Labarin wasanni daga 5 zuwa 12 ga watan Disamba 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 5 zuwa 5 12 ga watan Disambar 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Osimhen, Zaidu da sauran ƴan wasan da za su wakilci Najeriya a Afcon 2025

    Victor Osimhen

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta fitar da sunayen ƴan wasan Super Eagles da za su wakilci ƙasar a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta Afirka ta 2025 da za ta gudana a Moroco.

    Hukumar ta fitar da sunayen ne bayan rairaye su daga cikin ƴan wasa 50 da ta fitar tun farko.

    Ƴanwasan Super Eagles ɗin da aka sanar a ranar Laraba su ne:

    Masu tsaron raga:

    • Stanley Nwabali
    • Francis Uzoho
    • Amas Obasogie

    Masu tsaron baya:

    • Calvin Bassey
    • Zaidu Sanusi
    • Semi Ajayi
    • Bruno Onyemaechi
    • Igoh Ogbu
    • Chidozie Awaziem
    • Bright Osayi-Samuel
    • Ryan Alebiosu

    Ƴan wasan tsakiya:

    • Wilfred Ndidi
    • Frank Onyeka
    • Fisayo Dele Bashiru
    • Muhammed Usman
    • Alex Iwobi
    • Ebenezer Akinsanmiro
    • Raphael Anyedika
    • Tochukwu Nnadi

    Ƴan wasan gaba:

    • Ademola Lookman
    • Victor Osimhen
    • Akor Adams
    • Samuel Chukwueze
    • Cyriel Dessers
    • Salim Fago
    • Moses Simon
    • Chidera Ejuke
    • Paul Onuachu

    A ranar 21 ga watan Disamban 2025 ne za a take wasan farko na gasar tsakanin Moroko da Comoros a birnin Rabat.

    Najeriya za ta buga wasanta na farko ne ranar Talata 23 ga watan Disamba a birnin Fes, inda za ta kara da ƙasar Tanzaniya.

  2. Har yanzu ina sa ran za a buga La Liga a wata kasar - Tebas

    Tebas

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban gasar La Liga, Javier Tebas ya ce har yanzu suna ta fadi tashin ganin an buga wasu daga wasannin a wata kasar.

    A cikin watan Oktoba aka soke tsarin da Barcelona da Villareal za su kara a birnin Miamin Amurka.

    Tun farko an tsara yin fafatawar a sitadiya mai suna Miami Hard Rock ranar 20 ga watan nan, daga baya aka yi ta caccakar tsarin da ta kai an soke gabaki daya.

    Tuni dai hukumar kwallon kafa ta Turai ta sahale da tsarin da har yanzu ake jiran hukuncin da Fifa za ta yanke.

    A lokacin da yake gabatar da jawabi a wani taro a jiya a birnin Riyadh, Tebas ya ce yana fatan zai samu izinin gudanar da gasar a Amurka da kuma nan gaba a Saudiyya.

  3. Ingila za ta yi wasan sada zumunta da Uruguay da kuma Japan

    Thomas Tuchel

    Asalin hoton, Getty Images

    Tawagar Ingila za ta karbi bakuncin Uruguay da Japan a wasan sada zumunta a Wembeley a watan Maris din badi, domin shirye shiryen buga gasar cin kofin duniya a 2026.

    Cikin watan Mayu ake sa ran koci, Thomas Tucel zai bayyana yan wasan da za su wakilci Ingila, kafin nan za ta fafata da Uruguay ranar 27 ga watan Maris, sannan ta kece raini da Japan kwana uku tsakani.

    Tuchel na fatan kara yin wasu wasannin sada zumunta biyu a Amurka, kafin a bude labulen babbar gasar tamaula ta duniya da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico a badi.

    Ingila tana rukuni na 12 da ya hada da Croatia da Ghana da kuma Panama - za kuma ta fara wasan farko da Croatia ranar 17 ga watan Yuni a birnin Dallas.

  4. Haenni ta zama ta farko da za ta shugabanci ƙungiyar Bundesliga

    Fifa

    Asalin hoton, Getty Images

    Tatjana Haenni ta zama macen farko da za ta shugabanci kungiyar tamaula ta Bundesliga, bayan da RB Leipzig ta sanar mata da mukamin.

    Tsohuwar yar wasan Switzerland ta rike mukamai da yawa har da a hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa fiye da shekara 10.

    Mai shekara 59 za ta fara gudanar da aikin ranar 1 ga watan Janairun 2026.

    Leipzig, tana mataki na biyu a teburin Bundesliga da tazarar maki takwas tsakani da Bayern Munich mai jan ragama.

    Za a yi hutu a gasar Bundesliga daga 21 ga watan nan zuwa tara ga Janairun badi, domin yin shagulgulan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

  5. Ali Maalou zai wakilci Tunisa gasar kofin Afirka karo na biyar

    Tunisia

    Asalin hoton, Getty Images

    Zakakurin ɗan ƙwallo, Ali Maaloul yana cikin yan wasa 28 da Tunisa za ta je da su wasannin kofin nahiyar Afirka a Morocco – kuma zai buga gasa ta biyar kenan da ake yi duk bayan shekara bibiyu.

    Maaloul, wanda zai cika shekara 36 da haihuwa, rabon da ya buga wa Tunisa tamaula kusan shekara biyu,

    bayan da ta gayyace shi wasan sada zumunata a watan jiya da kuma yi mata gasar Arab Cup a Qatar, inda aka yi waje da Tunisia ranar Lahadi.

    A gasar kofi Afirka da za a yi a Morocco a cikin watan nan, Tunisia tana rukuni na uku da za ta fara fuskantar Uganda a birnin Rabar ranar 23 ga watan nan, tana kuma rukuni da Najeriya da kuma Tanzaniya.

    Tunisia za ta je buga babbar gasar tamaula ta Afirka karo na 17 a jere.

  6. Sifaniya ta ci gaba da zama ta farko a ƙwallon kafar mata a duniya

    Spain

    Asalin hoton, Getty Images

    Spain ta ci gaba da zama ta farko a jadawalin kwallon mata a duniya, Amurka ce ta biyu, bayan doke Italiya a wasan sada zumunta a cikin Nuwamba.

    Jamus ce ta uku da Ingila ta hudu - Brazi wacce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya ta mata a 2027 tana ta shida,

    sai Faransa da Japan da Koriya ta Kudu da Canada daga cikin yan 10 farko.

    Nigeria ce ta daya a Afirka ta 37 a duniya, Afrika ta Kudu ta biyu da kuma Ghana ta uku a nahiyar, sannan ta 62 a duniya.

  7. Messi zai kai ziyarar kwana huɗu a birane huɗu a Indiya

    Messi

    Asalin hoton, Getty Images

    Magoya bayan Lionel Messi yan gani kasheni sun gina butum-butuminsa a Kudancin birnin Kolkata a lokacin da kyaftin din Argentina ke shirin kai ziyara Indiya.

    An gina butum-butumin mai taka leda a Inter Miami dauke da kyautar Ballon d'Or da kuma kofin duniya da ya lashe a 2022 a Qatar.

    Masu shirya karɓar bakunci Messi na aiki tukuru kafin ziyarar da zai kai ranar 13 ga watan Disamba.

    Magoya bayan Messi, suna da damar yin tozali da kofunan da yake da su ciki har da Champions League da La Liga da kuma na duniya.

    Ziyarar kwana huun da Messi zai kai India, bayan Kolkata zai je Mumbai da Delhi da kuma Hyderabad.

  8. An dakatar da Folliot daga shiga sabgogin tennis shekara 20

    An dakatar da ɗan kasar Faransa, Quentin Folliot daga buga kwallon tennis tsawon shekara 20, bayan da aka same shi da laifi 27 da suka shafi cin hanci a wasan, kamar yadda aka sanar ranar Alhamis

    Folliot shi ne kan gaba a jerin wasu gungun yan wasa dake cogen sakamakon gasar kwallon tennis.

    Wanda yake mataki na 488 a tennis a duniya ya musanta aikata ba daidai ba, daga ciki har da laifi 11 da ake tuhumar ya aikata tsakanin 2022 zuwa 2024 ya kuma buga wasa takwas a lokacin.

  9. Morocco ta saka sunan Hakimi cikin waɗanda za su buga mata gasar kofin Afirka

    Hakimi

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai masaukin baƙi, Morocco ta saka sunan Achraf hakimi cikin ƴan wasa 26 da za su buga mata gasar kofin nahiyar Afirka, duk da raunin da yake jinya.

    Sai dai ana tantama ko zai warke ya yi mata wasannin da za a fara daga 21 ga watan Disamba, bayan raunin da ya ji a watan jiya a Champions League a karawar da Bayern Munich ta doke Paris St Germain 2-1.

    Sai dai kociyan tawagar, Walid Regragui ya ce mai riƙe da ƙyautar gwarzon ɗan wasan Afirka na bana, zai yi wa Morocco ƙyaftin, kuma yana sa ran zai fara fuskantar Comoros da shi a birnin Rabat.

    Sai dai kuma Morocco ba ta gayyaci ɗan wasan Lille ba, Hamza Igamane, wanda ya ji rauni ranar Juma'a a fafatawa da Olympique de Marseille a gasar Ligue 1.

    Morocco wadda za ta karɓi bakuncin gasar bana, wadda ta kai zagayen daf da karshe a gasar kofin duniya a 2022 tana rukunin farko da ya ƙunshi Mali da zambia.

    Ƴan wasan da Morocco ta gayyata domin buga mata kofin Afirka:

    Masu tsare raga: Yassine Bounou (Al Hilal), Munir El Kajoui (Renaissance Berkane), El Mehdi Al Harrar (Raja Casablanca)

    Masu tsare baya: Nayef Aguerd (Olympique de Marseille), Abdelhamid Ait Boudlal (Stade Rennais), Mohamed Chibi (Pyramids), Jawad El Yamiq (Al Najma), Achraf Hakimi (Paris St Germain), Adam Masina (Torino), Noussair Mazraoui (Manchester United), Romain Saiss (Al Sadd), Anass Salah-Eddine (PSV Eindhoven)

    Masu buga tsakiya: Sofyan Amrabat (Real Betis), Eliesse Ben Seghir (Bayer Leverkusen), Brahim Diaz (Real Madrid), Neil El Aynaoui (AS Roma), Bilal El Khannous (VfB Stuttgart), Azzedine Ounahi (Girona), Oussama Targhaline (Feyenoord)

    Masu cin ƙwallaye: Ilias Akhomach (Villarreal), Ayoub El Kaabi (Olympiakos), Youssef En-Nesyri (Fenerbahce), Abdessamad Ezzalzouli (Real Betis), Soufiane Rahimi (Al Ain), Ismael Saibari (PSV Eindhoven), Chemsdine Talbi (Sunderland). (Writing by Mark Gleeson in Cape Town; Editing by xx)

  10. Zambia ta gayyaci matasa huɗu, domin buga mata gasar cin kofin Afirka

    Zambia

    Asalin hoton, Getty Images

    Zambia ta gayyaci matasa huɗu daga 28 da za su buga mata gasar kofin Afirka, kamar yadda kociya, Moses Sichone ya sanar.

    An gayyaci David Hamansenya, wanda ya fara buga wa kasar tamaula a wasan sada zumunta da Afirka ta Kudu da matashi ɗan shekara 18, Eliya Mandanji wanda a watan jiya ya fara yi wa Zambia wasa a karawa da Angola.

    Sauran sun hada da mai shekara 19, Joseph Liteta, mai taka leda a Cagliari mai buga Serie A da kuma Joseph Sabobo Banda mai wasa a Israila.

    Akwai kuma guda 14 da suka buga wa Zambia gasar cin kofin Afirka a shekara biyu baya da aka yi a Ivory Coast da za ta je da su Morocco.

    Zambia ba ta haura wasannin cikin rukuni ba a Ivory Coast, sakamakon samun maki biyu daga wasa uku.

    An bai wa Schone aikin horar da Zambia a watan jiya, sakamakon da Avram Grant ya bar aikin, bayan kasa samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya.

    Zambia za ta fara wasan cin kofin Afirka da fuskantar Mali ranar 22 ga watan Disamba a Casablanca za kuma ta fuskanci Comoros da kuma Morocco a rukunin farko.

    Ƴan wasan Zambia da za su buga mata gasar kofin Afirka:

    Masu tsare raga: Lawrence Mulenga (Power Dynamos), Francis Mwansa (Zanaco), Willard Mwanza (Power Dynamos)

    Masu tsare baya: Mathews Banda (Nkana), Dominic Chanda (Power Dynamos), Obino Chisala (Al Merrikh), Kabaso Chongo (Zesco United), David Hamansenya (Leganes), Gift Mphande (Zesco United), Frankie Musonda (Bahrain SC), Benson Sakala (Bohemians), Stoppila Sunzu (Changchun Yatai)

    Masu buga tsakiya: Joseph Sabobo Banda (Hapoel Be’er Sheva), Lameck Banda (Lecce), Miguel Chaiwa (Hibernian), Wilson Chisala (Zanaco), Given Kalusa (FC Muza), Kings Kangwa (Hapoel Be’er Sheva), Joseph Liteta (Cagliari), Lubambo Musonda (FC Magdeburg), Pascal Phiri (Zesco United), Fashion Sakala (Al Fayha), David Simukonda (Zesco United), Owen Tembo (Power Dynamos)

    Masu cin ƙwallaye: Patson Daka (Leicester City), Jack Lahne Kalichi (Austria Lustenau), Eliya Mandanji (Zanaco), Kennedy Musonda (Hapoel Ramat Gan).

  11. An roki Fifa ta dakatar da sayar da tikitin kallon gasar kofin duniya 2026

    Fifa

    Asalin hoton, Getty Images

    An roƙi FIFA ta dakatar da sayar da tikitin kallon gasar cin Kofin Duniya bayan da aka gano cewar magoya bayan ƙasashe za su fuskanci biyan farashi “mai tsananin tsada”, inda mafi arha ga wasan karshe ya haura £3,000.

    Hukumar ƙwallon ƙafar Croatia ta wallafa cikakken bayani kan farashin tikiti ga mambobin tawagarta, waɗanda ke halartar wasanni a koda yaushe, tare da farashin tikitin da ya dace maimakon waɗanda aka canjawa farashin.

    Sai dai hukumar ƙwallon ƙafar Croatia ta bayyana cewa mafi arha ga tikitin wasan karshe ranar 19 ga Yuli ya kai dalar Amurka 4,185 ko kuma fam £3,120 kowanne.

  12. Na ɗauka ba zan sake buga tamaula ba - Jesus

    Ɗan wasan Arsenal, Gabriel Jesus ya ce ya ɗauki kusan shekara ɗaya yana ta tunanin ko zai sake komawa taka leda kuwa?

    Ɗan kasar Brazil ya koma buga wa Arsenal tamaula a karon farko a Champions League da Gunners ta je ta doke Club Brugge a Belgium ranar Laraba, bayan kwana 332 yana jinya

    Jesus, mai shekara 28, wanda ya ci ƙwallo shida a wasa bakwai daga baya ya ji rauni a wasan FA Cup da Manchester United ranar 12 ga watan Janairu.

    Sai dai ɗan ƙwallon ya ce ya sha wahala jinya kafin ya murmure.

    Jesus

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Pogba ya zama jakadan gasar tseren rakuma ya kuma sa hannun jari

    Pogba

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan ƙwallon Monaco, Paul Pogba ya zama jakadan tseren rakuma ya kuma sa hannun jari a wasan

    Ɗan wasan tawagar Faransa ya ƙulla yarjejeniya da Al Haboob na Saudiyya.

    Tseren rakuma yana da farin jini a gabas ta tsakiya da ake samun makudan kuɗi.

    A watan jiya Pogba ya koma taka leda a karon farko a karawa da Rennes, bayan sama da shekara biyu da aka dakatar da shi kan laifin shan abubuwan kara kuzarin wasa.

    Tun farko a dakatar da Pogba shekara huɗu daga cikin Fabrairun 2024 - daga baya aka rage hukuncin, sakamakon shigar da kara ga kotun ɗaukaka kararrakin wasanni ta duniya

  14. Ko Arsenal za ta ci wasa na shida a jere a bana a Champions League?

    Bukayo Saka

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasa ɗaya Club Brugge ta yi nasara daga fafatawa 18 a gasar zakarun Turai da ta fuskanci ƙungiyoyin Ingila, aka doke ta 14 da canjaras uku.

    Sai dai ƙungiyar ta Belgium an doke ta wasa biyu daga 19 baya da ta yi a gasar ta zakarun Turai a gida da lashe 12 da canjaras biyar - kuma ba a doke ta ba a karawa biyar a gida a Champions League da yin canjaras biyu da lashe uku daga ciki.

    Nicolo Tresoldi ya ci wa Club Brugge ƙwallaye a wasa uku a gida a gasar ta zakarun Turai.

    Arsenal ba ta yi rashin nasara ba a fafatawa tara da ƙungiyoyin Belgium a gasar zakarun Turai daga ciki ta lashe bakwai da canjaras biyu - ta kuma cinye tara baya a Champions League, inda ƙwallo uku ne ya shiga ragarta.

    A bana Gunners ce kaɗai ta lashe dukkan wasa biyar da fara kakar nan - Gasar zakarun Turai da ta fara da cin wasa biyar a jere ita ce a 2005/06, wadda ta kare a kwata fainal.

    Arsenal na bukatar cin ƙwallo huɗu su zama 400 da ta ci a gasar zakarun Turai, yayin da Gabriel Martinelli ya zura ƙwallo a raga a wasa huɗu da ya yi a Champions League.

  15. Wasan Villareal da Copenhagen zai ɗauki hankalin ƴan kallo

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Villarreal ta yi rashin nasara ɗaya daga wasa shida a gasar zakarun Turai da ta fuskanci ƙungiyoyin Denmark da cin huɗu da canjaras ɗaya daga ciki, har da lashe dukkan uku a gida.

    Ƙungiyar ta Sifaniya ba ta ci wasa ba daga takwas baya a Champions League, aka doke ta shida da canjaras biyu - har da rashin nasara uku ba tare da cin ƙwallo ba.

    Wasa ɗaya ne daga 37 baya da Villareal ta tashi canjaras a gasar ta zakarun Turai.

    Sai dai kuma Copenhagen ba ta yi nasara ba a wasa 15 baya a gasar zakarun Turai da ta kara da ƙungiyoyin Sifaniya daga ciki aka doke ta tara da canjaras shida.

    Ƙungiyar Denmark na fatan cin wasa na biyu a jere a Champions League a karon farko tun bayan uku da ta yi nasara a jere a 2006/07 da kuma 2010/11.

    Viktor Dadason (Mai shekara 17 da kwana 149) ya zama matashin da zura ƙwallaye da yawa a Champions League da ya ci Kairat a karawa ta biyar-biyar, ya doke tarihin Lamine Yamal (Mai shekara 17 da kwana 200) a lokacin.

  16. Leverkusen da Newcastle za su buga gasar zakarun Turai karo na biyu a tsakaninsu

    Karawar da suka fafata tsakanin Leverkusen da Newcastle ita ce a 2002/03 a Champions League wasa na biyu a cikin rukuni, inda ƙungiyar Ingila ta yi nasara 3-1 a gidanta da kara cin 3-1 Jamus.

    Leverkusen ta yi rashin nasara ɗaya daga shida baya a gasar zakarun Turai da ta fuskanci ƙungiyoyin Ingila daga ciki ta yi nasara uku aka doke ta biyu daga ciki - da yin wasa huɗu ba tare da ƙwallo ya shiga ragarta ba har da 2-0 da ta doke Manchester City a Etihad a wasan zagaye na biyar-biyar.

    Patrik Schick ya ci wa Leverkusen ƙwallo biyu a Champions League, bayan da ɗaya kacal ya ci a fafatawa 28 a baya a gasar.

    Bayan da Newcastle United ta yi nasara huɗu a karawar da ta fuskanci ƙungiyoyin Jamus, yanzu ta kasa cin uku daga ciki ta yi canjaras ɗaya da rashin nasara biyu - na baya-bayan nan shi ne wanda Borussia Dortmund ta ci 1-0 a Ingila da yin nasara 2-0 a Jamus a kakar 2023/24 a Champions zagayen cikin rukuni.

    Haka kuma wasa biyu Newcastle ta ci daga 13 a gasar zakarun Turai da ta buga a waje da yin canjaras shida aka doke ta biyar.

    Harvey Barnes ya zura ƙwallo huɗu a raga a wasa huɗu da ya yi wa Newcastle United a Champions League.

  17. Athletic Club za ta karɓi bakuncin PSG mai rike da Champions League

    PSG

    Asalin hoton, Getty Images

    Athletic Club ta yi nasara biyu daga wasa 10 a gasar zakarun Turai da ta kara da ƙungiyoyin Faransa daga ciki ta yi canjaras biyu aka doke ta shida.

    Ƙungiyar mai buga La Liga an doke ta wasa biyu daga 16 baya a gasar zakarun Turai a zagayen cikin rukuni a gida, amma ta yi nasara 13 da canjaras ɗaya - ta kuma lashe bakwai daga fafatawa takwas da rashin nasara ɗaya.

    Yuri Berchiche ya buga wasa 32 a dukkan karawa a ƙungiyar birnin Paris a 2017/18 daga baya ya koma Athletic Club a kakar 2018.

    Paris St Germain ta yi rashin nasara uku daga fafatawa 13 baya a gasar zakarun Turai da cin takwas da canjaras biyu daga ciki - haka kuma ta yi nasara uku bayan nan da ƙungiyar da ta kaiwa ziyara a Sifaniya.

    Mai riƙe da Champions League ta ci ƙwallo huɗu ko fiye da haka a wasa biyar daga bakwai a Champions League.

    Joao Neves (Mai shekara 21 da kwana 74) watakila ya zama matashi daga Portugal da zai buga wasa 30 a Champions League, zai doke tarihin da Cristiano Ronaldo ya kafa (Mai shekara 22 da kwana 226) a lokacin.

  18. Qarabag da Ajax za su kara karo na biyu a gasar zakarun Turai

    Wasan da suka fuskanci juna a gasar zakarun Turai shi ne a bara a Europa League, inda ƙungiyar Netherlands ta yi nasarar cin 3-0 a Azerbaijin.

    Qarabag ba ta yi nasara ba a wasa biyar a gasar zakarun Turai da ta fafata da ƙungiyoyin Netherlands da canjaras uku aka doke ta biyu.

    Haka kuma Qarabag ta sha kashi a wasa ɗaya daga biyar a gida a kakar nan a gasar ta zakarun Turai da cin uku da canjaras ɗaya - kuma tana zura ƙwallo bibiyu a kowanne wasa huɗu a gida.

    Kawo yanzu Ajax ta yi fafatawa takwas ba tare da nasara ba a gasar kofin zakarun Turai - karon farko da ta dade ana doke ta a tarihin ƙungiyar.

    Ajax ta zura ƙwallo 397 a gasar zakarun Turai a tarihi, tana bukatar cin uku a raga ta zama ta farko daga Netherlands da ta zazzaga 400 a gasar.

  19. Watakila Juventus ta doke Pafos ƙungiyar Cyprus a gasar zakarun Turai

    Juventus

    Asalin hoton, Getty Images

    Juventus ta lashe dukkan wasa shida a gasar zakarun Turai da ta kece rainin da ƙungiyoyin Cyprus.

    Ƙungiyar ta Italiya ta yi rashin nasara biyu daga fafatawa 11 a gasar zakarun Turai da ta yi a gida cin biyar da canjaras huɗu.

    Juventus kan fara kwasar ƙwallo a raga a karawa biyar da fara wasannin Champions League a kakar nan.

    Pafos ta yi rashin nasara ɗaya daga wasa 11 a gasar zakarun Turai a kakar nan da cin biyar da canjaras biyar - kuma ba a doke ta ba a karawa biyar baya da cin uku da canjaras biyu da wasa huɗu ƙwallo bai shiga ragarta ba.

    Mai tsaron bayan Pafos, David Luiz mai shekara 38 da kwana 218, ya zama na biyu mai shekarar haihuwa da yawa da ya ci ƙwallo a Champions League a wasa da Monaco karawa ta biyar-biyar a cikin rukuni.

  20. Dortmund na bukatar taka rawar gani a kan Bodo

    Dortmund ta yi rashin nasara ɗaya daga wasa 20 baya a Champions League a gida da lashe 13 da canjaras shida daga ciki - ta kuma zura ƙwallo huɗu a raga a wasa biyar a gasar ta kakar nan.

    Serhou Guirassy ya zura ƙwallo 18 a raga a wasa 23 a Champions League - Haaland ne ke gabansa mai 28 a raga daga karawa 23.

    Idan har Dortmund ta yi nasara za ta zama ta 100 kenan a tarihin gasar zakarun Turai, tana kuma bukatar cin ƙwallo biyu su zama 300 a Champions League.

    Bodø/Glimt ta ci wasa ɗaya daga 10 baya a gasar ta zakarun Turai da rashin nasara bakwai da canjaras biyu daga ciki.

    Ƙungiyar ta Norway ba ta zura ƙwallo ba a raga a biyu daga fafatawa 21 a gasar zakarun Turai.