Jami'an tsaro a jihar Borno sun kama wani malami da ake zargi da cin zarafin wani ƙaramin yaro ta hanyar zane shi, wanda aka gani cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta.
Bidiyon, mai tayar da hankali, ya nuna yadda malamin ke dukan ɗan ƙaramnin yaron da sanda yayin da wani yaron kuma ke watsa masa ruwa da kasa a jikinsa cikin zafin rana.
Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce yara 6 cikin 10 na fuskantar wani nau’i na cin zarafi a Najeriya.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Borno, Dauda Iliya ya bayyana wa BBC cewa lamarin ya ɗaga hankalin Gwamnan jihar, Babagana Zulum, wanda hakan ya sa gwamnan ya bayar da umarnin a nemo malamin.
Sai dai ya ce tun a lokacin azumi ne lamarin ya faru, "amma sai yanzu ya fito ya karaɗe shafukan sada zumunta. Gwamna ya kaɗu matuƙa. Shi ya sa ya bayar da umarnin a nemo mutumin, wanda malamin yaron ne. Yanzu an kama shi, an miƙa shi ga jami'an tsaro."
Dauda Iliya ya ƙara da cewa gwamnan ya sa an kawo masa yaron, kuma ya ce a kawo masa mahaifiyarsa.
"Mahaifiyar tana zaune ne a Munguno, Boko Haram sun kashe mahaifinsa. Amma yanzu gwamna ya saya musu gida a cikin Maiduguri, sannan zai ɗauki nauyin karatunsa."