Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 1404/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/04/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Umar Mikail da Isiyaku Muhammed

  1. 'Mahara sun sake kashe gomman mutane a Filato'

    Aƙalla mutum 40 ne aka sake kashewa a wani hari da wasu mahara suka kai a garin Zike da ke yankin Kwall a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.

    Mai bai wa gwamnan jihar Filato shawara kan harkokin tsaro Admiral Shipi Gakji mai ritaya ya tabbatar wa BBC cewa an kai harin ne a cikin dare, wayewar garin yau Litinin.

    Bayanai sun nuna cewa maharan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi a lokacin da suka shiga ƙauyen.

    Gakji ya shaida wa BBC cewa "E haka ne, an kai harin, muna ƙoƙarin haɗa yawan mutanen da aka kashe, amma tabbas yawan ya kai haka ɗin (40)."

    Wannan na zuwa ne kimanin mako ɗaya bayan wani hari da ƴan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar ta Filato, wanda ya yi sanadin kashe fiye da mutum 50 da tarwatsa wasu da dama.

    Filato jiha ce mai al'umma masu mabambantan ƙabila da addini, wadda ta daɗe tana fama da rikici mai nasaba da addini da kuma ƙabilanci.

    Sau da yawa akan zargi makiyaya da laifin kai irin waɗannan hare-hare, sai dai a lokuta da dama sukan musanta hakan.

    Hukumomi a baya sun sha kafa kwamitoci domin magance matsalar, amma duk da haka, lamarin ya ci tura.

  2. Za mu yi tankaɗe da rairaya a sana'armu- Ƴan gwangwan

    Ƙungiyar dillalan ƴan gwangwan ta Najeriya ta fara yin tankaɗe da rairaya sakamakon yadda wasu daga cikin mambobinta ke yin biris da ƙa’idojin gwamnati da suka shafi saye da sayar da kayan gwangwan da ake zargi na sata ne.

    Wannan na zuwa a daidai lokacin da wasu da ake zargi cewa sun sayar da ƙungiyar sukutum kan naira miliyan goma ba tare da sahhalewar shugabannin ƙungiyar ba.

    Sai dai shugabanni riƙo na ƙungiyar sun ce wannan ciniki bai yi ba.

  3. Za a kammala sabunta titin Abuja-Kaduna-Kano cikin wata 14 - Ministan ayyuka

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sake ƙaddamar da aikin sabunta titin Abuja-Kaduna-Kano.

    Da yake jawabi a madadin shugaban a wajen ƙaddamar, gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana titin a matsayin mai muhimmanci, wanda ya ce yana haɗa babban birnin tarayyar ƙasar da sama da jihohi 12 a arewa maso yamma da arewa ta tsakiya da arewa ta gabashin ƙasar.

    A wajen taron wanda aka yi a garin Jere da ke ƙaramar hukumar Kagarko, Uba Sani ya ce an yi watsi da hanyar na tsawon lokaci, wanda hakan a cewarsa ya jawo asarar rayuka da illata tattalin arzikin ƙasar.

    "Sabunta wannan titin zai sauƙaƙa zirga-zirga, sannan zai samar da ayyukan yi tare da inganta tsaro da walwalar al'umma," in ji shi kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook.

    Ya ce abin da ya jawo tsaikon aikin a baya shi ne rashin tsaro, wanda ya ce yanzu ana samu nasara a ɓangaren, inda ya ce matafiya suna tafiya a kowane lokaci ba tare da fargaba ba.

    A nasa ɓangaren, ministan ayyuka, David Umahi ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar Kaduna wajen tabbatar da an ci gaba da aikin, inda ya tabbatar da cewa za a kammala aikin a cikin wata 14.

  4. Manoman Nijar sun koka kan rashin biyansu diyyar gonakinsu da aka yi bututun mai

    A jamhuriyar Nijar, dubban manoma masu gonaki a wurin da aka gudanar da aikin bututun mai, sun koka game da rashin biyansu kuɗin diyya na wurarensu na noma, inda zuwa yanzu suka kwashe kimanin shekara uku suna jiran gawon shanu.

    Lamarin dai ya shafi masu gonaki da dama a jihohin Damagaram da Tahoua da kuma Dosso wuraren da suka kasance na yawancin manoma masu samar da abincin da al’ummar ƙasar ke amfani da shi.

    Alhaji Daouda Tanƙama ɗaya ne daga cikin ƴanƙungiyar farar hula da suka gudanar da bincike kan lamarin daga ƙungiyar ADRODEV, inda ya yi kira da a yi wa manoman adalci.

  5. Shugaban Ecuador ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasar

    Shugaban Ecuador mai ci Daniel Noboa ya ce ya lashe zaɓen shugaban ƙasa mai cike da tarihi bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zagaye na biyu na zaɓen inda ya samu 56 na ƙuri'un da aka kaɗa.

    Shugaban ƙasar mai shekara 37 ya ga masu zaɓe sun yi na'am da tsauraran matakansa na murƙushe ƙasurguman masu hada-hadar miyagun ƙwayoyi da ƙungiyoyi masu aikata laifuka.

    Abokiyar karawarsa a zaɓen Luisa Gonzalez ta ce ba ta amince da sakamakon zaɓen ba tana iƙirarin an tafka maguɗi a cikinsa, duk da ba ta bayar da hujjar faɗin haka ba.

    Ta dai ce za ta nemi a sake ƙidaya ƙuri'un, inda ta ce "ina Allah wadai a gaban al'ummata da kafafen watsa labarai da kuma duniya cewa Ecuador ta kasance ƙarƙashin mulkin kama-karya kuma muna fuskantar maguɗin zaɓe mafi muni a tarihin zaɓen ƙasar."

  6. Gwamnatin Najeriya za ta hukunta masu saɓa ƙa'idar samun izinin shiga ƙasar

    Gwamnatin Najeriya ta sanar da wasu sabbin dokokin da suka shafi samar da takardun izinin shiga ƙasar ga ƴanƙasashen waje, inda ta yi gargaɗin cewa masu karya doka za su iya fuskantar haramcin sake samun damar shiga Najeriyar har na tsawon shekara 10.

    Wannan matakin dai zai soma aiki nan da watan gobe na Mayu.

    A cewar ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, za a tabbatar da an tantance waɗanda za su shiga ƙasar, tare da cin waɗanda bizarsu ta ƙare amma ba su sabunta ba tarar dala 15 kowace rana.

  7. Sojojin Nijar sun tarwatsa sansanin ƴanbindiga

    A jamhuriyar Nijar, dakarun tsaron ƙasar sun zafafa ayyukansu a yankin Tillabéri, inda ake fama da ƙalubalen tsaro.

    A cewar sabon rahoton da aka fitar a hukumance, wasu hare-hare da aka yi niyyar kaiwa sun ba da damar kawar da wasu masu aikata laifuka 14, da tarwatsa sansanin ƴanbindiga da ke Goundey, da kuma ƙarfafa tsaro a yankunan da ke da haɗari.

    Haka kuma a jihar Diffa, rundunar sojin Nijar ta sanar da kame wasu mahara 12 bayan wani hari da suka kai a ƙauyen Jagada.

  8. Buɗewa

    Jama'a barkan mu da wannan safiya ta Litinin, wadda ake yi wa laƙabi da tushen aiki.

    A yau ma za mu kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta irin su X da Facebook da Instagram da YouTube domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku shiga shafinmu na WhatsApp domin samun labarai da ɗumi-ɗuminsu.

    Ku kasance tare da mu.