Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labarin wasanni daga 5 zuwa 12 ga watan Disamba 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 5 zuwa 5 12 ga watan Disambar 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Napoli ta karɓi bakuncin Benfica a Champions League a Italiya

    Napoli ta yi nasara uku daga wasa huɗu a gasar zakarun Turai da Benfica da rashin nasara ɗaya har da wasa biyu a Champions League a cikin rukuni a 2016/17 da ta ci 4-2 a gida da kuma yin nasara 2-1 a waje.

    Benfica ta sha kashi karo biyu daga takwas baya a gasar zakarun Turai da ta fuskanci ƙungiyoyin Italiya daga ciki ta yi nasara uku da canjaras uku.

    Napoli ta yi rashin nasara biyu daga 15 baya a gasar cin kofin zakarun Turai da ƙungiyoyin Portugal da cin wasa tara da canjaras huɗu - ta kuma lashe biyar a jere.

    Scott McTominay ya ci ƙwallo uku a wasa uku a Champions League, bayan zura ɗaya a raga a wasa 24 baya a wasannin.

    David Neres ya ci ƙwallo 17 a wasa 33 a dukkan fafatawa a kaka biyu a Benfica daga baya ya koma Napoli a Agustan 2024.

  2. Za a buga wasa tara a Champions League ranar Laraba

    Wasa tara za a buga a gasar zakarun Turai, fafatawa ta shida-shida a cikin rukuni da za a ɓarje gumi ranar Laraba.

    Daf ake da kammala zagayen cikin rukuni, domin a samu 16 da za su ci gaba da karawar zagaye na biyu a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai.

    Gasar da aka fara da ƙungiya 36, saura za su koma gida su jira kakar baɗi, itama sai idan sun samu gurbin shiga wasannin. Shin me kuke son sani kan fafatawar da za a buga?

    Wasannin da za a buga ranar Laraba:

    • Athletic Bilbao da Paris St-Germain
    • Borussia Dortmund da Bodo Glimt
    • Bayern Leverkusen da Newcastle United
    • Benfica da Napoli
    • Club Brugge da Arsenal
    • Juventus da Pafos
    • Qarabag da Ajax
    • Real Madrid da Man City
    • Villarreal da Copenhagen
  3. Ko Real za ta samu maki uku a kan Man City a Champions League?

    Real Madrid da Manchester City sun fuskanci juna sau 14 a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai, inda Real Madrid ta yi nasara biyar, City ta ci huɗu da canjaras biyar.

    Sun fuskanci juna a kowacce kaka huɗu baya a Champions League.

    A bara ne Real Madrid ta fitar da City a zagayen cike gurbi da suka yi 3-2 a wasan farko a Manchester da cin 3-1 a Sifaniya.

    Real Madrid ta yi nasara 13 daga wasa 14 a Champions League zagayen cikin rukuni a gida da rashin nasara ɗaya.

    Eduardo Camavinga (Mai shekara 23 da kwana 30) watakila ya zama matashi daga Faransa da zai buga wasa na 50 a Champions League, bayan Kylian Mbappé (Mai shekara 22 da kwana 339) a lokacin.

    Kylian Mbappe na taka rawar gani a Champions League mai ƙwallo tara, wanda ya ci bakwai daga wasa bakwai a gasar da ya fuskanci Man City - har da cin uku rigis a bara da Real Madrid ta yi nasara 3-1.

    City ta lashe wasa shida daga fafatawa bakwai a Champions League zagayen cikin rukuni da ta kara da ƙungiyoyin Sifaniya da rashin nasara ɗaya.

    Erling Haaland ya zura ƙwallo tara a raga a fafatawa tara baya da ya fuskanci ƙungiyoyin Sifaniya a Champions League - ya kuma jefa ƙwallo a wasa biyar a gasar mai bakwai a raga.

  4. Ivory Coast ta gayyaci Zaha gasar cin kofin Afirka

    Mai riƙe da kofin nahiyar Afirka, Ivory Coast ta gayyaci Wilfred Zaha cikin ƴan wasa 26 da za su buga mata wasannin da za a yi a Morocco a cikin watan Disamba.

    Mai shekara 33, wanda ya buga wa Ingila wasa biyu daga baya ya koma taka wa kasarsa tamaula, ya ɗauki shekara uku bai buga mata tamaula ba.

    Kuma bai yi wa Ivory Coast wasa ba a gasar cin kofin da ta karɓi bakunci a 2023 ta kuma lashe shi.

    Haka kuma tawagar ta gayyaci mai shekara 34, Jean-Michael Seri, wanda ya buga tamaula a Fulham da kuma Hull City, yanzu yana wasa a Slovenia, wanda rabon da ya yi wa kasar wasa tun cikin watan Oktoba, saboda jinya.

    Sai dai Ivory Coast ta ajiye wasu ƴan ƙwallon da ya haɗa da Simon Adingra, wanda ya taka mata rawar gani a gasar kofin Afirka da ta lashe da Nicolas Pepe da kuma mai tsaron baya, Wilfried Singo da ke jinya.

    Ivory Coast za ta fara wasan kare kofinta a rukuni na shida da za ta fuskanci Mozambique a Marrakech ranar 24 ga watan Disamba.

    Tana kuma rukunin da ya haɗa da Kamaru da Gabon.

    Ƴan tawagar Ivory Coast da za su buga mata kofin nahiyar Afirka:

    Masu tsare raga: Yahia Fofana (Rizespor), Mohamed Kone (Charleroi), Alban Lafont (Panathinaikos)

    Masu tsare baya: Emmanuel Agbadou (Wolverhampton Wanderers), Willy Bolly (Nottingham Forest), Ousmane Diomande (Sporting Lisbon), Guela Doue (Racing Strasbourg), Jean-Philippe Gbamin (Metz), Jean-Ghislain Konan (Gil Vicente), Odilon Kossounou (Atalanta), Evan Ndicka (Roma), Christopher Operi (Basaksehir), Armel Zohouri (Iberia 1999)

    Masu buga tsakiya: Seko Fofana (Stade Rennais), Christ Oulai (Trabzonspor), Franck Kessie (Al Ahli), Ibrahim Sangare (Nottingham Forest), Jean-Michael Seri (NK Maribor)

    Masu cin ƙwallaye: Vakoun Bayo (Udinese), Oumar Diakite (Cercle Bruges), Amad Diallo (Manchester United), Yvan Diomande (RB Leipzig), Sebastien Haller (FC Utrecht), Jean-Philippe Krasso (Paris FC), Bazoumana Toure (Hoffenheim), Wilfried Zaha (Charlotte) (Writing by Mark Gleeson in Cape Town; Editing by Christian Radnedge)

  5. Za a buga wasa tara a Champions League ranar Talata

    Wasannin Champions League Talata:

    • Atalanta da Chelsea
    • Bayern Munich da Sporting
    • Barcelona da Frankfurt
    • Inter Milan da Liverpool
    • Kairat Almaty da Olympiakos
    • Monaco da Galatasaray
    • PSV Eindhoven da Atletico Madrid
    • Tottenham da Slavia Prague
    • Union St Gilloise da Marseille
  6. Alonso na fuskantar kalubale a Real Madrid

    Makomar Xabi Alonso a Real Madrid na tangal-tangal, amma fitila za ta iya haska shi, bayan Champions League da zai fuskanci Manchester City ranar Laraba a Sifaniya.

    Tuni wasu magoya bayan suka fara dawowa daga rakiyarsa - har da yi masa ihu a wasan da Celta Vigo ta je ta doke Real 2-0 a La Liga ranar Lahadi.

    Karon farko da Celta ta je har gidan Real Madrid ta ci wasa a La Liga tun bayan 2006.

    Hakan ya sa Real ta ci gaba da zama ta biyun teburi da tazarar maki hudu tsakani da Barcelona ta daya – kuma wasa daya ta ci daga biyar baya a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

    Kai tun bayan da Real Madrid ta doke Barcelona a cikin watan Oktoba, abubuwa ke ta balbalcewa mai rike Champions League 15 jimilla

  7. Arsenal za ta kara da Portsmouth a zagaye na uku a FA Cup

    Wacce take buga gasar tamaula ta Ingila mai daraja ta shida, Macclesfield za ta karbi bakuncin Crystal Palace a zagaye na uku a FA Cup da aka raba jadawali a ranar Litinin.

    Palace ce mai rike da kofin da ta lashe a kakar da ta wuce.

    Akwai karawa tsakanin yan Premier Tottenham da Aston Villa, Everton da Sunderland, Newcastle da Bournemouth da na Manchester United da Brighton.

    Wasu daga fafatawar Arsenal za ta je gidan Portsmouth, Manchester City da Exeter mai buga League One Exeter City da wanda Liverpool za ta karbi bakuncin Barnsley a Anfield.

    Za a yi wasannin a makon farko da zai kama ranar Asabar 10 ga watan Janairun 2026.

    FA Cup: Jadawalin wasannin zagaye na uku

    • Wolves v Shrewsbury Town
    • Doncaster Rovers v Southampton
    • Tottenham v Aston Villa
    • Port Vale v Fleetwood
    • Preston North End v Wigan Athletic
    • Ipswich Town v Blackpool
    • Wrexham v Nottingham Forest
    • Charlton Athletic v Chelsea
    • Manchester City v Exeter City
    • West Ham v Queens Park Rangers
    • Sheffield Wednesday v Brentford
    • Fulham v Middlesbrough
    • Everton v Sunderland
    • Liverpool v Barnsley
    • Burnley v Millwall
    • Norwich v Walsall
    • Portsmouth v Arsenal
    • Derby County v Leeds United
    • Swansea v West Brom
    • Salford v Swindon
    • Boreham Wood v Burton Albion
    • Grimsby v Weston-super-Mare
    • Hull City v Blackburn Rovers
    • Newcastle United v Bournemouth
    • MK Dons v Oxford United
    • Cheltenham Town v Leicester City
    • Cambridge United v Birmingham City
    • Bristol City v Watford
    • Stoke City v Coventry
    • Macclesfield v Crystal Palace
    • Manchester United v Brighton
    • Sheffield United v Mansfield Town
  8. Salah ya ce ana ɗora masa alhakin rashin kokarin Liverpool a kakar nan

    Mohamed Salah ya jefa makomarsa a Liverpool cikin shakku, bayan da ya ce ana ɗora masa alhakin mummunan halin da ƙungiyar ke ciki na kasa taɓukawa a kakar nan.

    A wata hira da ya yi da ƴan jarida bayan tashi 3-3 da Leeds United, wanda ya fara da ɗumama benci kuma karo na uku a jere ya ce dangantaka tsakaninsa da koci, Arne Slot ta yi tsami.

    Salah ɗan wasan tawagar Masar shi ne na uku mai yawan ci wa Liverpool ƙwallaye a raga mai 250 kawo yanzu.

    Wanda ya koma Anfield da taka leda daga Roma a 2017 yana cikin kashin baya da aka lashe Premier League, bayan shekara 30 rabonta da shi da kuma wanda ta ɗauka a bara da kuma Champions League a 2019.

  9. Kano Pillars ta samu maki uku a kan Kun Khalifat

    Kano Pillars ta doke Kun Khalifat 2-1 a wasan mako na 16 a Premier League da suka kara ranar Lahadi.

    Rabiu Ali ne ya ci wa Pillars ƙwallayen.

    Da wannan sakamakon Pillars, wadda ake kira sai masu gida tana matakin karshe ta 20 a teburi da maki 12, Kun Khalifat kuwa mai maki 17 tana ta 17 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Najeriya.

  10. Barau FC ta je ta tashi ba ci a gidan El-Kanemi Warriors

    El-Kanemi Warriors da Barau FC sun tashi 0-0 a wasan mako na 16 a gasar Premier ta Najeriya da suka kara ranar Lahadi.

    Barau FC mai kwantan wasa tana ta 18 a kasan teburi da maki 17, bayan bayan cin wasa huɗu da canjaras biyar aka doke ta shida daga ciki.

    Ita kuwa El Kanemi mai maki 19 tana ta 15 ɗin teburi, bayan nasara biyar da canjaras huɗu da rashin nasara bakwai.

    Barau FC za ta karɓi baƙuncin Shhoting Stars a karawar mako na 17, ita kuwa El-Kanemi za ta kece rainin a gidan Niger Tornadoes.

  11. ''Ban san me yasa ake zura mana ƙwallo daga bugun tazara da kusurwa ba''

    Kociyan Liverpool, Arne Slot ya ce bai san dalilin da ake zura musu ƙwallo a raga daga bugun kusurwa ko tazara ba a kakar nan a Premier League.

    Liverpool ta fara cin 2-0 ranar Asabar a karawar mako na 15 daga baya Leeds ta farke, sai Dominik Szoboszlai ya ci na uku saura minti 10 a tashi, amma ana cikin karin lokaci sai Leeds ta kara farkewa ta hannun Ao Tanaka.

    Kawo yanzu an zura wa Liverpool ƙwallo 10 daga bugun kusurwa ko tazara, Nottingham Forest ce kan gaba da aka ci 11 a kakar nan.

    A kakar da Liverpool ta lashe Premier League a bara, guda tara ne suka shiga ragar ƙungiyar daga bugun kusurwa ko tazara jimilla.

  12. Inter Miami ta lashe MLS Cup, bayan doke Vancouver Whitecaps

    Lionel Messi ya lashe MLS Cup, bayan da Inter Miami ta doke Vancouver Whitecaps 3-1 ranar Asabar.

    Ƙyaftin ɗin Argentina, wanda ya lashe ƙyautar fitatcen ɗan ƙwallon gasar, shi ne ya bayar da biyu daga ciki da aka zura a raga a wasan na ranar Asabar.

    Mai shekara 38 yana da hannu a cin ƙwallo 15 daga ciki ya bayar da tara aka zura a raga a wasan cike gurbi shida da suka yi.

    A kakar da ta wuce da wuri aka yi waje da Inter Miami a zagayen farko.

    Kawo yanzu Messi ya ci ƙwallo 29 ya bayar da 19 aka zura a raga, yanzu saura ɗaya ya yi kan-kan-kan da Carlos Vela na Los Angeles FC mai 49 da ya kafa tarihin a 2019.

  13. Liverpool ta ɓarar da dama a gidan Leeds a Premier League

    Leeds United da Liverpool sun tashi 3-3 a wasan mako na 15 a Premier League da suka kara ranar Asabar a Elland Road.

    Tun da fari sun kammala zagayen farko ba tare da cin ƙwallo ba.

    Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Hugo Ekitite ya ci biyu a minti na 48 da kuma ta biyu minti biyu tsakani.

    Daga nan ne Leeds ta zare ɗaya ta hannun Dominic Calvert-Lewin a bugun fenariti, sannan Anton Stach ya farke ta biyu.

    Saura minti 10 a tashi daga wasan Liverpool ta kara ta uku ta hannun Dominik Szoboszlai, sai dai daf a tashi ɗan wasan Leeds, Ao Tanaka ya farke ta ukun.

    Liverpool wadda ke cin karo da kalubale a kakar nan, wadda ta yi rashin nasara tara daga 12 baya, ta yi wasa uku ba tare da an doke ta ba, amma sai ta kare da samun maki ɗaya a gidan Leeds United ranar Asabar.

    Haka kuma a karo na uku a jere ƙungiyar Anfield ba ta fara wasan da Mohamed Salah ba, wanda ya yi zaman benci.

    Da wannan sakamakon Leeds ta yi sama zuwa mataki na 16 a teburin Premier League, ita kuwa Liverpool ta koma ta takwas da maki 23.

    Ranar Talata Liverpool za ta ziyarci Italiya, domin fafatawa da Inter Milan a Champions League daga nan ta kara da Brighton a Anfield ranar Asabar 19 ga watan Disamba.

    Ita kuwa Leeds United za ta ziyarci Brentford ranar Lahadi 20 ga watan Disamba.

  14. Kane ya ci Stuttgart uku rigis, ya zura ƙwallo 58 a 2025 kenan

    Wanda yake kan gaba a cin ƙwallaye a Bundesliga a bana, Harry Kane ya ci VfB Stuttgard ƙwallo uku rigis a wasan Bundesliga da Bayern Munich ta yi nasara 5-0 ranar Asabar.

    Bayern, wadda ta bayar da tazarar maki 11 a kan teburin Bundesliga, ta kasa yin abin kirki, har sai da aka saka ɗan wasan tawagar Ingila, wanda ya sa ƙwazon da ta kai ya zura uku rigis a raga.

    Stuttgart ta karasa fafatawar da ƴan ƙwallo 10 a cikin fili, sakamakon da aka bai wa Lorenz Assignon jan kati.

    Kawo yanzu Kane ya ci ƙwallo 58 jimilla a 2025 tsakanin Bayern Munich da tawagar Ingila.

    A kakar da ta wuce tsohon ƙyaftin ɗin Tottenham ya zura 56 jimila a raga a Ingila da kuma Bayern Munich.

    Kane, ƙyaftin din tawagar Ingila ya ci ƙwallo 17 a Bundesliga a bana da hakan ya sa Bayern Munich take da maki 37 a matakin farko a kan teburi.

  15. City ta rage tazarar maki tsakaninta da Arsenal ya koma saura biyu

    Ɗan wasa Ruben Dias da Josko Gvardiol ne suka ci wa Manchester City ƙwallo 3-0 da ta doke Sunderland a gasar Premier League ranar Asabar a Etihad.

    Phil Foden ne ya zura ta uku a raga, kuma ta biyar da ya ci a kakar nan.

    Sai dai Sunderland ta kare fafatawar da ƴan wasa 10, bayan da aka bai wa Luke O'Nien jan kati a minti na biyar da ya shiga ya canji ɗan wasa.

    Da wannan sakamakon City ta koma ta biyun teburi da maki 31, bayan da Arsenal, wadda ke matakin farko da maki 33 ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Aston Villa a Villa Park ranar Asabar a wasan farko da aka fara a tsakar rana.

    Sunderland ta koma ta bakwai a teburi da maki 23, kafin a kammala wasannin mako na 15 a Premier League.

    Wasannin da za su buga na gaba:

    Manchester City: Ƙungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama za ta je Sifaniya ranar Laraba, domin fuskantar Real Madrid a Champions League.

    Sunderland: Ita kuwa ƙungiyar da Regis le Bris ke horarwa za ta karɓi bakuncin Newcastle United a wasan hamayya ranar Lahadi da ake kira Wear-Tyne derby..

  16. Arsenal ta yi rashin nasara shida a hannun Aston Villa karkashin Arteta

    Ƙungiyar Arsenal ta yi rashin nasara 2-1 a gidan Aston Villa a wasan mako na 15 a Premier League da suka fafata a Villa Park ranar Asabar.

    Matty Cash ne fara ci wa Villa ƙwallo a minti na 36, haka suka je hutu, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Arsenal ta farke ta hannun Leandro Trossard.

    Daf da za a tashi ne Villa ta haɗa maki uku, bayan da Emiliano Buendia ya ci na uku.

    Wasa na shida kenan da Arsenal ta yi rashin nasara a hannun Aston Villa a Premier League karkashin kociya ɗan kasar Sifaniya, yayin da Pep Guardiola ya doke shi sau bakwai.

    Kenan Aston Villa ta lashe wasa tara daga 10 baya a Premier League da rashin nasara ɗaya ta koma ta biyun teburi kafin a kammala sauran wasannin ranar Asabar da maki 30.

    Ita kuwa Gunners tana nan a matakin farko da maki 33.

  17. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.