Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 13/10/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 13/10/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Labarai da dumi-dumi, Isra'ila ta fara sakin fursunonin Falasɗinawa daga gidajen yarinta

    Isra'ila ta fara sakin fursunonin Falasɗinawa da ke tsare a gidajen yarinta bayan da Hamas ta kammala sakin duka Isra'ila masu rai da ke hannunta.

    Rukunin Farko na manyan motoci 38 ɗauke da fursunonin ya isa Ramallah da ke Gaɓar Yamma.

    Ana sa ran sakin Falasɗinawa kusan 2,000 daga gidajen yarin Isra'ila, kamar yadda yarjejeniyar ta tanada

  2. Wani ɗan Isra'ila da Hamas ta saki yau ya haɗu da matarsa

    Omri Miran, mai shekara 48, ya gana da matarsa Lishay a wurin da ake keɓe za su gana da ƴan'uwansu a kudancin Isra'ila.

    An yi garkuwa da Omri daga gidansa da ke Nahal Oz ranar 7 ga watan Oktoba.

    Lishay ta ce gani na ƙarshe da ta yi masa shi ne lokacin da aka kama shi a cikin motarsa.

    A watan Afrilun 2025 ne Hamas ta fitar da wani bidiyon Omri lokacin da ya cika shekara 48.

    Lishay ta bayyana cewa dama tana cike da fatan cewa mijinta a nan da ransa.

  3. Isra'ila ta bayyana sunayen Isra'ilawa 13 da Hamas ta saki a rukuni na biyu

    Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta wallafa sunayen ƴan ƙasar 13 da Hamas ta saki a rukuni na biyu da suka haɗa da:

    • Elkana Bohbot
    • Avinatan Or
    • Yosef-Chaim Ohana
    • Evyatar David
    • Rom Braslabski
    • Segev Kalfon
    • Maxim Herkin
    • Bar Kupershtein
    • Eitan Horn
    • Ariel Cunio
    • David Cunio
    • Matan Zangauker
    • Nimrod Cohen

    An sake su ne bayan mutum bakwai da aka fara saki yau da safe a Gaza.

    Ya zuwa yanzu an saki duka ragowar Isra'ilawa 20 masu rai da suka rage a hannun Hamas.

  4. Madagascar ta yi Allah-wadai da barazanar da ake yi wa shugaban ƙasar

    Fadar shugaban ƙasar Madagascar ta yi Allah-wadai da abin da ta kira barazanar da ake yi wa shugaban ƙasar Andry Rajoelina.

    Cikin wata sanarwar da fadar ta wallafa a shafinta na Facebook ta kira hakan cin zarafin dimokuraɗiyya tare da gargaɗin cewa za a ɗauki matakin doka kan masu hannu a ciki.

    Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da tashin hankali bayan wasu sashen manyan sojoj sun yi fatali da gwamnati, tare da shiga zanga-zangar matasa kan wahalar tattalin arziki da rashin shugabanci nagari.

    Sanarwar ta ce: “Shugaban ƙasa bai taɓa bayyana wata niyyar tsayawa takara ko sauya tsarin mulki ba; barazana ga lafiyarsa ta wuce gona da iri, kuma ba za a lamunta da hakan ba.”

    Rundunar da ta yi tawaye wato Capsat wacce ke da alaƙa da hawan Rajoelina mulki a 2009, ta bayyana cewa ita ce ke da iko kan dakarun soji, abin da fadar shugaban ƙasa ta kira yunƙurin juyin mulki.

    Ɓangaren Capsat ɗin ya sanar da naɗin Janar Demosthene Pikulas a matsayin sabon shugaban rundunar soji a ranar Laraba, abin da ake cewa ministan tsaro ya amince da shi lamarin da ya ƙara rura wutar rikicin cikin sojoji.

    Har zuwa safiyar yau, ba a san inda shugaban ƙasa Rajoelina yake ba, abin da ya ƙara haifar da zargi kan tsaronsa

  5. 'Asibitin Gaza na jiran Falasdinawan da Isra'ila za ta sako daga gidajen yari'

    Tawagar likitoci a asibitin Gaza sun kammala shirin karɓar fursunonin Falasɗinawa da za a sako daga gidajen yarin Isra'ila, domin duba lafiyarsu, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Hamas ta bayyana

    Ma'aikatar ta ƙara da cewa za a samar da wurin kula da mutanen a asibitin Nasser Hospital da ke Gaza.

    Ana sa ran sako Falasɗinawa kusan 2,000 daga gidajen yarin Isra'ila.

  6. Ana jiran Isra'ila ta fara sakin Falasɗinawa daga gidajen yarinta

    Yayin da Hamas ta kammala sakin duka ISra'ilawa masu rai da take garkuwa da su, a yanzu hanakula sun koma Isra'ila domin fara sakin fursunonin Falasɗinawa da ke tsare a gidajen yarinta, kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.

    Falasɗinawa da ake sa ran saki sun haɗa da mutum 250 da ke zaman hukuncin ɗaurin rai da rai da masu dogon ɗauri, da kuma mutum 1,700 ƴan Gaza da ake tsare da su, da suka haɗa da yara 22.

    Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce yanzu haka an shirya fursunonin domin sako su daga giudan yarin Ofer da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

  7. Labarai da dumi-dumi, An saki duka Isra'ilawa masu rai da ake garkuwa da su - Hamas

    Ƙungiyar Hamas ta ce ta saki duka Isra'ilawa masu rai da take garkuwa da su a Gaza.

    Nan gaba ne za a bayar da duka gawarwakin Isra'ilawan da ke hannun ƙungiyar, a cewar Hamas.

    Dama dai an tsara cewa a yau ne za a saki duka ragowar Isra'ilawa 20 masu rai da ke hannun Hamas da kuma gawarwaki 28.

  8. Trump ya isa Majalaisar Dokokin Isra'ila

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya isa zauren Majalisar Dokokin Isra'ila, inda ake sa ran zai yi jawabi ga majalisar.

    Trump ne shugaban Amurka na huɗu da ya yi wa majalisar jawabi tun bayan kafa a 1949 - kuma na farko tun 2008.

    Kakakin Majalisar Amir Ohana ya tarbi shugaban tae da yi masa maraba lale.

  9. 'Ƙarin ƙananan hukumomin Katsina uku sun yi sulhu da ƴanbindiga'

    Ƙananan hukumomin Malumfashi da Funtua da Bakori sun bi sahun wasu takwarorinsu da suka yi sulhu da ƴanbindigar a jihar da ke fama da matsalar tsaro.

    Jihar Katsina na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar ƴanbindiga masu kai hare-hare a ƙauyuka da garuruwan jihar da kashe mutane da sace wasu domin neman kuɗin fansa.

    An gudanar da zaman sulhun ne a garin Kakumi da ke yankin ƙaramar hukumar Bakori, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta bayyana.

    Taron sulhun ya samu halartar shugabannin alumomin yankunan da wakilan ƴanbindigar.

    A baya-bayan nan ana ta samun ƙaruwar ƙananan hukumomin Katsina a ke rungumar sulhu a wani mataki na magance matsalar tsaron jihar.

  10. Labarai da dumi-dumi, 'Hamas ta ƙara sakin Isra'ilawa 13'

    Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce Hamas ta saki rukuni na biyu na Isra'ila 13 da take garkuwa da su a Gaza.

    Ƙungiyar ta miƙa mutanen ne ga ƙungiyar Agaji da Red Cross a kudancin Gaza, wadda ta ɗauke su zuwa Isra'ila.

  11. Isra'ilawa bakwai da Hamas ta fara saki

    Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta wallafa sunayen mutum bakwai da Hamas ta saki a safiyar yau.

    Mutanen sun haɗa da:

    • Eitan Mor
    • Gali Berman
    • Ziv Berman
    • Omri Miran
    • Alon Ohel
    • Guy Gilboa-Dalal
    • Matan Angrest
  12. Trump ya sauka a Isra'ila

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sauka a Isra'ila yayin da ake ci gaba da sakin Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su.

    Jirgin Trump ya sauka a filin jirgin saman Ben Gurion da ke wajen birnin Tel Aviv, yayin da ya fara wata ziyara zuwa yankin Gabas ta Tsakiya domin sanya hannu a hukumance kan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

    Ƙusoshin gwamnatin isra'la da dama ne suka taru a filin jirgin domin tarbarsa - ciki har da Firaminista benjamin Netanyahu da matarsa Sara Netanyahu.

    Haka akwai wakilan Amurka da yanzu haka ke ƙasar, da suka haɗa da jakadan Amurka na musamman, Steve Witkoff da mai bai wa Trump Shawara Jared Kushner da matarsa Ivanka Trump.

  13. Hamas ta fara sakin Isra'ilawan da take garkuwa da su

    Ƙungiyar Hamas fara sakin Isra'ilawan da take garkuwa da su a Gaza a wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Gaza.

    Hamas ta miƙa rukunin farko na waɗanda take garkuwar da su (su bakwai) ga ƙungiyar agaji da Red Cross wadda ke shiga tsakani a musayar fursunonin.

    Yarjejeniyar tsagaita wutar ta tanadi cewa za a saki duka Isra'ilawan 48 da ake garkuwa da su a Gaza, rayayyu da matattu.

    Nan gaba kaɗan ne Isra'ila za ta saki Falasɗinawa kusan 2,000 da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila.

  14. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin, Mande tushen aiki ko da nasara na tsoranki, kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.