Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta ce ta karɓi ƴan ƙasar 104 da aka dawo da su daga Algeria a ƙarƙashin wani shirin hukumar kula da masu ƙaura ta duniya da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya.
Sanarwar da NEMA ta fitar a shafinta an X a ranar Talata ta ce ofishinta na Lagos ne ya tarbi ƴan Najeriyan, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed.
Mutanen da aka mayar da su Najeriya sun haɗa da maza 80 da mata 14 da ƙananan yara bakwai da kuma jarirai uku.
NEMA ta ce an ɗauki bayanan mutanen domin bai wa hukumar shige da fiice ta Najeriya damar gudanar da aikin ta.
Ta kuma ce an ɗauki matakin tabbatar da ganin sun koma cikin sauran jama'a domin ci gaba da rayuwa ba tare da tsangwama ba.
An gudanar da jana'izar Alhaji Aminu Dantata a Madina
Asalin hoton, Muhammad Jameel Yusha'u/Facebook
An gudanar da jana'izar hamshaƙin ɗankasuwar nan na Najeriya, Marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a masallacin Annabi (S.A.W) da ke birnin Madina.
Jana'izar ta gudana ne bayan sallar magariba, inda kuma aka binne gawarsa a maƙabarta Baƙiyya mai tarihi a birnin na Madina.
Mutane da dama ne daga Najeriya suka halarci jana'izar - wadda aka jinkirta tun da farko sakamakon wasu dalilai na ciƙa ƙa'ida.
Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ta halarci jana'izar, tare da tawaga mai ƙarfi da ta ƙunshi manyan jagororin jihar.
Amurka ta kawo ƙarshen ayyukan USAID a ƙasashen duniya
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar tallafawa ƙasashen duniya ta Amurka ta rufe dukkan ayyukanta na tallafi ga ƙasashen duniya a hukumance.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, a cikin wata sanarwa, ya ce daga yanzu Amurka za ta karkatar da kuɗaɗen da take kashewa a hukumar tallafawa ƙasashen duniyan wajen bunƙasa muradun ƙasar da zuba jari a harkokin da suka shafi abokan huɗɗar ta da kuma fafatawa da China.
Mr Rubio ya ce a 2023 mafi yawan ƙasashen yankin Saharar Afirka ba su goyi bayan Amurka ba a wajen kaɗa ƙuri'ar raba gardama a zauren Majalisar Dinkin Duniya duk da samun tallafin fiye da dala biliyan 60 tun daga 1991.
Ya kuma ce China ta fi Amurka yin suna tsakanin ƙasashen Gabas ta Tsakiya, amma duk da haka Amurka ta kashe aƙalla dala biliyan 90 a yankin.
Majalisa ta zartar da ƙudirin dokar harajin shugaba Trump
Asalin hoton, US Pool
Majalisar dattawan Amurka ta zartar da ƙudirin dokar haraji da kashe kuɗi na shugaba Trump.
Majalisar ta rabu gida biyu tsakanin ƴan Republican da kuma Democrat, lamarin da ke nufin ƙuri'ar mataimakin shugaban ƙasar JD Vance ce raba gardama.
Za a mayar da ƙudirin dokar zauren majalisar wakilai, inda ake zaton za ta fuskanci turjiya daga wasu a cikin ƴan jam'iyyar shugaba Trump.
Sun bayyana damuwa a kan ƙarin tiriliyoyin dala kan bashin gwamnatin Amurka.
Ƙudirin zai ƙara wa'adin rage yawan haraji a wasu ɓangarori, da bunƙasa kashe kuɗi ga dakarun soji da kuma rage kuɗin da ake kashewa wajen tafiyar da wasu cibiyoyin kiwon lafiya.
An yi wa tsohon shugaban Liberia jana'izar karramawa
Asalin hoton, Getty Images
An yi wa tsoho shugaban Liberia, William Tolbert jana'izar karramawa, shekaru 45 bayan an kashe shi a wani juyin mulki.
An ajiye hotunan Mr Talbort da ƴan majalisarsa 13 da aka kashe su tare, a wajen da aka yi jana'izar.
Ba a dai iya gano gawarwakin Mr Talbort da ƴan majalisarsa ba, amma raotanni na cewa an binne su a wani kabari.
Ana dai ganin jana'izar a matsayin wata hanyar sasanci a Liberia.
A makon jiya aka binne Samuel Doe, wanda ake zargin ya kashe Mr Tolbert, shekara goma bayan shi ma an kashe shi.
Ƴanbindiga sunkai wa sojojin Mali hari
Rundunar sojin Mali ta ce ƴan bindiga masu iƙirarin kishin addini sun kai hare-hare a kan cibiyoyin ta.
Daga cikin wuraren da aka kai harin harda sansanin soji da ofishin ƴan sanda da ke birnin Kaye da ke yammaci.
Rahotanni sun ce an kai hare-haren a sassa aƙala bakwai.
Rundunar sojin ta ce ta daƙile harin da aka kai mata kuma ta kashe mayaƙa aƙalla 80, tare da ƙwato makamai da motoci da kuma babura.
Ƙungiyar JNIM mai alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda ta ce ita ce ta kai hare-haren, kuma ta yi iƙirarin cewa har yanzu tana mamaye da barikin sojin.
Tawagar wasu jagorori a Kano ta kai ta'aziyya ga iyaan Dantata a Madina
Asalin hoton, Barau I Jibrin
Wata tawaga da ta ƙunshi wasu manyan jagorori da ƴansiyasar Kano ta ziyarci iyalan Aminu Alhassan Dantata domin miƙa ta'aziyyar rasuwar hamshaƙin ɗan kasuwar.
Tawagar ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I Jibril - ta ƙunshi tsohon shugaban jam'iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da Hon. Alhassan Ado Doguwa da shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas.
Bayan sallar magariba a Saudiyya ne za a gudanar da jana'izar hamshaƙin ɗan kasuwar.
Tuni dai tawagogi daban-dban da suka ƙunshi a gwamnatin tarayya da na gwamnatin jihar Kano suke ƙasar domin halartar jana'izar.
Trump ya soke takunkuman da ya ƙaƙaba wa Syria
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu a kan dokar shugaban ƙasa domin kawo ƙarshen takunkumin da aka ƙaƙabawa Syria, lamarin da fadar White House ta ce zai taimakawa shirin ƙasar na komawa turbar zaman lafiya da bunƙasa.
Amurka ta sanya wa Syria takunkumi ne a lokacin gwamnatin Bashar al-Assad, wadda ƴan tawaye suka kifar da ita a watan Disamban bara, kuma ya haramta bai wa ƙasar duk wani bashi daga ƙasashen waje.
Fadar White House ta ce za ta sanya ido a kan ayyukan gwamnatin Syria, domin tabbatar da cewa da gaske take wajen inganta alaƙa da Isra'la da hana ƙungiyoyin ƴan ta'ada shiga ƙasar da kuma haramta ayyukan ƙungiyoyin ta'adda masu alaƙa da Falasɗinu.
Ministan harkokin wajen Syria, Asaad al-Shibani ya ce matakin zai janye ƙalubalen hana bunƙasa tattalin arzikin ƙasar da kuma bata damar huɗd da ƙasashen waje.
Amma Amurka ta ce ba ta janye takunkumin da ta ƙaƙabawa Assad da muƙarrabansa da kuma ƙungiyar IS.
Hukumomin Kenya sun kama mutum 485 bayan zanga-zangar adawa da gwamnati
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin Kenya sun bayyana cewa sun kama mutum 485 da ake zargi da hannu a zanga-zangar adawa da gwamnati da ta faru makon da ya gabata, wadda ta rikiɗe zuwa tashin hankali a sassa da dama na ƙasar.
A wata ganawa da manema labarai da aka yi a Nairobi, daraktan binciken laifuka, Mohamed Amin, ya ce an kama waɗannan mutane ne saboda tuhumar aikata laifuka daban-daban, ciki har da kisan kai da ta’addanci da fyade da sata da lalata dukiya da kuma kai hari ga jami’an ‘yan sanda.
A cewar shugaban hukumar binciken laifuka, daga cikin waɗanda aka kama,448 sun riga sun shiga gaban kotu, yayin da sauran 37 ke ƙarƙashin bincike.
Zanga-zangar dai an shirya ta ne tun da farko domin tunawa da zagayowar shekara ɗaya tun bayan zanga-zangar nuna adawa da harajin gwamnati da matasa suka jagoranta a shekarar 2023.
Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Dantata
Ga wasu hotuna da ke nuna yadda tawagar gwamnatin Kano da Jigawa suka kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu yana da shekara 94.
A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne shahararren ɗankasuwan ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bayan fama da jinya.
Tuni dai tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina ta isa ƙasar Saudiyya domin halartar jana'izar fitaccen attajirin.
Ana sa ran a yau Talata, bayan sallar La'asar ne za a gudanar da jana'izarsa a masallacin Madina.
Asalin hoton, Khalifa Studio
Asalin hoton, Khalifa Studio
Asalin hoton, Khalifa Studio
Asalin hoton, Khalifa Studio
Asalin hoton, Khalifa Studio
Asalin hoton, Khalifa Studio
Sojojin Najeriya sun ce sun kashe mayaƙan Boko Haram Takwas a jihar Borno
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe aƙalla mayaƙan Boko Haram/ISWAP takwas a wani artabu da ya ɓarke a ƙauyen Manawaji, cikin ƙaramar hukumar Gamboru Ngala da ke jihar Borno.
Rundunar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Litinin, 30 ga Yuni, 2025.
Rundunar sojin Operation Hadin Kai, tare da hadin gwiwar ƙungiyoyin ƴan sintiri na CJTF da dakarun Hybrid Forces ne sun gudanar da wannan nasarar.
A yayin gumurzu mai zafi da suka fafata da mayaƙan, dakarun sun samu nasarar kashe guda takwas daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere da raunuka.
"Bayan kammala fafatawar, sojojimu sun ƙwato bindigogi da dama da harsasai daga hannun mayaƙan da suka mutu da kuma waɗanda suka tsere." In ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa "Babu wanda ya jikkata ko ya mutu daga ɓangaren sojoji, da sauran da aka yi haɗin gwiwa da su."
Hukumomin tsaro sun bayyana cewa an ƙara matsa ƙaimi wajen sintiri da tabbatar da tsaro a yankin Gamboru Ngala da kewaye, domin hana mayar da su mafakar ƴan bindiga.
A halin yanzu, an ce yankin ya dawo daidai, sai dai har yanzu ana cigaba da lura da al’amura domin gudun duk wata barazana.
Ɗaliban kwalejin fasaha ta Ibadan sun yi zanga-zanga kan sauya sunan makarantar
Asalin hoton, SEYIMAKINDE/FACEBOOK
Ɗaliban kwalejin fasaha ta Ibadan sun gudanar da zanga-zanga a fadar gwamnatin Jihar Oyo a ranar Talata, suna nuna rashin amincewa da matakin gwamna Seyi Makinde na sauya sunan makarantar zuwa Omololu Olunloyo Polytechnic, Ibadan.
Ɗaliban, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar ɗalibai (SUG), Olamide Oladipupo, sun ce sunan da makarantar take da shi yana da tarihi da martaba, don haka ya kamata a bar shi yadda yake kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Makinde ya sanar da sauya sunan kwalejin ne a ranar 26 ga Yuni, 2025 yayin jana’izar tsohon gwamnan jihar, Dr. Omololu Olunloyo, wanda shi ne shugaban farko na makarantar kuma ya taɓa zama gwamnan jihar a shekarar 1983.
Sauya sunayen manyan makarantu a Najeriya yana ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce, inda ɗalibai da tsofaffin ɗalibai ke bukatar a soke irin wannan mataki.
Kotu ta dakatar da wa'adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290
Asalin hoton, Getty Images
Kotu da dakatar da wa'adin da Najeriya ta bai wai kamfanin Meta, mallakin Facebook da Instagram da WhatsApp, na biyan tarar dala miliyan 290 bayan da kamfanin ya shigar da ƙorafi a kotu, wanda hakan ya dakatar da wa’adin biyan tarar.
Tun da farko, hukumar sanya ido kan gogayya tsakanin kamfanoni da kuma kare haƙƙin masu sayen kayayyaki (FCCPC) ta sanya wa Meta wa’adin 30 ga Yuni, 2025, domin biyan tarar da aka kakaba masa bayan samun shi da laifin taka dokokin da suka jiɓanci gasa da tallan haja da kuma na bayanan sirri.
Sai dai FCCPC ta tabbatar wa BBC cewa Meta ta ɗaukaka ƙara kan hukunciN a kotun daukaka ƙara.
Kamfanin Meta ya kuma nemi a dakatar da aiwatar da hukuncin har zuwa lokacin da kotu za ta yanke shawara.
A watan Mayu ne kamfanin na Meta mamallakin Facebook ya yi barazanar rufe ayyukansa a Najeriya bisa abin da ya bayyana da tarar da ta wuce hankali.
Wani rahoto ya nuna cewa al'ummar Najeriya ka iya rasa damar ci gaba da hulɗa da shafukan Facebook da Instagram idan dai har kamfanin na Meta ya aiwatar da barazanar da ya yi na rufe ayyukan nasa a ƙasar.
Tsananin zafi ya hallaka mutane a Italiya
Asalin hoton, Getty Images
Mutum biyu ne suka mutu a Italiya sakamakon tsananin zafi da ke ci gaba da ƙara tsanani a sassan Turai.
A wasu sassan Turai kuma, dubban mutane ne suka yi hijira saboda gobarar daji a yammacin Turkiyya, yayin da aka rufe saman Tawer Eiffel a birnin Paris saboda zafin yanayi.
Wasu sassan Spain da Portugal su ma suna fuskantar tsananin zafin yanayi da aka taba samu a watan Yuni, inda aka auna zafin har zuwa digiri 46C a El Granado dake kudu maso yammacin Spain, kwanaki bayan da aka karya tarihin tsananin zafi a Mora, tsakiyar Portugal.
Hukumar yanayi ta Spain, Aemet, ta ce wurare da dama a yankin Iberian Peninsula na fuskantar tsananin zafi da ya haura digiri 43C, amma za a samu sauƙin zafin daga ranar Alhamis.
Tsananin zafi da dare da aka auna daga daren Litinin zuwa Talata ya kai digiri 28C a Seville da 27C a Barcelona.
Dangote ya rage farashin litar man fetur zuwa naira 840
Asalin hoton, X/@AlikoDangote
Matatar man Dangote ta rage farashin litar man fetur daga naira 880 zuwa naira 840 ga dillalan da ke siyan man daga matatarsa, a wani mataki da ya zo gabanin fara rabon man a faɗin ƙasa daga 15 ga watan Agusta.
Shugaban hulɗa da jama’a na matatar, Anthony Chiejina, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa rage farashin ya biyo bayan faɗuwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
A baya-bayan nan, kamfanin man Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin fetur zuwa naira 925 a wasu tashoshinsa a Legas, daga naira 915.
Dangote ya ce sun sayi motoci 4,000 masu amfani da iskar gas (CNG) don sauƙaƙa rabon mai ba tare da cajin ƙarin kuɗin sufuri ba.
Za su raba mai kai tsaye ga masu gidajen mai da masana’antu da kamfanonin sadarwa da sauran manyan masu amfani da mai.
Kamfanin ya kuma sanar da bada bashin sati biyu ga waɗanda ke sayen lita 500,000 na fetur ko man gas na dizil, inda za a ba su ƙarin lita 500,000 a bashi idan sun cimma sharaɗi (banki).
Dangote ya ce wannan mataki ya yi daidai da manufar tattalin arzikin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Sai dai wasu ƙungiyoyin kamar PETROAN da MEMAN sun nuna damuwa, suna cewa wannan tsarin zai iya haifar da ƙarancin aiki a sashen rarraba mai da kuma haɗarin kankane aikin raba man ga kamfani ɗaya
'Dole ne a kawo ƙarshen ƙungiyar agaji ta Amurka da Isra'ila a Gaza'
Asalin hoton, Reuters
Fiye da ƙungiyoyi 130 na jinƙai da sauran ƙungiyoyin fararen hula sun bukaci a gaggauta kawo ƙarshen ƙungiyar agaji ta Gaza (GHF), wani shiri na agaji da Isra’ila da Amurka ke marawa baya, suna mai cewa shirin ya zama barazana ga rayukan fararen hula.
A cewar ƙungiyoyin, fiye da Falasdinawa 500 ne suka mutu tun bayan da ƙugiyar agajin ta fara aiki a ƙarshen watan Mayu, bayan Isra’ila ta ƙulle Gaza na tsawon watanni uku.
Hakazalika, kimanin 4,000 ne suka jikkata yayin da suke ƙoƙarin karɓar agaji.
Ƙungiyoyin da suka haɗa da Oxfam da Save the Children da Amnesty International, da dai sauran su sun zargi dakarun Isra’ila da wasu ‘yan bindiga da buɗe wuta a kai a kai kan mutanen yayin da suka jira karɓan agaji.
Isra’ila ta musanta zargin cewa sojojinta na harbin masu karɓar agaji da gangan, tana mai cewa tsarin ƙungiyar agajin yana bai wa jama’a taimako kai tsaye ba tare da tsoma bakin Hamas ba.
A wata sanarwar haɗin gwiwa da manyan ƙungiyoyin jinƙan suka fitar a ranar Talata, sun bayyana cewa ƙungiyar agajin na karya ƙa’idojin ayyukan jinƙai na duniya, musamman ta hanyar tilasta wa mutane miliyan biyu zama a wuraren da ke cike da cunkoso da sojoji, inda suke fuskantar harbin bindiga a kullum.
Tun bayan da GHF ta fara aiki, rahotanni daga ma’aikatan jinya da shaidu da ma’aikatar lafiya da Hamas ke jagoranta sun nuna cewa kusan kullum ana samun mutanen da ake kashewa a wuraren rabon agaji.
Tsarin rabon agaji na GHF ya maye gurbin tashoshin rabon agaji guda 400 da aka yi amfani da su lokacin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas, da tashoshi guda huɗu da sojoji ke kula da su yanzu – uku a kudu maso yammacin Gaza da ɗaya a tsakiyar gundumar.
Elon Musk ya ƙara zafafa sukar da yake yi wa sabon ƙudirin harajin Trump
Asalin hoton, Reuters
Tsohon mai ba Shugaban Amurka Donald Trump shawara kan inganta ayyukan gwamnatin ƙasar, Elon Musk, ya ƙara zafafa sukar da yake yi wa sabon ƙudirin haraji da kashe kuɗaɗen gwamnati da shugaban ƙasar ya gabatar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan majalisar dattawa ke ci gaba da kada ƙuri’a kan sauye-sauyen da ake son yi wa dokar.
Elon Musk ya yi Allah-wadai da ƙudirin, yana mai cewa babu hankali ko tunani a cikinsa.
Ya kuma yi barazanar kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a matsayin martani kan lamarin.
’Yan jam’iyyar Democrat na ƙoƙarin ganin cewa wannan ƙuri’ar ta kasance mai wahala ga ’yan jam’iyyar Republican da ke goyon bayan ƙudirin.
Shugaba Trump na fatan sanya hannu kan ƙudirin dokar kafin ranar Juma’a mai zuwa.
Sama da mutum miliyan 14 da su iya mutuwa saboda ruguza USAID - Bincike
Asalin hoton, Getty Images
Wani sabon bincike ya yi hasashen cewa sama da mutane masu rauni miliyan 14 a duniya za su iya mutuwa nan da shekara biyar masu zuwa sakamakon ruguza babbar hukumar ba da agaji ta Amurka (USAID).
Binciken da aka wallafa a mujallar lafiya ta Lancet ya ce za a iya kwatanta tasirin rashin tallafi daga hukumar USAID da ɓarkewar annoba ko kuma wani gagarumin yaƙi.
Ya ce hukumar ta hana mutuwar sama da mutane miliyan 90 tsakanin shekarar 2001 zuwa 2021.
An wallafa binciken ne yayin da aka rufe hukumar ta USAID a matsayin hukuma mai zaman kanta, shekara sittin bayan kafa ta.
Assalamu Alaikum
Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Talata.
Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.
Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.