Shugabannin Commonwealth na son Birtaniya ta biya diyyar cinikin bayi
Shugabannin ƙasashe renon Ingina da aka fi sani da Commonwealth sun hallara tsibirin Samoa inda ake sa ran za su tattauna batun cinikin bayi da Birtaniya ta yi a wasu ƙasashen ƙungiyar a baya.
Wasu ƙasashen ƙungiyar musamman na yanki Caribbean na kiran a biya su diyya kan bautar da su da Birtnaiya ta yi a baya.
Shi dai firaministan Birtaniya Sir Kier Stermer ya ce yana son tattaunawar ƙungiyar ta mayar ta mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi ƙalubalen da duniya ke fuskanta musamman kan sha'anin tattalin arziki, da sauyin yanayi.
Sai dai wani daftari ya nuna shugabannin za su amince su ba da fifiko wajen yin magana kan cinikin bayi tun daga ƙarni na 16 har zuwa shekarun 1860.
Wani kakakakin gwamnatin Birtaniya ya ce batun biyan diyya ba ya cikin ajandarsu, don haka ba za a biya ba.
Birtaniyar na daga cikin manyan ƙasashen duniya da suka yi ƙaurin suna wajen cinikin bayi, har zuwa shekarar 1807 da ta kawo karshen fataucin.