Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/10/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Umar Mikail

  1. Ƙarshen labarai

    Mun zo ƙarshen rahotonni kai-tsaye a wannan shafi na ranar Lahadi.

    Ku sake leƙo mu gobe da safe domin karanta wasu sababbi daga sassan duniya.

  2. Amurka ta tura ƙarin jirgin ruwan yaƙi kusa da Venezuela

    Jirgin ruwan yaƙi na Amurka

    Asalin hoton, EPA

    Wani jirgin ruwan yaƙi na Amurka ya isa ƙasar Trinidad and Tobago saboda abin da jami'ai suka bayyana atisayen soja na haɗin gwiwa da za a yi na tsawon kwanaki.

    Jirgin USS Gravely zai tsaya a tashar ruwa ta Port of Spain da ke da tazarar kilomita 40 kacal daga Venezuela.

    Shugaba Trump na zargin Venezuela da safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Amurka, zargin da Shugaban Venezuelan Nicolas Maduro ya musanta.

    Wakiliyar BBC ta ce Mista Maduro ya kuma zargi Amurka da neman kirkirar yaki bayan tura jirgin ruwan yaki mafi girma a duniya zuwa yankin na Karebiya.

    Hare-haren sojin Amurka a kan jiragen ruwa da suka ce na safarar miyagun kwayoyi ne sun kashe sama da mutum 40 a makonnin nan.

    Amurkar dai ba ta iya nuna wata tartibiyar hujja ta sumogal din miyagun kwayoyin ba.

  3. 'Yan Kamaru na ci gaba da zanga-zanga kafin sanar da sakamakon zaɓe

    Kamaru

    Mazauna birnin Garoua na ci gaba da zanga-zangar adawa da mulkin Shugaban Ƙasa Paul Biya, yayin da sue jiran sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

    Tuni jami'an tsaro suka tarwatsa wasu masu zanga-zangar da hayaƙi mai sa hawaye a wasu sassan ƙasar.

    Babban ɗantakarar adawa Issa Bakary ne ya nemi magoya bayansa su gudanar da zanga-zangar, inda ya zargi gwmanatin Biya da yunƙurin sauya sakamakon zaɓen.

    A gobe Litinin ne hukumar zaɓen ƙasar za ta bayyana sakamakon. Amma tuni Bakary ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara.

    Zaɓen Kamaru
    Zaɓen Kamaru
  4. An tabbatar da mutuwar mutum 12 a hatsarin motar Kano Line

    Motar bas ta Kano Line

    Asalin hoton, Kano Line

    Hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutum 12 sakamakon hatsarin motar da ya auku ranar Asabar a garin Wudil da ke wajen birnin Kanon.

    Wata sanarwa daga ofishin kamfanin zirga-zirga na Kano Line mallakin gwamnatin jihar ta ce motar na ɗauke da mutum 16, inda 12 suka mutu ne nan take a kan titin Kano zuwa Gombe.

    "Hatsarin ya auku ne lokacin da wani direban babbar mota da ake aikin gyaran titi da ita ya juya ta a tsakiyar titi, abin da ya jawo motar bas ɗin ta ci karo da motar,” in ji sanarwar.

    Ta ƙara da cewa direbobin Kano Line biyu, Alhaji Sabo Alhaji Dan Azumi, na cikin mutanen da suka rasa rayukansu, yayin da sauran fasinjoji biyar, huɗu mata da namiji babba ɗaya, suka ji munanan raunuka.

  5. An kama mutum biyu kan zargin sace kayan tarihin Louvre a Faransa

    Gidan tarihi na Louvre

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'an tsaro a Faransa sun kama mutum biyu kan zargin sace kayayyaki a gidan ajiye kayan tarihi na Louvre.

    Ofishin mai shigar da ƙara ya ce ɗaya daga cikin mutanen an kama shi ne yana ƙoƙarin shiga jirgi a filin jirgin sama na Charles de Gaulle.

    An sace kayayyakin da suka kai darajar dala miliyan 102 daga gidan tarihin da aka fi ziyarta a dunya ranar Lahadi, lokacin da ɓarayi huɗu suka kutsa da tsakar rana.

    Ministan shari'a na Faransa ya ce tabbas tsaron wajen ya gaza, abin da ya jawo wa ƙasar abin kunya.

  6. Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga da hayaƙi mai sa hawaye a Kamaru

    Kamaru

    Jami'an tsaro a Kamaru sun tarwatsa masu zanga-zangar rashin amincewa da zaɓen shugaban ƙasar.

    Al'ummar ƙasar da dama sun fito titunan wasu sassan ƙasar ne domin bayyana rashin amincewarsu da sakamakon babban zaɓen ƙasar.

    Ana dai ta kai-komo ne kan wanda ya lashe zaɓen, wanda a hukumance za a sanar a gobe Litini 27 ga watan Oktoba.

    Shugaban Ƙasar Paul Biya da Issa Bakary ne manyan ƴan takarar da suka shiga zaɓen, inda Bakary yake ikirarin ya lashe zaɓen, a gefe guda kuma alƙaluman akwatuna suke nun Paul Biya ne ke gaba da ƙuri'u.

    Wannan ya sa Bakary ya ce an yi maguɗi ne a zaɓen, inda ya nanata cewa lallai ya lashe zaɓen.

    Kamaru
    Kamaru
    Kamaru
  7. Yadda maganin ƙarfin maza ya sauya yadda ake kallon al'adar saduwa

    Maza

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana ganin gano maganin ƙarfin maza na Viagra a matsayin wani muhimmin abu a tarihin rayuwar jima'i, sai dai wani abun mamaki shi ne an gano maganin ne kwatsam - yayin da ake gwajin magungunan wata cuta, wadda take buƙata ta daban.

    An fara sayar da Viagra ne a shekarar 1998, kuma nan take ya zama maganin da aka fi saya a duniya.

    Wannan magani wanda wani kamfanin magunguna a Amurka ya gano bagata-tan, ya zama maganin da ya fi kawo musu ɗimbin kuɗi a yanzu.

  8. Hisbah ta kama waɗanda take zargi da yunƙurin auren jinsi a Kano

    Hisbah

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Hisbah ta Kano ta ce ta banƙado wani yunƙuri na auren jinsi a jihar, inda ta ce jami'antsa sun kama matasa guda 25 a wajen taron da ke da alaƙa da auren na jinsi.

    Hisbah ta ce ta yi kamen ne a daren ranar Asabar a wani wajen da ke babban titin Hotoro a ƙaramar hukumar Tarauni da ke jihar Kano.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito mataimakin kwamdan hukumar ta Kano, Sheikh Mujahid Aminuddeen Abubakar yana cewa sun samu bayanan sirri ne kan taron, wanda hakan ya sa suka kai samame gidan har suka samu nasarar kamen.

    Ya ce jami'an Hisbah sun yi dirar mikiya ne, inda suka tarar ana raƙashewa. "sun tarar da dandazon maza da mata waɗanda alamu suka nuna bikin aure suke yi," in ji Dr. Mujahid.

    Ya ce sun kama mutum 25, "ciki har da ƴandaudu 18 da mata guda bakwai daga yankunan Sheka da Yar Gaya da Ƙofar Nasarawa na jihar Kano."

  9. "Matsalolin sauyin yanayi na barazana ga rayuwar al'umma"

    Yanayi

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani sabon rahoto ya yi gargadin cewa za a iya shafe kusan rabin al’ummar duniya da ba a damu da su ba nan da shekara 10 masu zuwa idan har gwamnatoci ba su ba su kariyar da ta dace ba.

    Kungiyar da ke fafutukar kare hakkin dan'adama ta Survival International ta ce har yanzu irin wadannan al'ummar kusan dari biyu na zaune a ware a duniya.

    Wakiliyar BBC ta ce kungiyar Survival Internationa ta ce mutanen suna fuskantar barazana daga ayyukan sare bishiyoyi, da na hakar man fetur da ma'adinai Sannan suna fuskantar hatsarin kamuwa da cututtuka kamar mura, da za ta iya yaduwa ta hanyar hulɗa da baƙin mutane

  10. Amurka ta shawarci ƴan ƙasarta da ke Kamaru su yi taka-tsantsan

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Amurka ta shawarci ƴan ƙasarta da ke Kamaru da su yi taka-tsantsan tare da sa ido kan abubuwan da ke faruwa a kusa da su a daidai lokacin da ake shirin fara zanga-zangar rashin amincewa da zaɓen shugaban ƙasar.

    A gobe Litinin ne za a sanar da sakamakon babban zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a ranar Lahadi 12 ga watan Oktoban 2025.

    A wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka da ke Kamaru ya fitar, ya ce duk da cewa babu ruwan ƴan Amurka a lamarin, "muna ba su shawarar su guji zuwa wajen tarukan mutane."

    Sanarwar ta ƙara da cewa, "zanga-zangar lumanar za ta iya rikiɗewa zuwa tarzoma, musamman a cikin dare, kuma jami'an tsaro za su iya amfani da ƙarfi wajen tabbatar da oda."

    Ofishin ya kuma ce dukkan taruka da aikace-aikacen da za a yi a ofishin "daga ranakun Litinin 27 da Talata 28 da a dakatar da su a canja ranaku."

  11. Trump ya ce zai lafta wa Canada ƙarin haraji kashi 10

    Trump

    Asalin hoton, EPA

    Shugaba Trump ya ce zai lafta wa Canada karin harajin kashi 10 na kayayyakin da take shigarwa Amurka - bayan wata talla game da haraji da ta fusata shi.

    Amurka ta dakatar da tattaunawa da Canada a ranar Alhamis a matsayin martani kan wata talla daga Canada inda aka yi amfani da kalaman tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan a 1987.

    Tallar na gargadi ne cewa Haraji - cutarwa ne ga ma'aikatan Amurka da kuma mabukata.

    Tun a ranar Juma'a Trump ya yi barazanar mayar da martani

  12. Gwamna Abba ya ba masarautun Kano umarni su riƙa gudanar da hawa duk shekara

    Kano

    Asalin hoton, Sunusi Bature Dawakin Tofa

    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya buƙaci sarakunan jihar baki ɗaya da su riƙa gudanar da bikin hawan daba a duk shekara.

    Gwamnan ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta riƙa ba sarakunan da masarautun dukkan gudunmuwar da suke buƙata domin tabbatar da adana al'adun gargajiya da nuna su zuwa ga ƙasashen duniya.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamnan ya bayar da wannan umarnin ne a ranar buɗe bikin kalankuwa na al'adun gargajiya na jihar Kano na wannan shekarar, wanda gwamnatin jihar ta shirya domin nuna wa duniya al'adun Kano da bayyana basirar mata da matasan jihar tare da neman haɗin gwiwar ƙasashen waje domin inganta al'adun gargajiya.

    A nasa jawabin, Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi godiya ga gwamnatin Kano bisa ƙoƙarin sake dawo da martabar al'adun mutanen jihar Kano.

  13. Jamaica na shirin fuskantar guguwar Melissa mafi ƙarfi a shekara 35

    Guguwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasar Jamaica na kara shirin tunkarar guguwar Melissa - tare da fargabar cewa za ta iya zama guguwa mafi karfi da ta afka wa tsibirin cikin sama da shekara 35.

    Guguwar na gurgusowa sannu a hankali ta yankin Caribbean kuma tana kara ƙarfi sosai yayin da take tunkarar Jamaica.

    Goguwar mai tafe da iskar sama da kilomita dari da ashirin a cikin sa'a guda, ana sa ran za ta haifar da ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa a sassan Jamhuriyar Dominican da Haiti, yayin da yankin gabashin Cuba zai iya jin tasirinta.

    Wakilin BBC ya ce mutane na nuna damuwa kan gidajensu da hanyoyi inda ake hasashen za a samu zabtarewar kasa da kuma mummunan ambaliyar ruwa Tuni mutane uku suka mutu a Haiti sakamakon ruwan sama da aka tafka da zaftarewar kasa.

  14. Majalisa ta amince a ƙirƙiro jihohi shida a Najeriya

    Majalisa

    Asalin hoton, iStock

    Kwamitin haɗin gwiwa na majalisar dattawa da ta wakilan Najeriya kan yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar garambawul ya amince da a ƙirƙiro jihohi guda shida.

    Wannan na cikin matsayar da aka cimmawa a ƙarshen taron ƙara wa juna sani na kwana biyu, wanda mataimakin majalisar dattawa Sanata Barau I. Jibrin da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu suka jagoranta a jihar Legas.

    Kwamitin ya tattauna ne kan buƙatu guda 69, ciki har da buƙatar ƙirƙirar jihohi 55 da buƙatar a ƙirƙirar ƙananan hukumomin 278 kamar yadda jaridar Daily Trust mai zaman kanta ta ruwaito.

    A game da buƙatar ƙirƙirar jihohi 55 da aka gabatar a ranar Asabar, kwamitin ya amince da ƙirƙirar jihohi guda shida a duk shiyoyin ƙasar guda shida.

    Idan aka amince da ƙirƙirar sababbin jihohi, Najeriya za ta zama tana da jihohi 42 ke nan.

  15. Yau Lahadi India da China za su koma jigilar jirage tsakaninsu

    India a China za su dawo yin jigilar jiragen fasinja tsakanin kasashen biyu, bayan dakatar da zirga-zirgar jiragen shekara biyar da suka gabata sakamakon rikicin kan iyaka.

    A yau Lahadi jirgin farko na fasinja zai tashi daga Kolkata da ke gabashin India zuwa Guangzhou da ke kudancin China.

    Manyan kasashen biyu na yankin Asia na kokarin farfado da huldar kasuwanci tsakaninsu, da kuma neman hanyoyin da za su rage barazanar rikicin kan iyakar Himalayan tsakaninsu

  16. Gwamnatin Kamaru ta zargi jam'iyyun hamayya da yunƙurin tayar da hargitsi

    Kamaru

    Asalin hoton, BBC/Collage

    Ministan harkokin cikin gidan Kamaru, Paul Atanga Nji ya zargi jam'iyyun hamayya na ƙasar da yunƙurin tayar da hargitsi a daidai lokacin da ake jiran sanar da sakamako zaɓen shugaban ƙasar na bana a hukumance.

    Wannan na zuwa ne bayan ƴansandan ƙasar sun kama wasu fitattun ƴansiya masu alaƙa da babban abokin karawar Paul Biya, wato Issa Bakary, kamar yadda jaridar ActuCameroun mai zaman kanta a Kamaru ta ruwaito.

    A daidai lokacin da ake tsimayin sakamakon zaɓen, alƙaluman ƙuri'ar na nuna cewa shugaban ƙasar mai shekara 92 Pul Biya ne ke kan gaba da kusan kashi 54.

    Sai dai Issa Bakary ya yi watsa da sakamakon yana mai cewa shi ne ya lashe zaɓen.

    A jawabin da ministan ya yi, ya ce Bakary ya yi amfani da sakamakon bogi da aka riƙa yaɗawa a kafofin sadarwa ne wajen yanke hukunci, sannan ya yi gargaɗin cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen magance barazanar tayar da hargitsi a ƙasar da ya zargi ƴan jam'iyyun hamayyar da yunƙurin shiryawa.

    Tuni gwamnatin ta sanar da dokar haramta zanga-zanga "ba bisa ƙa'ida ba."

  17. Trump ya sulhunta Thailand da Cambodia

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Trump ya isa Malaysia inda ya jagoranci wani biki da Thailand da Cambodia suka sa hannu kan yarjejeniyar daidaita dangantaka tsakaninsu bayan wani gajeren yakin kan iyaka da suka yi a watan Yulin da ya gabata.

    Wakilin BBC ya ce Mr Trump ya yaba yarjejeniyar ta zaman lafiya wadda ya ce shi ya yi sanadinta.

    Sai dai har yanzu kasashen biyu na ci gaba da zaman doya da manja a kan iyaka da suke da juna, inda a yanzu sun amince ne su janye sojojinsu.

    Mr Trump kuma zai halarci taron kasashen yankin kudancin Asia, tare da kuma tattaunawa da shugaban China Xi Jinping a Koriya ta Kudu, Trump kuma zai kuma kai ziyara a Japan

  18. Buɗewa

    Barkanmu da wannan rana ta Lahadi, barkanmu da sake saduwa a wannan shafin na labaran kai-tsaye.

    Da fata za ku kasance tare da mu.