Fiye da ƙungiyoyi 130 na jinƙai da sauran ƙungiyoyin fararen hula sun bukaci a gaggauta kawo ƙarshen ƙungiyar agaji ta Gaza (GHF), wani shiri na agaji da Isra’ila da Amurka ke marawa baya, suna mai cewa shirin ya zama barazana ga rayukan fararen hula.
A cewar ƙungiyoyin, fiye da Falasdinawa 500 ne suka mutu tun bayan da ƙugiyar agajin ta fara aiki a ƙarshen watan Mayu, bayan Isra’ila ta ƙulle Gaza na tsawon watanni uku.
Hakazalika, kimanin 4,000 ne suka jikkata yayin da suke ƙoƙarin karɓar agaji.
Ƙungiyoyin da suka haɗa da Oxfam da Save the Children da Amnesty International, da dai sauran su sun zargi dakarun Isra’ila da wasu ‘yan bindiga da buɗe wuta a kai a kai kan mutanen yayin da suka jira karɓan agaji.
Isra’ila ta musanta zargin cewa sojojinta na harbin masu karɓar agaji da gangan, tana mai cewa tsarin ƙungiyar agajin yana bai wa jama’a taimako kai tsaye ba tare da tsoma bakin Hamas ba.
A wata sanarwar haɗin gwiwa da manyan ƙungiyoyin jinƙan suka fitar a ranar Talata, sun bayyana cewa ƙungiyar agajin na karya ƙa’idojin ayyukan jinƙai na duniya, musamman ta hanyar tilasta wa mutane miliyan biyu zama a wuraren da ke cike da cunkoso da sojoji, inda suke fuskantar harbin bindiga a kullum.
Tun bayan da GHF ta fara aiki, rahotanni daga ma’aikatan jinya da shaidu da ma’aikatar lafiya da Hamas ke jagoranta sun nuna cewa kusan kullum ana samun mutanen da ake kashewa a wuraren rabon agaji.
Tsarin rabon agaji na GHF ya maye gurbin tashoshin rabon agaji guda 400 da aka yi amfani da su lokacin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas, da tashoshi guda huɗu da sojoji ke kula da su yanzu – uku a kudu maso yammacin Gaza da ɗaya a tsakiyar gundumar.