro na ministocin ƙungiyar da aka kammala a yau Lahadi 23 ga wannan wata da muke cikin.

    Ministocin na AES ne suka ƙaddamar da tutar mai launin kore da kuma tambarin ƙungiyar a tsakiyarta.

  2. Zan iya haƙura da shugabancin Ukraine domin a samar da zaman lafiya - Zelensky

    Ukraine

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce a shirye yake ya haƙura da kujerar shugabancin ƙasar idan haka ne zai zama silar samar da zaman lafiya a ƙasarsa.

    Zelensky ya bayyana haka ne a daidai lokacin da aka cika shekara uku ana gwabza yaƙi tsakanin Ukraine da Rasha.

    "Idan kuna so in sauka daga mulki, zan amince. Amma ina so ƙasata ta shiga ƙungiyar Nato," in ji shi a lokacin da yake amsa tambayoyi a wani taron manema labarai.

    Wannan jawabin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya kira shi da "mai kama-karyar mulki ba tare da zaɓe ba."

    "Maganarsa ba ta ɓata min tai ba," in ji Zelensky wanda aka zaɓa a watan Mayun shekarar 2029.

    Zelensky ya ƙara da cewa tabbatar da zaman lafiyae ƙasar ne a gaban shi, amma ba ya tunanin daɗewa a mulkin ƙasar.

    Majalisar Ukraine ce ta dai yi dokar hana zaɓe a ƙasar tun bayan da Rasha ta faɗa mata da yaƙi a watan Fabrairun 2022.

    Shugabannin ƙasashen turai da na wasu ƙasashen za su yi taro a birnin Kyiv na Ukraine domin nuna goyon baya, tare da haɗin kansu ga ƙasar.

  3. Wanda ake kyautata zaton zai zama shugaban Jamus ya yaba da zaɓen ƙasar

    Jamus

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutumin da ake kyautata zaton zai zama shugaban gwamnatin Jamus na gaba ya yaba da nasarar da jam'iyyarsa take samu a zaɓen ƴan majalisar dokokin ƙasar.

    Friedrich Merz ya buƙaci a gaggauta kafa gwamnati, bayan ƙuri'ar jin ra'ayin jam'a ya nuna jam'iyyarsa ta Christian Democrats da ƙawarta ta Bavaria ke kan gaba da kusan kashi 29 cikin ɗari.

    Ƙuri'ar ta nuna cewa jam'iyyar Alternative for Germany a matsayin ta biyu, da kaso mafi girma na ƙuri'u da ta taɓa samu a zaɓen ƙasar, inda take da kusan kashi 20 cikin 100.

    Da alama za ta doke jam'iyyu biyu da ke cikin ƙawancen marasa rinjaye a halin yanzu --Jam'iyyar shugaban gwamnati Olaf Scholz ta Social Democrats da Jam'iyyar Greens.

    An samu fitowar jama'a da dama da suka kaɗa ƙuri'a a zaɓen, bayan yaƙin neman zaɓe da ya janyo rarrabuwar kawunan al'umma a ƙasar.

  4. Gwamnatin Sudan ta ce ta ƙwace iko da birnin El-Obeid

    Sudan

    Asalin hoton, AFP

    Sojojin Sudan sun ce sun kawo ƙarshen farmakin da dakarun RSF suka yi na kusan shekara biyu a Birnin El-Obeid, hedkwatar lardin Kordofan ta Arewa.

    An ga sojojin gwamnati suna murna bayan buɗe babbar hanyar shiga birnin, wanda aka fara kai wa hari tun bayan da yaƙin basasa ya ɓarke wata 22 da suka gabata.

    Wakilin BBC ya ce manazarta dai na ganin wannan farmaki a matsayin gagarumar nasara ga sojojin ƙasar da ke ci gaba da samun galaba a cikin ƴan makonnin nan.

    Rikicin dai ya raba ƙasar Sudan biyu, inda sojoji ke riƙe da yankunan arewaci da gabashin ƙasar, sannan ƙungiyar RSF ce ke riƙe da mafi yawan yankunan Darfur da kuma wasu sassan kudancin ƙasar.

  5. Gwamnatin jihar Sokoto ta fara biyan malaman firamare mafi ƙanƙantar albashi

    Sokoto

    Asalin hoton, Others

    Makonni uku bayan wani rahoton da BBC ta yi game da ƙorafin da malaman makarantun firamaren jihar Sokoto suka yi na rashin biyansu sabon albashi mafi ƙanƙanta na naira 70,000, gwamnatin jihar ta biya su, har ma da yi musu ƙari.

    Malaman makarantun firamaren sun shaida wa BBC irin farin cikin da suka ji game da alƙawarin da gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya cika, na biyansu sabon albashin kamar kowa tare da sauran ma’aikatan gwamnatin jihar da suka hada da na kananan hukumomi 23.

    Mai magana da yawun gwamnan jihar, Abubakar Bawa, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin ta saurari ƙorafin da ma’aikatan suka yi ne, shi ya sa ta cika alƙawarin da ta ɗaukar musu tun da farko.

    A watan Yulin shekarar 2024 ne, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da ƙara albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikatan ƙasar daga naira 30,000 zuwa 70,000.

  6. Wane ne Aristotle shahararren masanin falsafa na duniya?

    Aristotle

    Asalin hoton, Getty Images

    Shin a iya cewa Aristotle ne mutumin da ya fi tasiri da aka taɓa gani a doron ƙasa? Wani fitaccen malamin falsafa ɗan Birtaniya, John Sellars na ganin haka.

    Ya ce ana iya ganin tasirin masanin falsafar ɗan asalin Girka a fagage da dama da irin yadda ya taimaka da tunaninsa a fannoni daban-daban na rayuwa.

    Kama daga fagen siyasa da kimiyya, rubuce-rubuce zuwa tunani da dabaru, ana iya ganin tasirin Aristotle a ko'ina.

    Ya yi nazarin ilimin halittun cikin ruwa, wani abu da ya haifar da ilimin 'Biology'.

  7. Isra'ila za ta tura ƙarin sojoji yankin Jenin na Falasɗinawa

  8. Ɗan arewacin Najeriya da ya shiga kundin Guinness saboda ɗaukar hoto

  9. Minista ya yi barazanar barin APC idan ba a sauya shugabancinta na Kano ba

  10. Mutum huɗu sun mutu goma sun ji rauni a wata motar bas da ta ƙone a jihar Jigawa

  11. Ƙungiyar RSF ta ƙulla yarjejeniyar kafa kishiyar gwamnati a Sudan

  12. Afirka ta Kudu ta sake faɗawa matsalar ƙarancin wutar lantarki

  13. Isra'ila ta kai hare-hare Lebanon sa'o'i kafin jana'izar shugaban Hezbollah, Nasrallah

  14. An kashe mutum ɗaya da raunata 'yansanda a harin wuƙa a Faransa

  15. Hamas ta zargi Isra'ila da neman gurgunta yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta da gangan

  16. Ana zaɓe mai zafi a Jamus wanda ya ɗauki hankalin Turai da Amurka