Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/10/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/10/2024

Taƙaitattu

  • Daniel Chapo ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Mozambique
  • Al'ummar Nijar na ci gaba da alhinin rasuwar Hama Amadou
  • Najeriya na matsayi na 36 a duniya cikin jadawalin FIFA
  • Matatar Dangote ta fara sayar da man fetur kai-tsaye ga 'yan kasuwa
  • Shugabannin Commonwealth na son Birtaniya ta biya diyyar cinikin bayi
  • Ƴan majalisar Najeriya na son a yi dokar ɗaure iyayen da suka ƙi kai 'ya'yansu makaranta

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Abdullahi Bello Diginza

  1. An kashe gomman mutane a zanga-zangar zaɓe a Mozambique

    An kashe gomman mutane yayin zanga-zangar da ke gudana a garuruwa da dama na Mozambique, bayan bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasar.

    An yada hotunan yadda ake ƙona tayoyi da kuma jami'an ƴan sanda jibge.

    Rikicin ya ɓalle ne bayan da hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana ɗan takarar jam'iya mai mulki

    Yadda aka bayyana Daniel Chapo a matsayin wanda ya lashe kashi saba'in na ƙuru'un da aka kaɗa a zaɓen da aka yi cikin wannan watan kenan

    Kafofin watsa labaran cikin gida sun ce ana zaman ɗar-ɗar a babban birnin ƙasar Maputo, inda mutane suka yi rukuni-rukuni suna sauraren labarai daga tashoshin ƙasashen waje.

  2. Shugaban Mossad zai je Qatar kan tattaunawar tsagaita wuta a Gaza

    Isra'ila ta ce shugaban hukumar leƙen asiri ta ƙasar,Mossad zai je Qatar a matsayin babban mai shiga tsakani a yaƙin Gaza, domin tattauna yadda za a sako wadanda Hamas ke garkuwa da su.

    Sanarwar da ofishin firaiministan Isra'ila ya fitar na zuwa ne bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka ya kai Qatar.

    Anthony Blinken ya ce za a ci gaba da tattaunawar sako ƴan Isra'ila da aka yi garkuwa da su da kuma tsagaita wuta a Gaza nan gaba kaɗan.

  3. Duniya na gab da fuskantar mummunan sauyin yanayi - Antonio

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa duniya na gaf da faɗawa cikin abin da ta kira da ifti'la'in sauyin yanayi, madamar al'umma ba su rage yawan amfani da abubuwan da ke gurɓata muhalli ba.

    Majalisar ta ce a yanayin zafi da ake ciki a duniya na kan hanyar haurawa matakin maki uku da digo daya inda ya linka adadin da ake so a cimma a cikin shekaru ashirin.

    Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutreess ya ce sakon da ke cikin wannan rahoton na yau mai taken giɓin gurbatacciyar iska a fayyace yake.

    Ya ce muna tafiya ne a kan siratsi, kamata ya yi kowane shugaba yayi abunda za a cike giɓin da aka samu na gurbatacciyar iska da ake fitarwa a muhalli ko kuma a tsunduma cikin masifa.

    Zirga-zirgar jirage a sararin samaniya da kuma motoci da masana'antu dake fitar da gurbataccen iska na daga cikin abubuwan da ke ƙara ta'azzara lamarin.

  4. Ba bu wanda ya isa ya hana mu gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Kano - Abba Kabir Yusuf

    Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce "babu mutuimn da ya isa ya hana mu gudanar da zaɓe a jihar Kano" kasancewar duk jihohi sun yi nasu.

    Gwamnan dai ya yi wannan magana ne a cikin gajeren bidiyo da ke nuna gwamnan na yi wa magoya bayansa bayani mai kama da yanayin kamfe.

    "Duk jihohin faɗin Najeriya babu jihar da ba ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi ba saboda haka ba mu ga dalilin da wasu maƙiya jihar Kano....a yau su fito su nemi su hana mu mu yi zaɓe.......

    Jihar Kano a wannan lokacin babu mahaluki da za mu bari ya shigo jihar Kano ya dinga cin mutumcin jihar Kano mu ƙyale shi." In ji gwamna Abba.

    Ya ƙara da cewa "gwamnatin Kano da hukumar zaɓe duka ba mu saɓa kowacce ƙa'ida ba saboda haka muna kan turba kuma za mu yi zaɓe cikin lafiya da lumana."

    A ranar Talata ne dai wata kotun tarayya a Kano a wani hukunci da ta yi ta rushe dukkannin shugabannin hukumar zaɓen jihar Kano mai zaman kanta, KANSIEC bisa abin da ta kira rashin cancanta tare da yin umarnin ka da a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da aka shirya yi a watan Oktoba, har sai an naɗa mutanen da suka cancanta domin jagorantar hukumar.

  5. Kamfanin haƙar ma'adanai na ƙasar Faransa zai rufe a Nijar

    A jamhuriyar Nijar Kamfanin haƙar uranium na ƙasar Faransa, Orano zai rufe kamfaninsa na Arlit da ke arewacin ƙasar ta Nijar a ranar 31 ga watan Oktoba, sakamakon ƙarancin kuɗi.

    Kamfanin ya koka da matsalar fatara dangane da kamfanin Somair, reshensa a Nijar, da kuma killace kan iyakokin Nijar da Benin tun a watan Yulin 2023.

    A ranar 20 ga watan Yuni ne gwamnatin mulkin sojan Nijar ta soke izinin Orano na gudanar da aikin haƙar uranium na Imouraren a arewa maso gabashin ƙasar ta Sahel.

    Ana tunanin mahaƙar na ɗauke da ɗaya daga cikin manyan ma'adinan Uranium a duniya.

  6. Tinubu ya umarci ministoci da su yi amfani da motoci uku kacal a tawagarsu

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya taƙaita yawan motocin da ministocinsa da sauran shugabannin hukumomin gwamnati ke amfani da su a tawagarsu zuwa guda uku, inda ya ce ba za a ƙarawa kowa ba.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin, Bayo Onanuga ya fitar, shugaba Tinubu ya ce wannan wani mataki daga cikin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka na rage kashe kuɗaɗen gwamnati.

    Sanarwar ta ce shugaba Tinubu ya kuma bai wa ministocin nasa da shugabannin hukumomi da ka da su yi amfani da masu kare lafiyarsu ko jami'an tsaro da suka wuce biyar, inda kuma ya umarci mai bai wa shugaban shawara kan tsaron ƙasa domin tattaunawa da sojoji da ƴansanda da sauran masu ɗamara kan yadda za a rage yawan jami'an tsaron.

    Da ma dai ko a watan Janairu sai da shugaban ya ce ya ɗauki matakan rage kashe kuɗaɗen inda ya rage yawan ƴan tawagarsa yayin bulaguro ƙasar waje daga 50 zuwa 20 sannan shi kuma mataimakin shugaban ƙasa aka bar masa mutum biyar.

  7. Majalisar wakilai za ta binciki yawan lalacewar babban layin wutar Najeriya

    Majalisar wakilan Najeriya ta umarci kwamitinta kan wutar lantarki da ya binciki dalilin da ya sa babban layin wutar lantarkin ƙasar ke yawan samun matsala, al'amarin da ke janyo katsewar lantarki a sasan ƙasar da dama musamman arewacin Najeriya.

    Majlisar ta nemi kwamitin ya gabatar da rahoto nan da makonni uku masu zuwa.

    Hon Mansur Manu Soro da ke wakiltar mazabar Darazo da Ganjuwa a jihar Bauchi a majalisar wakilan Najeriya, shi ne ya gabatar da kudurin.

    Babban layin wutar na Najeriya dai ya lalace fiye da sau 10 a wannan watan inda a ranar ɗaya ma ya lalace sau biyu.

  8. Helikwafta ya yi ɓatan dabo a Najeriya

    An gano wani jirgi mai saukar ungulu da kamfanin mai na NNPCL ya ɗauka haya wanda ya yi ɓatan dabo a safiyar ranar Alhamis.

    Wata sanarwa daga kamfanin na NNPCL ta ce jirgin wanda ya tashi daga hedikwatar sojojin sama ta birnin Fatakwal, zuwa Nuims Antan wani wurin lodin mai da ke tsakiyar ruwa ya ɓace wa na'urar sadarwa da jirage da misalin ƙarfe 11:22 na safiyar ranar.

    Sanarwar ta ce akwai mutum takwas a cikin jirgin.

    Tuni ma'aikatan aikin ceto suka fara neman jirgin kuma kawo yanzu an gano gawar mutum uku.

  9. 'Dalilin da ya sa Tinubu ya sallami ministocinsa'

    Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa sallamar ministoci da shugaban nasa ya yi ya dogara ne ga irin kallon da yadda ƴan Najeriya ke yi wa ministocin.

    A wata hira da gidan talbijin na ARISE TV, Onanuga ya ce Tinubu ya yi amfani da tunanin ƴan Najeriya ne.

    "A lokacin da aka rantsar da ministocin, shugaban lallai ya shaida musu cewa yana ƙarfin ikon ɗauka da sallamar mutum aiki kuma ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ya kori duk wani ministan da ya fahimci ba ya aikin da ya kamata."

    "An yi wani taro a watan Oktoban bara inda shugaba Tinubu ya nanata maganarsa cewa a koyaushe zai iya sallamar duk wanda ya ga ba ya yn aiki."

    Onanuga ya ƙara da cewa sallamar ministocin ba lallai na nufin cewa ba su yi abin da shugaba Tinubun yake tsammani daga gare su ba.

    "Shugaba Tinubu ya yi amfani da abin da ƴan Najeriya ke tsammani daga wurinsu. Makonnin da suka gabata a lokacin taron majalisar zartarwa, Shugaban ya ƙalubalanci ministocin su je su shaida wa ƴan Najeriya abin da suka yi a tsawon shekara guda."

    Shugaba Tinubu dai ya fahimci cewa ƴan Najeriya ba su gamsu da riƙon ludayin da dama daga ministocinsa amma kuma yana da ƙwarin gwiwar cewa gwamnati na yin bakin ƙaƙarinta amma ministocin ba sa fitowa su shaida wa al'ummar ƙasa abin da gwamnatin ke yi." In ji Onanuga.

    A ranar Laraba ne dai shugaba Tinubu ya sanar da yin garambawul ga ministoci da ma'aikatun gwamnatinsa, inda ya sallami ministocin guda biyar sannan ya sake wa mutum 10 ma'aikatu tare da naɗa sabbi guda bakwai.

  10. Amurka za ta tallafa wa Falasɗinawan da suka rasa muhallansu - Blinken

    Babban sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken, ya ce Amurka za ta ba da tallafin fiye da dala miliyan 130 don taimaka wa Falasɗinawa da suka rasa matsugunansu a Gaza.

    Mista Blinken na ganawa da shugabannin Qatar a birnin Doha, yayin ya ke ƙoƙarin ganin an tsagaita wuta.

    Ƙasar Qatar - wadda shalkwatar siyasar Hamas ke cikinta - ita ce babbar mai shiga tsakani a rikicin.

    Jami'in diplomasiyyar na Amurka na fuskantar ƙalubale da dama, kama daga tsaikon da aka samu a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza zuwa ɓarkewar yaƙi tsakanin Isra'ila da Hezbollah.

    Hamas ba ta sanar da sabon shugaba ba tun bayan kisan da Israila ta yi wa Yahya Sinwar a makon da ya gabata.

  11. Daniel Chapo na jam'iyya mai mulki ya lashe zaɓen shugaban Mozambique

    Jam'iyya mai mulki a Mozambique, Frelimo, ta lashe zaɓen da aka gudanar mai cike da taƙaddama, inda ya za ta ɗora a kan shekaru 49 da ta yi tana mulki.

    Hukumar zaɓen ƙasar wadda ta sanar da Daniel Chapo a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kaso 71 na ƙuri'un da aka kaɗa, ta ce mai biye masa ya samu kaso 20 ne kacal.

    Daniel Chapo mai shekaru 47 zai maye gurbin shugaba Filipe Nyusi wanda ya yi zango biyu a kujerar shugabancin ƙasar.

    Zaɓen dai ya kasance mai cike da taƙddama inda jam'iyyu suka yi ta zargin junansu da tafka maguɗu wani abun da ya haifar da zanga-zanga a kasar.

  12. Al'ummar Nijar na ci gaba da alhinin rasuwar Hama Amadou

    A jamhuriyar Nijar al'ummar ƙasar na ci gaba da nuna alhininsu kan rasuwar tsohon fiamninistan ƙasar, Hama Amadou.

    Marigayin mai shekara 74 ya rasu ne a daren da ya gabata a babban asibitin birnin Yamai bayan fama da rashin lafiya.

    Hama Amadou ya riƙe wannan matsayi har sau biyu a ƙasar, farko tsakanin 1995 zuwa1996 sannan daga 1999 zuwa 2007.

    Za'ayi jana'izarsa a gobe Juma'a a fadar shugaban ƙasar kafin a ɗauki gawar zuwa garinsu, Youri dake cikin jihar Tillabery inda za a binne gawarsa.

  13. Ana zaman ɗar-ɗar a Mozambique yayin da ake dakon sakamakon zaɓe

    Manyan titunan Maputo, babban birnin ƙasar Mozambique sun koma fayau a daidai lokacin da ƙasar ke dakon sakamakon zaɓen da ake sa ran a sanar da shi a kowane lokaci daga yanzu.

    Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ce ana zaman ɗar-ɗar bisa zargin yin maguɗi a zaɓen da kuma kisan da aka yi wa lauyan babban jagoran adawa Viniyansi Molanya.

    Jagoran ƴan hamayyar ƙasar ya yi kira ga jama'a su fantsama kan tituna don zanga-zanga bayan da aka kashe lauyansa a ranar Juma'ar da ta gabata.

    A ranar Litinin, 'yan sandan kwantar da tarzoma sun harba hayaƙi mai sa hawaye da harsasai masu kisa kan dandazon masu zanga-zangar da ke cike da fushi.

  14. Jami'an asibitin Gaza sun ce harin Isra'ila ya kashe mutum 17

    Jami'an asibitin tsakiyar Gaza sun ce harin da Isra'ila ta kai kan wata makaranta ya kashe aƙalla mutum 17, ciki har da ƙananan yara.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kai harin ne kan cibiyar gudanarwar Hamas da ke sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat.

    Jami'an Falasɗinawa sun ce suna amfani da wurin ne a amatsayin wajen da suke tsugunnar da ' yan gudun hijira.

    Isra'ila ba ta bai wa kafafen watsa labaran ƙasashen waje ciki har da BBC damar shiga Gaza.

  15. Najeriya na matsayi na 36 a duniya cikin jadawalin FIFA

    Hukumar ƙwallo ƙafa ta duniya FIFA ta saka Najeriya a matsayi na 36 na jerin ƙasashen da suka fi taka leda a duniya.

    Cikin jadawalin da ta fitar ranar Alhamis, hukumar FIFA saka Najeriya a matsayi na huɗu a nahiyar Afirka.

    Ƙasar Moroco ce ta farko a nahiyar Afirka, kuma ta 13 a duniya, yayin da Senegal ke matsayi na biyu a Afirka kuma ta 20 a duniya.

    Masar ta 30 a duniya da Najeriya ta 36, da kuma Algeria ta 37 ne na uku da na huɗu da kuma na biyar a nahiyar Afirka.

    Ƙasashen da ke kan gaba a duniya su ne Argentina da Faransa da Sifaniya da Ingila da Brazil.

  16. Mun gano matsalar da ta kawo rashin wuta a rewacin Najeriya - TCN

    Kamfanin samar da lantarki na Najeriya TCN ya ce ya gano abin da ya haifar da matsalar rashin wutar lantarki a wasu yankunan arewacin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da ya fitar, kamfanin ya ce layin samar da lantarki na Ugwuaji-Apir 330-kilovolt ne ya samu matsala.

    A 'yan kwanakin baya-bayan ne wasu yankunan arewacin ƙasar suka fuskanci matsalar katsewar wutar lantarki, lamarin da TCN ya alaƙanta da faɗuwar layin Ugwaji–Apir.

    Sanarwar mai ɗauke da sa hannun daraktan hulɗa da jama'a na kamfanin, Ndidi Mbah, ya ce an gano matsalar ne a yankin Igumale na jihar Benue.

    Mista Mbah ya ce sai a ranar Laraba ne kamfanin ya gano haƙiƙanin abin da ya faru.

    Ya ƙara da cewa tuni kamfanin ya kammala shirye-shiryen tattara kayan aikin da yake buƙata domin fara gyaran layin a wurin da abin ya faru a yau Alhamis.

  17. Turkiyya ta kai wa ƙungiyar Kurɗawa harin 'ramuwar gayya'

    Gwamnatin Turkiyya ta ce sojojinta sun kai hari maɓoyar mayaƙan ƙungiyar Kurɗawa ta PKK masu alaƙa da Iraƙi da Siriya, bayan da aka zarge su da kai wani hari kan masana'atar jiragen sama.

    A ranar Laraba ne wasu mutane biyu mace da namiji suka buɗe wuta a kusa da mashigar masana'antar, mai nisan kilomita 40 daga wajen babban birnin ƙasar Ankara, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyar tare da jikkata 22.

    Ma'aikatar tsaron Turkiyya ta ce harin da sojojin ƙasar suka kai moɓayar mayaƙan ƙungiyar ya lalata gine-gine 47 na ƙungiyar.

    Shugaban ƙasar, Recep Tayyip Erdogan ya bayyana hari kan masana'atar jiragen saman da ''abin taƙaici'' a shafinsa na X.

    Ministan tsaron cikin gida na ƙasar, Ali Yerlikaya ya ce ɗaya daga ckin maharan ɗan ƙungiyar PKK ne mai suna Ali Orek.

    Ƙungiyar Kurɗawa ta PKK, haramtacciyar ƙungiyar ce da aka bayyana da ta'addanci a Turkiyya da Amurka da Birtaniya, inda kuma take yaƙi da hukumomin Turkiyya tun shekarun 1980, kan abin da ta kira ƙwatar 'yancin Kurɗawa marasa rinjaye a ƙasar.

  18. Masu sayen abinci su ɓoye ne ke haifar da hauhawar farashi - Gwamnatin Najeriya

    Hukumar kula da hakkin masu sayayya ta Najeriya, FCCPC ta zargi masu sayen kayan abinci su ɓoye da haifar da ƙaruwar hauhawar farashin kayan abinci a ƙasar.

    Shugaban hukumar, Tunji Bello ne ya bayyana haka ranar Laraba a wani taron masu ruwa da tsaki a birnin Kano da ke arewacin ƙasar, kamar yadda jaridun ƙasar suka ruwaito.

    Ya ƙara da cewa binciken da hukumarsa ta yi, ta gano yadda wasu 'yan kasuwa ke rububin sayen sabon kayan abinci da aka fara girbewa suna ɓoye, lamarin da ya ce yana ƙara ta'azzara ƙarancin abincin a kasuwanni, abin da kuma ya ce shi ke haifar da ƙaruwar hauhawar farashin kayyaki.

    “Waɗannan mutane ba su damu da halin da al'ummar ƙasarmu za su shiga ba, don haka suke bi goankin manoma suna sayen kayan a bincin da suka noma, ko su je kasuwanni suna sayen kayan abincin da aka tara domin su riƙa ɓoyewa, suna kuma safararsu zuwa ƙasashen waje don sayarwa a farashi mai tsada, wanda kuma hakan na jefa ƙasarmu cikin matsalar ƙarancin abinci,'' kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana.

  19. Tsohon ministan gidaje ya gode wa Tinubu bayan sallamarsa daga aiki

    Tsohon ƙaramin ministan gidaje na Najeriya, Abdullahi Tijjanai Gwarzo ya yaba wa shugaban ƙasar Bola Tinubu bisa damar da ya ce ya ba shi na hidimta wa ƙasar.

    Gwarzo na cikin jerin ministoci biyar da shugaba Tinubu ya sanar da sallamarsu daga aiki a ranar Laraba, a wani garambawul a majalisar ministocin ƙasar.

    A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, tsohon ministan ya ce shekara guda da ya yi a matsayin, ya mayar da hankalinsa wajen magance matsalar gidaje a ƙasar da inganta birane.

    Tsohon ministan ya kuma ce a ɗan taƙaitaccen lokacin da ya yi a matsayin, yana alfahari da irin gudunmowar da ya bayar tare da gode wa shugaban ƙasar.

    ''Ina miƙa godiyata ga shugaban ƙasa bisa amincewar da ya yi da ni, har ya ba ni wannan matsayi... Duk da cewa lokacina taƙaitacce ne, amma ina alfahari da ayyukan da na faro'', kamar yadda ya wallafa a shafin nasa.

    Haka kuma ya taya sabbin ministocin da aka sanar da naɗinsu, waɗanda ya ce yana da yaƙinin za su ɗora kan ayyukan da suka faro.

  20. Muna neman a yi dokar ɗaure iyayen da suka ƙi kai 'ya'yansu makaranta - Majalisar Dattawa

    Majalisar dattawan Najeriya ta ce tana son yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar gyara fuska, ta yadda za a samar da dokar hukuncin ɗauri ga iyayen da suka ƙi sanya 'ya'yansu a makaranta.

    Shugaban kwamitin ilimi na majalisar, Sanata Lawan Adamu Usman ya ce majalisar na duba yiwawar sanya hukunci ɗaurin wata shida ga duk iyayen da suka kasa sanya 'ya'yansa a makaranta.

    Yayin da yake zantawa da manema labarai, bayan gabatar da rahoton kwamitinsa a gaban majalisar a ranar Laraba, Sanata Lawan ya ce “muna son a yi dokar ɗaurin wata shida ga iyayen da suka ƙi sanya 'ya'yansu a makaranta. Shi ma ilimi masu iya magana na cewa shi ne gishirin rayuwa, kuma shi ne maganin duka matsalolin da ke faruwa a ƙasar nan,'' in ji sanatan.

    Tun da farko shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio ya ce akwai yara fiye da miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, waɗanda ya ce idan ba a ɗauki matakin kula da su ba, za su iya zama ɓata-gari idan suka girma.

    Shi ma Mataimakain Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin ya ce matsalar rashin zuwan yara makaranta, babbar damuwa ce ga ƙasar, wanda ya ce ta fi ƙamari musamman a yankin arewacin ƙasar.